
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 17
.....yeah." Farida said, "Hajiya, go and prepare now, I will fix the kitchen." "You are tired," said Zahra, "No, by the way." Zahra smiled and then she turned and went upstairs. When she entered her room, she found Ibrahim sitting by the bed and checking his phone. He raised his head and they locked eyes, he just stopped looking at her. "What?" Zahra said smiling a little. "You are more beautiful than my eyes" she laughed while removing her hijab. "Leave Noory." He stood up and ended up next to her. "Is the cooking done?" "Yes." "Hmm... Zahra is a married woman." She pushed him a little while laughing. "Please let me take a bath." "Yes ma'am." She entered the toilet. She turned on the warm water and felt her body's tiredness slowly subside. After she finished, she came out of her body with the smell of gel and the smell of bath perfume. She wore a very beautiful long gown, the color of a light wine, the arms were full of sparkling stones. Her veil was matching with the clothes. She stood in front of the mirror and fixed her lips. In the back Ibrahim stopped and looked at her in the mirror. "Zahra..." "Hmm?" "You know right? Every time you prepare like this, I don't want to go out b
FARASHIN IZZAH Jiddatulkhayr writes
Young talented writers ass.. (YOTA)
Book 1 Chapter 17
Kitchen ɗin gaba ɗaya ya ɗauki ƙamshin girkinta mai daɗi. Farida na tsaye tana miyan kayan lambu yayin da Zahra ke haɗa spicy jollof rice ɗin da ta dafa da chicken mai dadi, Gefe kuma akwai fried meat da salad da suka haɗa cheffing dish
“Wallahi Hajiya kin iya girki,” Farida tace tana murmushi.
Zahra ta ɗan yi dariya. “Da gaske?”
“Eh mana, tun da na fara jin ƙamshin shikenan na fara ji yunwa.”
“Ke dai bari kawai,” Zahra tace tana ɗan motsa cokalin hannunta. “Maman Oga tana son abinci mai ɗan haɗi ne shiyasa nace bari muyi abin kirki.”
“Toh ai zata ji daɗi sosai.”
Bayan sun gama komai, suka fara zubawa a warmers masu kyau. Zahra na gyara yadda komai zai yi neat cikin basket ɗin.
“Wannan salad ɗin ki saka a gefe.” Cewar Zarah
“Toh Hajiya.”
“Kar chicken ɗin ya zube fa.”
Dariya Farida tayi. “Toh.”
Bayan sun gama jera komai cikin basket mai kyau, Zahra ta sauke numfashi tana kallon abincin.
“Alhamdulillah.”
Farida tace, “Hajiya ki tafi ki shirya yanzu, ni zan gyara kitchen.”
“Kin gaji fah” inji Zahra
“A’a wallahi.”
Murmushi Zahra tayi sannan ta juya ta fita, haurawa sama tayi
Tana shiga ɗakinta ta samu Ibrahim zaune bakin gado yana duba wayarsa. Ya ɗaga kai suka haɗa ido, kallonta kawai ya tsaya yi.
“Me?” Zahra tace tana murmushi kaɗan.
“Kin ƙara kyau ne ko ido nane”
Dariya tayi tana cire hijab ɗinta. “Ka bari Noory.”
Ya miƙe ya ƙaraso kusa da ita. “An gama girkin?”
“Eh.”
“Hmm… Zahra matar aure.”
Ta tura shi kaɗan tana dariya. “Please bari nayi wanka.”
“Toh madam.”
Toilet ta shiga. Ruwa mai ɗumi ta kunna tana jin gajiyar jikinta na sauka a hankali. Bayan ta gama ta fito jikinta na ƙamshin gel tare da kamshin turaren wanka
Wani dogon gown mai matuƙar kyau ta saka, colour ɗin wine mai ɗan haske, hannayensa cike da stones masu kyalli. Veil ɗinta kuwa ya yi matching da kayan. Ta tsaya gaban mirror tana ɗan gyara lips ɗinta.
A baya Ibrahim ya tsaya yana kallonta ta mirror.
“Zahra…”
“Hmm?”
“Kin sani ko? Duk lokacin da kika shirya haka bana son fita da ke saboda kowa sai ya tsaya kallon matata.”
Ta ɗan cije lips ɗinta tana murmushi. “Drama king.”
Shi ma ya shirya cikin wata black native mai matuƙar kyau. Agogon hannunsa da turarensa suka ƙara fito da ƙyansa sosai.
Bayan sun gama, suka fito tare.
A parlorn ƙasa Ibrahim ne ya ɗauki basket ɗin warmers ɗin. Zahra ta kalleshi tace,
“Bari na ɗauka mana.”
“Karki damu.”
Suka fito tare har zuwa wajen motar, suka shiga, Ibrahim ya kunna wata soft love song mai sanyin gaske.
A hankali motar ke tafiya yayin da song ɗin ke tashi.
Zahra ta jingina kanta jikin seat tana kallon waje, Ibrahim kuma lokaci zuwa lokaci yana kallonta yana murmushi.
“Me kuma?” tace bayan ta kamashi yana kallo.
“Nothing… ina kallon matata ne kawai.”
Ta ɗan kau da kai tana murmushi.
Haka suka isa gidan Mama.
A compound Ibrahim yayi parking. Ya fito ya zagaya ya buɗe mata ƙofa. Ita kuma ta sauko a hankali yayin da shi ya ɗauki basket ɗin warmers ɗin.
Tare suka shiga ciki.
Suna shiga kuwa suka haɗu da Mama, shigowarta kenan daga backyard . Tsayawa tayi tana kallonsu, musamman basket ɗin dake hannun Ibrahim.
“To oo…” tace tana ɗan ɗaga gira. “Yanzu Ibrahim kai ne da ɗaukar basket? Ko dai dama da gaske ne abinda naji?”
Nan take Zahra taji wani iri a ranta, ta ɗan sunkuyar da kai.
Ibrahim ma wani iri yaji, amma sai yayi saurin cewa, “Haba Mama ai kinsan Zahra ba lafiya take da shi ba”
Sai Mama tayi murmushi irin na manya. “Toh ku shigo mana, kun tsaya a bakin ƙofa.”
“Ai Mama ke kika tsayar da mu,” Ibrahim ya amsa.
Shiga suka yi.
Zahra ta zauna a parlorn tana jin kanta not comfortable kwata-kwata. Ita kanta batasan dalilin da yasa maganar ta tsaya mata a rai haka ba.
Ibrahim kuwa dining ya wuce ya ajiye basket ɗin.
Yana juyowa zuciyarsa ta ɗan cunkushe. Haka kawai yaji bai so abin da Mama tayi ba. Musamman ganin yadda fuskar Zahra ta canza a take.
A parlorn suka zauna tare da Mama suna hira lokaci zuwa lokaci. Mama ta tambayi Zahra ya jikinta, ya makaranta, ita kuma tana amsawa cikin ladabi duk da zuciyarta bata gama sakin jiki ba.
Ibrahim kuwa ya lura da canjin Zahra tun bayan maganar basket ɗin, yasan pretending take yi wajen faking murmushi, shiyasa lokaci zuwa lokaci yana kallonta idan Mama bata kula ba.
Har aka kira sallar magrib suna gidan. Ibrahim ya tashi ya tafi masallaci, bayan ya dawo sannan suka dawo parlorn suka ci abincin da Zahra ta kawo. Mama ma ta yaba sosai da girkin.
“Zahra kin iya girki sosai,” Mama tace tana ɗan ɗiba miyan.
Murmushi kawai Zahra tayi. “Nagode Mama.”
A haka suka gama dinner. Bayan sun ɗan zauna kuma, suka yi wa Mama sallama.
“Allah ya kai ku lafiya,” Mama tace.
“Ameen,” suka amsa tare.
A cikin mota kuwa daga Zahra har Ibrahim babu wanda yace komai. Song ɗin da aka kunna ma a hankali yake tashi amma dukansu suna cikin nasu tunanin.
Ibrahim ya ɗan kalleta sau biyu amma bata ɗago ba.
Sai kawai ya juya steering ya tsaya a wani eatery mai kyau.
Ta ɗan kalleshi. “Me kuma?”
“Mu ci abinci.”
“Ai mun ci a gidan Mama.”
“Still…”
Bata ƙara magana ba suka shiga ciki.
Wajen ya yi sanyi da haske mai kyau. Suka zauna a wani corner mai nutsuwa sannan suka yi order.
Zahra ta ɗauki noodles da chicken, shi kuma ya ɗauki burger da drink.
Duk da suna cin abinci ne, akwai wani irin shiru tsakanin su.
A ƙarshe Ibrahim ya sauke spoon ɗinsa yace, “Zahra…”
Ta ɗago tana kallonsa.
“I’m sorry.”
Shiru tayi.
“Ban so yadda Mama tayi magana ɗazun ba.”
“Ai babu komai,” ta amsa a hankali.
“Da gaske?”
Kai ta gyada masa. “Please kar ka damu.”
Yadda tayi maganar yasa ya ɗan sake.
A hankali ya kamo hannunta saman table ɗin. “Thank you.”
Ta ɗan murmusa masa. “Ka daina wannan worried face ɗin.”
Daga haka ya ɗan saki jiki suka fara hira kaɗan-kaɗan. Har dariya Zahra tayi lokacin da Ibrahim ya fara bata labarin wani abu da ya faru a office.
Da suka fito daga eatery ɗin, yanayin dake tsakaninsu ya ɗan lafa.
A mota ma Ibrahim ya riƙe hannunta yana driving da hannu ɗaya. Ita kuma duk da zuciyarta bata gama warkewa ba, tayi ƙoƙarin nuna masa komai lafiya ne saboda taga ya damu sosai.
Da suka isa gida, Ibrahim ya wuce toilet domin yayi wanka. Ita kuma Zahra kitchen ta tsaya tana duba wasu abubuwa kafin daga baya ta haura sama.
Tana shiga ɗakin, idanunta suka sauka kan wayarsa dake gefe tana ringing.
Sunan da aka yi saving ɗin number ɗin yasa gabanta ya faɗi.
“Lovie Dovie…”
Wani irin abu taji ya tsinka mata zuciya.
Wayar ta daina ringing.
Sai kuma wani call ɗin ya sake shigowa.
Kafafuwanta kamar sun manne a wajen.
Har ta matsa zata ɗauki wayar… sai kuma ta fasa.
Wani irin zafi taji a zuciyarta.
Jin motsin Ibrahim zai fito yasa ta bar wajen da sauri. Gaba ɗaya mood ɗinta ya canza.
Kai tsaye toilet ta shiga itama dan tayi wanka ba tare data sake kallon inda wayar take ba.
Bayan ta fito tana saka kaya, Ibrahim kuma yana gyara sleeve ɗin kayansa a mirror.
Sai kuma wayar ta sake ringing.
A wannan karon Zahra ta sace kallon wajen.
Shi ma Ibrahim ɗin ya ɗaga kai ya kalli wayar.
Da ganin number ɗin, nan take ya ƙarasa ya ɗauki wayar ya mayar silent sannan ya saka a aljihu.
Sai kuma ya juya da sauri yana kallon Zahra.
Ita kuwa tayi kamar hankalinta baya kansa kwata-kwata.
Ga mamakinta, sai kawai ya fita daga ɗakin.
Zahra ta tsaya tana kallon ƙofar bayan ya fita.
A hankali ta ƙarasa bakin gado ta zauna. Ta dauki lokaci ba tare data san tana wajen ba
Mintuna suna wucewa… Tara… Goma…
Har ƙarfe goma sha ɗaya na dare Ibrahim bai dawo ba.
Yanzu kam abin ya fara damun Zahra sosai.
Jikinta har rawa yake yi.
Ta rungume pillow tana ƙoƙarin hana kanta tunani, amma ta kasa.
Batasan sanda hawaye suka fara zubo mata ba.
Tasani sarai… idan har ta fita nemansa a wannan lokacin, babu abin da bazata iya aikatawa ba saboda ɓacin rai.
A haka bacci ya ɗauke ta cikin kuka da ciwon zuciya.
Can cikin dare ta farka a firgice. Da sauri ta kai dubanta gefen gadon.
Baya ɗakin.
Wani irin mamaki ne ya kamata.
Tun daga ranar da suka shirya bayan dawowarta daga gidan su, Ibrahim bai taɓa barinta ta kwana ita kaɗai ba.
Sai yau…
Sai da wannan “Lovie Dovie” ɗin ta kira shi.
Sosai Zahra ta shiga damuwa.
Tun daga lokacin da ta farka taga Ibrahim baya ɗakin, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa. Wani irin tunani ne ya fara yawo a kanta—tun daga kan “Lovie Dovie” ɗin har zuwa fitarsa daga ɗakin ba tare da ya dawo ba.
Ta juya gefe tana ƙoƙarin danne tunanin, amma hakan ya gagara.
Daga ƙarshe dai gajiyar kuka da tunani ne suka rinjaye ta, bacci ya sake ɗaukarta.
Da asuba ta sake farkawa.
Da sauri idanunta suka nufi gefen gadon.
Har yanzu babu Ibrahim.
Wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta. Ta daɗe zaune tana kallon wajen kamar tana jiran kawai ya buɗe ƙofa ya shigo.
Amma shiru.
A hankali ta sauke ƙafafunta daga kan gadon. Gabanta na mata wani irin nauyi.
Toilet ta shiga tayi alwala sannan ta fito ta tada sallah.
Bayan ta idar, bata tashi daga sallayar ba. Kwanciya tayi a kanta tana kallon ceiling, idanuwanta cike da tunani da ciwon zuciya.
Can taji an buɗe ƙofa.
Ibrahim ne ya shigo.
Da sauri ta miƙe ta zauna akan sallayar.
Ko kallonsa bata yi sosai ba tace, “Ina kwana.”
“Lafiya,” ya amsa a taƙaice.
Muryarsa kaɗai ta sake ɗaure mata zuciya.
Ya tsaya na ɗan lokaci kamar zai yi magana, sai kuma ya juya ya fita daga ɗakin.
Zahra ta bishi da kallo har ya fita, sannan ta sauke idanunta tana jin zuciyarta na mata nauyi fiye da da.
Kai tsaye kitchen ya wuce.
Bayan wasu mintuna ita ma ta sauka ƙasa.
Tana shiga kitchen ta samu Farida har tayi morning. Irish take ferewa a hankali.
“Ina kwana Hajiya,” Farida ta gaidata cikin fara’a.
“Lafiya,” Zahra ta amsa da ƙyar.
Kitchen ɗin ma gaba ɗaya sai taji bata son ganinsa. Kamar komai a gidan yana tunasar da ita Ibrahim ne.
Bata tsaya ba ta juya ta fita.
Ta koma sama.
Tana shiga ɗakin taga baya nan, hakan ya ɗan bata sauƙi.
Kai tsaye toilet ta shiga tayi wanka. Bayan ta fito ta fara shirinta na makaranta cikin sauri.
Wani plain gown mai kyau ta saka tare da hijab. Bata tsaya wani gyara sosai ba.
Abu ɗaya kawai take ji…
Bata son duk wani abin da zai haɗata da Ibrahim yau.
Yau gara ta fita ta bashi space ɗinsa, saboda idan ta ci gaba da kallonsa zata iya kasa ɓoye damuwar dake ranta….
To her own surprise, Zahra ta gama shirya wa cikin lokaci ƙanƙani. Ita kanta batasan yadda ta iya haɗa kanta haka ba.
Tana gyara hijab ɗinta a mirror kawai sai taji ƙarar buɗe gate.
Da sauri ta matsa ta buɗe curtain ɗin ɗakinta.
Motar Ibrahim ce ke fita da sauri daga compound.
Kamar an dasata a wajen haka ta tsaya cak.
Wani irin abu taji ya tsaya mata a zuciya ganin har ya fita bai mata sallama ba.
Ko message babu. Ko knocking ɗin ƙofa bai yi ba.
Sai yanzu taji ainihin nauyin abin da yake mata.
A hankali ta ɗauki school bag ɗinta da key ɗin mota sannan ta sauka ƙasa.
Farida na tsaye a dining tana gyara plates.
“Hajiya yau ba zaku karya bane?”
Kai Zahra ta gyada mata kawai ba tare data tsaya ba.
Daga haka ta fita.
Har ta isa school bata san yadda tayi driving ɗin ba. Hankalinta gaba ɗaya baya jikinta.
A bakin hall ta hango friends ɗinta—Firdausi, Asiya da Suhaima.
Suhaima ce ta fara magana tana kallonta sama da ƙasa.
“Nikam ni kaɗai naga sai glowing Zahra ke yi?”
Wani murmushin yaƙe Zahra tayi kawai sannan ta juya gefe saboda bata da interest a hirar.
Firdausi ta lura da yanayinta, shiyasa itama bata ƙara mata magana ba.
Daga haka suka shiga lecture hall ɗin tare.
Lecturer na shigowa ya fara teaching ɗinsu kai tsaye. Students da yawa na rubutu, wasu na tambaya, wasu kuma hankali tasu na kan board.
Amma Zahra… Ko kaɗan bata tare da su a wajen.
Pen ɗin dake hannunta ma juyawa kawai take yi. Idanuwanta na kan lecturer amma hankalinta gaba ɗaya yana wani wajen.
Tunani take…..
Ina Ibrahim ya kwana? Wacece “Lovie Dovie?” Me yasa ya fita haka ba tare da ya dawo ɗakin ba?
“Mrs Ibrahim…”
Sai taji an kira sunanta.
Da sauri ta ɗago.
Lecturer ɗin ne yake kallonta. “Can you answer the question?”
Wani irin ruɗani ya kamata. Bata ma san wace tambaya yayi ba.
Hall ɗin gaba ɗaya suka juya suna kallonta.
Firdausi tayi saurin tura mata notebook ɗinta ƙasa-ƙasa tana nuna mata inda lecturer ɗin ya tsaya.
Sai Zahra tace da ƙyar, “I’m sorry sir…”
Lecturer ɗin ya ɗan girgiza kai. “You need to concentrate.”
“Yes sir.”
Ta zauna a hankali tana jin kunya na rufeta.
Firdausi ta matsa kusa da ita kaɗan. “Zahra lafiya kuwa?”
Kai ta girgiza mata. “I’m fine.”
Amma ita kanta tasan ba fine ɗin bane ko kaɗan. Zuciyarta gaba ɗaya a cunkushe take kamar zata fashe.
#08110615256