Kenza eBookz
Cover art for FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 15

Post

FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 15

.....finish for us," Firdausi said, putting her hands together. "When I saw you, I said let me come and collect Aunty Bride." "I don't want to be provoked by God," Zahra said, shaking her head. "No..." Firdausi said, holding her mouth as if she had been wronged. "What did I do?" Then she came closer to her, lowering her voice. "I didn't think you would come to school today. "Firdausi..." Zahra called her name in a warning tone. "Check the comments section for us..." "Enough Firdausi!" Firdausi quickly swallowed her laughter but still wanted to smile. "But like seriously..." she said looking at Zahra from top to bottom, "you fine die." You really raised my head." Zahra went straight ahead and left behind. "Arrey stop for us!" Firdausi said she was quickly following her. As they entered the lecture hall, Zahra noticed that many eyes followed her. Some clicks are watching her smiling, and some are whispering to each other. Even some dudes were looking at her but she didn't show any attention at all. She went directly to their seat and sat down, taking out her notebook. Firdausi was sitting next to her and smiling evilly. "By God, they all know that a celebrity has come in." Zahra didn

Standalone post2,257 words

*FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes

Young talented writers association (YOTA)

Book 1 Chapter 16

Idanunta suka buɗe sosai cikin mamaki. Zooming hoton tayi tana kallonshi da kyau, kamar zata tabbatar ba mafarki take ba.

Sai kuma wani irin dariya ya kwace mata lokaci guda da kunya.

Ta rasa dalilin da yasa Ibrahim kullum idan suka ɗauki hoto sai ya saka a media. Yanzu ga shi har Ya Umar ya ɗauka ya saka a status ɗinsa ma.

Da sauri ta kashe data ta fita daga WhatsApp ɗin tamkar yana kallonta kai tsaye. A ranta ta tabbatar tunda ya ga wannan ma, definitely ya ga wanda ita da Ibrahim yake kissing forehead ɗinta.

“Ya salam...” ta faɗa tana dafe goshinta cikin kunya.

AC ɗin motar ma kashewa tayi sannan ta buɗe ƙofar zata fita.

Dai-dai lokacin taji muryar Firdausi daga bayanta tana dariya.

“Amarya...”

Zahra ta tsaya cak.

A ranta tace,

“Yau nikam na shiga uku...”

Karasowa Firdausi tayi tana kallonta da wani irin murmushi mai cike da tsokana.

Zahra ta ɗan bata fuska tana gyara handbag ɗinta.

“Mu ƙarasa mana,” Firdausi tace tana haɗa hannuwanta. “Dama ganin ki nayi nace bari in zo na tara Anty Amarya.”

“Bana son tsokana wallahi,” Zahra ta faɗa tana harararta.

“Laaa...” Firdausi tace tana riƙe baki kamar wacce aka zalunta. “Me nayi kuma?”

Sai kuma ta matso kusa da ita tana rage murya.

“Ni fa ban ɗauka yau zaki zo school ba. Dan jiya media ya ɗauki wuta”

“Firdausi...” Zahra ta kira sunanta cikin warning tone.

“Ki duba comments section mana....”

“Enough Firdausi!”

Da sauri Firdausi ta haɗiye dariyarta amma har yanzu murmushi ke son ƙwace mata.

“But like seriously...” ta faɗa tana kallon Zahra daga sama har ƙasa, “you fine die. Gaskiya kun tashe kai na.”

Kai tsaye Zahra tayi gaba ta barta a baya.

“Arrey tsaya mana!” Firdausi tace tana saurin bin bayanta.

Suna shiga lecture hall ɗin, Zahra ta lura da yadda idanu da yawa suka biyo ta. Wasu click na kallonta suna murmushi, wasu kuma na raɗa-raɗi tsakaninsu. Har wasu dudes ma sai kallonta suke yi

Amma ko kaɗan bata nuna ta kula ba. Kai tsaye ta wuce seat ɗinsu ta zauna tana fiddo notebook ɗinta.

Firdausi kuwa tana zaune kusa da ita tana murmushin mugunta.

“Wallahi duk sun gane celebrity ta shigo.”

Zahra bata ko kalleta ba.

“Please keep quiet.”

Ana haka Asiya da sauran friends ɗinsu suka shigo.

Asiya na ganin Zahra ta zaro ido.

“Kaiii Amarya!”

“Ke ma don Allah...” Zahra tace tana dafe kanta.

Asiya ta zauna kusa da ita tana dariya.

“Wallahi jiya kun yi kyau sosai. Har Mom dina sai data tambayeni wai wannan ba kawarki bace?”

Firdausi ta fashe da dariya.

“Nifa nace muku media ya ɗauki wuta.”

Zahra ta rufe fuskarta da notebook.

“Allah yasa lecturer ya shigo yanzu.”

Kamar maganar ta yake jira, lecturer ɗin ya shigo hall ɗin, nan take kowa yayi shiru aka fara lecture.

Bayan first lecture ɗin, sun fito gaba ɗaya cikin gajiya.

“Asiya wallahi yunwa nake ji,” Firdausi tace tana gyara hijabinta.

“Mu je cafeteria mana bayan sallah,” Asiya ta bata amsa.

Duk suka yarda sannan suka nufi masallaci.

Bayan sun idar da sallah, suka wuce cafeteria ɗin school. Wajen cike yake da students, hayaniya na tashi ta ko’ina.

Suka samu wani table a gefe suka zauna.

“Me zaku ci?” Asiya ta tambaya.

“Nifa rice zan ci,” Firdausi tace da sauri.

“Ke kullum rice,” Zahra ta faɗa tana ɗan murmushi.

“To meye matsala idan ina da loyalty ga rice?”

Duk suka yi dariya.

Zahra ta ɗauki shawarma da yoghurt yayin da Asiya ta siyo noodles.

Suna cin abincin, hirarsu ta koma kan school gist da assignments. Amma duk bayan wasu mintuna sai Firdausi ta dawo kan maganar hotunan Zahra da Ibrahim.

“Wallahi yadda yake kallonki a pics ɗin nan...”

“Firdausi!”

“Okay okay na yi shiru.”

Asiya ta kwashe da dariya.

“Amma gaskiya Ibrahim na sonki, ki jira Suhaima ta zo gobe kin shiga uku ai”

A hankali murmushi ya bayyana a fuskar Zahra kafin ta sunkuyar da kanta tana haɗa yoghurt ɗinta.

Bayan sun gama, suka ɗan zauna suna hutawa kafin aka fara second lecture.

Har zuwa lokacin tashin su, Zahra bata sake shiga social media ba saboda yadda take jin kunya duk sanda ta tuna status ɗin Ya Umar.

Da aka tashi, suka fito tare suna tafiya a hankali cikin compound ɗin school. Rana ta fara lafa kaɗan yayin da students ke fita groups-groups.

“Ashe yau ma driver ɗinki baizo ba?” Firdausi ta tambaya.

“Motata nazo da ita mana.”

“Ohooo rich aunty.”

Zahra ta girgiza kai tana dariya kaɗan.

Kafin su rabu, Asiya tace, “Ki gaida mana Mr Romantic.”

Zahra ta cije lips ɗinta tana jin kunya.

“Ku bari mana...”

Firdausi tace, “Ki gaya masa next time ya rage posting mana, kin kusa zama Layla celebrity.”

Duk suka fashe da dariya yayin da Zahra ta shiga motarta tana girgiza kai a kunyace.

Zahra na shirin kulle motarta kenan Firdausi tace,

“Please bari kiyi dropping ɗina a hanya kawai. Na fasa zaman school yau.”

Wani kallo Zahra ta mata kafin tace, “Shiga mana.”

Jiran ta tayi har sai da Firdausi ta shiga sannan ta kulle motar suka kama hanya.

Tun daga fitarsu gate ɗin school, Zahra tayi shiru tana driving cikin nutsuwa. A fili yake bata buƙatar wata doguwar hira.

Firdausi ta ɗan sace kallonta kafin tace,

“Amma Zahra... nayi murnar ganin Ibrahim ya canza.”

A hankali Zahra ta sauke numfashi.

“Toh Allah yasa. Dan haka ya faɗa kuma ni ma na fara ganin alamu.”

Firdausi ta gyada kai tana murmushi.

“Allah ya ƙara muku fahimta da zaman lafiya.”

“Ameen oo,” Zahra ta amsa cikin sanyin murya.

A haka suka cigaba da hira kaɗan-kaɗan har ta kai Firdausi inda zata sauka. Bayan ta sauke ta, Zahra ta juya ta kama hanyar gida.

To her surprise, tana shiga compound ɗin gidan idanunta suka sauka akan motar Ibrahim a parke.

Ta ɗan tsaya tana kallon motar kamar wacce bata yarda da abinda take gani ba. Bata ma tuna yaushe rabon data dawo gida ta same shi a gida da wuri haka.

A hankali murmushi ya bayyana a fuskarta kafin tayi parking ta sauka daga motar.

Kai tsaye ciki ta wuce.

Daga kitchen taji motsin wanke-wanke, hakan yasa ta leƙa. Farida ce ke gyara wajen cikin sauri.

Da ganin Zahra, da sauri ta juya tana murmushi.

“Sannu da zuwa Hajiya.”

“Yauwa Farida, ya aiki?”

“Alhamdulillah. Oga ma ya dawo.”

Kai ta gyada kawai tana murmushi kaɗan kafin ta juya ta nufi sama.

A parlorn saman ta same shi zaune yana kallon ball. A gabansa akwai plate ɗin abinci, sai snacks da drinks a side stool.

Bata san sanda murmushi ya subuce mata ba.

Yana ɗago kai ya ganta, nan take fuskarsa ta sauya zuwa murmushi.

“Welcome back wife.”

Sai ya kashe TV volume ɗin kaɗan yana kallonta sosai.

“Daga gani dai mutanen nan suna baki wahala.”

Karasowa tayi a hankali ta faɗa jikinsa ta kwantar da kanta a kafaɗarsa tare da sauke numfashi kamar wanda yayi trekking mai nisa.

“Kai dai ka bari...”

Hannunsa ya zagayo bayanta ya rungumota.

“Lectures sosai ko?” ya ce

“Fafa muke sha saboda final semester.”

“Sorry Zahratyy...”

Murmushi tayi tana ɗago kai kaɗan.

“Thank you Noory.”

Daga nan ta miƙe daga jikinsa.

“Bari na watsa ruwa.”

“Abincin fa?”

Kai ta girgiza.

“Bana jin cin abinci. Gwara ma nasha tea ko cornflakes.”

“Okay.”

Ta wuce ɗaki ta shiga toilet.

Bayan tayi wanka ta fito cikin wani fitted English wear mai kyau sosai. Kayan sun zauna a jikinta ta yadda suka fito da shape ɗinta cikin tsari mai kyau. Ƙamshinta ya cika ɗakin.

Tana fitowa parlorn, Ibrahim dake ɗaga plate ɗin abincinsa ya tsaya kallonta.

Wani lallausan murmushi ya saki yana bin ta da ido har ta ƙaraso kusa dashi.

Kai tsaye ta ƙarasa ta faɗa jikinsa.

Ya rungumeta yana shafa bayanta.

“Ya baby na toh?”

Ta ɗan bata rai tana ɗaga kai ta kalleshi.

“Kaza yake son ci.”

Dariya yayi.

“Dole kuwa naje na nemo masa.”

Sai ya ɗan matsa yana gyara mata zama a jikinsa.

Amma kafin ma ya ƙara magana, rufe idanunta keda wuya bacci ya fara ɗaukarta. Numfashinta ya fara sauyawa alamun tayi nisa cikin bacci.

Ibrahim ya sauke ido yana kallonta cikin tausayi da so.

“A tired baby...” ya furta a hankali.

A tausashe ya gyara mata kwanciyarta sosai a jikinsa, ya janyo hijab ya rufe mata ƙafafu sannan ya kashe TV ɗin gaba ɗaya domin kada hayaniya ta tasheta.

Daga nan ya jingina da kujera yana ci gaba da kallonta, yatsunsa na yawo a hankali cikin gashinta yayin da ita kuma take bacci lafiya a jikinsa.

Can wajajen magrib, Ibrahim ya ɗan sunkuyar da kansa kusa da fuskarta yana hura mata iskan bakinsa a hankali tare da shafa gefen fuskarta cikin tausasawa.

A hankali ta buɗe idanunta.

Murmushi ya sakar mata yace, “Tashi, mai ciki, magrib yayi.”

Har zata sake rufe idanunta cikin kasala, jin yace magrib yayi yasa ta buɗe su sosai cikin mamaki.

“Magrib?”

Kai ya gyada mata yana dariya yace

“Eh mana. Kin sha bacci sosai.”

Da sauri ta miƙe ta zauna tana gyara gashinta.

“Ban san har haka nayi bacci ba.”

Shi kuma ya miƙe daga kujerar.

“Bari nayi alwala na tafi masallaci.”

Daga haka ya wuce ɗakinsa, ita ma ta miƙe ta nufi nata ɗakin domin alwala da sallah.

Washegari da misalin ƙarfe ɗaya na rana, Zahra na kitchen tare da Farida suna girki. Ita ce ke guiding ɗinta lokaci zuwa lokaci saboda tana son komai ya kammala kafin ƙarfe biyu.

Ƙamshin girkin ya cika kitchen ɗin gaba ɗaya.

Da taga komai ya kusa kammala, sai tace,

“Farida idan ya nuna ya gama sai ki kwashe ki zuba a warmer nan. Daga nan ki kai dining, sannan ki fito min da zobon dake fridge ki kai shi ma.”

“Toh shikenan Hajiya,” Farida ta amsa cikin girmamawa.

Zahra ta gyada kai sannan ta fita daga kitchen ɗin ta wuce sama.

Wanka ta shiga tayi. Bayan ta fito ta shafa mai sannan ta saka wani fitted gown mai bala’in kyau. Kayan sun zauna a jikinta tamkar an zana su.

Ta yi daurin ture kaga tsiya, sannan ta feshe jikinta da turare masu sanyin ƙamshi.

Tana gyara mirror taji an buɗe gate ɗin gidan. Da sauri ta leƙa ta window taga Ibrahim ne ya shigo da motarsa.

Wani murmushi mai sanyi ya bayyana a fuskarta kafin ta sake labulen.

Can ba’a jima ba sai gashi ya hauro sama.

Da jin takunsa, ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito.

Yana dai-dai dosar ƙofar suka haɗu.

Karasowa tayi ta karɓi jakkarsa tana murmushi.

“Sannu da zuwa mijina.”

Ya kalleta daga sama har ƙasa kafin murmushi ya suɓuce masa.

“Yauwa matata.”

Hannunsa ta kama tana jansa ciki.

“Ka shiga kayi wanka, na saka maka ruwan wanka. Idan ka fito kuma sai muje muyi lunch.”

“Alright Zahratyy na.”

Daga haka ya wuce toilet, ita kuma ta fito masa da kayan da zai saka ta aje saman gado sannan ta zauna tana jiransa.

Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet ɗin cikin fresh look, yana goge gashinsa da towel. Kayan da ta fito masa dasu ya saka, ƙamshin sabulunsa na gaurayawa da nata turaren.

Bayan ya gama saka kayan, idanunsa suka sauka akanta.

“Kin yi kyau sosai yau.”

Murmushi tayi tana ɗan sunkuyar da kanta.

“Thank you.”

Sai ya ƙaraso kusa da ita ya ɗan taɓa haɓarta.

“Very beautiful wife.”

Daga haka suka sauka ƙasa tare zuwa dining area.

Dining table ɗin ya cika da abinci kala-kala da suka girka. Zobo mai sanyi na gefe sai kamshi ke tashi

“Wow...” Ibrahim ya faɗa yana kallon abincin. “Da alama yau akwai special treatment.”

“Maybe,” tace tana murmushi.

Zama sukayi suka fara lunch ɗin.

Lokaci zuwa lokaci Ibrahim na debo mata abinci yana bata a baki, ita ma tana mayar masa. Dariya da hira mai daɗi ne a tsakanin su.

“Open your mouth,” ya faɗa yana miƙa mata spoon.

Ta buɗe baki tana dariya

“Good girl.” ya ce

Ita ma ta debo masa chicken tana cewa, “Yau kai ne patient dina.”

“Idan ke ce nurse ɗin, zan yarda.”

Duk suka yi dariya.

Bayan sun gama cin abincin, Zahra ta kwanta a jikinsa akan parlorn chair tana hutawa yayin da yake shafa hannunta.

Can kuma sai ta ji wani irin tashin zuciya.

Nan take ta tashi kaɗan tana dafe ƙirji.

Kallonta yayi cikin damuwa.

“Lafiya?”

“Amai nake ji...”

Nan take ya fara shafa bayanta a hankali.

“Sannu... maybe abincin ne.”

Kafin su ƙara magana aka buɗe ƙofar parlorn aka shigo ciki.

Duk tunaninsu Farida ce, saboda haka babu wanda ya juya. Ibrahim duk hankalinsa yana kan Zahra ne.

Sai dai da Zahra ta ɗago kai, idanunta suka haɗu da Mummy.

Da sauri ta miƙe ta ja kujera baya sannan ta nufi toilet a guje.

“Mummy...” Ibrahim ya faɗa cikin mamaki yana miƙewa.

Mummy ta ƙaraso parlorn ɗin da sallama a bakinta.

“Wa alaikum salam,” ya amsa cikin girmamawa kafin yayi saurin bin bayan Zahra.

A toilet ya same ta tana amai.

“Sannu baby...” yake ta faɗa yana riƙe mata baya.

Bayan ta gama, ya buɗe ruwa ya wanke mata fuskarta cikin kulawa sannan ya gyara wajen kafin ya fito da ita.

A parlorn ta zauna tana maida numfashi.

Mummy kuwa sai sannu take mata.

“Sannu daughter... meke damunki ne?”

Zahra ta ɗan gyara zama.

“Ina wuni Mummy.”

“Lafiya lau,” Mummy ta amsa. “Sannu. Dama daga aiki na taso nazo na dubaki. Ashe baki gama warkewa ba.”

Murmushi kawai Zahra tayi cikin sanyin jiki.

A lokacin Ibrahim ya fito daga toilet ya ƙaraso parlorn.

#Jiddatulkhayr writes #08110615256