Kenza eBookz
Cover art for KOMAI YA YI FARKO  HAUSA NOVEL 2

Post

KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 2

..... I always give you advice, some things are not because you don't know, I have already done something necessary for you, Humaira, it is not because God hates you that he gave you this test, he wanted to test the strength of your faith, please God, bind yourself and overcome this test." She slowly said: "I Sha Allah Abba." Abba continued to speak; Next week you will go back to school and continue preparing for your WAEC, because God willing we will never let this decision be your end." "God willing Abba." She also said, because at this point she doesn't know what to say, she doesn't even know how to continue with her life, she must need someone to tell her what to do, because now her memory can't process anything, her heart doesn't beat well, everything is not normal anymore. Abba said; "You can go, God He has blessed you." She slowly stood up and left the room feeling as if the wind would blow her away because she felt her body was very light like paper. She didn't want to go back to the room because she knew if she went back to the room she would say something, then k.....

Standalone post2,362 words

https://chat.whatsapp.com/CGm8zTMQDDO1e9sf3BmDKQ?mode=hqctcla

KOMAI YA YI FARKO

PAGE 2

Bayan Sallar La'asar Humaira na zaune akan darduma tana karatun Alkur'ani, Abba ya leƙo ɗakin, ya tsaya shiru a bakin ƙofa, kafin daga baya ya ce; "Humaira idan kin gama karatun ki same ni a ɗakina." Ya juya baya ya fita daga ɗakin.

Tana kai ƙarshe ayar da take karantawa, ta rufe Ƙur'anin ta ajiye, ta fita daga ɗakin zuwa ɗakin Abba. A ƙasa ta zauna, ta sunkuyar da kanta ƙasa, tace; "Ina wuni Abba."

Abba ya tsaya shiru for sometimes yana karantar yanayinta, sannan yace; "Lafiya Humaira, ɗazun da safe na leƙa kafin na fita wajen aiki, amma kina bacci."

Kanta a ƙasa, ba tare da ta iya ɗaga idanunta ta kalle Abbanta ba, tace; "Eh na samu bacci yau."

"Alhamdulillah, Allah ya ƙara mana dangana."

"Aameen Abba."

Shiru ne ya ɗan ratsa tsakani, kafin Abba ya gyara murya, yace; "Humaira..."

Ɗago kai ta yi a hankali tq kalle Abba, sanan ta mayar da kanta ƙasa, ta ce; "Na'am Abba."

"Humaira tunda abin nan ya sameki kullum ina miki nasiha, wasu abubuwan ba wai don ba ki sani bane, tunine wanda ya zama dole na yi miki, Humaira ba wai Allah ya ƙi ki bane yasa yayi miki wannan jarabawar, ya na son ya gwada ƙarfin imanin ki ne, don Allah ki ɗaure ki cinye wannan jarabawar."

A hankali ta furta; "In Sha Allah Abba."

Abba ya ci gaba da magana; "Kamar yadda muka yi shawara tun farko wannan maganar sirri ce a tsakanin mu, babu wanda ya sani, kuma babu wanda zai sani, don haka next week za ki koma makaranta ki cigaba da shirye-shiryen rubuta WAEC ɗinki, saboda In Sha Allah ba za mu taɓa barin wannan ƙaddarar ta zama ƙarshen ki ba."

"In Sha Allah Abba." Ta kuma faɗi, don at this point bata san me zata faɗa ba, ba ta ma san yadda zata cigaba da rayuwarta ba, dole tana buƙatar mai faɗa mata abinda za ta yi, saboda yanzu ƙwaƙwalwarta bata iya processing komai, zuciyarta ma ba ta bugawa da kyau, komai ɗinta is not normal anymore.

Abba ya ce; "Za ki iya tafiya, Allah ya yi miki albarka."

A hankali ta miƙe, ta fita daga ɗakin tana jin kamar iska zai ka da itasaboda yadda take jin jikinta very light kamar paper. Ba ta yarda ta koma ɗaki ba, saboda ta san idan ta koma ɗakin wani tunanin za ta faaɗa, sai kawai ta zauna a tsakar gida tare da matan Abbanta da ƴan uwanta, ta saka hannu ta fara taya Mama Lantana tsintar shinkafar da za a dafa na dare.

------

Sati ɗaya ta yi a gida tana jinyar jikinta da zuciyarta kafin 5a koma makaranta. Daga ɗalibai har malamai sai sannu suke yi mata, dukkan su sun yarda akan rashin lafiya ta yi, duba da yadda ta rame sosai kamar wace ta yi jinyar shekara. A aji ta zama so silent kamar, daman tun can ita ɗin ba mai hayaniya ba ce, amma tana amsa questions a class, yanzu kuwa ko tambayar ba ta amsawa sai dai ta yi ta bin kowa da ido, kuma ba wai don ba ta fahimtar abinda ake yi ba, kawai she just choose to be silent.

Wata biyu da afkuwar ƙaddararta ta zana WAEC, a wannan lokacin saurayinta Kamis ya shigo gida, Abbanta yace lallai ta faɗa mishi abinda ya faru da ita tunda da aure yake sonta, kar ya zamana an ɓoye masa wani abu, bayan an yui aure ya find out kuma ya zama matsala.

Kamis ya zo wajenta zance da daddare, A zaure ta shimfiɗa tabarma suka zauna, ra kawo mishi ruwa. Bayan ta gaishe shi ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsuna.

Kamis na kallonta yace; "Wai Humaira me yasa kwana biyun nan kika zama so silent ne, duk da daman ke ba mai surutu bace, amma tun bayan zazzaɓi da kika yi kwanakin baya na lura rashin son maganarki ya ƙaru."

Numfashi ta sauke, tace; "Kamis akwai maganar da nake son na maka." Ta ɗago ta ɗan kalle shi, sannan ta mayar da idanunta ƙasa, cikin ƙarfin hali ta yi mishi bayanin komai. Tana ɗaga ido ta gan yana bin ta da wani irin kallon ƙyama, ba tare da ɓoye-ɓoye ba, yace matq; "Gaskiya ba zan iya aurenki ba idan haka ne."

Ta ɗaga ido ta kalle shi da mamaki, bat ta taɓa tsammanin haka daga Kamis ba, a tunaninta ko me zai sameta Kamis ba zai iya juya mata baya ba, saboda tun tana shekara sha huɗu ya nuna yana sonta, ya jure dukkan yarantarta, dangi kowa da kowa an san su tare, daman jira kawai ake ta yi candy a ɗaura musu aure, amma yau saboda ƙaddara ta sameta ya ce ba zai iya aurenta ba? Kafin ta gama processing komai a ƙwaƙwalwarta dake wahalar processing abu yanzu, Kamis ya tashi ya tafi, ya bar ta zaune cike da mamaki da baƙin ciki. Hawaye ne suka fara sintiri a fuskarta, ta fara tunanin; yanzu dukkan buri da take dashi ya rushe, dukkan tanadin da tayi na aurensu da Kamis ya rushe lokaci guda, wani zafi ta fara ji a zuciyarta, da ɗaci-ɗaci a maƙwogwaronta, kukan da babu sauti ta fashe da shi.

Sunanata A'isha Humaira Mu'azu, ƴa ta huɗu a cikin jerin ƴaƴan Malam Mua'azu, kuma ƴa ɗaya tilo a wajen Mahaifiyarta Umma Salamatu. Mahaifinta yana siyar da kayan gwari ne a kasuwa, yana da mata uku; Mahaifiyarta Umma Salamatu, Mama Lantana, sai Mama Hafsatu. Mama Lantana ce matar sa ta fari, sai Umma Salamatu, sai amarya Hafsatu. Mama Lantana na da yara huɗu; Kabir, Kamal, kausar, Khalid. Mama hafsatu kuma tana da biyu; "Bilal da Balki. Sai kuma Humaira da Mahaifiyata ta haifeta ita kaɗai. Yaya Kabir ne babba a gidan, sai Yaya Kamal, sai Ya kausar, sai Humaira,bsai Khalid, sai Bilal, sai auta Bilki. Akwai kuma Yayar Malam Mua'azu, Inna Habi wacce mijinta ya rasu, bayan takabarta sai ta dawo gidan da zama, tana da yara biyu; Yusuf da Imrana.

Humaira na da shekara bakwai Mahaifiyarta ta rasu bayan zazzaɓin kwana biyu da ta yi. Tun bayan rasuwarta riƙon Humaira ya dawo hannun Inna Habi, wacce ta riƙeta cike da so da tausayawa, Inna Habi ba ta taɓa bari ta yi kukan maraici ko na daidai da second ɗaya ba, ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin ta maye mata gurbin uwa da ta rasa a ƙanƙanin shekaru.

Wata ranar Asabar Mama Hafsatu ta aike Bilki ta siya mata kukan da za a kaɗa na yamma a maƙwabta, da Bilki ta kawo kukan aka kaɗa sai ya kasa saboda rashin yauƙin kukar, Mama Hafsatu ta ƙwalawa Bilki kira, ta ce; "Bilkisu don ubanki a ina kika siyo min wannan kuka mara yauƙin?" Bilkisu tace a gidan wata ƙawarta ce, Mamarta na siyar da kuka, shine ta tafi can. Mama ta fara mata faɗa sosai, sannan tace ta je ta ƙaro mata wani kukan da canjin aiken. Bilki na zumɓure-zumɓuren baki ta fita daga gidan don siyan wani kukan. Shiru-shiru tun La'asar har Maghrib Bilki ba ta dawo ba, Hankalin mutanen gida ya fara tashi don ba ta saba daɗewa a saƙo ba. Humaira ta yi alaular sallar maghrib, amma ganin yadda hankali Mama Hafsatu ya tashi sai ta ce bari ta dubo gidan ƙawartata ɗin ƙilla ta tsaya wasa ne a can. Inna Habi ta ba ta ɗan tocilanta da suke haskawa dashi ya fita daga gidan. Gidan ƙawar Bilki, 'Sa'a' ta fara tafiya, amma sai tace mata ba ta zo gidansu ba, amma kuma ƙawarsu Rabi ce mamarta ke siyar da kuka.

Humaira na cikin tafiya a hanyar gidansu Rabi da yake shiru-shiru ko da rana balle yanzu da yamma ta yi, yawancin maza sun shiga Masallaci, sai ta ji kamar sahun tafiya a bayata, juyowar da zara yi sai ta gan Lukman ɗan Alhaji Mai canji da abokansa biyu ne a bayanta suna hirarsu suna tahowa, juyowa ta yi ta cigaba da tafiyarta ba tare da ta kawo komai a ranta ba, sai dai ba ta yi tafiya ya kai taku biyar ba bayan juyowarta, ta ji an janyo mata hijjabi da ƙarfi ta baya, kafin ta kai ga yin ihu aka toshe mata baki da hanky, aka rinƙa janta, duk iya ƙoƙarinta wajen ganin ta ƙwace kanta ta gagara saboda ƙarfinta da na namiji va ɗaya ba, na mijin ma ba ɗaya ba har biyu, wani gini da ba a ƙarasa ba suka shigar da ita, suka danneta suka tsofa mata tsuma a baki sannan suka yi amfani da wani daban suka ɗaure bakin ta hanyar da ba za ta iya ihu ba, tana ji tana gani kartin mazan nan suka danneta, suka ba wa Lukman dama ya keta mata mutuncina ba tare da ko ɗigon tausayi ba, mazan anguwar da ya kamata su zama ma su kare ta idan wani zai yi mata haka, amma sune suka lalata mata rayuwa a cikin incomplete building a ranar asabar daidai lokacin da ake sallar maghriba, sannan suka bar ta a yashe a wajen suka yi tafiyarsu. Tana kwance a yadda suka barta har aka yi sallar Isha, har dare ta fara yin nisa, tun tana jin wucewar ɗaiɗaikun mutane har ta daina jin sahu, gashi babu halin ta yi ihu saboda tulin tsumar dake bakinta, ta yi ƙoƙarin miƙa hannuna zuwa baya ta kwance ɗaurin amma ta gagara saboda yadda take jin hannunta kamar ba a jikinta ba, sakamakon danneta da suka yi.

Bayan dare ya tsala sosai, ba abunda ake ji sai kukan gyare, sai ta ji tsayawar mota a daidai incomplete building da take,addu'a ta fara yi a zuciyarta akan Allah ya sa wani ya zo ya ganta a nan ya taimaka mata. Toci aka haska mata a ido, aikuwa nan take zuciyarta ta tsinke saboda ganin Lukman da abokansa na ɗazun, wannan karon ba su ma dannata ba saboda ba ta da ƙarfin kokuwa, ya kuma biyan buƙatar shi da ita a karo na biyu, tun tana hawaye har hawayen suka kafe, raɗaɗi kan raɗaɗi, azaba kan azaba shine abinda ta ji a wannan lokacin. Yana sauka daga kanta, abokansa suka cicciɓeta zuwa mota, tana ji suka kira wani a waya ya duba musu ko akwai sahun mutane ta ƙofar gidansu, ba ta san me ɗayan ya faɗa musu ba, sai kawai gani ta yi sun ja motar. A daidai ƙofar shiga gidansu suka ajiyets.

A gidan Malam Mua'azu kuwa babu wanda ya iya runtsawa saboda tashin hankali. Bayan fitar Humaira da kaɗan Bilki ta dawo, ashe ɓatar da kuɗin ta yi tana tsoron dawowa gida Mama Hafsatu ta doke ta, shiyasa ta yi ta ɓoye-ɓoyenta har bayan Maghrib lokacin da ta san Abba zai dawo gida, kafin ta shigo, don ta san ba zai bari a doketa ba, tana shigowa Mama Hafsatu ta tambayeta; "Ina Humaira?"

"Ban ganta ba." Bilki ta amsa tana mai shiga ɗakin Abba da gudu. Har aka fara kiran sallar Isha Humaira ba ta dawo gida ba, hakan ya sa Mama Hafsatu da kanta ta fita nemanta, amma ba ta ganta ba, kowa ta tambaya sai su ce sun gan lokacin da ta yi layin gidansu Rabi, amma da ta je gidan kuma sai aka ce mata Humaira ba ta shiga gidan ba. Abu kamar wasa har ya zama babba, ƙule ƙofar gidan Malam Mua'azu aka yi, gabaki ɗaya aka fita neman Humaira, har sha biyun dare ana abu ɗaya, Abba ya umarce matan da su koma gida, su mazan za su cigaba da nemanta, idan kuma ta dawo gida sai su bugo waya su sanar. Har ɗayan dare babu Humaira babu labarinta, hankalin Abba idan ya yi dubu to dukka sun tashi, amma haka ya daure ya cewa su Ya Kabir da sauran ƴan unguwar da suke taya su nemanta akan a je a kwanta, gobe da safe sai a kai report gidan rediyo da police station.

Mama Hafsatu ta yi kuka sosai, don gani take yi ita ce sillar duk abinda ya faru, Inna Habi kuwa ta kasa ma yin kukan, Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un kawai take ta maimaitawa. Abba ya kalli kowa dake tsakar gidan yace; "Ku yi alaula ku yi sallah raka'a biyu, sannan ku yi adduar Allah ya baiyana mana Humaira a duk inda take cikin ƙoshin lafiya." Ya kalle Yaya Kabir, yace; "kai kuma ka je ka rufe ƙofa.

Yaya Kabir ya zo rufe ƙofar kenan wani zuciya ta ce ya leƙa waje ƙilla ya gan Humairar, yana leƙa waje ya gan mutum a kwance a ƙofar gida, a lokacin Humaira ta riga da ta pass out. Wayarsa ya ciro daga aljihun wandonsa ya kunna haske, haskawar da zai yi ya gan Humaira a yashe a ƙasa unconscious, da gudu ya ƙaraso inda take, tsugunawa yayi, ya girgizata, yana faɗin; "Humaira! Humaira!! Me ya same ki?" Amma shiru babu response, cicciɓarta ya yi zuwa cikin gida, ɗakin Inna ya ' shigar da ita direct, dukkan ƴan gidan suka bi shi a baya da sauri. Inna ta fara matsowa kusa da ita kamar mai tsoron taka ƙasa, tana ƙarasa kusa da ita ta shafa fuskarta tace; "Me ya sameki hakan Humairata? Me ya yaga miki rigarki?"

Maganarta ce ta saka hankalin kowa ya kai kan rigarta da yake a yage. Riƙe ƙirjinta Inna ta yi da wani tunani ya faɗo mata, ta kalle su Abba tace; "Mu'azu ku ɗan ba mu waje, zan canza mata kaya."

Mazan na fita gabaki ɗayansu, Inna ta ɗaga rigar Zahra, abunda ta yi tozali dashi ne ya saka ta fashe da wani irin kuka, tana faɗin; "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, mun shiga uku" Mama Hafsatu da aka yi komai a gaban su, suma suka fashe da kuka, Mama Lantana ce ta yi ƙarfin hali, ta share idonta, ta ja zanin gado ta rufewa Humairan saboda mazan da taji suna shigowa ta sanadiyyar kukan da suka jiyo.

Abba ya riƙe Inna da ke kuka kamar za ta shiɗe, yace; "Adda menene? Me ya sami 'yata?"

"Mu'azu mun shiga uku, an zalunce mu, an zalunce marainiyar Allah, an raba ƴar mu da mutuncinta." Inna ta faɗa tana fashewa da sabon kuka.

INALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN, WHAT A DESTINY 😭