Kenza eBookz
Cover art for KOMAI YA YI FARKO  HAUSA NOVEL 1

Post

KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 1

..... the woman who was at the door of the room, without any fear, went to the bathroom, she came out, she started to pray, she heard her father asking "who is there" but she could not answer because her mind was not in her body, her thoughts were far away, the light of the torch that shined in her eyes brought her back from the world of thoughts that she had expanded, she put her hand to protect her eyes from the light of the torch. My father took down the toast and said; "What are you doing out in the middle of the night?" In the coldness of her voice, she sees more and more worry, she said; "It's my duty." "Then hurry up and go back inside." He said as he went back to his room. She also fetched water and poured it into the butan, because she finished the tea that I put without knowing if she did the alawat correctly, her thoughts prevented her from being calm, she put a new alawat, and went into the room. She did not close the door of the room until she used the light of the moon to take the hijab and rug before closing the door. She straightened the rug, she went up and faced the east, she prayed in the grave, and she started to pray calmly. Every time she finds herself in a st

Standalone post1,690 words

KOMAI YA YI FARKO.

Na

Shamseeya Rabi'u Garba (Jikargarba.)

A ƙarƙashin jagorancin Young Talented Writes Association(YOTA).

A 2026 novel.

Bismillah Alrahman Alrahim.

Sadaukarwa zuwa ga Bello Ado Usman

Page 1 ...... Dare ya yi nisa, gari ya nutsu cikin shiru kamar ruwa a tafki. Gidaje sun cika da numfashin masu barci, fitilu sun mutu, hatta iska tana kaɗawa a hankali kamar tana jin tsoron tayar da kowa. Amma idanunta sun ƙi rufuwa, zuciyarta na ta bugawa a hankali, saboda wata damuwa da ta dame ta. A cikin duhun ɗakin, ta ji kanta kamar zai rabe biyu saboda tunani da ta sa a gaba, ta kasa samun nutsuwa, zuciyarta na ta kai komo tsakanin tunanin da ba ta so, amma ba zai daina tashi ba, ko ta rufe idanunta bacci ba ya zuwa, sai ma zuciyarta ta rinƙa haska mata abinda bata son tunowa.

A hankali cikin gajiyar jiki da ta zuciya, ta tashi daga kan katifarta da ta suɗe ta koma kamar tabarma, laluɓawa ta yi ta fita daga ɗakin, da taimakon hasken wata da ya haske gari ta ɗauki buta ta ɗebi ruwa a randar da ke ƙofar ɗakin, ba tare da wani tsoro ba ta nufi banɗaki, tsarki ta yi ta fito, ta fara alawla, tana jin Abbanta na tambayar “waye a wajen“ amma ta kasa amsawa saboda hankalinta ba ya jikinta, tunanin ta ya yi nisa, hasken toci da ya dalla mata a ido ne ya dawo da ita daga duniyar tunani da ta faaɗa, hannu ta saka ta kare idonta daga hasken tocin. Abbanta ya sauke tocin, ya ce; "Me kike yi a waje a wannan tsakar daren?"

Cikin sanyin muryarta da daman haka take ga kuma ƙarin damuwa, ta ce; "Alawla na ke yi."

"To ki yi sauri ki koma ciki." Ya faɗa yana mai komawa cikin ɗakinshi. Ruwa ta kuma ɗebowa ta zuba a butan, saboda ta gama tsiyayar da na butar ba tare da ta san ko ta yi alawlar daidai ba, tunanin da take yi ya hanata natsuwa, ta ɗora sabon alawla, sannan ta shige ɗaki.

Ba ta rufe ƙofar ɗakin ba, har sai da ta yi amfani da hasken watar da ke haskaka, ta ɗauki hijjabi da darduma kafin ta rufe ƙofar. Shimfiɗa darduman ta yi, ta hau kai tana mai fuskantar gabas, kabbara sallah ta yi, ta fara sallah cikin nutsuwa. A duk lokacin da ta tsinci kanta cikin damuwa to fa dardumanta ne wajen zamanta, a nan take zama ta kai kukanta ga mahaliccinta, wadda take da tabbacin yana jinta kuma zai kawo mata ɗauki, a nan take zubar da hawayenta saboda ta san tana gaban mai share mata, a nan take faɗar dukkan matsalolinta saboda ta san tana gaban buwayi gagara misali, mai maganin dukkan damuwa.

Ta kai awa biyu a tsaye tana sallah ba tare da ta gajiya ba, saboda gajiyar dake zuciyarta ya hana ta jin kowacce irin gajiya a jikinta, daga bisani sai ta sallame, ta ɗaga hannuwanta sama na fara koro addu'o'i. Tana kan darduman har aka kira sallar asuba ba tare da ta rintsa ba. Tana jin lokacin da Inna Habi ta farka, ta lallaɓa ta ɗauki wayarta, ta kuna tocin wayarta, tana ganin ta, tace; "Humaira, kar dai yau ma ba ki yi bacci ba." Miƙewa ta yi, ta kabbara sallar asuba ba tare da ta amsata ba, sai Inna ta girgiza kai kawai ta fita tana faɗin; "Allah ya kyauta."

Bayan ta iddar da sallah, tana zaune kan darduma bacci ya ɗauke ta, baccin da rabonta dashi tun ranar da ƙaddara ta faɗo mata, kwanaki huɗu baya kenan. Bacci sosai ta yi, kuma babu wanda ya tashe ta, saboda baccin nan shine abinda dukkan masoyanta ke addu'ar ta samu ko zai ɗan rage mata wani zafin da take ji a zuciyarta. Ƙarfe goma da mintuna ta farka daga baccin da ya sace ta, miƙa ta yi saboda yadda take jin gajiya a dukkan gaɓoɓin jikinta. Inna Habi ta shigo ɗakin, ta kalle ta tace; "ashe kin tashi." "Eh, ina kwana Innata." Ta faɗa a lokacin da take linke darduma.

"Lafiya ƙalau Humairata, ya ƙarfin jiki?"

"Alhamdulillah."

"Masha Allah, akwai ruwan zafi a wuta, kije ki ɗeba ki yi wanka ko za ki ji daɗin jikinki." Inna ta kalle ta, da ta zauna a edge ɗin gado, sai tace; "Ko dai na kai miki ruwan ne?"

Girgiza kai ta yi, tace; A'a, yanzun zan tashi." Ta janyo akwatin kayanta, ta ciro kayan da za ta saka idan ta fito wanka, sannan ta ciro ɗankwalin tsofin kayanta, ta ajiye a gefe. Ta ɗauki kwandon soson wanka a bayan ƙofar ɗakin, ta zumbula hijjab akan zanin da ta ɗora a ƙirji.

Bokiti ta ɗauka a bakin ƙofar shiga ɗakin, ta ajiye a gefen rijiyar dake tsakar gida. Sai da ta fara shiga ɗakin matan Abbanta, ta gaishesu kafin ta dawo ta ja ruwa ta sirka da na zafin, ta shiga wanka.

A lokacin da ta fito daga wanka har Inna Habi ta gama gyara ɗakin, ta share ko ina tsaf, ta kuna turaren wuta, a hankali take yin komai har ta gama shirinta cikin doguwar rigar atamfa. Ta shimfiɗa tabarma a tsakiyar ɗakin, ta ɗauko wannan ɗankwalin da ta ajiye a gefe da scissors. Yankan rigar babyn roba ta yi, ta hau kan keken da NGO'S suka ba ta wata biyu da suka wuce baya sun kammala wani skill acquisition training, ta fara ɗinke rigar. Duk abinda take yin nan don kawai ta kawar da tunanin dake damunta. Inna Habi dake kallon duk abinda take yi, tace; "Ba za ki ci abinci ba tukunna?"

Ko ci kanki ba ta ce mata ba, ta cigaba da abinda take yi. Tana tsaka da haɗa rigar ta ji sallamar mutane a ƙofar gidan su, dake kekenta na kusa da window ne, sai ta ɗan yaye labule don ganin su waye ne. Ido ta zaro ganin wadda suka shigo gidan, classmates ɗinta ne, da malamai uku daga makarantarsu. Uwargidan Abbanta, Mama Lantana dake wanki a tsakar gida, ita ta rinƙa yi musu maraba. Ɗaya daga cikin malamar tace; "Mun zo duba Aisha ne, Allah ya sa tana nan."

Ai tana jin Mama Lantana ta ce musu tana ciki su shiga, ta yi maza ta tashi daga kan keken, ta faaɗa kan gado, ta lulluɓe bargo a jikinta, ta lumshe ido kamar mai bacci. Bayan sun gaggaisa da Inna, wannan malamar tace; "Bacci take yi?"

Inna tace; "Eh, ta ɗan samu bacci."

"Masha Allah, Allah ya ƙara mata lafiya."

"Aameen mun gode sosai."

Suna fita daga ɗakin, ta sauka daga kan gadon, ta zauna ƙasa ta kife kanta a jikin gadon, ta fashe da kuka, Inna da ta dawo daga rakiyar su ta isketa a hakan, ƙarasowa kusa da ita ta yi, tace; "Why Humaira? Me kukan nan zai amfana miki?"

Cikin kuka ta fara magana; "Yanzu Inna kowa ya san abinda ya sameni kenan?"

Rungumeta ta yi, tace; "Babu wanda ya san komai, a makarantar kuma ce musu aka yi ba ki ji daɗi ba, don haka ki daina wannan kukan."

Ƙwaƙume Inna ta yi sosai kamar za ta koma cikinta, murya ƙasa-ƙasa tace; "Inna ki yi min alfarma, idan kin yi sallah ki taya ni da addu'a Allah ya ɗauki raina cikin gaggawa..."

"Haba Humaira, ya kike magana kamar jahila, ashe za ki iya mance dukkan rahamar da Ubangiji ya miki akan ɗan ƙanƙanin jarabawa, har za ki buɗe baki ki iya furta wannan irin mummunar kalma, to ahir ɗinki wallahi." Inna Habi ta cire ta daga jikinta, ta fita daga ɗakin, sulalewa ta yi, ta kwanta a leda kafet dake shimfiɗe a ɗakin ta fashe da kuka mara sauti, wallahi gabaki ɗaya duniyar ta ishe ta, zuciyarta zafi take mata kamar an hura wuta a ciki, kanta kuma barazanar tsagewa take yi, jikinta dukka ciwo kamar an yi mata duka saboda gajiya, gajiya ce da ba iya jiki ya tsaya ba, har zuciya da ƙwaƙwalwarta sun gaji.

Inna Habi ta shigo da kwanun abinci, ta tura shi gabanta, fuska a haɗe tace; "Tashi ki ci."

Yamutsa fuska ta ɗan yi, tace; "Inna ba na jin yunwa."

"Ban tambayeki ba, kawai cewa na yi ki tashi ki ci."

A hankali ta miƙe, ta share hawayen dake fuskanta, jan kwanon ta yi, ta fara tura abuncin ba wai don tana jin daɗinsa ba, sai don ba ta gan alamar wasa a idanun Inna ba, kuma tabbas ta san tana buƙatar abinci, don ta mance rabon da ta ci wani abu.

Ta ci kusan rabin shinkafar kafin ta tura kwanon saboda yadda ta fara ji kamar zata yi amai, ta marairaice fuska, tace; "Inna amai nake ji."

Kwanon Inna ta ɗauka ta fita da shi, sannan ta zo mata da ruwa, sosai ta sha ruwan saboda yadda maƙogwaronta ya bushe, ta kuma kwanciya a ƙasan sabobin hawaye na bin fuskarta. "Tashi ki hau gado." Inna ta faɗa tana tsaye a kanta. A hankali ta tashi ta haura kan gadon ƙarfe dake ɗakin.

Inna ta nema waje ta zauna, ta ɗora kanta akan ƙafafunta, cikin lallashi ta fara magana; "Humaira ban san ki da haka ba, na san ke ɗin mai Imani da tawwakkali ce, don haka a wannan lokacin ki zama mai karɓar ƙaddararki, ki yi ta istighfari a duk lokacin da kika ji sheɗan na kitsa miki wani abu a zuciyarki, don Allah ki ci abinci, ki sha ruwa, ki yi walwala, ki move on da rayuwar ki, kar ki taɓa bari rayuwar ki ta tsaya waje ɗaya saboda abinda ya farun nan, kin ji Humairata?"

Kai ta gyaɗa mata a hankali, tana fatan Allah ya sa ta iya duk abubuwan da Inna ta lissafa.

"Kin yi min alƙawari?" Ta kuma tambaya tana shafa kanta.

"In Sha Allah Inna."

Tana kwance a ƙafafun Inna bacci ya ƙara ɗaukarta, baccin ma da take yi, ba baccin daɗi ba ne, don cike da rashin natsuwa take yinta. Rabon da ta samu bacci mai natsuwa da kwanciyar hankali tun ranar da mummunar ƙaddara ta faɗa mata, ƙaddarar da ba ta taɓa tunanin zai taɓa faaɗa kan wani makusancinta ba, balle kuma ita kanta.

TOH FAH🤔

WANNAN WACCE IRIN ƘADDARA CE?

https://chat.whatsapp.com/CGm8zTMQDDO1e9sf3BmDKQ?mode=hqctcla