Kenza eBookz
Cover art for FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 11

Post

FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 11

.....that's what they talked about. She said, "What did she tell you?" He said, "What you know." She was silent again and then said, "I didn't think about what to do before, that's why I turned off my phone... I don't even know you know. Please be patient for hiding what I did." He smiled and said, "I'm the one who should apologize, because I got involved in something that didn't concern me." She shook her head and said, "No Yaya, my life has affected you." He said, "Good... that's what I want you to know." She slowly said, "What are you going to say now?" He said, "I will say whatever you say." They were all silent. Then he said, "Do you want to go back to your room?" She was silent. He said, "Talk to me." She slowly said, "How I want before I go back... at least he knows my value. He regretted and promised me that he won't do this to me again. If he does, I will return home." Even though Ya Umar didn't want to hear that from her mouth, he smiled and said, "Good. Shikenan, that's okay too. Let's see where his patience will take him. Continue to leave your phone switched off." She said, "But Abbah will come back tomorrow, what will he say about my stay at home?" He said, "Because y

Standalone post2,090 words

*FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes

Young talented writers association (YOTA)

Book 1 Chapter 11

Ya Umar ne ya shigo parlorn Mami, hannunsa riƙe da bowl ɗin gauta. Zama yayi kusa da Zahra dake kwance a kan tiles ɗin parlorn yace, “Ya jikin?”

Ta ɗago kai, sannan ta miƙe ta zauna a hankali tace, “Da sauƙi Yaya.”

Miƙa mata bowl ɗin yayi, ta karɓa tace, “Nagode.”

A hankali ta soma ci. Kamar ba zai ce komai ba sai yace, “Wani shawara kika yanke?”

Ba tare da ta kalle shi ba tana cin abincin tace, “Shawarar me kenan Yaya?”

Yace, “Akan mijinki.”

Lokaci guda taji gautar ta fita mata a rai. Ta ajiye bowl ɗin tana kallonsa tace, “Yaya ban gane shawarar akan mijina ba?”

Yace, “Zahra, ina tare da ke tun ranar da aka haife ki. Kina tunanin wai zaki iya ɓoye min wani abu ne?”

Murmushin dole tayi tace, “Ai ban fahimce ka bane.”

Yace, “Kenan bakuyi magana da Firdausi ba?”

Da sauri ta ɗaga kai tana kallonsa da mamaki, amma a lokaci guda jikinta yayi sanyi. Duk da Firdausi bata gaya mata komai ba, tasan sunyi magana kenan.

Tace, “Yaya me ta faɗa maka?”

Yace, “Abin da kika sani.”

Ta sake yin shiru, can kuma tace, “Yaya nima bansan tunanin me zan yi ba tukunna, shiyasa na kashe waya ta… ban san ma kai ka sani ba. Ka yi haƙuri da ɓoye maka da nayi.”

Murmushi yayi yace, “I’m the one who should apologize, saboda na shiga abin da bai shafe ni ba.”

Ta girgiza kai tace, “A’a Yaya, ai rayuwata ta shafe ka.”

Yace, “Good… dama haka nake so ki sani.”

A hankali tace, “Yaya yanzu me zaka ce?”

Yace, “Abin da zaki ce shi zan ce.”

Duk suka yi shiru. Sai kuma yace, “Kinason komawa ɗakinki ne?”

Tayi shiru.

Yace, “Talk to me.”

A hankali tace, “Yaya ina so kafin na koma… at least ya san value ɗina. Ya yi nadama sannan ya min alkawarin ba zai sake min haka ba. Idan ya tsaɓa zan dawo gida.”

Duk da Ya Umar bai so jin hakan daga bakinta ba, sai yayi murmushi ya miƙe yace, “Good. Shikenan, hakan ma it’s okay. Let’s see inda haƙurinsa zai kai shi. Ki cigaba da barin wayarki a kashe.”

Tace, “But Abbah jibi zai dawo, me zance akan zaman da nake yi a gida?”

Yace, “Saboda kina laulayi mana.”

Kai ta gyaɗa masa.

Daga haka ya fita, his mind filled with lots of thoughts.

Sosai Zahra taji damuwa a ranta. Kullum cikin dare idan ta kunna wayarta sai ta ga countless messages from Ibrahim. Amma ko kaɗan bata ji a ranta cewa da gaske Ibrahim ya shirya canzawa ba.

Miƙewa tayi ta wuce bedroom ɗin Mami.

Tea yake sha a hankali, amma ko kaɗan bai taɓa abin dake cikin plate ɗin gabansa ba. Kamar ma bai san inda yake ba, gaba ɗaya hankalinsa baya jikinsa.

Ta daɗe tana zaune tana kallonsa kafin takaici ya cika ta tace, “Wai kai Khalil, tunanin me kake yi haka ne? Abin cin gabanka ma ka kasa ci.”

A ɗan razane ya juya, saboda bai san tana wajen ba. Ya sauke ajiyar zuciya yace, “Mama… babu komai.”

Tace, “Yaushe zasu baka matarka ne?”

Yace, “Ban sani ba.”

Tace, “Ai kafi su ƙarfi akanta. Babu wanda yake da iko yanzu sama da kai. Idan kace kana son a dawo maka da matarka ai basu isa suce a’a ba. Just be a man mana. Kana buƙatar matarka, kuma suka ce a gida zata yi laulayi… ai kai ma zaka iya kula da ita.”

A hankali yace, “Okay.”

Miƙewa tsaye yayi saboda baya son dogon surutu.

Tace, “Ina zaka?”

Yace, “Zan koma gida.”

Tace, “Abincin fa?”

Yace, “Zan tafi da shi.”

Daga haka ya ɗauki kulolin abincin yace, “Sai anjima.”

Ta ce, “Toh, duk yadda ake ciki ka sanar dani.”

Kai kawai ya gyaɗa mata.

Bayan ya koma gida, yana trying Zahra’s number, luckily kiran ya shiga. Zahra kuwa, data saka sim ɗinta a ƙaramin waya saboda zata yi transfer ɗin kuɗi, sai taga kiran sa ya shigo.

Kallo kawai ta tsaya yi har ya yanke. Wani kiran ya sake shigowa, ta sake bari ya yanke. Ganin da gaske Khalil ba zai barta tayi abin da zata yi ba, ita kuma bata son yin magana da shi, yasa kawai ta kashe wayar gaba ɗaya.

Tana kallon mai aikinsu tace, “Dauko min ATM ɗina, zan tura miki wani account number sai a min transfer na 30k zuwa account ɗin.”

“Tomm Hajiya.”

Daga haka ta juya ta fita.

Khalil kuwa ya sake kira, amma cikin mamaki yaji an kashe wayar.

“What?!” ya furta a hankali, saboda ba ƙaramin mamaki hakan ya bashi ba.

Duk messages da calls ɗin da yake mata bai taɓa samunta ba, amma wannan karon ya nuna masa cewa tana amfani da wayar ne, ganin kiransa ne yasa ta kashe ta.

Lumshe idanunsa yayi. Ya rasa ta inda zai fara. Gashi baya son ace ya je wajen iyayenta su gane meke faruwa.

Miƙewa yayi daga inda yake ya fita.

Washegari Anty Jiddah tazo duba Zahra. Suna zaune a ɗakin Zahra na gidan.

Anty Jiddah tace, “Yaushe zaki koma gidan ki ne?”

Zahra ta turo baki tace, “Anty Jidss na warke ne toh?”

Anty Jiddah tace, “Ai ke da warkewa sai kin haihu. Dan haka ki daina ce sai kin warke.”

Zahra tace, “Toh naji… amma gaskiya not now. Dan shima ai baya nan.”

A lokacin Mami ta buɗe ƙofar ɗakin ta shigo. Tana kallon Zahra tace, “Zahra ki sauko, kina da baƙo.”

“Baƙo kuma Mami?”

“Eh mana, anzo gaishe ki da jiki.”

Da kyar ta miƙe ta ƙarasa wajen wardrobe ta ɗauki hijab ta saka. Daga haka Mami ta fita ta tsaya bakin ƙofa tana jiranta.

Anty Jiddah tace, “Mun shiga uku Zahra. Ciki tun bai girma ba har kin fara riƙe baya da tafiyar masu ciki? Ni tsoro na ma kar kije ki fara posting a social media acc ɗinki”

Dariya Zahra tayi tace, “Da gaske Anty Jidss kin manta wacece Zahra? Ai ba komai nake sawa a social media ba.”

“Toh ni na sani ne?” ta faɗa tana dariya.

Zahra ta nufi ƙofa tace, “Bari na dawo Anty.”

Tana sauka ƙasa taji muryar Mami a kitchen. Ta ƙarasa wajen tace, “A ina baƙon yake?”

Mami tace, “Je ki second parlor.”

Har ta juya zata tafi sai kuma ta dawo tace, “Mami wani kalan baƙo ne?”

Mami tace, “Idan kin je ai zaki gani.”

Haka kawai taji zuciyarta ta fara bugawa.

Ta ƙarasa bakin ƙofar parlorn ta tsaya na wasu seconds, kamar mai nazari. Sai kuma ta buɗe ƙofar a hankali ta shiga, bakinta ɗauke da sallama.

Curtains ɗin parlorn a sauke suke saboda sanyin AC, bulb ɗin ɗakin kuma mara haske ne. Gashi bata ɗauko glass ɗinta ba, idanunta ma ba zasu nuna mata mutum sosai ba sai kamshin turare.

Kai hannu tayi ta ƙara hasken ɗakin.

Sai da idanunta suka sauka kansa sannan ta gane kamshin turarensa ne.

Juyawa tayi zata fita ba tare data ce komai ba, amma cikin sauri ya riƙota yadda ba zata wahala ba.

Bata san sanda ta daka masa tsawa ba tace, “Ka sake ni!”

Yace, “No please Zahra, ki tsaya muyi magana mana.”

Tace, “Ka sake ni kafin na maka ihu.”

Da sauri ya ja ta ciki sannan ya rufe ƙofar parlorn, ya saka key ya cire.

A ruɗe take kallonsa tace, “Wai me hakan ke nufi?”

Gaba ɗaya ta tsorata.

Yace, “Calm down Zahra, magana nake so muyi.”

Tace, “Ka buɗe ƙofar idan kana son na saurare ka.”

Yace, “It’s fine then, sai mu cigaba da zama a haka.”

Wani kallo take masa, amma a lokaci guda tana kallon Khalil ɗinta da ta daɗe tana missing. Ba kaɗan ba ya zama calm.

Yace, “Zahra kin dawo gida ba tare da izinina ba. Nayi ta kiranki baki ɗagawa. Gashi ko nazo baki fitowa… taya kike so mu solve issues ɗinmu a haka?”

Wani dariyar takaici tayi tace, “You still have the guts to talk?”

Ta cigaba da cewa, “Amma baka da kunya ko kaɗan Ibrahim. Ko ka manta abin da ka aikata ne sai na tuna maka?”

Yace, “Please Zahra, mu bar wannan maganar anan. Duk abin da zai faru, idan muka koma gida sai muyi magana akai.”

Wani dariya tayi tace, “Ka raina min hankali. Kana tunanin zan koma cikin kurkukun gidanka ne? Ko darajata baka sani ba balle ƙimata. Tausayi ma gaba ɗaya an cire maka a rai. Dan haka ni ba zan taɓa zama da fasiki ba.”

“Enough, Zahra!”

Yadda ya tsawa mata yasa tayi shiru na ɗan lokaci. Sai tace, “You see your life now? Ka zo kana min ihu a cikin gidanmu.”

Yace, “I’m sorry Zahra… but don’t call me a fasiki again.”

Tace, “Ƙarya nayi? Ka barni a gida bayan duk rashin kulawar da kayi min, ka kasa sauke hakkin kan ka, ka haɗa da ƙarya… amma ko kaɗan baka ji kunyar abin da kayi ba. Kuma a haka kake so na koma maka?”

Ga mamakinta, sai Ibrahim ya durƙusa kan gwiwowinsa ya haɗe hannayensa yace, “Zahra ki tausaya min ki dawo gida. Na miki alkawari ba zan sake saka ki cikin takaici ko nadama ba. I’m very sorry. Nasan nayi kuskure, shiyasa nake nan ina neman gyara.”

Zahra tayi shiru tana kallon wani waje. Ita kanta ta fara rasa me zata ce.

Ganin yanayinta yasa ya sake riƙo hannayenta yace, “Zahra please… ki tausaya min. Zan canza. Ni kaina nasan ba hankali nake amfani dashi wajen yi miki haka ba. Ki yafe min.”

Tace, “Ka buɗe min ƙofa.”

Ya girgiza kai yace, “Ki bani amsa Zahra.”

Tace, “Gaskiya bansan me zan ce maka ba. Ka yi magana da Ya Umar idan da gaske kana son na dawo.”

Wani irin furzar da iska yayi yana hargitsa gashin kansa.

A hankali yace, “Idan na samu amincewarsa shikenan ko?”

Kai ta gyaɗa masa.

Ya miƙe tsaye, ya sumbaci goshinta sannan ya durƙusa ya ɗaga hijab ɗinta da rigarta kadan yayi kissing cikin nata.

Ita dai ta kasa cewa komai.

Kamar mai raɗa yace, “Ka daina wahalar da mummy baby… be a good son.”

A hankali Zahra ta sauke idanunta.

Ya miƙe ya buɗe ƙofar yace, “Ki kira Mami ina son muyi sallama… amma ki dawo tare da ita.”

Tace, “Gaskiya hawa da sauka yana bani wahala. Let me just call her.”

Daga haka ta kira Mami ta sanar da ita cewa Ibrahim zai koma gida ne, yana son yi mata sallama.

Ta buɗe curtains ɗin parlorn da ƙofar sannan ta koma ta zauna da kyar.

Shi kuwa murmushi kawai yake mata, amma ta hana kanta kallon direction ɗinsa.

Can sai ga Mami ta shigo da sallama a bakinta. Ya zame daga kan kujera ya zauna ƙasa yace, “Mami dama zan koma ne.”

Tace, “Ayyah Ibrahim, toh ka gaishe da Mamanka ko?”

“In shaa Allah.”

Sai kuma yace, “Dama tace bai kamata na bar Zahra a gida ba saboda babu daɗi tayi laulayi ba a ɗakinta ba. Shine nace ai ban san al’adunku bane.”

Zahra bata san sanda ta sake baki tana kallonsa cikin mamaki ba. Like seriously? Har wannan maganar ma ya iya haɗawa?

Mami tace, “Ai nima da ba kuyi magana da ita akan ta zauna saboda laulayi ba, da tuni na maidata ɗakinta. Sai dai yanzu an bamu sharuɗɗa sosai akanta. Ko zata koma sai da mai aiki.”

Yace, “Ba damuwa Mami, ai wannan ba wani abu bane.”

Mami tace, “A’a anan ma za’a samu mata.”

Duk maganar da Mami take babu fara’a a fuskarta. Amma Zahra kam, Ibrahim ya gama cika ta da mamaki.

Mami ta miƙe tace, “Bayan aikin da aka ce ba’a so tayi, sannan ba’a son a daga mata hankali saboda komai can happen to the pregnancy.”

Yace, “Eh In shaa Allah babu abin da zai faru Mami.”

“Tohm yayi kyau.”

Daga haka ta fita.

Tana fita Zahra ta miƙe zata bi bayanta yace, “Zahra.”

Ta juya a fusace kamar dama jira take tace, “Me na kiran sunana? Uwar me zan maka? Ga yadda muka yi magana shine zaka min haka?”

Yace, “Nope Zahra, ai dole Mami tasan zaki koma. Shi yasa na mata magana.”

Tace, “Toh ka sani, idan har baka samu Ya Umar ba babu inda zani. Ko Mami ta min magana ma zaka sha mamakin abin da zai fito daga bakina.”

Ganin yadda ranta ya ɓaci yasa yace, “Kiyi haƙuri… zan yi masa magana Zahra. Anjima zan dawo na same shi kamar yadda kika buƙata.”

Tace, “Better.”

Daga haka ta fita ta bar masa wajen.

#Jiddatulkyar writes #08110615256