Kenza eBookz
Cover art for FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 12

Post

FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 12

.....okay, go to sleep. But no matter what, don't keep things in your mind. Did you hear what was said to you in the hospital?" She shook her head and adjusted her bed. God immediately helped her sleep. In the west, it was their arrival in Asia that caused it to descend. After they finished their conversation, she accompanied them to the gate and then came back. Mummy and Batoul are entering the parlor through the window, it seems that they are about to go out. Zahra said, "Mummy, where are you today?" She said, "It's okay." I thought you went home since I haven't seen you since morning." Zahra said, "No." Batoul said, "But this is the only way to go home if there is no problem, Zahra?" You are fine now, he said, you are cured." Zahra said, "There is nothing left." And he comes and checks my body every day." Batoul said, "Uhmm, God is generous." But this is a kind of set-up." Zahra didn't follow her own path anymore, she went to her place. As she entered Mami's room, Mami raised her head and looked at her and said, "And now what connects you with Batoul?" She said, "No, she is asking a question, but she is telling me something." Mami said, "It's okay, I don't want to talk." When I

Standalone post1,998 words

*FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes

Young talented writers association (YOTA)

Book 1 Chapter 12

Sauke ajiyar zuciya Ibrahim yayi, daga haka ya fita shima.

A compound suka haɗu da Ya Umar, shima waya ce a kunnensa yana magana. Ga mamakinsa, Ibrahim ya karaso wajensa. Shi kuwa yayi pretending kamar bai gansa ba, ya cigaba da wayarsa har ya haura staircase ɗin bakin main parlorn.

Ibrahim kuwa ya juya ya fita.

Ya Umar kasa ƙarasa shiga ciki yayi. Ya juya yana kallon Ibrahim ɗin. Duk da ba yau ya saba ganin Ibrahim yana zuwa gidan ba, amma wannan zuwan nasa ko kaɗan bai masa daɗi ba. Musamman yadda yaga ya zama calm sannan yana zuwa towards him cikin nutsuwa, gaba ɗaya abin ya ɗaure masa kai.

Juyawa yayi ya shige ciki. Kamar zai hau sama wajen Mami sai kuma ya fasa ya wuce ɗakin Mummy.

Anty Jiddah tace, “Toh ke kuma me aka miki ne kika canza tun da kika shigo?”

Ta juya tace, “Babu komai fa Anty Jidss.”

Tace, “Toh hirar tamu yanzu an fasa kenan?”

Tace, “Anty bacci nake son yi.”

Tace, “It’s okay, kiyi baccin ki. Amma koma mene ne kar ki sa abu a ranki. Kinji me aka ce miki a asibiti ko?”

Kai ta gyaɗa mata, ta gyara kwanciyarta. Nan da nan Allah ya taimaka bacci ya kwashe ta.

Can yamma, zuwan su Asiya ne yasa ta sauko ƙasa. Bayan sun gama hirarsu ta raka su har gate sannan ta dawo.

Tana shiga parlorn taga Mummy da Batoul, da alama fita zasu yi.

Zahra tace, “Mummy ina wuni?”

Tace, “Lafiya lau. Ai na ɗauka kin tafi gidanki tunda tun safe ban ganki ba.”

Zahra tace, “A’a.”

Batoul tace, “Amma dama haka kawai ake zuwa gida ne idan ba matsala aka samu ba Zahra? Lafiya kam yanzu yaci ace kin warke.”

Zahra tace, “Ai da saura. Kuma ai yana zuwa yana duba jikina kullum.”

Batoul tace, “Uhmm toh Allah ya kyauta. Amma wannan wani irin jibge ne.”

Zahra bata sake bi ta kanta ba, ta wuce sama abinta.

Tana shiga ɗakin Mami, Mami ta ɗaga kai tana kallonta tace, “Yanzu kuma me ya haɗa ki da su Batoul?”

Tace, “A’a wai tambaya take yi, amma tana gaya min magana ne.”

Mami tace, “It’s okay, bana son magana. Da zan sauko ai, ina jin ta yasa na fasa.”

Zahra tace, “Wallahi saboda Ya Umar ne nake ɗaga mata ƙafa, kar yace bana ji.”

Mami tace, “A’a babu ruwanki da su, ki kyale su.”

Zahra ta zauna bakin gado tace, “Mami masu aiki me zasu girka mana yau?”

Mami tace, “Ai yanzu duk abin da kika ce shi za’a girka.”

Tayi shiru kamar mai tunani sannan tace, “Toh Mami ni dai ayi mana saƙwara.”

Mami tace, “Tohm shikenan, bari nayi musu magana.”

Tace, “Yawwa Mami nagode.”

Mami tace, “Toh yanzu sai yaushe zaki koma gidan ki tunda har mijinki ya buɗe baki yayi magana?”

Zahra ta sauke kai ƙasa bata ce komai ba.

Mami tace, “Ina miki magana kin yi shiru ko baki ji bane? Ai kinji me yasa nake miki magana. Ko baki ji yace har Mamarsa tace ya kamata ki koma gidanki bane?”

A hankali tace, “Naji Mami… shi yasa nima bansan sanda zan koma ba tukuna. Bari idan munyi magana.”

Mami tace, “Ai na ɗauka yau zaki bar min gida.”

Nan take hawaye suka fara zubo mata tace, “Mami dan Allah ki daina min magana akan aure haka. Idan kina haka auren ba zai taɓa samun albarka ba. Ki tausaya min… ki kuma yafe min.”

Nan take Mami taji Zahra ta bata tausayi matuƙa, ta tuna maganar likita.

Ta rungume ta tace, “Sorry Zahra, ba wai baki nake miki ba. Kawai bana so ki samu matsala da mijinki da dangin mijinki ne. Shi yasa nake son ki dinga obeying abin da yake faɗa miki.”

Zahra ta sauke idanunta ƙasa tana wasa da fingers ɗinta.

Mami tace, “Zahra.”

Ta ɗaga kai tana kallonta.

Tace, “Ki sake fuska mana toh.”

Tace, “Toh.”

Mami tace, “Duk yadda kukayi zaki koma, sai ki fara shiri.”

“Tohm Mami.”

Mami ta miƙe tace, “Bari naje na sa masu aiki su girka miki saƙwarar.”

Kai ta gyaɗa mata.

Da Mami ta fita, Zahra ta faɗa kan gado ta sake shiga duniyar tunani.

Ya Umar da zai fita sallar Isha’i ya leka ɗakin Mami, saboda yanzu nan-ne wajen zaman Zahra.

Yace, “Baby akwai abin da kike so ne?”

Tace, “Eh Yaya.”

Ya ƙaraso ciki yace, “Me kike so toh?”

Tace, “Ragadada… sai kuma Fanta mai sanyi.”

Yace, “Sai kuma me?”

Tace, “Ai hakanan babu komai.”

Yace, “Alright. Idan na tashi daga sallah zan saya.”

Daga haka ya mata sallama ya fita.

Tana nan kwance tana jin komai boring. Sai ta kunna wayarta, ta shiga Instagram. Nan take memories ɗinta na baya suka fara dawo mata.

Can wajen ƙarfe tara na dare Ya Umar ya dawo.

Yana parking ya hangi mutum zaune yana danna waya. Da mamaki yake kallonsa har ya fito daga motar ya kulle.

Sai da ya kusa isa wajensa sannan yaga Ibrahim ne ya miƙe ya saka wayar a aljihu, ya miƙa masa hannu yace, “Assalamu alaikum.”

Ya Umar kamar zai wuce, amma saboda sallamar da yayi sai ya kasa. Ya miƙa masa hannu shima yace, “Wa’alaikumus salam.”

Ibrahim yace, “Fatan muna lafiya?”

A taƙaice Ya Umar yace, “Lafiya.”

Ibrahim yace, “Ina son magana da kai idan babu matsala.”

Ya Umar yace, “Magana kuma da ni? Ban gane ba, wani irin magana kenan?”

Ibrahim yace, “Toh mu zauna mana. A tsaye muke, ba lallai ka fahimce ni ba.”

Ya Umar ya tamke fuska yace, “Me zai hana na fahimta? Ai naga kamar a tsaye ma yafi. Idan har za’a kai fist ma kaga zai fi daɗi a haka.”

Murmushi Ibrahim yayi yace, “Toh shikenan. Dama maganar Zahra ce. Ina son zan tafi da matata, shine tace sai nayi magana da kai.”

Wani irin dariya Ya Umar yayi. Wannan dariyar ta kona ran Ibrahim amma ya daure.

Da kyar Ya Umar ya taƙaita dariyar yace, “Ikon Allah kenan. Ashe zaka iya zuwa neman alfarma. No wonder ma nake yi naga ka zama calm.”

Ya gyara tsayuwarsa sannan yace, “Well… amma kai ko kaɗan baka da kunya ne? Har zaka iya sake haɗa ido da ni? Can you just imagine? After everything you did to my sister, har yanzu kana kallona kamar zaka iya danne ni?”

Ya ɗan matso kusa da shi yace, “Ai na ɗauka yanzu baza ka iya tsayawa ka nemi taimakona ba ko wani abu makamancin haka. Amma yanzu kai ne a nan.”

Ibrahim ya kulu amma ya danne zuciyarsa yace, “Yanzu muna maganar abin da ya wuce ne ko kuma maganar Zahra? Ita ce ma ta aiko ni wajenka. I think maganar baya ta riga ta wuce.”

Sosai maganarsa ta ɓatawa Ya Umar rai. Har yaso ya juya ya tafi, amma sai yayi tunanin yin hakan zai bawa Ibrahim damar cigaba da halinsa.

Sai ya daure yace, “Matarka zata koma gidanka, amma ka sani sai under certain conditions… ko kuma ka jira har sai Abbah ya dawo.”

Ibrahim yace, “Da zan jira zuwan Abbah ai da ban zo ba. Dan haka menene conditions ɗin naka?”

Ya Umar yace, “Fine. Mu shiga ciki muyi magana da kyau.”

Daga haka ya fara gaba, Ibrahim ya bi bayansa.

Bayan sun zauna, Ya Umar yayi murmushi yace, “Ibrahim Khalil, ba wai Zahra ba zata koma gidanka bane. Yes zata koma, amma ka sani wallahi duk wani abu da kake mata sai ka gyara. Ban damu sai kayi min magana ba, saboda nima I have no business with you. Zahra tana under medical observation saboda lafiyarta. Idan ka cigaba da saka kanwata cikin kunci, zaka sha mamaki. Wallahi ko duk abin da na mallaka sai na zuba wajen ganin na rabaka da ita.”

Yana gama faɗin haka ya miƙe yace, “Zaka iya zuwa ka ɗauki matarka gobe tunda kun gama magana. Ni kuma na gama magana. Idan naga akasin haka zan ɗauki mataki.”

Daga haka ya fita.

Ibrahim ma ya miƙe ya bishi da kallo. Da kyar yake calming kansa har ya iya masa magana cikin nutsuwa.

Daga ƙarshe shima ya fita gaba ɗaya, amma a zuciye.

Bayan Ya Umar ya wuce ɗakinsa, yaji gaba ɗaya hankalinsa ya kasa kwanciya idan baiyi magana da Zahra ba.

Can ya sauko a hankali ya wuce parlorn Mami. Ya zauna fiye da minti goma a wajen.

Can sai ga Mami ta shigo tace, “Ahh dama Umar kana nan ne?”

Yace, “Eh. ɗazu muka yi magana da Zahra akan zan saya mata wannan.”

Ya ƙarasa maganar yana nuna mata ledar gabansa.

Yace, “Na ɗan tsaya ne a hanya shi yasa nayi dare. Gashi nazo ban san ko tayi bacci bane.”

Mami tace, “Anya? Ai naga kamar tana chatting ɗazu. Bari na duba maka.”

Ta wuce bedroom ɗinta. Ta buɗe taga Zahra kwance.

Tace, “Yayanki yana parlorn nan yana jiranki.”

Nan take ta ajiye wayarta ta miƙe tace, “Toh bari na same shi.”

Mami tace, “Ki saka hijab mana, ko haka zaki fita?”

Tace, “Eh dama zan saka.”

Ta ɗauka ta saka hijab ɗin.

Mami ta fita, Zahra ma ta fito parlorn ta same shi yana danna waya.

Tace, “Yaya ai har na gaji da jiranka. Nace ko lafiya?”

Bai ɗago ba yace, “Sorry, na ɗan tsaya ne wani abu shi yasa nazo late.”

Zahra ta ƙaraso gabansa tace, “Wannan ne ledar?”

Yace, “Uhm shine.”

Ta ɗauka tace, “Nagode sosai Ya Umar.”

Bai ce komai ba.

Ta koma ɗaya seat ɗin ta zauna ta buɗe takeaway ɗin ragadadar ta fara ci a hankali.

Sai sannan ya ɗaga kai ya kalleta. Suna haɗa ido ya sauke nasa idon ya cigaba da danna wayarsa.

Can bayan ta gama tace, “Ya Umar wai meke damunka ne? Kamar baka jin daɗi.”

Murmushi yayi yace, “I’m fine.”

Tace, “Okay.”

Yace, “Zamu iya magana idan babu damuwa?”

Nan take taji gabanta ya faɗi. Ta ɗaga kai ta kalleshi amma ta kasa cewa komai, kai kawai ta gyaɗa masa.

Yace, “Baby kunyi magana da Ibrahim ne?”

A hankali tace, “Eh, ɗazu ya zo. Ban san ma shi bane Mami tace naje ina da baƙo, da naje sai naga ashe shi ne.”

Yace, “Good. Kunyi maganar komawarki?”

A hankali tace, “A’a Yaya. Ya durƙusa yana roƙona… sai kuma ya bani tausayi. Na kasa ce masa a’a. Shine nace ya zo ya same ka, duk abin da kace shikenan.”

Yace, “A’a? Duk abin dana ce kuma?”

Ya ɗan gyara zamansa yace, “Ai tunda kika ce ya zo wajena, kin riga kin gama making up your mind.”

“Yaya…”

“Yes.”

Ya koma ya jingina da kujera sannan yace cikin ɗan fusata, “Har yanzu zaki yarda da abin da zai faɗa miki? Kince ya durƙusa? Kafin ya aure ki ai ya durƙusa yana neman soyayyarki. Saboda haka ne ma na goya miki baya akansa tunda kin yarda da shi. Yanzu kuma zaki sake yarda da salon yaudararsa?”

Ya ƙara kallonta yace, “Talk to me, baby.”

Gaba ɗaya Zahra ta rikice. Ta tsorata da yanayin Ya Umar ɗin.

Tace, “Yaya kayi haƙuri dan Allah.”

Yace, “Shut up.”

A tsorace tace, “Yaya na fasa komawa.”

Ganin yadda tayi maganar yasa ya sassauta muryarsa yace, “Zaki koma Zahra, ba zan hanaki ba. Amma duk abin da yake miki idan bai canza ba ki sanar dani. Dan wallahi akwai alkawarin ba zai sake bata miki rai ba.”

Ya ɗan yi shiru sannan yace, “Abin da nake so dake Baby shine, duk abin da zai miki ki sanar dani. Kar kiyi shiru ya cigaba da cutar mana dake, kinji?”

Kai ta gyaɗa masa.

Yace, “Kina buƙatar wani abu ne?”

Ta girgiza kai tace, “A’a babu.”

Yace, “Toh zaki iya zuwa ki kwanta.”

Ta gyaɗa masa kai.

Yace, “You can go.”

A hankali ta miƙe. Gaba ɗaya jikinta yayi sanyi.

Tace, “Yaya sai da safe.”

Yace, “Allah ya tashe mu lafiya.”

Har ta fara tafiya yace, “Baby…”

Ta juya.

Yace, “Please kar ki sa komai a ranki kinji?”

Tace, “In shaa Allah. Nagode sosai.”

#Jiddatulkyar writes #08110615256