Kenza eBookz
Cover art for FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 16

Post

FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 16

.....he went to the eatery. When he arrived, he parked and got out of the car, fixing his watch. The place was filled with the smell of grilled food and the noise of a few people. He went inside, a waiter finished with a smile. "Good evening sir." "Evening. I like grilled chicken, very spicy... then add fries and chilled juice." "Okay sir." He stood leaning on the counter waiting for the order. From time to time he checks his phone. In his mind, he was thinking about how Zahra said that she wanted to eat chicken before she fell asleep. After the packing was done, he accepted and paid and went out to his car. On his way back, his phone started ringing. He picked up the phone and looked at the screen. It's an unknown number. His finger lingered on the screen before picking up the call. "Hello?" The caller is also silent. Then he could only hear a little breathing from the other side. Abraham's face changed a little. "Who's this?" Until then there is no answer. He slowly frowned and hung up the call and put the phone aside. It wasn't long before he called again. He quickly looked at the number one. This time he didn't pick up, he cleared the phone and continued driving. That's how he

Standalone post2,415 words

FARASHIN IZZAH Jiddatulkhayr writes

Book 1 Chapter 16

Ya gaida Mummy cikin girmamawa, ita kuma ta amsa tana tambayar,

“Ya jikin Zahra?”

“Da sauƙi,” ya amsa yana kallon Zahra cikin kulawa.

Daga haka ya miƙe zai shiga ciki.

Mummy ma ta miƙe tana gyara hijabinta.

Ta tsaya tana kallon Zahra tace, “Allah baki lafiya daughter.”

A hankali Zahra tace, “Ameen.”

“Bari na tafi yanzu ko”

“Thank you Mummy,” Zahra ta faɗa cikin girmamawa.

Murmushi Mummy tayi sannan ta fita.

Bayan tafiyarta, Zahra ta gyara kwanciyarta akan kujera tana jin kasala sosai. Ta ce

“Kaza nake son ci”.

Kafin ma Ibrahim ya dawo daga sama, bacci ya sake ɗaukarta.

Saukowa daga stairs yayi yana gyara hannun rigarsa, idanunsa suka sauka akanta tana bacci luf a kujera, sai ya tsaya yana kallonta cikin tausayi da ƙauna.

A hankali Ibrahim ya ɗauki keys ɗin motarsa sannan ya sake kallon Zahra dake bacci a parlorn. Blanket ya ƙara gyara mata kafin ya fita daga gidan cikin nutsuwa kada hayaniyar ƙofar ta tasheta.

Kai tsaye wani classy eatery ya nufa.

Da ya isa, parking yayi sannan ya fito daga motar yana gyara agogonsa. Wajen ya cika da ƙamshin grilled food da hayaniyar mutane kaɗan-kaɗan.

Shiga yayi ciki, wani waiter ya ƙaraso da murmushi.

“Good evening sir.”

“Evening. Ina son grilled chicken, spicy sosai… sannan ku haɗa da fries da chilled juice.”

“Okay sir.”

Ya tsaya jingine a counter yana jiran order ɗin. Lokaci zuwa lokaci yana duba wayarsa. A zuciyarsa yana tunanin yadda Zahra ta faɗi tana cewa kaza take son ci kafin bacci ya kwasheta.

Bayan an gama packing ɗin, ya karɓa ya biya kuɗi sannan ya fita zuwa motarsa.

A hanyarsa ta dawowa ne wayarsa ta fara ringing.

Ɗaga wayar yayi yana kallon screen ɗin. Unknown number ne.

Yatsansa ya ɗan tsaya akan screen ɗin kafin ya ɗaga call ɗin.

“Hello?”

Wanda ya kiran kuma yayi shiru. Sai ƙaran numfashi kawai ya ɗan ji daga ɗaya ɓangaren. Fuskar Ibrahim ta ɗan canza.

“Who’s this?”

Har lokacin babu amsa.

A hankali ya tsuke fuska sannan ya katse call ɗin ya ajiye wayar a gefe.

Bai jima ba aka sake kira.

Da sauri ya kalli number ɗin ɗaya ne. Wannan karon bai ɗaga ba, ya share wayar gefe yana cigaba da driving.

A haka ya isa gida.

Yana shiga compound ɗin, idanunsa suka ɗan ɗaga zuwa balcony ɗin saman gidan kafin ya fito daga motar da ledar grilled chicken ɗin hannunsa.

Ciki ya wuce cikin sauri yana son ya ga ko Zahra ta tashi daga baccin nata.

Yana shiga parlorn ɗin ya tsaya yana kallonta. Har yanzu bacci take yi cikin nutsuwa, kanta na kwance jikin cushion ɗin kujera yayin da blanket ɗin da ya rufe mata ya ɗan zame gefe.

Murmushi yayi a hankali yana girgiza kai.

“Baby na…” ya furta ƙasa-ƙasa.

Ledar grilled chicken ɗin ya aje saman center table sannan ya sunkuya kusa da ita.

Yaso ya ɗagata ya kai ɗaki amma kallon yadda take bacci cikin comfort yasa ya fasa.

A hankali ya zauna ƙasa akan carpet ɗin, daga nan kuma ya kwanta ya jingina kansa a jikinta, hannunsa ɗaya na riƙe da nata.

A cikin bacci Zahra ta ɗan motsa tana maida hannunta cikin nasa tamkar tasan shi ne.

Wani lallausan murmushi ya suɓuce masa.

“Sleepy wife…”

AC ɗin parlorn na busawa a hankali yayin da hasken evening lamp ke bada wani irin calming atmosphere.

Gajiyar yini da sanyin wajen suka fara ɗaukar Ibrahim ma. Idanunsa suka fara rufewa a hankali yana jin ƙamshin turaren Zahra.

Kafin wani lokaci ma, bacci ya kwashe sa shima a wajen

Zahra na kwance saman kujera cikin natsuwa, Ibrahim kuma na kwance a jikinta akan carpet, hannayensu sarƙafe cikin na juna kamar wasu yara ƙanana da suka gaji da wasa.

Farida tana zaune a dakinta, gaba ɗaya ta mayar da hankalinta kan kallon TV. Sai kawai ta ji wayarta na vibration. Ta kalli inda wayar take, sannan ta kau da kai ta mayar da hankalinta kan TV ɗin kamar ba ta ji ba dan bata kaunar abun da zai hana ta kallonta

Amma da ta tuna wanda ke kira, sai ta mike da sauri ta je ta dauko wayar. Ta daga, ta kai kunne tare da sallama a hankali.

Magana take kasa-kasa take yi, ta fara sauraron abin da ake ce mata. Daga bisani ta ce, “Eh, toh gaskiya ban ga wani abu ba… kuma ai mijinta yana gida.”

Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ƙara da cewa, “Eh… wata mata ma ta zo.”

A hankali ta ce, “Kaiii… gaskiya ni dai ina tsoro.”

Bayan wanda ke kiran ya ƙara gaya mata wani abu, sai ta mike da sauri ta nufi kofar dakin. Ta bude a hankali tana leƙawa parlorn, sannan ta ja baya ta rufe kofar.

Ta ce, “Eh… yanzu dai na gansu, ita da shi duk suna bacci a parlorn su na kasa.”

Bayan ɗan lokaci ta sauke ajiyar zuciya. Sannan ta ce, “Toh zan gwada….”

A nan aka katse wayar.

Ta ajiye wayar, sannan ta koma ta zauna ta cigaba da kallon TV ɗin, amma zuciyarta ta riga ta shiga cikin tunani, rabi da kwata ba ta ma san abin da take kallo ba

Can da magriba ta yi, sai ga Ibrahim ya farka. Ya ɗan zauna yana kallon parlorn cikin nutsuwa, idanuwansa na bin ko’ina kamar yana duba yanayi. Daga bisani ya kalli agogo, sannan a hankali ya maida hankalinsa kan Zahra da ke zaune.

Ya matso kusa da ita a hankali, sannan ya fara tashinta.

Zahra ta motsa idanu tana budewa sannu a hankali, “Meke kamshi?” ta tambaya cikin kasala.

Ibrahim ya ɗan yi murmushi, ya nuna mata center table ɗin da ke gabansu.

Ta miƙa hannu ta ɗauka, ta fara buɗewa tana duba abin da ke ciki. Shi kuma ya miƙe, ya nufi hanyar sama, sai kuma ya juya yana kallonta da husky voice dinsa ya ce, “Better stand up… kar ayi sallah kina zaune.”

Zahra ta gyada kai da ɗan murmushi, idanuwanta har sannan a cike yake da bacci

Ganin ya juya kawai ta bude laidar ta fara cin abunta

Ibrahim ya tsaya daga sama ya kalleta ya sake cewa cikin taushi, “Please, pray first… sai ki zo ki ci.”

Wannan ya sa murmushi ya kubuce mata. Ta miƙe a hankali, ta nufi sama domin yin sallah.

Washegari da safe, bayan Ibrahim ya dawo daga masallacin asuba, gidan gaba daya ya cika da kamshin turare, one thing da yake son zahra akwai son tsafta da kamshi

Samunta yayi suka hadu tare suka yi breakfast Zahra ta yi serving cikin so da kulawa, ta zuba tea mai ɗumi a cups, ta shirya bread da eggs a plate, sannan ta ƙara fruit a plate, ta dauko burger ta ajiye shima

Ibrahim kuwa yana zaune yana kallonta, murmushi a fuska, yana jin dadin yadda take tafiyar da komai ba tare da hayaniya ba.

Suka fara breakfast dinsu cikin so, Ibrahim ya ɗaga kai ya kalli Zahra ya ce, “Idan mun dawo yau, zamu je mu gaida Mama.”

Zahra ta amsa cikin ladabi, “Allah ya kaimu.”

Sannan ta ƙara da murmushi, “Ko lectures ɗin yamma aka sa yau zan dawo, ba zan wani tsaya ba”

Ibrahim ya kalle ta kai tsaye, “No, babu ruwa na.”

Ta yi dariya

Ya sake tambaya cikin wasa, “Ya baki ci?”

Ta ce, “Awara nake so. Zan bari idan na shiga school sai na saya.”

Ya gyada kai, “Alright.”

Bayan sun gama, suka tattara komai suka haura sama domin yin wanka.

Daga baya suka sake saukowa ƙasa cikin shiri. Dukansu sun shirya tsaf, kowa cikin shirin fita, keys din ya dauko musu, ya mika mata nata

Suna fita compound already an wanke musu motocinsu, ko wanne ya karasa wajen motarsa, a haka suka bar gidan.

A gaban department ɗinsu Zahra ta yi parking motarta. Ta zauna a ciki na ɗan lokaci kamar ba zata sauka ba. Idanuwanta a lumshe, zuciyarta cike da nauyin abubuwan da ke mata yawo a kai.

Daga ƙarshe ta sauke ajiyar zuciya, ta buɗe motar ta sauka.

Class ɗin ta wuce kai tsaye. Bayan sun kammala lectures na ƙarfe 12, bata ji tana da ƙarfin zama a makarantar ba. Duk maganganun da ta yi da ita sun tsaya mata a rai, suna mata nauyi fiye da yadda ta zata.

A hanya zuwa gida, ta tsaya a wani lungu ta sauka daga mota.

Ta shiga cikin karamin unguwa inda akwai mutane zaune a waje. Da ta shigo, duk da cewa ta saka face mask, hakan bai hana tsohuwa dake zaune a baranda gane ta ba.

Nan take fuskarta ta haska da murmushi mai kyau.

“Zahra!” tsohuwar ta kira cikin murna.

Zahra ta ɗan yi murmushi ta ƙarasa kusa da su, ta gaishe su cikin ladabi. Tsohuwar ta amsa da fara’a tana kallonta da kauna.

A gefe kuwa wata budurwar matashiya ce ta fito daga cikin gida, tana ganin Zahra sai ta saki murmushi mai faɗi har da nuna farin ciki sosai. Ta yi saurin ƙaraso ta tsaya kusa da ita tana kallonta kamar wacce ta dade bata ganta ba.

“Hajiya Fatima ke ce?” ta ce cikin murna.

Zahra ta ɗan yi dariya a hankali, tana gyara face mask dinta da kyau dan bata so ya sauka aga fuskanta

“Eh, na dawo,” ta amsa cikin nutsuwa.

Wannan tsohuwa ta ɗaga hannu tana murmushi, ta c

“Kiyi hakuri nasan ba kinga sakon mu mun kuma dago ki”

Zahra ta ɗan sunkuyar da kai cikin kunya. “Kar ki damu Mama”

Matashiyar matar tace ki zauna mana kar ki gaji da tsayuwar, murmushi kawai zahra tayi

Matashiyar matar ta ƙaraso kusa da Zahra tana murmushi ta shimfida mata sallaya ta ce

“Sannu anty Zahra, ki dan zauna kar kafar ki ya gaji”

Wani ƙaramin yaro ne daya shigo daga waje ya yi saurin nufar Zahra da gudu kamar zai rungumeta, mahaifiyarsa ta yi saurin riƙe shi.

“Kar ka bata mata jiki mana,” tace cikin lallashi.

Zahra kuwa dariya kawai tayi tana kallon yaron. “A’a kyale shi mana.”

Sai kuma ta kalli matar tace, “Ina sauran? Suna zuwa makaranta kuwa?”

“Eh,” matar ta amsa. “Duk suna school yanzu.”

Kai Zahra ta gyada a hankali. Daga handbag ɗinta ta ciro envelopes guda biyu ta ajiye musu.

Matashiyar matar ta zaro ido. “Anty Zahra wannan kuma….”

Amma kafin ta ƙarasa magana, Zahra ta ɗaga mata hannu alamar tayi shiru , ajiye musu tayi

Daga haka ta juya zata fita ba tare data jira godiya ko surutu ba.

A wajen motarta kuma wasu yara ne suke wasa kusa da titi. Ta kira su.

“Kuzo nan.”

Da gudu suka taho wajen motar.

Ta buɗe booth ɗin motar, wanda ke cike da ledojin kayan abinci da wasu kayayyaki.

“Ku kwashe ku kai ciki.”

“Toh anty!” suka amsa cikin murna.

Nan take suka fara ɗaukar kayan suna kaiwa cikin gidan, kowanne na son ya nuna ƙoƙari.

Zahra ta tsaya tana kallonsu na ɗan lokaci. Wani irin nutsuwa ne ya ratsa ta ganin farin cikin da abu kaɗan ya saka musu.

Bayan ta tabbatar sun gama shiga da kayan, ta shiga mota ta tada ta nufi gida.

A parlorn sama ta tarar da Ibrahim zaune a kujera, laptop ɗinsa a gabansa yana aiki a system ɗinsa. Glasses ɗin idonsa ya ɗan sauko ƙasa kaɗan yayin da hankalinsa ke kan screen.

Ko kallonta bai yi da farko ba sai bayan ya ji motsinta.

“Kin dawo?”

“Hmm,” kawai ta amsa tana cire hijab ɗinta.

Ya ɗan kalleta. “Ya lectures?”

“Ba dadi ga masu karamin ciki irina” dariya dukkansu suka yi

Sai ya lura da gajiyar dake tattare a fuskarta.

“Kin ci wani abu kuwa?”

Kai ta girgiza masa. “Ban jin yunwa.”

Laptop ɗin ya rufe a hankali sannan ya miƙe.

“Zahra…”

Ta ɗago tana kallonsa.

“Come here.”

Ta tsaya tana kallonsa na ɗan lokaci kamar mai tunani, kafin daga ƙarshe ta ƙarasa kusa da shi a hankali.

Tana isa, sai ya jawota jikinsa ya rungume ta.

“Kin gaji sosai ko?” ya tambaya cikin ƙasa da murya.

Zahra ta lumshe idanunta na ɗan daƙiƙa kaɗan. Duk da tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta, zuciyarta tana son irin wannan kulawar tasa.

A hankali tace, “Ka daina bani mixed feelings Ibrahim…”

Ya ɗan ja baya yana kallonta. “Me yasa?”

“Saboda duk lokacin da nace na tabbatar Kai din nawa ne sai daga baya ka nuna min wani gefenka”

Wani ƙaramin murmushi yayi kafin ya shafa kumatunta a hankali.

“Zahra mun Riga da mun wuce wancan stage din already, ki daina kawo abun daya riga ya wuce”

“Yanzu tashi mu shirya,” Ibrahim yace yana kallonta. “Na faɗawa Mama cewa muna hanya.”

Dariya Zahra tayi tana girgiza kai. “Ni fa jiya jin ka kawai nayi. Amma taya zamu je gidan Mama hannu sake? At least bari nayi girki mana.”

Ibrahim ya ɗan lumshe ido yana kallonta da wani irin so. “Kin cika raina da soyayyar ki zahra”

“Me kuma?”

“Saboda duk da abubuwan daya faru… har yanzu kina ƙoƙarin kasancewa matar aure ta gari.”

“Is okayyy” ta ce

Ko ɗakinta bata shiga ba, kai tsaye ta sauka ƙasa.

kitchen ta nufa, tana tunanin abincin da zata haɗa musu. Jim kaɗan sai taji knocking a ƙofar kitchen ɗin.

Farida ce ta buɗe ƙofar tana gaidata cikin ladabi.

“Ina wuni Hajiya.”

“Lafiya lau,” Zahra ta amsa tana murmushi. “Ke kam ko gajiya da zaman ɗaki baki yi ne?”

Farida dariya kawai tayi.

“Toh fito ki tayani dafa abinci. Zamu kai gidan surkai ne.”

“Toh Hajiya.”

Zahra ta ce “Bari na ɗan huta kadan, sannan nazo mu haɗa hannu”

“Toh… amma me zan dafa?” Farida ta tambaya

“Komai ma ki dafa. Duk abin da ya dace da gidan surkai.”

Farida ta gyada kai cikin sauri. “Toh shikenan.”

Daga haka Zahra ta bar kitchen ɗin ta haura sama.

Ko data shiga parlorn bata ga Ibrahim ba. Nan take ta fahimci ya shiga ɗakinsa ne saboda waya ko wani aiki.

Ita kuma nata ɗakin ta nufa kai tsaye domin ta ɗan huta.

Tana shiga ta kwanta akan gadonta, sai ta lumshe idanunta ta fada duniyar tunani

Har ga Allah tana son mijinta fiye da zaton mai zata,

Tana tuna yadda yake kallonta jiya da daddare. Yadda ya riƙe hannunta. Yadda yake ƙoƙarin lallashinta ko da bai iya furta nadamarsa yadda ya kamata ba.

Wani ƙaramin murmushi ya suɓuce mata.

A hankali ta rungume pillow ɗinta tana kallon ceiling.

“Allah…” ta furta ƙasa-ƙasa.

Saboda ita kanta ta fara jin tsoron yadda take ƙara son mijinta har cikin ranta

Afuwan da Jina shiru kwana biyu, na rasa wayata sai jiya na sayi wani, Nagode.