
Post
HIYAAM HAUSA NOVEL PAGE 7
.....he said "We entered three.... "Are you crying? Are you shedding tears?" He said, his voice was shaking and it was breaking his throat because of the fear and violence of today. Their mother is shedding tears, even though she knows that her tears are a punishment for them, especially for Ana who has a dry heart, she will not tolerate it if they are patient while removing you from their destiny. The destiny that God has chosen for them, he wants to see them in it. calmly as if salted fish were thrown, he said, "Are you shedding tears on Daada's words? Don't cry Innti, don't be sad please God" she shook her head slowly trying to stop Jaheed from wiping the tears from her eyes. She held them tightly and said "Ana.... "Did you hear what Ana said? Did you hear what she said about your father?" She took a deep breath and sprayed it on the side of Jadid's face. He quickly lowered his head while calling the name of God. He is trying to take them to the well instead of seeing water, Ana is trying to pass a test on them, what is really difficult especially for In.....
*H I Y Y A M*
Page 7: Abbaa, Save Me
Bright pens Yota/001
Stay blessing as always FALMATA.
Wani irin ɗauke ta da mari Innti ta yi, kafin Ana ta dawo hayyacinta ta sake sauke mata wani lafiyayyen mari a ɓarin dama na ƙuncin kyakkyawar fuskar yarinyar.
A firgice kuma ta ce
"Allah Ya shirya ki Allah kai bani yarinyar ka shirya mini Ayshatuna" ta ɗora "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Salatin Innti ya karaɗe cikin gidan har zuwa maƙota. Jikinta yana wani irin rawa ta sake durƙushewa a wajan ta kasa furta komai saboda yadda laɓɓanta suke rawa a saman bakinta. Da ƙyar ta ɗago kai ta kalli Ana, ta ɗauka za taga fuskar yarinyar cikin damuwa da tsoron kalaman data jefi mahaifin nata dasu, sai taga saɓanin hakan a tattare da ita. Babu tsoron, babu ladama ko guda dake mintsinin zuciyar Ana. Kamar ma ta shirya furta da wasu zantukan da suka fi na baya muni. Sharr hawaye ya sako a idanun Innti. Da rawar ɗari kamar jonin wutar lantarki haka Jaheed ya zame kusa da Innti da rawar murya cike da rauni ya ce
"Mun shiga uku....
"Kuka kike Innti? Hawaye kike fitarwa?" Ya yi furucin muryarsa na rawa tana kakkatse masa a maƙoshi saboda tsananin tsoro da tashin hankalin yau mahafiyarsu ke zubar wa da ƴar data haifa hawaye, duk da ta san hawayenta azaba ne a gare su, musamman ga Ana ɗin da take da busasshiyar zuciya, ba zata jure ba idan sun yi haƙuri wajan kawar da kai daga ƙaddararsu. Ƙaddarar da Ubangiji ya zaɓa musu yake son ganin su a cikinta.
Jadid ma riƙo hannun Inntin ya yi a cikin nasa yana kallon ta, a sanyaye kamar an watsawa kifi gishiri ya ce "hawaye kike zubarwa akan kalaman Daada? Kar ki yi kuka Innti, kar ki yi baƙin ciki don Allah" girgiza kai ta shiga yi a hankali tana ƙoƙarin dakatar da Jaheed daga goge mata hawayen idanunta. Ta riƙe su da ƙarfi ta ce
"Ana....
"Ka ji furucin da Ana ta yi? Ka ji me ta ce akan mahaifinku?" Ta ja numfashi me zafi ta yi feshin shi a gefen fuskar Jadid, da sauri ya yi ƙasa da kan shi yana kiran sunan Allah, hucin numfashinta ya bashi yaƙinin gwargwadon yadda zuciyarta ke ɗaukan ɗumi akan al'amuran Daada. Gashi wata haƙar na neman kai su ga rijiya madadin ganin ruwa, Ana na ƙoƙarin zame musu wata jarrabawa me wahalar gaske musamman ga Innti gama dukkan su gabaɗaya. "Jaheed, Jadid" ta kira sunayensu "Me ya sa ɗabi'un shalele yake da tawaya da naku? Me ya sa komai naku ya yi hannun riga da nata? Bafa ta san kuskure ta yi ba"
"Kuskure?" Ana ta faɗa tana wani irin lumshe manyan idanunta da suke gajiye da al'amuran gidan nasu ga raɗaɗin marin da Innti ta yi mata amma ko gezau ba ta yi ba, daman ita bata taɓa saka ciwon kan Daada a matsayin lalurarta ba, bata taɓa takaici akan abubuwan da yake yi na gurɓata musu suna ba. Da yawan lokaci tana cewa "Matsalolin Daada nasa ne, haka kuma damuwarsa tasa kawai bata Ana ba" yanzu ma take tsaye tana fuskantar Daada wanda ya yi mutuwar tsaye da jin furucin da ko matarsa bai taɓa hasasowa zata jefa masa su ba, balle ɗiyar daya haifa.
A hankali ta saka hannunta guda ɗaya ta ɗora a saitin ƙirjinta, ji take kamar zuciyarta ce take kekketa fatar ƙirjin tana ƙoƙarin ratso ƙirjinta ta fito waje. Bakinta ta ware tana ƙoƙarin cewa wani abu sai ta ji kamar ya tsaya mata, ta haɗe laɓɓanta waje guda ta taune su, taja idanunta ta lumshe su, idanun da shi kan shi Daada suke bashi ciwon kai a rayuwa. Da ƙyar ta iya cewa ta kalli Iftihal wacce take ta sharɓar kuka sosai. Da rashin fahimtar ma'anar kukan
Ana ta ce "Me na ce ne?"
"Tsoro nake ji mahaɗita, tsinewa Daada kikai" cewar Iftihal tana ƙanƙame jikinta. Ana ta juya ta ce
"Shine me? Daadan na farko ne da ba za'a iya tsine masa ba? Babu abin da zai faru sai hukuncin Allah" ta ƙarasa kusa da Iftihal ta ce "Ta ya kike tunanin bakin dake shan giya, jikin dake ɗaukan zunubi da Iskanci dana cin zarafin matarsa da ƴaƴansa don ya tsine mana zai yi tasiri akan mu? Wannan mutumin ko ledar pure water ya tsinewa babu abin da zai same ta, balle mu da muke tare da albarkar Innti" ƙuri Iftihal ta yi wa Ana da idanunta masu rauni da suka cika da tausayin Ana ɗin matuƙa saboda taurin kanta. Murmushi kawai Ana ta yi, tana ƙoƙarin riƙe kanta daga jirin dake ɗaukarta.
Sai ta ɗan daƙune fuska ta ce
"Rabin rai"
"Na'am Rabin rai" Iftihal ta amsa a sanyaye
"Smile for me, ki yi murmushi saboda ni" ta shafi fuskarta
"Kawai ina son ki ne Ana, ina jin kamar ba zan iya rayuwa ba idan babu ke a gefena"
Ana ta ware blue eyeballs ɗinta kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa, ta kafe Iftihal da ido sai kallon ta take yi kamar zata mayar da ita ciki, a hankali kuma take shafa fuskarta ta ɗauki lokaci a haka kafin ta sauke ajjiyar zuciya saboda ƙwarin gwiwar data samu sanda ta fahimci nutsuwa a tattare da Iftihal, wani irin sarawa kanta yake mata gefe guda kamar me shirin tafiya da ganinta ko kai ta lahira. Durƙusawa ta yi daidai inda Innti take zaune cikin sanyin murya da confidence ta ce "Na ɗauka za ki bani tukucin kalamaina ne Innti ta hanyar yi wa cikina alheri da abinci kar na kwana da yunwa. Ciwon kai na ke ji sosai a tattare dani" Innti ta yi mata shiru sai kallon ta kawai take yi kamar bata fahimci me take faɗa ba. A hankali Ana ta ce "Na yafe abincin, ko albarka ki saka mini da addu'ar samun kyakkyawan miji ko Aljani ko maye..," Kyakkyawan marin da Innti ta ɗauke Ana dashi hagu da dama a karo na biyu shine ya hanata ƙarasa faɗar abin da ta yi niyya, ta yi baya tare da yin zama raƙuma ta dafe kuncinta tare da zubawa Innti idanunta masu kaifi da haske.
Cikin zafin nama Innti ta ce "Har kike da kalmomin tara ta dasu bayan kin yi wa mahafinki rashin ɗa'a. Ba haka na ba ki tarbiyya ba, ba abin da na nuna muku kenan ba Aysha. Me ya sa don me ya sa?" Ta kalli Babban yaya da yake jingine da jikin bango yana kallon gefe guda kamar baya tsakar gidan abubuwan da suke faruwa suke wakana ɗin. "Ko dai ina da tawaya wajan gina tarbiyyar Aysha ne Yaya?"
"Me ya sa kamar bakya so na ne Innti?" Ta faɗa da rawar murya
Bata farfaɗo ba wasu kalaman na Ana suka sake cakar zuciyar Innti da yi mata wani irin rauni me zurfi. Da rawar murya Ana ta ce "Naga kamar bakya so na ne, a tunanina abin ƙwarai na yi ai, abin azo a yaba. Taya kike tunanin zan jure ganin ana cin mutuncinki da na dinga ganin haka gwara na bar muku duniya, gwara na bar wa mijin naki duniyar"
"Kept quiet Aysha!"
"Ki bari na faɗa Innti,naga kamar kin fi son mijin naki akan yaran naki, naga kamar ya fimu muhimmaci a rayuwarki. Ko babu komai muna saka ki farinciki, muna sawa ki yi alfahari damu, muna sawa ki ji mu yaranki ne da suka fito faga cikinki" ta juya ta kalli Daada da yake tamboɗe ta nuna shi da yatsa ta ce "Shi ɗin wanne hakƙi naki ya sauke, mene abu ɗaya da ya yi miki wanda kike jin ya cancanci amsa sunan miji da uba?" Innti ta juya ta kalli yaran nata gabaɗayansu ta ce
"Ta ce wai na bata amsa?"
Duk suka zubawa Innti ido ban da Ana. "Me ya sa ba zan so wanda ta silarsa na samu alarbarkatattun yara irinku ba?" Wani irin murmushin takaici Ana ta yi tana sake watsa idanunta akan Innti kafin ta girgizar kai ta yi baya tana ƙoƙarin zubewa a wajan saboda ciwon da kanta ke yi mata. "Uhm... Uhm haka ne"
Sai ta ce "Mashayi, ɗan giya, me fifita karuwarsa akan ki, me aibata yaranki, me yi mana fatan mu farraƙa, ɗan caca irin shi kike so, kike ƙauna har haka a ranki?"
"Innalillahi! Aysha;....
"Ki so mijinki Innti, ni kinga ubana nan" Ta nuna Babban yaya dake tsaye ya rungume hannunsa a ƙirji idanunsa sun yi jajur ilahirin jijiyoyin kan shi sun fito sosai a saman goshinsa dukkan wata gargasa da Ubangiji Ya halitta a jikin Babban yaya sai data mimmiƙe daga fatar jikinsa, ya dunƙule hannayensa hagu da dama har wata power ta tashi a damtsen hannunsa buɗaɗɗan jikinsa me ɗauke da gaɓoɓi suka gama bayyana. Wani abu ya tsarga masa lokacin da Ana ta kira shi da sunan uba, mahaifi wani irin responsibility ta ɗora masa na kulawa da ita, bai mata alƙawari ba, amma yana da tabbacin zai amsa mata, zai bata dukkan wata kulawa da uba yake bawa ƴarsa. Ji ya yi zuciyarsa tana rarrabewa wani abu yana shiga cikinta.
"Daga yau Babban yaya shine Abbaana, shine ubana, da sunansa zan dinga amfani har abada idan ya zama dole na yi amfani da sunan namiji a jikin sunana kenan"
Sai a lokacin ta ji kamar numfashinta na season a ƙirjinta yana kakkatse mata. "Ki so mijinki Innti, ina fatan soyayyar da kike masa ba zata ja rauninki zuwa ga tsine mana ba kamar yadda mijinki ya yi....," a hankali ta ce "You're my world Innti"
Buɗe baki Innti ta yi zata hau kan Ana da faɗa sai ta yi saurin sauya harshe daga faɗan zuwa addu'a a zuciyarta ta shiga yi;
"اللَّهُمَّ اهْدِ قَلْبَهُ، وَأَصْلِحْ حَالَهُ، وَاجْعَلْهُ مِنَ الْبَارِّينَ بِي، وَاغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ. Ma'ana. (Ya Allah ka shiryar da zuciyarta, ka gyara halinta, ka sanya ta cikin masu biyayya gare ni, ka gafarta mata ka yi mata rahama).
Juyawa Ana ta yi itama da niyyar barin wajan. Sai ta yanke jiki ta faɗi a wajan. Yunwar da ta ci ƙarfinta da ciwon da gefen kanta ke yi mata ne ya haddasa mata hakan. Kafin ta miƙe zaune Daada ya saka ƙafa ya taka mata ruwan cikinta, tsananin zafi da azaba sai gani sukai fitsari yana bin ƙafafuwanta a hankali ta zubawa Daada ido, kallon da yake nuna tsoro da mamakin kiran shi da Uba. Kafin numfashinta ya ɗauke ta miƙa hannunta da ƙyar zuwa ga Babban yaya ta ce "Zan mutu Abbaa ka ɗauke ni"
"Cikina Abbaa....
Bata iya ƙarasa faɗa ba saboda wani duka da Daada ya kai ruwan cikin Ana a karo na biyu daidai lokacin da numfashinta ya tsaya. Da wani irin fitar hayyaci Babban yaya ya saka haƙora wajan datse harshensa jikinsa na tsuma da kakkarwa ya yi kan Daada ya saka hannunsa guda ɗaya ya damƙo wuyan Daada ya ɗage shi sama, ƙafafuwan Daada suka fara lilo a ƙasa, wata sabuwar kururuwa Innti ta yi saboda abin da bata taɓa zato bane ya faru. "Yaya mene haka, ubanka ne mahaifi ka sake shi, muddin nina ɗauki cikinka wata tara, na shayar da kai nono wallahi idan baka sake shi ba ban yafe maka ba, ya zama na ƙarshe a rayuwa da za ka yi tunanin taɓa jikin mahaifinka"
Babban yaya bai ko kalli Innti ba jikinsa kamar an jona masa wutar lantarki haka yake tsuma, ya manne Daada da jikin bango wanda ya fara hango kabari kafin ya yi cilli dashi zuwa gefe guda.
A gigice kuma cikin wani slow ya yi kan Ana da yana durƙushewa akan ƙafafuwansa ya yi zaman raƙuma ƙoƙarin magana yake yi ya kasa sai laɓɓansa da suke rawa da wani sounds dake fita ta cikin gurnaninsa. Rabon da su ji sautin muryarsa ta fita har haka sun mata, yadda yake ƙoƙarin kiran sunan Ana kamar yadda ya sama idan yaso ya saka Innti saurin yin baya tana dafe ƙirjinta. Tashin hankali da tunanin Iftihal zata rasa Ana ya kasa ɗaukan zuciyarta ta yanke jiki ta faɗi cikin sauri Jaheed ya taro ta jikinsa yana kiranta.
Kakkar haka laɓɓansa da harshensa suke masa rawa ya zubawa fuskar Ana ido a cikin saman kan shi ya ji ya kira sunanta da ƙarfin gaske.
"Shettyyy...
Da wani irin slow Babban yaya ya rungumota jikinsa gabaɗaya yana bubbuga fuskarta yadda Jaheed ya wanzu yana kiran sunan Iftihal. "Jini... Jini a jikin Ana"
Jadid ya ce a firgice shima zuciyarsa na ƙoƙarin tsayawa da aiki jikinsa na wani irin rawa da kakkarwa idanunsa na ƙaƙƙafewa.
"Na rasa yarana na rasa aminai na" Gabaɗaya neman ficewa daga hayyacinta Innti take shirin yi saboda tashin hankali. Tsam kuma Babban yaya ya rungume Ana a jikinsa, gashi jikin nasa sanyi sosai kamar na maciji idanunsa suka rikiɗe tare da yin blue sosai wani haske na fita daga cikinsu sai girgiza kai yake yi. Ya rasa abin yi a nutse ya saka tafukan hannunsa wajan riƙo fuskarta yaga babu alamar numfashi a tattare da ita babu alamar tana jin shi, babu alamar akwai rai a jikinta. Da wani irin rawar jiki data zuciya ya manna bakinsa a goshinta ya sumbace ta.
Daidai lokacin Haysaam dake ta sallama ba'a amsa masa ba ya faɗo cikin gidan, Jallabiya ce a jikinsa ash wacce tabi farar fatarsa jikinsa ta kwanta bai iya tsayawa tambayar mene ya same ta ba ya kalli Jaheed ya ce "Jeka ka tashi Mas'ud ya ɗakko napep ɗinsa yanzu" yana faɗin hakan ya sunkuya ya sunkuci Ana a jikinsa ya yi waje da ita. Daidai nan Iftihal ta farka tana fasa wani irin gigitaccen ihu da kiran sunan Ana. Daada da yake numfashi da ƙyar yana riƙe wuyansa da yake jin kamar ya kumbura ya yi baya yana faɗin "Allah Ya sa ta mutu na huta, daman sun yi mini yawa ai ba zata taɓa albarka ba, Innti duka yaranki ba za su taɓa yin albarka ba, tsinannu ne" Babban yaya ne ya miƙe yana tattare hannunsa ya nufi hanyar ficewa daga cikin gidan. “MURAAD” cak ya tsaya bai juya ba saboda baya son taga sauyin da ya yi
"Muraad ka dawo mini da Shalele da ƙafafuwanta, Muraad ka dawo da ƴarka"
"Itama ta bashi Shetty kenan? Ta yarda shine uba kuma mahaifin Anarta?"
Ya yi jim.
"Muraad"
"In sha Allah" ya ce a taƙaice a karo na biyu bayan kiran sunan Ana da ya yi. Yana faɗin hakan ya saka kai ya fice yana ɗan ranƙwafar da kan shi abinka da dogo
Yana fita ya tarar har an fito da Napep ɗin, Mas'ud ba zai iya kai su ba, don haka Yaa Sam ne ya shiga gaba Babban yaya ya zauna a baya rungume da Ana suka tafi asibiti mafi kusa. Jaheed ya koma gida. Emergency aka amshi Ana babu ko biyar a hannun Babban yaya, kuɗin da Haysaam ya tanada domin tafiya Lagos dasu a gobe sune ya fito dasu ya bayar aka siyo kayan aiki dasu, suka jira a reception su kuma.
***
KANO/ MAITAMA SULE GRA BAFFAS ESTATE. An sanya sunan unguwar MAITAMA SULE ne domin girmama fitaccen ɗan siyasar Kano, Yusuf Maitama Sule wanda aka fi sani da Dan Masanin Kano. Ya kasance babban ɗan siyasa, jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma mutum mai daraja a tarihin ƙasar. Saboda irin gudummawar da ya bayar, aka sanya masa wannan yanki mai daraja. Maitama Sule GRA yana cikin sabbin yankunan birnin Kano. Yana kusa da manyan hanyoyi da wuraren gwamnati Tsarinsa na “GRA” (Government Reserved Area) yana nufin an tsara shi ne musamman domin manyan mutane da attajirai tare da masu faɗa a ji na faɗin Jihar Kano. Gidajen MAITAMA SULE GRA mafi yawansu manyan mansions masu tsada ne wanda aka yi su da arziƙi bada kuɗi ba. Duplex da gidajen zamani Filayen suna da girma sosai (ba kamar tsofaffin unguwanni ba) Yawancin gidaje suna da: CCTV tsaro na sirri,lambuna (gardens) a matsayin arziƙi ana ɗaukanta matsayin unguwar masu kuɗi sosai (elite area) Mazauna sun haɗa da: ƴan kasuwa masu arziƙi ƴan siyasa manyan ma’aikatan gwamnati. Farashin gida ko haya a nan ya fi yawancin unguwanni tsada.
A cikin jerin estate dake Maitama sule Baffas Estate daban yake, gida ne da aka yanki gininsa na musamman tsarinsa komai ya bambanta da sauran, an yi masa ado da zane irin na gidan sarauta wanda bai san asalin BAFFA ba, zai ɗauka iyalinsa da shi kan shi jinin sarauta ne madadin sanin da aka yi masa na kasancewarsa Babban Malamin Addinin Musulunci dashi da zuri'arsa. Mabiyin Izala (Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa lqamatis sunna) Ta dalilin SHEIKH HAFIZZ HAFIZZ BAFFA jama'ar da suka koma ɓangaren Izala suna da matuƙar yawan gaske al'amarin daya kawo ruɗu da ceceku ce tsakanin bambanta Addinai al'amarin daya yi ƙamari kenan yaja hankalin mabiya Shi'a (Shi'a Islam) a wani wa'azi da ya yi ya ya taɓo su, ya yi musu caccakar da taɓa har ƙasar Iran. Sheikh Hafizz Hafizz Baffa bai yi zaton girman abin ya kai har haka ba. Sai da aka wayi gari an kashe Sheikh Hafizz Hafizz Baffa, kisan da ba'a san su waye ba, tun daga lokacin har kawo yanzu, an kashe shi tare da babbar ƴarsa a kan hanyarsu ta zuwa Qatar. Sai jaririnta guda biyu ne suka tsira, wanda a ranar ne kuma ta haife su ba tare data san me ta haifa ba, aka yi mata yankan ragu aka ƙune Sheikh Hafizz Hafizz Baffa. Wannan jinin dake jikin Diyanah, jini ne da har abada ba zai taɓa fita daga zuƙatan BAFFAS FAMILY ba. Wannan jinin shine abu na farko da yake cin zuciyar mutumin da bai taɓa buɗe baki ya yi kukan rashin DIYANAH HAFIZZ HAFIZZ BAFFA ba.
Ba tsoran jinin yake ba, domin ya yi imani da Ubangijin Al'arshi kowanne rai zai ɗanɗani ɗacin dake cikin zare rai daga gangar jiki, ya yi imani da Allah da kuma ƙaddarar dake zane a rayuwar kowanne bawa. Baya tsoron dukkan abin da zai faru dashi muddin Ubangiji ne ya ƙaddaro masa.
"Wani rai ba zai sake salwanta ba ta dalilin Baffas Family, zai raini jinin DIYANAH HAFIZZ HAFIZZ BAFFA da soyayya da kulawa, zai ƙarar da rayuwarsa, shekarunsa wajan ingata jinin Diyanah Hafizz Hafizz" Ya ɗora da "Zai danne feelings da emotions ya manta cewa shi namiji ne, ya manta daɗin daya taɓa ji sau ɗaya a rayuwarsa" Shine abin da zuciya take faɗa masa a koyaushe. Daman zuri'ar daya samu da Diyanah Hafizz Hafizz Hafizz Baffa unexpected ne, ba zai iya tuna yadda ma komai ɗin ya kasance ba, shuɗewar shekara goma sha Bakwai kenan cif, a cikin shekarun 17 ɗin zai ware kwana ɗaya kawai, a wannan daren juma'ar ya kasance da Diyanah Baffa, kyakkywar yarinya fara tas kamar ita ta zaɓi yadda kyawunta zai kasance, ko a cikin daren ita ce wacce taja ra'ayinsa ita ce wacce komai nata ya yi tasiri a jikinsa ba'a zuciyarsa ba, daga wannan daren kuma sai komai ya lalace ya rasa kan shi a matsayin ɗa namiji ta dalilin hatsarin motar daya samu wanda yaja aka yi masa aiki a mararsa. Sai ya zama dashi da mace basu da bambanci sai na suna da suffa. Daga ranar ne kuma SAYYADI BAFFA ya fara kallon kowacce mace a suffar Garzali.
A hankali take sakkowa daga steps ɗin benen fuskarta ɗauke da yalwar murmushi tana sanye da atamfa ruwan ƙasa me zanen ɗawisu ta ɗora Jalbab a saman a atamfar wanda ya saukar mata har ƙasa hannunta ɗaya riƙe da counter tana tafe idanunta na kallon direction ɗaya tana sake faɗaɗa murmushinta wanda yafi maganarta yawa a koyaushe a haka har ta kammala sakkowa daga saman benen tana nufar kujera me cin mutum biyu ta zauna bakinta ɗauke da Bisimillah. "Barka da sakkowa Hajiya Umaimah" juyawa ta yi a nutse ta kalle shi, kamar ba zata ce komai ba sai ta jinjina kai
"Kana ta jira a downstairs Alhaji Sadi?" Ta ce a tausashe tana mai gyara zaman nata sosai. Ya jinjina kai yana murmushi ya ce
"Bai zama damuwa ba zaman ai Hajiya Umaimah nasan uzuri ne ya zaunar dake a can saman, ni abin kari ma nake jira a nan" ɗan ɗaga kai ta yi sai taga gabaɗaya 11:12 na safiya ta sake yin murmushi can ya ce "Gidan shiru yau ɗin" A nutse ta sake cewa
"Nadiyah Baffa ce babu lafiya"
Alhaji Sadi ya buɗe idanunsa cike da damuwa da tsoron jin abin da ya samu Nadiyah ɗin, dukkan wata damuwar da zata sake bawa Baffa damar shiga ƙunci baya son ta, yana jin kai tsaya damuwar Sayyadi Baffa ne na sauka a zuciyarsa tana haifar masa da rashin kuzari da walwala. Ya dubi Hajiya Umaimah a nutse ya ce "Nadiyah fa?"
"Nadiyah Sayyadi Baffa" ta bashi amsa. "Ikon Allah, mene ya same ta har haka? Ban taɓa jin ta yi lalura har ta kwanta ba, dama dai Diyanah ce wannan tana da laulayi" baya Hajiya Umaimah ta yi tana ɗauke kanta zuwa gefe kamar bata ji me yake cewa ba, a hankali ta ce "Ya za'ayi da lamarin Ubangiji Alhaji Sadi? Ciwo ai waraka ce" shima ɗin jinjina kai kawai ya yi ya ce
"Mun je nema wa Liman aure kamar yadda ya buƙata, to my surprise basu bamu matsala ba iyayen yarinyar akwai karamci sosai da alama"
"Allah Ya sa ba ƴar ƙananun mutane Liman ya ɗakko mana ba" yadda ta yi maganar tana neman wajan zama kai tsaye ya bawa Alhaji Sadi mamaki ya juya ya kalle ta na wani lokaci sai bai ce komai ba, ya mayar da idanunsa kan Umaimah ya ce "Sun amshi kuɗin, an kuma saka rana nan da watanni biyar masu zuwa"
"Allah Ya nuna mana, ya sa abokiyar zama ce" Hajiya Umaimah ta furta a sanyaye tana lumshe idanunta, bawai haka tasu ba, ba kuma hakan ta buƙata ba, yaronta namiji guda ɗaya tal a duniya ta yi masa buri da kwaɗayin auren ƴa gidan manyan mutane, wacce ubanta yake wani a garin nan a Jihar ko a ƙasar bakiɗaya. Sai gashi ya ɗakko wacce tsabar takaici bata iya tsayawa ta tambayi wacece ita ba, balle ta san ƴar wacece. "Ina so a yi mini iso wajan Baffa"
"Baffa...." Umaimah ta maimaita
"Sayyadi Baffa kake nufi?"
Cikin sauri matashiyar yarinyar dake zaune taja idanunta ta lumshe su, ji ta yi duk wani raɗaɗin zuciyarta ya kau, nauyin da ƙirjinta yake mata ta ragu wani sanyi da nutsuwa na saukar mata a jikinta ta dalilin kiran sunan Sayyadi Baffa da aka yi. Ta ɗauke kai gefe guda tana murmushi duk sun lura da hakan suka share. Alhaji Sadi ya ce "Ina son ganawa dashi ne" da mamaki Umaimah ta dube shi kafin ta ce "Babu shi aka je neman auren na Liman daman Alhaji Sadi?"
"E, daga ni sai Sheikh Nurain da Malami da Alhaji Huzaifa Abdallah muka je tafiyar ai"
"Na ɗauka girma da ƙimar Baffa suka duba wajan amincewa da batun auren Liman? Ashe dai kawai.....," cikin sauri ya dakatar da Hajiya Umaimah da faɗin "Mu bamu wadatar mu nema wa Liman aure ba sai dole akwai Baffa a ciki tafiyar? Ko mu ƙima da mutuncin ne bamu dashi? Sayyadi Baffa ɗa ne kawai a wajan Sheikh Hafiz Hafiz Baffa, mu kuma ƙannnen Sheikh Hafizz ne idan kika ɗauke Alhaji Huzaifa da yake yayanki, kenan duk wata martaba da kike tunanin Sayyadi Baffa na da ita sai data fara shafar mu kafin ta ruski inda Sayyadi Baffa yake"
Hajiya Umaimah kallon shi kawai take yi ganin yadda ya juya mata manufarta a fili.
"Alhaji Sadi ko dai kana son faɗa..," ya katse da faɗin
"Babu abin da zan faɗa miki Hajiya Umaimah wanda ya shige ce miki an bawa ɗanki Liman auren yarinyar da yake so"
Ta jinjina kai da girmamawa ta ce
"Na gode"
Alhaji Sadi ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin barin haɗaɗɗan parlourn ƙasan da ya gama gajiya da haɗuwa wanda shine main parlour na kowa da kowa. "Barka da Safiya uncle" kamilalliyar muryarsa ta riga shi zuwa
"Yawwa Mu'allim kana gida ashe?" Hannunsa ɗaya cikin aljihun wandon shaddar jikinsa sai ƙamshi yake da nutsuwa da kulawa ya ce
"Ina hutawa ne"
"Ga Liman nan ya tura maka Buzu" Uncle ya faɗa da sigar zolaya a fuskarsa
Mu'allim yaja idanunsa ya lumshe bayan ya zauna a kujera ya rungume hannunsa a ƙirji bai fahimci maganar Alhaji Sadi ba a gajarce ya ce "Buzu kuma Uncle?" Uncle Sadi ya ce "E, kuɗin aure muka kai masa yau ɗin nan, nan da wata Biyar za'ayi auren Liman fa" Mu'allim ya jinjina kai yana ciro wayarsa a cikin Aljihu a tausashe ya furta "Ahky yana da budurwa daman har ake maganar Nikkah?" Uncle Sadi ya buɗe hannayensa wajan faɗin "Yanzu da ta yi wari ba gashi kowa ya ji ba? Sai fatan Allah Ya sa Albarka"
"Sayyadi Baffa yana sashensa ne?"
"Ya je Da'awa"
Mu'allim ya bashi amsa.
"Wanne gari? Wacce ƙasar?"
Gabaɗaya suka juya a tare suna kallon Azizah wacce tun ɗazo laɓɓanta suke rawar tambayar son sanin inda Sayyadi Baffa ɗin yake, gida ɗaya suke rayuwa dashi, amma ta kusa wata ko fi bata sanya shi a idanunta ba, ko motsinsa bata ji. Babu ma wanda yake jin motsin Baffa ɗin daga Nadiyah sai Diyanah sai kuma Mu'allim Hafiz Baffa ɗin. Makomar baikonsa da yake kanta take son sani sama da shekaru Biyar amma babu wani cikakken lamarin da zai iya bata tabbacin zata zama mata a wajan shi, zata zama uwar da zata cigaba da kulawa da rayuwar yaransa Nadiyah Sayyadi Baffa da Diyanah Sayyadi Baffa, tana son ta maye gurbin murgayiya matarsa Diyanah Hafizz Hafizz Baffa, wacce a tunaninta rashin Diyanah ɗin a rayuwarsa shine ya hana shi aure. Damuwarta ɗaya ce, yana son ta? Yana jinta a ran shi kamar yadda itama take jin idan yaƙi aurenta za ta yi silar ɗaukan rayuwar duk wacce zai aura a matsayin mata. Ko kuma yana jin kamar ya tsufa ya girma da auren ne saboda tagwayen yaransa da suka zama Ƴan'mata? Ta sani Dattijo ne shi, amma irin su ne ake kira da Suger Daddy. Babbar hujjar dake sawa Azizah ta ji ta karaya da komai yadda tunda take zaune a gidan sama shekaru biyar bata taɓa ganin kamannin Sayyadi Baffa na, hatta ƙwayar idanunsa kodayaushe suna cikin glasses ne, ko a photo babu kamarsa, duka gidajen t.v da suke ɗora Wa'azinsa live ko recording babu kamanninsa.
"Na shiga uku"
"Maganin shiga uku Allah" Hajiya Umaimah ta bata amsa tana watsa mata harara ta gefen ido. Mu'allim ya ce "Wajan Nadiyaah da Diyanah kawai zaka san inda Baffa ya je uncle"
"Bari na je wajan nasu daman zan duba jikin Nadiyah Sayyadi Baffa, sai na ji bayani a can" Mu'allim ya miƙe yana nufar sashin mahafiyarsa ya ce "Laba'sa Uncle" daga nan Uncle ɓangaren yaran Sayyadi Baffa ya nufa
*** Da ƙyar ta samu shigowa Bright Fm ɗin yau idanunta a kumbure saboda kukan da ta yi a dalilin cire sunanta da aka yi aka saka na Yussy, gashi labarin ya hau iska sai positng ake yi a social media bayan Yussy ta ƙirƙiri photon Malam Sani da Maryama da Talatuwa sai jaririn a Ai. Mutane nata sharing suna jinjina mata wasu a dalilin hakan suke following page ɗinta. Ahlam ta yi kuka ta ji raɗaɗi da ƙuncin zuciya sai da ta yi kamar ta ajjiye aikin. Da ƙyar Engineer ya saka ta a gaba kamar yarinyar goye yana lallashinta kafin ta haƙura ta janye.
Program ne da ita amma bata da nutsuwar yi, dole Anees ya karɓeta ta hanyar amsa tambayoyin masu saurare da sanya musu waƙoƙin nishaɗi, mutane da yawa Golden voice kawai suke tambayarsa sun fi jin daɗin muryarta a program ɗin.
Bisa dole ta amsa.
"Mita 116 kuke sauraro, Bright Fm Redio mitar zamani tashar zamani...,"
Sai ta numfasa "Me sauraro barka da rana, barka da wayewar garin yau. Golden voice ɗinku ke tare daku a daidai wannan lokacin, kuma zan cigaba da kasance daku har zuwa lokacin da abokiyar aikina zata amshe ni..."
Nan ma ta sake yin shiru, Anees ya zuba mata idanu yana murmushi.
"Ehmn. Ko ina kake, ko zaka, ko me kake yi ka tabbata ka kasance da Golden voice domin mu yi nishaɗi tare, mu ilimantu a tare. Kiran farko dawa muke tare?"
Daidai lokacin da Ahlam ke yin program ɗin Anees ya saka a live mutane sai ganin kyakkyawar fuskarta suke. Daga gefe guda shima wayarsa me ƙirar Tap tana hannunsa a hankali ya numfasa kaɗan kafin ya juya ya kalli na kusa dashi ya ce
"Wacece ita?"
"Ahlam Abdallah Kurmi sunanta tana aiki a Bright Fm Rd"
Ya ɗan yi jim can ya ce "Ina son ganinta, a nemo mini ita immediately"
"Yes sir"
***
1976. TIVLAND.
Da ƙyar Dooshima ya danne zuciyarsa saboda sosai kukan Anum ɗinsa wacce yake so fiye da kowa da komai a duniyar yake hargitsa masa lissafi, idan ka cire Anum Jarumi shine abi mafi soyowa a zuciyar Dooshima idan yana buƙatar kasancewar su a raye dole ne ya ɓoye su kamar yadda aka saba wannan gudun tsira da ran a duk sanda Sojoji sukai musu wannan zuwan na bazata. Ya saka hannunsa ya share zufar dake bin fuskata yana kokarin mayar da hawayen idanunsa. Yana zuwa ya tarar Kaka baya harabar wajan sai ya nufi ƙofar gidan da suka ɗan zagaye. A ƙofar ya tarar da ɗan'uwansa Haan hannunsa riƙe da kibbau, daga can ɓangaren ya hangi iyalan Imande.
Ikur da Imande family ɗaya ne, kaka ɗaya ne ya haifi iyayensu. Kamar yadda Kaka ya haifi Dooshima da Haan haka a ɓangaren Imande mahaifinsu ya haifi Terhemba da Uji, da Kaka da Ityo uba ɗaya ne ya haife su, duk da sun fito daga ciki guda amma kowa yaja iyalinsa ya raɗawa iyalin sunan da suke ganin ya dace dasu. Akwai bambanci hali da ɗabi'a a bayyane, Imande sun kasance masu son zuciya da zafin rai, suna da mugata tare da ƙetar dasu kan su basu san adadinta ba.
Wannan dalilin ya saka suke da burin ganin duk abin da zai zo na samu da ci-gaba ya fito daga ɓangaren Imande kawai banda iyalan Ikur. Wajan ya ɗauki shiru sai kaka ne ya dubi Sojojin da fahimta da nutsuwa ya ce
"Kuna ganin tsoron da kuke ƙoƙarin sakawa zuƙatanmu zai saka ku samu abin da kuke so ne? Mun rasa rayuka masu yawa saboda ku, ku bari mu yi rayuwa yadda muke so"
Wani soja ya ce "Naga kamar kana da fahimta Dattijo, ƙarasu nan mu yi magana"
"A'a Kaka kar ka ƙarasa"
Kaka ya juya ya kalli Dooshima sai ya yi murmushi me kamala ya ce "Na yi imani da Aondo, babu abin da zai faru Dooshima"
Haan ne ya ce "Kaka suna ƙoƙarin kawo mana sauyi ta hanyar hana mu amfani da Addinin gargajiya ((Traditional beliefs)"
Kaka ya ce "Haan!"
"A gafarce ni Kaka, Aondo ya bayyanar mana da UWA MAMAA mu huta"
Sojan ya ce "Ba cutar daku za mu yi ba, sauyi za mu kawo muku wanda zai taimaki rayuwarku, a cikin jeji kuke rayuwa babu ilimi, baku da addini guda ɗaya da za ki ce shine kuke bi, ina so ku amshi addinin Yesu Almasih, a kafa muku gari a sanya masa suna, a gina muku makarantu, da kasuwanni na ƙawa da jin daɗin rayuwa, a baku dama na shigowa sabgar siyasa a ware muku yanki guda tare da wakilcin mutum ɗaya da zai jagorancin dukkan ƙabilar Tiv"
Uji daga ɓangaren Imande ya ce "Mutum ɗaya da zai mulki jama'ar Tiv? Kenan bamu da ikon yin abin da muke so sai bisa sahalewarsa? Ka bamu hujjar da zamu yadda" babu wasa a fuskar Sojan ya ce "A shekarar 1976, Najeriya tana ƙarƙashin mulkin soja, bayan kisan shugaban ƙasa Murtala Mohammed. Wannan ya kawo sauye-sauye da dama, ciki har da: Ƙirƙirar sabbin jihohi Inganta tsarin mulki da gudanarwa rasirin gwamnati ya ƙara shiga cikin yankunan karkara, ciki har da Tivland, har daku ƙabilar Tiv ɗin"
"Bamu yarda ba, bamu amince ba"
Dooshima ya yi furucin saboda wasu kuskure daya hango. Akwai soyayya mai girman gaske tsakanin Imande da Ikur family. Sai Uji ya ce yana buƙatar magana da shugaban sojojin, suka je gefe guda tare da yin magana. Bayan sun kammala sojan ya kalli Dooshima ya ce "Ina son na nuna maka komai a bayyane na tsarin da muke son kawo muku ka biyuni mu je" Dooshima ya juya ya kalli Kaka da Haan. Dooshima ya ce "Zan je, ka kula mini da Anum kafin na dawo, ka riƙe ta ita da Jarumi a wajanka ɗan'uwa Haan" Haan ya ce "Aondo na tare da kai" Dooshima motar sojojin ya shiga ta “trucks, jeep” wacce suka zo da ita saboda hanyoyi basu da kyau akwai “dirt roads”
Suna tafiya Terhemba ya kalli ɗan'uwan nasa da suke uwa ɗaya uba ɗaya Uji ya ce
"Kamar kun ce wani abu da sojojin nan ko?"
Uji ya ce "Ka yi tunani Terhemba, idan za'a sake fitar da mulki a Tiv Imande sune mafi cancanta, muna buƙatar hakan idan Dooshima yana nan, ba zai bari mu samu cigaban zamani ne, na yi abin da ya kamata"
"Me ka yi?" Terhemba ya tambaya da tsoro.
Sai Uji ya buɗe hannunsa ya ce "Na siyar da Dooshima, na siyarwa da sojoji shi matsayin Bawa" daidai nan wata iska ta karaɗe wajan da wani ihu da gurnani mara daɗin ji, iskar na lafawa suka fara ganin mutane na faɗuwa ƙasa matattu fiye da mutane 20.
A tsoron Kaka ya ce "An sake yin abin kuskure wannan bala'in ba zai lafa ba zai UWA MAMAA ta bayyana" ya juya da sauri ganin gidansu na rushewa yana shigewa ciki. "Anum Jarumi, suna ciki" Haan ya faɗa a gigice yana nufar ciki da sauri Kaka ya riƙe shi ya ce "Sai haƙuri amma mun rasa su"
***A hankali take juya kanta da ya yi mata nauyi tana fuskar numfashi da ƙyar ƙoƙarin tashi take yi amma kamar an saka dutse an danne ta haka take ji, kamar me shayar da yaro haka take ji ana sha mata Nono wata zufa ta wanke mata jikinta, ilahirin jikinta ciwo suke mata gabar an saka abu an mata dukan tsiya ga wani irin sanyi da gaɓɓanta sukai mata. Duk yadda take ƙoƙarin buɗe ido da dakatar da abin da yake faruwa da ita ta kasa, ji ta yi ba zata iya tashi ba, an danne ta sosai ta kowanne ɓangare a jikin nata.
"Ayshatu" ya kira sunanta yana kunna hasken ɗakin asibitin da take ƙwance. Sai ya yi turus ganin zanin jikinta a bankaɗe sai motsi take amma ta kasa buɗe idanunta.
Babban yaya ya koma gida balle ya kira shi shine muharraminta sannu a hankali ya fara takawa zuwa inda take ya ranƙwafa kaɗan ya ce "Nanaah" a hankali ta buɗe idanunta ta sauke ganinta akan Haysaam ɗin.
Luu taja idanun ta lumshe su. Hannunsa ya saka me taushi a saman goshinta ya share mata zufar wajan ya gyara mata zanin jikinta ita kuma ta tsora masa ido, kamar me son gano wani abu a fuskarsa sai ya ɗan kashe mata ido yana ja baya saboda har zuciyarsa kallon ta ke saukar masa da wani irin yanayi. A hankali ya ji ta ce "Yaa Sam"
"Na'am, menene ina ke miki ciwo?" Ta girgiza kai sai kuma ta nuna masa tsakiyar ƙirjinta ta ce "Ina Anum da Jarumi? Ina aka kai Dooshima Abban Anum?" Ganin ya yi shiru ta sake kallon shi ta ce
"Da gaske Anum ta rasu ne....
Haysaam ya yi jim ya ce "Su waye haka?"
Sai ta yi masa shiru tana tuna abin da ta ji bayan mafarkin da ta yi, a cikin mafarki Babban yaya ne ta gani yana sha mata ƙirji...
Ga duk me buƙatar ƙarin bayani akan littafin nan ya yi magana ta waɗannan numbobin a WhatsApp.
08082101373 08164069385 Akwai page 8 zuwa 12 duk a ArewaPen ku yi searching HIYAAM za ku ga free chapters ɗin. Ta application ko Website..
Today's HIYAAM sponsor is Annoor Foods your trusted choice for healthy and delicious food. Kamfanin da suke haɗa garin ɗan wake, garin funkasu, garin kunun Aya, Zobo mix yaji dakan hannu. Duk garin da mutum yake zai biya Rabin kuɗin delivery ne mu mu biya rabi. Kayan ANNOOR FOODS, ingantattu ne masu kyau da tsafta. Ku tuntuɓi wannan number. 09075181211
*HIYAAM dama ce ga masu Business da za su yi sponsoring mu kuma mu tallata musu kayansu har zuwa facebook. Ga duk me buƙata ya yi magana a wannan number 08164069385*