Kenza eBookz
Cover art for FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 13

Post

FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 13

..... smile at me like before. Sleep well, my star After she finished reading, she hung up the phone because she had nothing to say. She put her head on the pillow. She has been sleeping early for the past two days, but today she is struggling to sleep. Both her eyes were open until twelve o'clock at night. She fell asleep there around dawn. The next morning, Mami was sitting with Zahra having breakfast in her main parlor. It was Umar who came in with greetings. Mami answered him, and he finally sat on the chair and greeted me. "Oh body?" Umar asked Zahra in a cold voice. "Alhamdulillah," Zahra answered, playing with her fingers. "How am I sleeping?" she asked more slowly. "Alright. How strong are you?" "Naturally." He looked at her and said, "Is there something you need?" She shook her head at him. "If there is, then speak up." "Okay." she said. He said, "You will go back to your house soon, won't you?" She couldn't raise her head, let alone say yes. Mami turned to look at her and focused on the Irishman in front of her. "Umar, sit down and lie to us," Mami said. "We did it with Abbah." "Okay." Zahra stood up and went inside as if she wanted to do something. O Umar looked at Mami

Standalone post2,273 words

*FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes

Young talented writers association (YOTA)

Book 1 Chapter 13

Zahra tun data shiga ɗaki ta kwanta, amma sam bacci yaƙi zuwa idanunta. Ko chatting ɗin ma ta ji ba zata iya yi ba. Maganganun Ya Umar ne kawai suke yawo a cikin ranta. Ta sani bata kyauta masa ba, amma ita tausayi ne yasa ta aikata hakan. A hankali ta share hawayen da suka zubo mata.

Ƙarar shigowar saƙon waya taji. Wayar ta ɗaga tana kallon sunan da ya bayyana a screen ɗinta, abin mamaki sosai ganin saƙon Khalil.

Good night, my Zahratyy Na san kina fushi da ni, kuma kina da duk wani dalili na hakan… amma wallahi tun lokacin da kika fita daga gidan nan babu abin da yake min daɗi. Gidan ya yi shiru babu ke.

Ki yi ƙoƙarin ki huta, please. Bana son ki damu da komai yanzu. Abin da nake so kawai shine ki samu lafiya da nutsuwa. Dan kin haifi mana Ɗan mu cikin kushin lafiya

Tomorrow zan zo na ɗauke ki in sha Allah. Mu fita lunch ko? Wani wuri mai kyau, just me and you… maybe hakan zai sa ki ɗan murmusa min kamar da.

Sleep well, tauraruwa ta

Bayan ta gama karantawa, ta kashe wayar saboda bata da abin cewa. Ajiye kanta tayi akan pillow. Ita da take yin bacci da wuri kwana biyun nan amma yau bacci yaƙi ɗaukanta. Har ƙarfe goma sha biyu na dare idanunta biyu buɗe suke. Dakyar dai bacci ya ɗauke ta can wajajen asuba.

Washegari da safe, Mami na zaune ita da Zahra suna breakfast a main parlorn ɗinta. Ya Umar ne ya shigo da sallama. Mami ta amsa masa, shi kuma ya ƙaraso ya zauna a kujera yana gaidata.

“Ya jiki?” Ya Umar ya tambayi Zahra cikin sanyin murya.

“Alhamdulillah,” Zahra ta amsa tana wasa da fingers ɗinta.

“Yaya ina kwana?” ta ƙara tambaya a hankali.

“Lafiya. Ya ƙarfin jiki?”

“Da sauƙi.”

Sai ya ɗan kalleta yace, “Akwai abin da kike buƙata ne?”

Kai ta girgiza masa.

“Idan akwai sai ki yi magana.”

“Toh.” ta ce

Ya ce “Anjima zaki koma gidan ki ko?”

Ta kasa ɗaga kai balle tace eh. Mami ta juya ta kalleta sannan ta maida hankalinta kan Irish ɗin gabanta.

“Umar, ka zauna ka karya mana,” Mami tace.

“Ai tare da Abbah muka yi.”

“Okay.”

Zahra ta miƙe ta wuce ciki kamar mai son yin wani abu. Ya Umar ya kalli Mami yace,

“Mami me kika yanke akan komawarta?”

“Kamar me kuma?”

“Ba za’a tura mata mutum ba?” Ya Umar ya ce

“Eh, nima nayi tunanin haɗa ta da mai aiki. Yana da kyau ace akwai mutum kusa da ita, shiyasa nake son haɗa ta da mai aiki.”

“Good. Nima abin da nayi tunani kenan. Amma akwai wacce kuka yi magana ne?”

“Eh, nayi magana da Rabi’a tun jiya. Anjima kanwarta zata zo ta koma can ɗin da zama.”

“Okay. Idan tazo Mami ko ina wajen aiki ne, please call me. Ina son na kaita da kaina.”

“Toh shikenan, tana zuwa zan kira ka.”

Ya ɗan yi murmushi sannan yace, “Amma Mami kina mata addu’a kawai. Kamar har yanzu kina fushi.”

Murmushi Mami tayi tace, “Umar wani fushin kuma? Ai komai ya wuce yanzu.”

“Yauwa Mami.”

“Addu’a kam kullum ina cikin yinta.” Mami ta ce

Ya miƙe yace, “Mami bari zan wuce.”

“Allah yayi albarka ya bada sa’a.”

“Ameen.”

Daga haka ya fita.

Can sai ga Zahra ta fito cikin shirinta. Mami ta kalleta tace, “Zahra kamar wanda ake kora, ace ƙarfe takwas zaki koma gidan ki?”

“A’a Mami, ba gida zan koma ba. Ina son na shiga school.”

“Yanzu har kin warke da zaki fara fita school?”

“Mami zan bi a hankali. Bana son karatu ya wuce ni. Wannan final semester na ne, kuma tun farkon semester bana zuwa. Kar nazo nayi missing abubuwa da yawa, though su Firdausi suna min attendance.”

“Toh, ƙarfe nawa zaki koma gidan?” Mami ta ce

“Idan na dawo da yamma.”

Mami ta gyada kai. “Toh sai driver ya kai ki school ɗin. Ki faɗa masa lokacin da zaki taso sai yaje ya ɗauko ki. Da yamma kuma Yayanki zai maida ki.”

“Toh Mami.”

“Allah ya bada sa’a.”

“Ameen.”

Daga haka ta juya ta fita.

A department ɗinsu driver yayi parking. Zahra ta buɗe back seat ta sauko. Kusan duk idanu sun dawo kanta. Idan da sabo ta saba, amma yau sai taji bata son kallon nasu.

Tana shiga hall ɗin ta samu waje a edge ɗin gaba. Bata ma damu data nemi su Asiya ba. Firdausi ce ta taso ta ƙaraso wajenta.

“Dama Zahra zaki shigo yau?”

“Eh, kawai naji ina missing abubuwa ne.”

“Hakane kam. Ya jikin naki?”

“Alhamdulillah da sauƙi.”

Firdausi ta ɗan kalleta sosai. “Amma ya naga kina wani iri ne? Ko dai jikin ne?”

Kai ta girgiza mata.

Daga haka Firdausi tayi shiru ganin kamar Zahra bata son magana. Duk wanda ya shigo sai ya mata “ya jiki?”

A haka har suka yi first lecture ɗinsu na three hours.

Gaba ɗaya Zahra ta rasa meke mata daɗi a duniya. Gashi bata isa ta tunkari Mami da wannan maganar ba.

Dafe kanta tayi.

“Zahra wai nikam tunanin me kike yi haka?” Firdausi tace. “Kar kije ki jawo wa kanki ciwo. Kin manta kina under conditions ne?”

“Firdausi ban san yadda zanyi bane… na rasa meke min daɗi.”

“Me ya faru?”

“Anjima zan koma gidan Ibrahim.”

“What!?” Firdausi ta faɗa cikin mamaki. “Yanzu duk abin da Khalil yayi miki sai ki koma gidansa?”

Zahra ta dafe kanta. “Ban san yadda zanyi bane Firdausi. Gaba ɗaya nima kai na ya kulle. Har gida yazo yana rokona, shine ma na haɗa shi da Ya Umar.”

“Haba Zahra! Yau kika fara sanin Ibrahim ne? Yaushe har zaki yarda da roƙonsa? At least ki basa wahala mana ko da zaki koma masa. Sai kace baki san right ɗinki ba.”

Ta ɗan numfasa sannan tace, “Wallahi idan nice a matsayin ki, babu namijin da zai taka ni yana wulaƙanta ni ina kallo na kyale shi. Tuni na koma gidanmu.”

“Amma Ya Umar ya masa warning sosai,” Zahra tace a hankali. “Kinga dole zai canza tunda Ya Umar ya shiga maganar.”

Firdausi ta kalleta kawai. A ranta ta fahimci Zahra tana son mijinta ne sosai.

“Toh shikenan,” tace daga ƙarshe. “Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Allah yasa kuma da gaske ya canza.”

“Ameen.”

Daga haka bata ƙara cewa komai ba.

“Tashi muje masallaci,” Firdausi tace. “Daga can mu wuce cafeteria ki saka wani abu a ciki. Karki zauna da yunwa.”

“Toh.”

Daga haka suka miƙe suka nufi masallacin.

Sosai Ya Umar yayi magana da Farida, kanwar Rabi’a, yana mata bayanin komai da ya dace ta sani game da zaman gidan da kuma kula da Zahra. Farida na zaune tana saurare cikin nutsuwa, lokaci zuwa lokaci tana gyada kai alamar fahimta.

A lokacin ne Zahra ta buɗe ƙofar parlorn ta shigo. Ganinsu tare yasa ta ɗan tsaya na wani lokaci kafin tace,

“Ya Umar ina wuni?”

“Lafiya,” ya amsa yana kallonta. “Ya school ɗin?”

“Alhamdulillah.”

Farida ma ta gaidata cikin girmamawa, “Ina wuni.”

“Lafiya lau,” Zahra ta amsa mata.

Daga haka ta wuce ɗakin Mami.

Ya Umar ya bita da kallo sannan yace, “Idan kin gama shiryawa sai ki faɗa min na kai ki.”

Ta dakata sannan ta ce “Toh.”

Ta ƙarasa shiga ɗakin.

Kunna wayarta tayi, wacce tun ɗazun Khalil ya addabi rayuwarta da kira. Tana kunnawa kuwa sai wani kiran nasa ya shigo kamar wanda yake jira.

Ta ɗaga tare da sallama.

“Haba Zahra,” muryarsa ta fito cike da ƙorafi, “ina ta kira baki ɗagawa? Har gida ma nazo aka ce min babu kowa.”

A hankali tace, “Na tafi school ne.”

“Yanzu inzo na ɗauke ki?”

“A’a… Ya Umar ne yace zai kawo ni.”

Wani irin shiru Ibrahim yayi.

“Hello?” Zahra ta kira a hankali.

“Ina ji.”

“Ai naga kayi shiru ne.”

“A’a… toh sai ya kawo ki ɗin.”

“Toh, sai anjima.”

Daga haka ta kashe wayar.

Kiran Mami tayi.

“Mami kina ina ne wai?”

“Ina part ɗin Abbanku ne, ina ɗan gyare-gyare kafin ya dawo. Wani abu ne?”

“A’a, dama ban ganki bane.”

“Kin shirya ne?”

“A’a.”

“Toh ki shirya. Ni ɗin ma na kusa karasawa.”

Daga haka ta kashe wayar.

Toilet ta shiga tayi wanka sannan ta fito. Wani dogon gown mai sauƙin kyau ta saka tare da hijab, hand bag kawai riƙe a hannunta kamar mai zuwa unguwa.

Da fitowarta parlorn, babu kowa. Zama tayi tana jiran fitowar Mami. Jim kaɗan sai ga Mami ta buɗe ƙofar ta shigo.

“Kin gama ne?”

“Eh.”

“Toh sai kima Yayanki magana, naga yana jiran ki.”

Sai kuma tace, “Kin ga kayan da na haɗa miki? Wacce zata riƙa taimaka miki ta fita da su zuwa mota.”

“Mami waccece?”

“Idan kika je ai zaki ganta.”

Ta ɗan tsaya sannan tace cikin kulawa, “Kuma kar kiyi wannan shaye-shayen magunguna idan ba asibiti da likita ya baki ba. Kinsan condition ɗinki.”

Kai Zahra ta gyada kawai.

“Toh ki sauka ki same su a ƙasa. Allah ya baki lafiya ya raba lafiya.”

“Ameen,” ta amsa tana kallon ƙasa.

A parlorn ƙasa ta samu Ya Umar yana waya. Daga gani da mace yake magana saboda yadda muryarsa tayi laushi. Yana ganinta sai ya kashe kiran.

“Tashi mu tafi.”

Miƙewa tayi. A wajen taga Farida tsaye da wasu ledoji a hannunta.

“Zo mu tafi,” Ya Umar yace.

Bin bayansu tayi zuwa mota.

Ya buɗe mata gaba ta shiga, sannan shi ma ya zagaya ya shiga driver seat. Farida kuma ta shiga baya.

Ya tada motar suka nufi gidan Zahra.

Tun daga lokacin da suka kama hanya zuciyar Zahra ke bugawa da ƙarfi. Wani irin tsoro da fargaba ne suka cika mata ƙirji. Ita kanta batasan me yasa take jin hakan ba.

A compound ɗin gidan yayi parking.

Ta juya tana kallonsa tace, “Yaya nagode.”

“Duk wani abu da zai faru Zahra, just let me know please.”

Kai ta gyada masa.

“Anjima zan miki transfer.”

“Kaiii!” tace tana ɗan murmushi. “Yaya baka gajiya ne?”

Ya ɗan murmusa yace, “Ohh… yanzu kin fara girma kenan. Da ke ce ai ina ruwanki da mutum ya miki transfer. Yau gobe sai kice kuɗi sun ƙare.”

Dariya ne ya ƙwace mata, kuma hakan ya saka wani daɗi ya ratsa zuciyar Ya Umar.

“Toh shikenan,” tace tana buɗe ƙofar motar. “Kafin transfer ɗin ma nagode sosai.”

“Alright.”

Ta sauka. Shi ma ya sauka tare da Farida.

Ya buɗe bayan motar yana kwaso kayan yana miƙawa Farida tana kaiwa baranda.

Bayan ya gama ya juya yana kallon Zahra yace, “Mijin naki yana nan ne? Mu gaisa nace na kawo masa matarsa.”

“Bari na kira shi. Ka shigo.”

Ta buɗe ƙofar parlorn.

“Farida, kitchen zaki riƙa kai kayan.”

“Toh,” Farida ta amsa tana ɗaukar ledar farko.

Ita kuma Zahra ta wuce sama zuwa ɗakin Ibrahim.

Tana buɗe ƙofar ɗakin ta same shi yana saka kaya, alamar daga wanka yake. Da suka haɗa ido murmushi ya sakar mata.

A take duk fargabar da take ji ta ragu.

“Ya Umar yana ƙasa wai ku gaisa.”

Ya ɗan matsa kusa da ita yace, “Babu ko gaisuwa ne tauraruwa?”

Dariya tayi tana shiga cikin ɗakin. “Har ka tuna min da wannan sunan?”

“Ya baby na?”

“Kai ni ka bari… kunya nake ji.”

“Okay toh, bari naje mu gaisa da Yayanki kafin ya canja shawara.”

Dariya tayi.

Ya ƙarasa fesa turare sannan ya ajiye kwalbar. Hannunta ya kama suka fito tare.

Tun suna saukowa daga stairs Zahra tayi saurin cire hannunta daga nasa saboda ganin Ya Umar a parlorn.

Da suka ƙaraso, Ibrahim ya miƙa masa hannu suka gaisa.

“Ɗan bani ruwa mana,” Ya Umar yace yana kallon Zahra.

Ta juya zuwa kitchen.

Da zarar ta bar wajen, Ya Umar ya maida kallonsa kan Ibrahim.

“Gashi na kawo maka ita,” yace cikin sanyin murya. “Amma ka sani… idan ka cigaba da musgunawa kanwata, kamar yadda na kawo ta haka zan zo na ɗauke ta. Kuma a lokacin sai ta maka nisa har abada.”

Ibrahim yayi folding hannuwansa yace, “Wai ya kake so ne? Ka dinga gaya min magana yadda ranka yaso? Zahra matata ce. Kuma idan son ta ne, ina sonta.”

Ya Umar ya ɗan tafa hannayensa a hankali Ya ce

“Good. Sai dai idan ba kai ɗin bane.” Ya ɗan matsa kusa da shi yace, “Well… duk yadda kace dai-dai ne. Amma ni kuma, I’m done talking.”

A lokacin Zahra ta fito daga kitchen da ruwa da snacks.

“Ya Umar har zaka tafi? Ko ka fasa shan ruwan ne?”

“Naga an fara kiran sallah ne. Ina son na koma gida.”

“Amma ka karɓa mana.”

Saka hannu yayi ya ɗauki bottle water ɗin.

“Allah ya huta gajiya.”

Daga haka ya juya ya fita.

Zahra ta bishi da kallo kafin ta juya. A lokacin ne taga Farida zaune can gefe cikin nutsuwa.

“Taso bari na nuna miki ɗakin ki,” Zahra tace. “Sai dai akwai ɗan ƙura saboda ba’a buɗe shi ba.”

Ta nuna mata ɗakin dake kusa da kitchen.

Farida ta gyada kai suka wuce.

Bayan ta gama nuna mata komai, Zahra ta dawo parlorn.

Ibrahim na zaune ya lumshe idanunsa kamar mai tunani.

“Lafiya?” ta tambaya tana tsayawa gabansa.

Ya buɗe idanunsa a hankali yana kallonta. “Lafiya Zahra.”

Ta juya zata wuce sama sai yace, “Wacece wannan?”

“Wacce zata taimaka min aiki ce. Mami ai ta faɗa maka.”

“Okay.”

Daga haka ta wuce sama direct zuwa ɗakinsu.

Toilet ta shiga tayi alwala, sannan ta fito. Darduma ta shimfiɗa tare da tada kabbarar sallah, zuciyarta cike da wani irin nauyi da take fatan Allah kaɗai zai sauƙe mata

Ku fara ajiye ishirin, hamsin a asusun ku🤣 akwai chakwakiya ne sosai a book 2

#08110615256