
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 14
..... is he?" Mummy said in a neutral tone. As she finished speaking, she turned towards the upper stairs. Mami just watched. After disappearing from her sight, she shook her head slowly, feeling something in her heart. She herself knows that there are things that are happening that shouldn't be happening, but she doesn't want things to get worse. She slowly got up and went to her upper room, her heart full of various thoughts. **** She stood up from the carpet and folded it slowly. At the same time, Ibrahim entered the room, he had just returned from the mosque. He looked at her for a while before he came close to her and took off her hijab calmly. She went back to the bed and sat down. She took her phone and pressed it without looking at him. He also sat next to her and said, "Zahra, get ready, we will go out now." Without looking up, she said, "I have nowhere to go." I also want to sleep." "Zahra, I'm telling you what to do. Are you telling me?" She looked at him and said, "Yes, I have the right to say that, since I am the one who will go out and I will not go." He was just looking at her, and she turned away and focused on her mobile phone. He grabbed her hand slowly and said,
*FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes
Young talented writers association (YOTA)
Book 1 Chapter 14
Mami na zaune a parlorn tana kallon tv lokacin da taji an buɗe gate. A take ta tuna cewa Mummy bata gidan lokacin da aka maida Zahra, kuma tasan idan taji komai zai iya zama wata magana.
Da sauri ta miƙe ta sauka ƙasa domin tararta kafin ta shigo.
Sai dai tana isa parlorn, tuni Mummy ta shigo ciki. Bayan sun gaisa ne Mami tace cikin son kaucewa wata magana,
“Ai baki san mene ba… yarinyar nan dai ta koma ɗakinta.”
Mummy ta ɗan tsaya tana kallonta.
“Mijinta yace Mamarsa tayi faɗan wai a barta tayi laulayin a ɗakinta, shine yazo ya tafi da matarsa.”
Wani irin dariya Mummy tayi, mai cike da ma’ana.
“Lallai ma,” tace. “Ai nasha faɗa da kun nuna mata matsayina tun farko ai da bata yi kan kanta ba. Da zata jira Ni har sai nazo, ko da safe ta faɗa min kafin na fita.”
Mami ta ɗan gyara zamanta tace, “Ai Yayanta ne ma ya kai ta, ganin baki nan, ba haka nan ta tafi ba.”
“Dama yayan nata baku shanye shi bane?” Mummy tace da ɗan tsaki.
Tana gama maganar ta juya ta nufi stairs ɗin sama.
Mami ta bita da kallo kawai. Bayan ta ɓace daga ganin ta, sai ta girgiza kai a hankali tana jin wani iri a zuciyarta.
Ita kanta tasan akwai abubuwan da suke faruwa da basu kamata ba, amma duk da haka bata son abubuwa su ƙara lalacewa
A hankali ta miƙe itama ta wuce ɗakinta na sama, zuciyarta cike da tunani iri-iri.
****
Miƙewa tayi daga kan dardumar ta ninke ta a hankali. A daidai lokacin ne Ibrahim ya shigo ɗakin, daga gani ya dawo ne daga masallaci. Kallonta yayi na ɗan lokaci kafin ya ƙaraso kusa da ita ya zare hijabin jikinta cikin sanyin jiki
Komawa tayi bakin gado ta zauna, ta ɗauki wayarta tana danna wa ba tare da ta kalleshi ba. Shima ya zauna kusa da ita yace,
“Zahra ki shirya, zamu fita yanzu.”
Ba tare data ɗago ba tace, “Babu inda zan tafi. Bacci ma nake son yi.”
“Zahra ina faɗa miki abinda zakiyi kina ce min no?”
Ta ɗago tana kallonsa tace, “Yes, ai ina da right ɗin faɗar hakan, tunda nine zan fita kuma banji zan je ba.”
Kallonta kawai yake yi, ita kuma ta kauda kanta ta mayar da hankali kan wayar hannunta.
Hannunta ya kamo a hankali yace,
“Zahra...”
Sai ta ɗago idanunta ta kalleshi ba tare data ce komai ba.
“Are you still angry with me?”
Wani ɗan murmushi mai ciwo tayi ta kashe wayar hannunta ta ajiye.
“Tambayata kake yi? Ibrahim anya kasan wani abu wai shi kunya? Just imagine... idan nice na maka irin wannan ƙaryar, bana tunanin ma zan iya sake haɗa ido da kai.”
Ta ɗan yi shiru kafin ta cigaba.
“Kasan yadda nake a media, kasan yadda bikinmu yayi trending. Amma har zaka fara cheating tun yanzu? Kana tunanin ba za’a samu wasu su ɗauka su yaɗa a duniya ba?”
Hargitsa gashin kansa yayi yana furzar da iska daga bakinsa.
“Please Zahra, komai ya wuce mana.”
Kai ta girgiza.
“Ibrahim baka yi kama da mijin da yake nadama ba. Sau nawa baka zama a gidan nan idan nayi magana ba shi zai sa ka canza ba? Bikinmu ko sati ɗaya bai yi ba amma ka canza. Yaushe rabon da muka kwana tare cikin farin ciki da soyayya? Ashe mata kake bi...”
Tsawa ya daka mata.
“Kar ki sake cewa ina bin mata Zahra! I hate those words.”
Dariya tayi mai ɗaci.
“You will never change Ibrahim. Ka dake Ni kawai.”
Wani numfashi mai nauyi ya sauke yana kallon gefe.
Ta cigaba cikin sanyin murya, “Think well please… kana sauke hakkokina dake kanka?”
Shiru yayi.
“Na dawo gidan nan ne ba wai dan soyayyar da nake maka ta farko ba. Na dawo ne saboda bana son Abbah ya sani tun yanzu ya ɗauki mataki. Kuma dukkanmu ba zamu ji daɗi ba. Ka riga ka nuna wa Yayana halinka tun kafin ya gama yarda da kai. Firdausi ma ka nuna mata halinka, gashi kuma tare muka kama ka da ita.”
Idanunta suka cika da ƙwalla.
“Gaskiya bazan iya rayuwa cikin wannan takaicin ba. Tun kafin ka kashe ni da bakin ciki, idan baka canza ba zan bar maka gidanka. Saboda yanzu naga baka sona…”
Mikewa yayi da sauri yace,
“Enough Zahra! Ban ce bana son ki ba. Idan kuma zaki cigaba da sauraron masu zugaki, ba zaki taɓa ganin son da nake miki ba.”
Ta ɗan yi murmushi mai ciwo tace, “Fine.”
Har ya juya zai fita sai kuma ya tsaya ya juyo.
“Ki shirya. Zamu fita dinner.”
Sai ta miƙe daga kan gadon tana gyara ɗankwalinta tace,
“Alright.”
****
Bayan kusan rabin awa, Zahra ta fito cikin wata doguwar riga mai launin royal blue da ɗan ƙaramin farko blue veil, ƙamshinta na tashi a hankali. Ibrahim dake jingine da motarsa a compound ya ɗago yana kallonta, na ɗan lokaci ya manta komai.
Karasowa tayi ba tare data ce komai ba, ya buɗe mata motar cikin gentlemanly manner, ita kuma ta shiga. Shima ya zagaya ya shiga ya kunna motar.
A hanya babu wanda yayi magana sosai, sai dai lokaci zuwa lokaci Ibrahim na satar kallonta. Ita kuma tana kallon window kamar bata lura ba.
Bayan mintuna kaɗan suka ƙarasa wani babban wajen shakatawa mai cike da haske da flowers masu kyau. Couples ne sosai a wajen, wasu na ɗaukar hoto, wasu kuma na cin abinci cikin nishadi.
Da suka shiga, waiter ya kai su wani table na gefe kusa da glass wall ɗin wajen, daga nan ana hangen city lights masu kyau.
Zama sukayi.
“What would you like to eat?” Ibrahim ya tambaya cikin nutsuwa.
Menu ta karɓa tana dubawa, daga ƙarshe tace, “Grilled chicken da fried rice… sai mocktail.”
Shi kuma yace, “I’ll go with seafood pasta.”
Bayan an kawo musu abincin, shiru ne ya ɗan ratsa tsakaninsu kafin Ibrahim ya ɗauki spoon ya debo rice ya miƙa mata.
Da farko kallonsa tayi kawai, sai kuma ta buɗe baki a hankali ta karɓa.
Murmushi yayi karon farko cikin dare ɗin.
“Good girl.”
Ita ma spoon ta ɗauka ta debo pasta ta miƙa masa.
“Kar ka ce ni kaɗai ake feeding.”
Dariya yayi ya karɓa daga hannunta.
A hankali yanayin tsakaninsu ya fara sauyawa. Ibrahim na bata labarai masu dariya har tana dariya tana dan bugun kafaɗarsa lokaci zuwa lokaci.
Daga baya suka fita garden area na wajen. Hasken fitilu masu laushi na sauka a jikinsu yayin da iska ke kaɗa veil ɗin Zahra.
Ibrahim ya jawo ta kusa dashi yace,
“Smile mana ko sau ɗaya ne”
Sai ta ɗan turo baki.
“Ban so.”
“Please…” ya ce
A ƙarshe murmushi tayi, nan ya fito da wayarsa suka fara ɗaukar hotuna tare. Wani yana riƙe da hannunta, wani kuma ya rungumota daga baya yayin da ita ke dariya.
Har wani couple photographer na wajen ya zo ya ɗaukar musu wasu hotuna masu kyau sosai a ƙarƙashin flowers da lights ɗin wajen.
Bayan sun gama, Ibrahim ya riƙe hannunta suna tafiya a hankali.
Cikin sanyin murya yace, “Wallahi bana son wannan rashin fahimtar tsakaninmu Zahra.”
Ta ɗago tana kallonsa.
“Then stop hurting me.”
Tsayawa yayi cak, ya kamo hannunta ya sumbaci bayan hannun nata.
“I’ll try…”
Kallonsa tayi na wasu seconds kafin ta ɗan jingina da kafaɗarsa a hankali, shi kuma murmushi yayi yana ƙara matse hannunta cikin nasa.
Dare ya fara nisa sosai kafin suka bar wajen. Tun daga parking lot ɗin har cikin mota, yanayin tsakaninsu ya ɗan sauya, ba kamar yadda suka fita daga gida ba
Zahra na zaune tana kallon hotunan da suka ɗauka a wayarta, wani ɗan murmushi na bayyana a fuskarta lokaci zuwa lokaci. Ibrahim kuwa yana driving amma idanunsa na satar kallonta
“Wannan hoton yayi kyau sosai,” Ibrahim yace yana nuna wani da ta jingina da kafaɗarsa.
Ta ɗan murmusa tace, “Kai dai duk naka ne yafi kyau”
“Saboda matar tawa ce a ciki.”
Sai ta girgiza kai tana ɓoye murmushinta
Da suka isa gida, Ibrahim ya parking motar sannan ya zagayo ya buɗe mata ƙofa. Hannunta ya kama yayin da suke shiga ciki tare. Gidan shiru yake, da alamu na farida ta daɗe da bacci
Da suka shiga ɗaki, Zahra ta cire takalmanta ta nufi wardrobe tana ɗauko kayan bacci. Ibrahim kuma ya cire agogonsa da wayarsa ya aje saman side stool.
“Zan shiga wanka,” tace ba tare data kalleshi sa ba
Kai ya gyaɗa mata kawai.
Bayan wasu mintuna ta fito daga toilet ɗin cikin doguwar rigar bacci mai kyau, jikinta na ɗauke da ƙamshin shower gel data yi wanka, gashinta a ɗaure cikin scarf mai kyau.
Ibrahim dake zaune bakin gado ya ɗago yana kallonta, idanunsa suka bi ta da wani irin kallo mai cike da so. Ita kuma kamar bata lura ba ta ƙarasa gaban mirror tana shafa handcream a hannunta.
Shi ma miƙewa yayi ya shiga toilet ɗin.
Lokacin da ya fito, farin towel ne ɗaure a kugu, daya a kafaɗarsa ga ruwa ke ɗiga kaɗan daga gashinsa. Ya sauya zuwa kayan bacci, ya kashe manyan fitilun ɗakin, small bedside lamp kawai ya bari.
Zahra ta riga ta kwanta ta juya baya kamar mai bacci.
A hankali Ibrahim ya hau gadon ya matsa kusa da ita. Hannunsa ya zagayo ya riƙo ta ta baya.
Da farko bata motsa ba, sai kuma ta ɗan sauke numfashi.
“Har yanzu kina fushi dani?” ya tambaya cikin ƙasa da murya.
Shiru tayi na wasu seconds kafin tace, “Ban sani ba.”
Murmushi yayi kaɗan ya matso da bakinsa kusa da kunnenta.
“But you’re calmer now.”
Ta juya a hankali tana kallonsa. Haske daga lamp ɗin na sauka akan fuskokinsu.
“I just want peace Ibrahim.”
Kallonta yayi cikin idanunta sannan ya shafa gefen fuskarta a hankali.
“And I want you.”
Idanunta suka sauka ƙasa na ɗan lokaci. Ibrahim ya janyo ta jikinsa, ita kuma bata ƙi ba. Ta kwantar da kanta a ƙirjinsa yayin da hannunsa ke shafa bayanta cikin lallashi.
A haka suka cigaba da hira cikin ƙananan muryoyi, suna tuna abubuwan dariya da suka faru a dinner ɗin, har bacci ya fara ɗaukar Zahra.
Ibrahim ya sumbaci goshinta a hankali yace,
“Goodnight wife.”
Cikin muryar bacci tace, “Goodnight…”
Sai ya ƙara rungumota sosai, ɗakin yayi sit cikin shiru da dumin soyayyarsu.
****
Ya Umar dake kwance saman king size bed ɗinsa yana scrolling through Instagram kawai idanunsa suka sauka akan sabon post ɗin. Da sauri ya tashi zaune tamkar wanda aka tsikara.
Kallon pictures ɗin ya tsaya yi cikin mamaki. Hotunan Zahra ne tare da Ibrahim daga dinner ɗin ɗazu, yadda suke manne da juna cikin farin ciki kamar ba su taɓa samun matsala ba.
Zooming yake yi ɗaya bayan ɗaya, yana kallon yadda murmushin Zahra ya fito sosai a hotunan.
A hankali ya kashe data ɗinsa ya ajiye wayar gefe ya kwanta saman gadon. Duk da wani irin abu da ya tsaya masa a zuciya, akwai abu guda ɗaya daya saka shi murmushi kaɗan, ganin cewa at least sun daidaita, sun koma kamar yadda ya kamata tsakanin ma’aurata.
***
Washegari da sassafe, Ibrahim ne ya fara farkawa. Juya kansa yayi yana kallon Zahra dake kwance kusa dashi cikin bacci, fuskarta na ɗauke da wani irin natsuwa.
Murmushi yayi a hankali kafin ya matsa kusa da ita yana shafa gefen fuskarta.
“Baby...” ya kira cikin sanyin murya.
Ta ɗan motsa tana lumshe ido.
“Hmm...”
“Sallah fa.”
Bata buɗe idanunta ba ta matsa kusa dashi tana ƙara lulluɓe jikinta da blanket. Dariya yayi ƙasa-ƙasa kafin ya sunkuyar da kansa ya sumbaci goshinta.
“Zahra...”
A wannan karon ta buɗe idanunta a hankali tana kallonsa.
“Ka cika damuna da asuban nan.”
“Saboda bana son ki makara.”
Miƙewa tayi tana murmushi. Ibrahim ya sauka daga gadon ya shiga toilet domin alwala sannan ya shirya zuwa masallaci. Kafin ya fita sai da ya juyo ya kalleta.
“Ki tayani addu’a.”
Kai ta gyaɗa masa kawai tana sauka daga kan gadon.
Bayan ya fita masallaci, Zahra ta idar da sallarta tana nan zaune akan darduma tana addu’o’i. Daga nan ta miƙe ta shiga kitchen.
Farida mai aiki na shirin fara breakfast ɗin, amma Zahra tace mata
“Barshi yau zan yi. Ke ki fara preparations na lunch kawai.”
“To Hajiya. Dama gyara wajen nake son yi naga sunyi kura ne, kafin ki fito shine na share”
Kai ta gyada mata, daga haka ta bar kitchen ɗin
Egg sauce da tea ta fara haɗawa, sai bread da sausages. Kitchen ɗin ya cika da ƙamshi mai daɗi.
Bayan wani lokaci Ibrahim ya dawo daga masallaci. Kai tsaye kitchen ya nufa bayan ya ga babu ita a ɗaki.
Yana shiga ya tsaya yana kallonta cikin apron ɗinta tana juyawa a cooker.
“Wow...”
Ta juyo tana kallonsa.
“Meye wow ɗin?”
“Matata ce ke min breakfast da kanta.”
Idanu ta juya tana murmushi.
“Ji sharri sai kace bana yi. Zo ka taimaka min mana.”
Nan ya ƙaraso kusa da ita yana tayata haɗa table ɗin breakfast, lokaci zuwa lokaci yana sata dariya da surutunsa.
***
Bayan ta shirya tsaf cikin elegant outfit ɗinta, Zahra ta ɗauki keys ɗin motarta ta nufi school.
Da ta isa, parking tayi a bakin faculty ɗinsu. Ganin har lokacin lecturer bai zo ba, sannan generator ɗin school ɗin ma ba'a kunna ba yasa ta zauna cikin motar ta saukar da kujera kaɗan ta kunna AC.
Wayarta ta ɗauka tana chatting casually kafin ta shiga status ɗin mutane.
Tana scrolling kawai status na Ya Umar ya bayyana.
Da sauri ta miƙe zaune ba tare data sani ba.
“This can’t be...” ta furta a hankali.
Da sauri ta buɗe status ɗin. Hotonta ne na jiya ita da Ibrahim yayin dinner ɗinsu. Ibrahim ya rungumota tana dariya.
Caption ɗin kuwa:
“Lil sis ❤️ Get well soon.”
#Jiddatulkhayr writes #08110615256