
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 10
....."Let me just call Mami, I want fish pepper soup." He said, "Alright, tell Mami the workers to install it for you." Then she called Mami. Mami was standing in the parlor after giving Abbah a cup of tea. She even got tired of Mummy's frequency. Mummy said, "Surely, if you have taken something from me in this house, it will not be said that until Zahra spent the night in the hospital, I don't know." Abbah stood up and said, "Enough, Khadija. Don't you know that you have to be patient? It was night when we found out. Seeing that you shouldn't be disturbed, that's why you were told to leave it until the morning. But now you're turning this issue around as if it's a big deal." Mummy shook her head and said, "You will never see what I see. If people outside see me, they will say that I am a bad person. Now if I am considered as her mother, I would have been told about it. She was not told about it at night either. But that's it, it doesn't matter." Abbah spoke to Mami and she went back inside, so she turned and left. As she entered her room, her phone started ringing. She raised the window and it was Ya Umar.... Ya Umar really took Zahra's head away from all thoughts, because he didn
*FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes
Young talented writers association (YOTA)
Book 1 Chapter 10
Wani kallo Ibrahim ya bi Ya Umar da shi, sannan ya ɗauke kansa ya mayar da kallonsa kan Zahra. Ita ma wani kallon take masa kafin ta ɗauke kanta. Haka kawai sai taji wani kuka ya ƙwace mata, ta juya kanta gefe ta fara shessheƙa.
A hankali Ibrahim ya juya ya fita daga ɗakin. Ya Umar ya ɗaga kai ya kalli ƙofar da ya fita, sannan ya ja ƙaramin tsaki. Ɗan kallonta yayi sannan ya miƙe haɗi da saka wayarsa a aljihu. A hankali ya taka har inda take kwance, ya ɗago ta zaune yace
“Baby, kukan me kuma?”
Ta girgiza masa kai.
Yace, “Please stop it. Bana son ki sake saka wa kanki ciwo, and stop thinking about everything right now. We can talk about it later when you feel better.”
Ta gyaɗa masa kai sannan tace,
“Firdausi tace zata zo ne?”
Ya gyada mata kai yace,
“Tana hanya.”
Tace, “Wayata fa?”
Yace, “Yana wajen Mami”
Shiru tayi sannan tace,
“Yaya, ka kira min ita.”
Miƙa mata wayar yayi, sai kuma tace,
“Bari na kira Mami kawai, dama fish pepper soup nake so.”
Yace, “Alright, ki faɗa wa Mami masu aiki su girka miki.”
Daga nan ta kira Mami.
Mami na tsaye a parlour bayan ta miƙa wa Abbah cup of tea. Har ta gaji da mitar Mummy. Mummy tace,
“Tabbas da ace kun ɗauke ni wani abu a gidan nan, ba za’a ce wai har Zahra ta kwana a asibiti ban sani ba.”
Abbah ya miƙe yace,
“Enough, Khadija. Baki san kiyi haƙuri bane? Dare ne fa lokacin da muka sani. Ganin kar a dame ki yasa aka ce a bari sai da safe. Amma yanzu kina ta juya maganar nan tana zama kamar wani babban abu.”
Mummy ta girgiza kai tace,
“Ai ba zaka taɓa ganin abin da nake gani bane. Mutane a waje su gani suce ni ce mai mugun hali. Yanzu da ace ana ɗauka na a matsayin mahaifiyarta, koman dare ai da za’a faɗa min. Ita ɗin ma ba da dare aka faɗa mata ba. Amma shikenan, ba komai.”
Abbah yayi wa Mami magana da ido akan ta koma ciki, hakan yasa ta juya ta fita.
Tana shiga ɗakinta sai wayarta ta fara ringing. Dagawa tayi sai taga Ya Umar ne....
Sosai Ya Umar ya ɗauke wa Zahra kai daga duk wani tunani, domin bai bata wani space na yin tunani ba, sai hira yake mata, and she really enjoyed being around him.
Buɗe ƙofar ɗakin aka yi, sai ga Firdausi da Mama.
Zahra tace,
“Laaa, wai Mama! Ke da baki da lafiya, Firdausi ta kama ta ɗago ki?”
Mama na dariya tace,
“Haba Fatima, ai ni na warke. Sannu da jiki. Ya jikin naki?”
Tace, “Da sauƙi.”
Firdausi ta ajiye kulan akan drawer kusa da Zahra tace,
“Ya jikin naki dai Zahra?”
Tace, “Da sauƙi Alhamdulillah.”
Firdausi tace,
“Ma sha Allah. Na saka miki ne yanzu?”
Zahra ta gyada mata kai.
Ya Umar ya gaishe da Mama sannan yana kallon Firdausi yace,
“Yanzu zaku koma ne?”
Tace, “A’a, zuwa ɗan anjima.”
Yace, “Bari naje na dawo toh.”
Daga haka ya fita.
Anty Jiddah ce ta shigo babban parlourn nasu da sallama da zimmar ta wuce wajen Mami. Haɗuwa tayi da Mummy zaune tana danna waya.
Tace, “Ah Anty Khadija, ina wuninmu?”
Ba tare data ɗaga kai ba tace,
“Lafiya.”
Abin ya bata mamaki matuƙa. Kawai sai ta fasa maganar da zata yi ta wuce sama zuwa ɗakin Mami. Babu kowa a ciki, hakan yasa ta zauna akan sofa haɗi da cire hijabin jikinta.
Sai ga shi an buɗe ƙofar ɗakin, Mami ce ta shigo.
Tace, “Ah Jiddah, kin ƙaraso ne?”
Tace, “Eh Anty.”
Mami ta ƙarasa shiga ta ajiye abin hannunta tace,
“Ai ina ɗakin Abban su ne. Dake yau ne tafiyar tasu, shine nake ɗan masa tattare-tattare.”
Anty Jiddah tace,
“Hmmm… ai naga mutumiyar tawa kamar zata fashe a parlour. Ina gaishe ta ma tana wani ɗaɗɗaga min hanci. Ke ma kinsan ni, daga haka kawai sai nayi tahowa na.”
Mami tace,
“Ai da kin tura mata a niyarta Jiddah. Kin san tun jiya take masifar ba’a faɗa mata Zahra ba lafiya ba.”
Wani kallo Anty Jiddah tayi tace,
“Dama expecting gaya mata za’a yi? Eh lallai, sannun ta ma. Komai naki tana son sani, amma abunta ko da wasa ba zaki taɓa sa ni ba.”
Mami tace,
“Ina zuwa bari naje naga ko ya fito sai mu tafi asibitin tare, tunda shi daga can zai wuce.”
Buɗe ƙofar ɗakin asibitin aka yi, duk suka maida kallonsu bakin ƙofar. Mami ce suka shiga tare da Anty Jiddah. Zahra bata san sanda murmushi ya suɓuce mata ba tace,
“My Anty Jidddsss, oyoyo!”
Anty Jiddah ta ƙaraso tayi hugging ɗinta tace,
“Sannu my love. Ashe mun kusa rasa ɗan baba”
Zahra ta turo baki tace ƙasa-kasa
“Haba Anty, kina ganin Abbah fa yana nan”
Tace,
“Ya bleeding ɗin? Ya tsaya?”
Kai ta gyada mata.
Anty Jiddah tace,
“Mu dai ki kula mana da jikanmu.”
Firdausi ta gaishe su, Abbah ya mata ya gajiyarta na jiya, suka ce babu komai.
Abbah ya ƙarasa kan Zahra, murmushi ta masa tace,
“Abbah ka shirya ne?”
Yace,
“Na shirya Baby.”
Anty Jiddah ta miƙe ta basu waje. Shafa kanta yayi yace,
“Zan wuce Baby. Zan miki transfer na wani abu, ko zaki ji sha’awar wani abin ci then use the money.”
Tace,
“Nagode Abbah. Allah ya kai ka lafiya.”
Da “Ameen” ya amsa, sannan ya miƙe yace,
“Ina Ibrahim ne? Ban gansa ba fa.”
Tayi shiru tana kallon Anty Jiddah.
Daga haka ya juya ya fita.
Maman Firdausi ma tayi mata fatan samun sauƙi sannan suka tafi. A ɗakin sai Mami da Anty Jiddah kawai suka rage.
Buɗe ɗakin aka yi sai ga Mama da Ibrahim.
Nan take Zahra tayi dana-sanin rashin kwanciyar da bata yi ba, ai da tuni tayi pretending ɗin bacci.
Shigowa ciki sukayi, aka fara gaggaisawa.
Mama tace,
“Allah sarki daughter, ashe abin da ya faru kenan.”
Zahra taji wani takaici ya tokare mata maƙogaro. Ta sauke idanunta tace,
“Ina wuni.”
Mama tace,
“Lafiya daughter. Sannu, Allah ya baki lafiya.”
A hankali tace,
“Ameen.”
Khalil ya ƙaraso jikin gadon ya ɗan duƙa yace,
“Sannu Zahra, ya ƙarfin jikin?”
Yadda kasan bango yake wa magana haka Zahra tayi masa.
Sai ma ɗan sace kallonsu da tayi, zai kuma sake magana tace,
“Dan Allah ka tashi a kaina, zan iya maka ihu babu ruwana da akwai mutane akanmu.”
Yace,
“Zahra, wannan issue ɗin za mu iya solving ɗinsa a gida. Ki daina stressing kanki da magana kina asibiti.”
Tace,
“Okay, ka ci gaba da zuwa wajen kowa kuwa zai ji maganar da yake bakina.”
Daga haka ta kwanta abinta, ko kaɗan bata damu da ko za’a gane reaction ɗinta ba.
Ibrahim ya furzar da iska a bakinsa. Mamakin Zahra sosai ya fara yi. Ya miƙe ya koma can gefe ya tsaya.
Anty Jiddah taga kamar a takure yake, ga Mama da Mami sai hira suke sama-sama, ba abin ta ce ko a basu waje ba.
Ya Umar ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo. Suna haɗa ido wani kallo ya wurga masa, shima nan ya masa irin kallon.
Mama ta miƙe tace,
“Bari zan tafi wani waje ne. Ibrahim zaka kai ni, idan yaso sai ka dawo kan matarka, tunda dai yanzu kana hutu a wajen aiki.”
Zahra ta ɗago kai jin abin da Mama tace. Da sauri ta rufe ido kar Mama tace zata mata magana. Duk Ya Umar yana lura da ita.
Ya gaishe da Mama sannan ita kuma tayi wa su Mami sallama suka fita.
Ya Umar ya ƙaraso wajen Zahra ya duƙa. Ta buɗe ido haɗi da miƙewa zaune, yace
“Baby, inje in nema miki sallama tunda jikin ya ɗan sauƙa?”
Tace,
“Yes please.”
Dama ita bata buƙatar sake dawowar Ibrahim, kuma dama plan ɗin Ya Umar kenan, yana son idan Ibrahim ya dawo ya tarar babu kowa.
Wata nurse ce ta shigo. Ya ɗaga kai yace,
“Yauwa Nurse, nace ba za’a sallame mu bane?”
Tace,
“Za’a sallame ku, amma fa gaskiya idan da so samu ne a barta anan tana bed rest, dan ba’a buƙatar tana wahala ko shiga wani yanayi.”
Yace,
“Mun sani, dan munyi magana da likitan da ya fara dubata.”
Tace,
“Toh ku sake zuwa ya muku bayani sannan ya rubuta muku sallama.”
Nufar ƙofar yayi, ita kuwa ta tsaya tana tambayar Zahra ko akwai wani abu dake damunta yanzu.
Bayan Ya Umar yayi parking a cikin compound ɗinsu, wani murmushin gefen baki yayi. Yanzu yaji wani irin relief ganinsa a gida, dan baya son Ibrahim ya rigasa karɓo mata sallama.
Sauka yayi ya zaga ya buɗe wa Mami ƙofa ta sauka, Anty Jiddah ma saukan tayi. Yana riƙe da Zahra suka fara taku a hankali zuwa ciki. A haka har su Mami suka rigasu shiga, dan a hankali yake tafiya da ita.
Bayan ya kaita ɗaki ya wuce zuwa ɗakin Mummy. Yana shiga ya same ta tana waya. Ganinsa yasa ta yanke kiran tace,
“Lafiya kazo ka saka ni a gaba?”
Yace,
“Mummy me yasa kike haka ne? Yanzu fisabilillah har aka sallamo yarinyar nan ace baki je kin dubota ba?”
Mummy tace,
“Toh sannu ubana. Nace sannu ubana. Ai komai nayi a gidan nan sai kace zaka min gyara. Ban taɓa yin abu daidai ba a idanunka, amma uwar da ta tsuguna ta haife ka ai ita kam bata da laifi.”
Yace,
“Mummy yanzu kuma wannan wani magana ne? Naga duk abin nan bai kai kiyi fushi ba. Ai da sai ki tafi dan 'yar, ba dan uwarta ba.”
Ta ce,
“Toh ban ga dama ba ubana, nace ban ga dama ba. Tashi ka fita ka bani waje.”
Yace,
“Dama zan ce miki ne an sallameta.”
Tace, “Naji, Zan shiga na duba ta.”
Ya miƙe ya nufi ƙofa yace,
“A huta lafiya.”
Yana fita ya ja mata ƙofar ɗakin.
Sosai Zahra ta samu bacci, dan har sai da su Asiya suka zo bata ma sani ba, har suka tafi kuma bata farka ba. Mummy ma ta shiga ta dubata fiye da sau uku amma duk tana bacci.
Ya Umar kuwa, kafarsa a ɗakin tafi a irga, amma ganin tana bacci sosai ya saka yaji daɗi matuƙa.
Ibrahim ne yayi parking motarsa a compound ɗin asibitin. Ganin babu motar gidansu Zahra yasa yayi murmushi, dan ya fahimci Ya Umar baya nan kenan.
Sauka yayi ya ƙarasa ciki. Shi kaɗai yasan abin da yake planning a ransa.
Yana zuwa ya buɗe ƙofar ɗakin, wasu fuskoki biyu ya gani zaune, da alama ma hira suke yi. Ya kalli kan gadon sai yaga wani yaro ne aka kwantar akan gadon Zahra.
Yace,
“Sorry, na ɗauka wannan ɗakin ne, ashe nayi ɓata.”
Fita yayi ya nufi ɗakin gaba, amma to his surprise, shi ma ba ɗakin bane.
Ya sake dawowa ya buɗe ɗakin farkon yace,
“Dan Allah ina waɗanda suke ɗakin nan kafin yanzu?”
Suka ce masa basu sani ba, dan ba’a daɗe da kwantar da su ba.
Wani irin zufa ne ya fara keto masa. Da sauri ya sauka zuwa office ɗin likita. Shiga yayi ya tambayi patient ɗin ɗakin.
Likitan yace,
“A’a ai an sallame su.”
Ya juya ya fita haɗi da dukan iska yace,
“Lalle ne ma.”
Sosai abin ya dake sa.
Driving yake amma gaba ɗaya hankalinsa baya kan tuƙin.
Can bayan Magrib, Anty Jiddah na tare da Zahra a parlourn Mami sai ga Ya Umar ya shigo. Ajiye mata leda yayi, kamshin naman da ke tashi ne ya bugi hancinta.
Shikenan, ta miƙe da sauri. Tun kafin ta kai toilet ta fara kwarara amai.
Nan take Ya Umar yayi dana-sanin sayowa.
Ba kaɗan ba Zahra ta bashi tausayi.
Tun daga wannan ranar Zahra ta kulla da laulayi. Ita duk zaton Mami, Zahra tayi magana da mijinta ne shi yasa take gida saboda laulayin, while bata san meke faruwa ba.
Ibrahim yasha kiran Zahra amma wayarta kullum a kashe. Idan yazo gidan ma haka zai ƙarasa zamansa a waje, ko yayi aika a kirata bata fito wa.
Ko da kuwa zai haɗu da Ya Umar, babu mai cewa ɗan uwansa komai.
Ba kaɗan ba Ibrahim ya shiga damuwa, dan wajen sati guda kenan suna neman sulhu amma abin ya ci tura. Ga dukkan alamu kuma Abbah baya nan, hakan yasa yake tsoron zuwansa ace har lokacin Zahra tana gida.
#Farashin Izzah #08110615256