Kenza eBookz
Cover art for FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 24

Post

FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 24

"Yesterday night," Zahra raised her eyebrows. "So?" Firdausi smiled a little. I'm tired of this talk." She said, shaking her head. "By God, I don't want to see anyone who reminds me of him." Firdausi moved closer to her. "Listen to me, Zahra..." Zahra shook her head. "No." "Listen to me," Firdausi said. Me?" Firdausi smiled a little. "Have you forgotten how you cried a few days ago?" Zahra turned away. "Have you forgotten how Ibrahim looked down on you in front of people, showing slaves and women is like a con, Zahra" she remained silent without saying anything to her. Firdausi patted her hand "Well now you have a chance to show him that he can't play the way he wants, wherever he plays the ball.....

Standalone post2,094 words

Book 1 Chapter 24

Wajen kwana uku kenan Ibrahim bai tako gidan ba, ba kira, ba message, ba kuma wata alama da zata nuna yana tunanin dawowa

Da farko abin ya dinga ci wa Zahra tuwo a ƙwarya, amma sannu a hankali ta fara sabawa

Kullum idan ta tashi daga makaranta, gidan su take wucewa kai tsaye. Zama da Mami, Abbah da Ya Umar ya zama wani abu da yake rage mata damuwa.

Duk da ciwon da ke zuciyarta, amma akwai lokutan da take mantawa da Ibrahim gaba ɗaya idan tana tare da iyalinta, Duk da ga matsin lanbam Batoul.

Yau ma kamar yadda ta saba, ta tashi da safe, ta yi sallolinta da shirye-shiryenta kafin ta nufi makaranta.

Da ta isa, ta haɗu da Firdausi a harabar department ɗinsu.

Tun daga kallon farko Firdausi ta gane yau Zahra ta ɗan fi kwanakin baya walwala, ta fara dawowa ainahin pretty Zahratyy dinta na baya

Bayan sun gama lecture na farko ne suke zaune a wani cool down

Firdausi ta matsa kusa da ita ta ce

"Na yi magana da Lovie Dovie."

Zahra ta ɗaga kai ta kalleta "Me tace?"

"Mun yi chatting jiya da dare"

Zahra ta haɗe gira. "Toh?"

Firdausi ta ɗan yi murmushi "Tace ta dawo gari"

"Okay" kawai Zahra ta ce a takaice dan bata kaunar wannan maganar

"Kuma ta amince mu haɗu yau bayan lectures" Cewar Firdausi

Nan take fuskar Zahra ta canza Ta ce "A'a, babu inda zani"

Firdausi ta zaro ido "Meye a'a?"

Haɗe rai tayi ta ce "Bana zuwa."

"Why?" Firdausi ta tambaye ta

"Firdausi na gaji da wannan maganar." Ta ce Tana girgiza Kai "Wallahi bana son ganin kowa da zaina tunamin shi"

Firdausi ta matsa kusa da ita

"Listen to me, Zahra..."

Kai Zahra ta girgiza. "A'a."

"Ki saurare ni mana" Firdausi ta ce

Shiru Zahra tayi Tana kallon wani wajen daban

Firdausi ta ci gaba.

"Ba wai saboda yarinyar ba ne, ko shi kansa Ibrahim din"

"Toh?" Zahra ta ce

"Saboda ke."

Zahra ta haɗe gira tana mata wani kallo ta ce "Yaya saboda ni?"

Firdausi ta ɗan yi murmushi.

"Kin manta yadda kika yi kuka kwanakin baya?"

Zahra ta kau da kai

"Kin manta yadda Ibrahim ya raina ki a gaban mutane, nuna bayi da mata tamkar con fuska ne Zahra"

Shiru tayi ba tare data ce mata kala ba

Firdausi ta dafa hannunta

"Toh yanzu kina da damar da zaki nuna masa cewa ba zai iya wasa da ke yadda yake so ba, ta Duk inda ya buga kwallon sai dai ya fadi ba dai ya ciki ba"

"Bana son ɗaukar fansa" ta ce ba tare data kalli firdausi ba

Firdausi ta yi dariya.

"Wannan ba fansa ba ne, Zahra"

"Toh meye?"

"Reality check." Cewar Firdausi

Zahra ta kalleta

Firdausi ta ci gaba.

"Kin san me yasa yake jin zai iya yin duk abin da yake so?"

Zahra ta ce "Why?"

Firdausi ta ce "Saboda yana tunanin komai zai ƙare da haƙuri."

Ta ɗan yi shiru.

"Yanzu karon farko zai gane cewa akwai sakamakon abubuwa"

Zahra ta fara tunanin maganar firdausi

Firdausi ta sake cewa,

"Mu tafi kawai Zahra, muje muga yadda abun zai kasance"

Zahra ta ce "Firdausi..."

"Please." Firdausi ta katseta, ta kama hannunta.

"Ko ba komai ki zo ki ji me zata faɗa."

Na wasu daƙiƙu Zahra bata ce komai ba, sai daga ƙarshe ta sauke numfashi

"Okay."

Firdausi ta yi murmushi ta ce "Yauwa, ko ke fah Zahra"

"Amma idan na ga bana jin daɗi zan tafi."

"No problem."

Daga haka suka ci gaba da lectures ɗinsu.

Bayan an gama lectures na ranar, suka yi sallama da sauran friends ɗinsu.

Firdausi da Zahra suka wuce parking space

"Straight." Cewar Firdausi ta faɗa tana ɗaure seat belt

Zahra ta tada motar "Kinga dai ban san me kika shirya ba."

Firdausi ta yi dariya "Za ki sani nan da ɗan lokaci"

A haka suka kama hanya.

Bayan kusan mintuna talatin da tafiya, suka isa wani babban garden da ake yawan zuwa shakatawa.

Wajen ya yi kyau sosai, ga ciyayi kore, ga manyan bishiyoyi, da kujeru a wurare daban-daban

Zahra ta yi parking, ta kashe motar.

Sai ta juya tana kallon Firdausi.

"Anan?"

"Eh." Firdausi ta amsa.

Suka sauka tare

Yayin da suke shiga cikin garden ɗin, Zahra ta fara jin wani irin bugun zuciya.

Ba ta san me zata gani ba, ba ta san me zata ji ba

Amma abu ɗaya ta sani... Ayau akwai wani abu da zai fito fili, dole ta sake posting hotonta da Ibrahim ko zai tafi viral

A tare suka shiga cikin garden ɗin.

Idanun Zahra suka fara kaiwa kan yarinyar tun kafin su ƙarasa. Zaune take a wani gefen wajen, sanye da wasu matsattsun kaya, riga da wando ne a jikinta, sai kanta data daura vintage scarf, tana ta danna waya

Firdausi ta ja numfashi "Ga ta can."

Ba tare da Zahra ta ce komai ba suka nufi wajen.

Da suka isa, Firdausi ce ta fara magana.

"Hello."

Yarinyar ta ɗaga kai.

"Hello."

Idanunta suka sauka kan Zahra, ta tsaya kallonta

Kallo irin wanda ba a iya gane ko na mamaki ne ko na ƙiyayya ba, sai kallon take yi, tun daga kanta har ƙafafunta.

Zahra kuwa ta zauna cikin nutsuwa kamar bata lura da kallon data ke mata ba

Firdausi ta gyara zamanta.

"Yaya dai?"

Yarinyar ta ɗan yi dariyar gefen baki.

"Lafiya, Ashe dai kuke son gani na"

Amma idanunta suna kan Zahra ta karasa maganar

Firdausi ta lura da hakan

"Kin san dalilin da yasa muka kira ki ko?"

Kai ta girgiza. "A'a, ai sanin gaibu sai Allah"

Firdausi ta ce, "Maganar Ibrahim ne, Wanda kike tare da shi, wato khalil"

Nan take fuskar yarinyar ta canza.

"Toh? Ai nariga da nayi sensing hakan"

Firdausi ta nuna Zahra "Wannan ita ce matarsa"

Yarinyar ta kalli Zahra, sai ta sake kallonta, daga ƙarshe ta ce,

"Na sani, na mata farin sani a media, ai shiyasa Nace miki nayi sensing abun daya kawo ku"

Zahra da Firdausi suka kalli juna

Firdausi ta haɗe gira. "Kin sani?"

"Eh." Tace a takaice Tana tauna cingam

"Yaushe kika sani?" Firdausi ta ce

"Wannan kuma ruwana ne" Ta ce ba tare data kalle ta ba

"Bangane ba?" Firdausi ta ce

Ta ɗaga kafaɗa. "Dama ba lalle ki gane ba"

Firdausi ta fara jin haushi "Kin san yana da mata amma kika ci gaba da bin sa?"

Yarinyar ta kalli Firdausi "Haramun ne dan ina tare da shi?"

Firdausi ta yi shiru Tana mata wani kallo, Zahra kam bakinta rufe wa yayi dan mamaki

Yarinyar ta ci gaba. "Shi yake bina, ni bana binsa."

Zahra dai tana zaune tana kallonta.

A hankali ta ce, "Kin san amma auren mu bai dade ba ko?"

Yarinyar ta juyo gareta.

"Eh."

"Toh me yasa baki nesanta kanki ba?"

Wani murmushi yarinyar ta yi.

"Saboda ba ni ce matsalarki ba."

Nan take Firdausi ta fusata. "Excuse me?"

Yarinyar ta juya gareta.

"Ehhh kar ki tsoma dan ba'a min ihu! Idan mijinta yana bina ai shi ya kamata ki kama, ba ni ba."

Firdausi ta matsa gaba "Kin san me kike faɗa kuwa?"

"Na sani." Yarinyar ta amsa ba tare da tsoro ba.

"Ni ba wata yarinya ce da za a zauna a yi min kashe di ba. Idan Ibrahim ya kira ni, matsalarsa ce"

Firdausi ta zaro ido. "Wallahi kina bani mamaki."

"Ni kuma ke kike bani." Yarinyar ta mayar.

Zahra ta ji kanta yana sarawa. Tun da suka zo ba ta ga wata alamar nadama a tare da yarinyar ba, sai ma wani irin taurin kai.

Firdausi ta sake cewa,

"Toh idan kin san yana aure me yasa baki block ɗinsa ba?"

Yarinyar ta yi dariya.

"Saboda bani da tsoro kuma Ina son sa kamar yarda yake mutuwar so na"

Nan kam Firdausi ta fusata sosai

"Wallahi kina raina mana hankali, wani irin banzar magana ne wannan"

"Idan raini ne ma, ai ba ku ne kuka zo nemana ba?" Yarinyar ta mayar da martani

Zahra ta ji gaba ɗaya bata son zaman wajen, ta miƙe tsaye.

Firdausi ta kalleta." "Zahra...."

"Mu tafi" ta faɗa a taƙaice

Firdausi ta kalli yarinyar cikin takaici

Ita kuwa sai kallonsu take yi, tanaa tauna cingam tare da kaɗa kafa, kamar ma tana jiran su tafi ne dan kamar sun tare mata iska

Ba tare da ƙarin magana ba suka juya suka bar wajen.

Har suka isa motar Zahra babu wacce ta ce komai, ran kowa a ɓace yake.

Da suka shiga mota, Zahra ta dafa steering tana kallon gaba.

Sai daga ƙarshe ta juya ta kalli Firdausi.

"Kin ga abin da kika jawo mana?" Muryarta cike take da takaici "Wallahi da nan zo ba, gashi munja ma kanmu rai ni" sai kuma ta suke ajiyar zuciya ta ce

"Dama daga ganinta bata da tarrbiyya, dagaske nayi nadaman zuwa"

Firdausi ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta rasa abin cewa, domin ita kanta ba wannan take tsammani ba

Ta yi zaton za su haɗu da wata yarinya mai tsoro ko kunya like pretty, amma sai suka tarar da wacce ko kaɗan bata damu ba lalle taji ɗarr

A hankali Firdausi ta jingina da kujera.

Shiru ya mamaye motar. Kowacce na nata tunanin.

Kuma karon farko tun da suka fara wannan shirin, Firdausi ta kasa samun kalmar da zata kwantar wa Zahra hankali.

A haka dai suka rabu da Firdausi.

Tun daga hanyar dawowa gida, Zahra bata sake cewa komai ba. Abubuwan da suka faru a garden ɗin ne suke ta yawo a kanta. Ko da Firdausi ta yi ƙoƙarin yin magana, amsawa kawai take yi da "hmm" ko "toh."

Da ta isa gida kai tsaye ɗakin Mami ta wuce.

Mami tana zaune kan kujera tana duba wasu takardu lokacin da Zahra ta shiga.

"Assalamu alaikum Mami."

"Wa alaikumus salam."

Mami ta amsa tana ɗaga kai.

Da kallon farko ta lura Zahra bata cikin yanayi mai kyau.

"Zahra lafiya?"

Murmushi Zahra ta yi wanda bai kai zuciya ba.

"Lafiya lau Mami."

"Kinga fa ,kamar ba lafiya ba."

"A'a Mami, stress ne kawai."

Mami ta ci gaba da kallonta na wasu daƙiƙu.

Sai daga ƙarshe ta gyada kai.

"Toh Allah ya sauƙaƙa."

"Ameen, Mami naa, ta ce

Zahra ta kwanta a gefen Mami na ɗan lokaci, amma gaba ɗaya hankalinta baya wajen.

Mami ma ganin bata son magana yasa ta ƙyaleta.

Can mai aikinsu ta shigo ɗakin da plate din snacks sai kuma smoothie, Zahra ta mike ta karba ta ce

"Sannu Fatima"

Murmushi tayi ta ce "Bakomai hajiya karama" tama Mami ma sallama daga haka ta juya ta fita

Kadan Zahra taci ta sake kwnaciya gefen Mami

Daga baya ta miƙe ta wuce ɗakinta na gidan ta kwanta, har aka yi Magrib.

Bayan ta idar da sallah ne ta yanke shawarar komawa gidanta.

Tayi wa Mami sallama, Mami ta ce

"Ki shiga kitchen ki ɗiba abincin kar ki tafi ki shiga kitchen"

Murmushi tayi ta ce "Mami kin manta akwai Farida ne, kuma nasan ta ajiye min" daga haka ta sake mata sallama

Ya Umar ma ya nace sai ya rakata har gida

Da ƙyar ta lallaba shi ta ce zata iya tafiya ita kaɗai.

A haka ta shiga motarta ta kama hanya.

Tafiyar ma ba daɗi take mata ba.

Tunanin Ibrahim ne ya sake dawowa. Kwana uku kenan, babu kira, babu message

Babu kuma wata alama daga gare shi. Wani lokaci har tana mamakin ko yana tunaninta ma

Da ta iso layinsu, horn tayi mai gadi ya bude mata gate, shiga tayi da motar

Sai dai tun kafin ta ƙarasa parking, idanunta suka sauka kan wata mota

Nan take ƙafarta ta tsaya, ta sake kallon motar

Ta san motar sarai, Motar Khalil ne

Wani irin mamaki ya bayyana a fuskarta.

"Khalil?" Ta faɗa a hankali

Ta kashe motarta amma bata fito nan take ba, zama kawai tayi tana kallon motar

Me yake yi a gidan? Yaushe ya zo? Kuma me ya kawo shi bayan duk abubuwan da suka faru?

Wani irin bugun zuciya ta fara ji. A hankali ta buɗe ƙofar motar ta fito.

Idanunta na kan motar.

Har yanzu ma kamar bata yarda da abin da take gani ba.

Ta ɗaga kai tana kallon saman gidan. Haske na fitowa daga parlorn ƙasa.

Alamar akwai mutane a ciki, ta haɗiye miyau.

Sannan ta kama hanyar shiga gidan a hankali.

Yayin da take isa bakin ƙofar parlorn, zuciyarta tana bugawa da ƙarfi.

Tayi sallama kafin ta tura ƙofar ta shiga.

Nan take idanunta suka sauka kan Khalil.

Yana zaune a parlorn, shi kaɗai.

Kuma kamar wanda ya daɗe yana jiranta.

#Farashin izzah #jiddatulhayr writes #08110615256