
Post
KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 11
.....because I am sure that I am the luckiest husband, I am asking God to give us peace and mutual understanding." Hunaif smiled happily and said; "Aameen Ya Rabbi, I'm very happy and proud to be called your husband. Now when will it be brought to me?" "Tell my husband." "I have given you the right to choose the date you want, then tell me." They continued their conversation of lovers to love each other. _____________ On the part of Humaira, the admission list of Bayero University went out and she saw her name on the first list as the Dean had promised to Alhaji Sani, Humaira was very happy with this admission that she got, Alhaji Sani's efforts made her start to work even though she did not have anyone. feelings for him, but she decided to teach herself to love him because he is her lover. Alhaji Sani went shopping for her, he was parking his car and said goodbye to him. Humaira came out to bathe and heard the boy who was sent to work outside. She calmly put on her black material gown Hijab on, she drank some lip gloss.....
KOMAI YA YI FARKO
PAGE 11
Zee na shiga gida ta kusan cin karo da Mamanta da ta fito daga kitchen ɗauke da cup ɗin shayi, har saida ruwan zafin ya ɗan zuba mata, not minding ruwan zafin da ya fantsamu mata, ta riƙe hannun Mama, tace; "Mama wai aure aka ɗaura min?" Mama na murmushi ta wuce falo, Zee ta bi ta a baya. Mama ta ajiye cup ɗin hannunta a kan table, ta nuna wa Zee wajen zama a gefen ta, Zee ta zauna tana kallon Mama waiting for explanation. Mama ta gyara murya tace; "Duk wanda ya faɗa miki, bai yi miki ƙarya ba, A yau iyayen saurayinki suka nemi alfarmar a ɗaura auren kawai, and their wish was granted, yanzu dai Hunaif ya zama mijinki." Wani rungume Mama Zee ta yi, ta ƙwaƙwumeta sosai, tace; "Alhamdulillah, I'm so happy Mama.''
Zee na shiga ɗakinta ta dannawa Hunaif kira, immediately ya yi picking kamar daman jiran kirar yake, murya cike da shauƙi Zee tace; "Hello angon Zee."
"Na'am Mrs Muhammad Hunaif, kin tabbatar da maganata kenan?"
"Eh na gasgata, kuma na fi kowa farinciki saboda ina da tabbacin na fi kowa sa'ar miji, ina roƙon Allah da ya bamu zaman lafiya da fahimtar juna." Murmushin jin daɗi Hunaif ya yi, yace; "Aameen Ya Rabbi, I'm very happy and proud to be called your husband. Yanzu dai yaushe za a kawo min ke?"
"Sai ka faɗa mijina."
"Na baki dama ki zaɓi ranar da kike so, sai ki faɗa min."
Suka cigaba da hirarakin su ta masoya ma su son juna.
_____________
A ɓangaren Humaira kuwa list of admission na Bayero University na fita ta gan sunanta a first list kamar yadda Dean ya yi wa Alhaji Sani alƙawari, Humaira ta yi murna sosai da wannan admission da ta samu, ƙoƙarin da Alhaji Sani ya yi mata ya saka ta fara kulashi duk da ba ta having wani feelings akan shi, amma ta ƙuddira a ranta zata koyawa kanta sonshi don shi ɗin mai sonta ne.
Ana gobe za ta tafi school Alhaji Sani ya yo mata siyayya sosai ya kawo mata, yana parking motarsa ya aike yaro cikin gidan ya yi masa sallama da Humaira. Humaira ta fito wanka kenan tana shafa mai taji yaron da aka aika yana faɗawa Mama Lantana dake aiki a waje wai ana sallama da Humairan a waje. A natse ta ƙarasa shafa manta, ta shirya cikin black material gownn sannan ta ɗora jan hijjabi akai, lip gloss ta ɗan shafa a laɓɓanta da suka fara bushewa saboda yanayi na hunturu, ta ɗauki ɗaya daga cikin slippers ɗinta ta saka, ta kalle Inna dake zaune tana karanta littafin akhadari, a ɗan kunyace tace; "Inna bari na ɗan fita."
Inna ta kalleta da kyau sai tace; "A dawo lafiya."
Tunda Humaira ta fito Alhaji Sani ya ƙureta da ido daga cikin motar, ta yi ƙara kyaune a idonshi, lips ɗinta sai shining ɗin lipgloss yake yi, buɗe ƙofar motar ya yi ya sauko don ya san ba za ta taɓa ƙarasowa ba, iyakarta ƙofar gidan ne ba ta ƙara ko one step. "Barka da wannan lokaci sarauniyar kyau."
Guntun murmushi Humaira ta yi, murmushin da ya kusan sa Alhaji Sani rikicewa, murmushi ne da ya ƙara fito da zallar kyau da Allah ya yi mata, tace; "Ina wuni."
"Lafiya ƙalau Humaria, ƴan matan Bayero University."
Rufe fuskarta ta yi da hannu, murmushi Alhaji Sani ya yi, yace; "I'm not staying long today, gobe zan yi tafiya zuwa Kaduna, ba zan samu zuwa na kai ki ba shiyasa na kawo miki ɗan abun da na samu na siya miki." Ya miƙa mata ledodin hannunsa. Karɓa Humaira ta yi, tace; "Nagode Allah ya saka, ya sa ka fi haka, amma don Allah ka daina yi min siyayya haka, siyayyar ta yi yawa."
"Ban yi miki komai ko ba Humaira, I can do anything for you saboda son da nake miki."
"Nagode." Humaira ta faɗa emotionally.
"Ki shiga ciki ina kallon ki kafin na tafi." Murmushi Humaira ta yi ta juya zuwa cikin gida Alhaji Sani na kallonta. Tana shiga gida shi kuma ya koma wajen motarsa, zai shiga kenan wani saurayi ya tare shi, yace; "Assalamualaikum bawan Allah, Allah ya sa ba sauri kake ba?" Girgiza kai Alhaji Sani ya yi, yace; "A'a, Allah dai ya sa lafiya."
"Eh to lafiya dai ba lafiya ba, daman game da wannan yarinya da kake zuwa wajenta Humaira." Alhaji Sani ya tattara hankalinsa ya ba wa saurayin, yace; "Me ya faru?"
Saurayin ya gyara tsayuwarsa yace; "Ban san ko ta faɗa maka cewa ta zubar da mutuncinta ba "
Sounding confused Alhaji Sani ya ce; "Ban fahimceka ba."
Nan saurayin ya tsara masa maganganun gaskiya da ƙarya akan fyaɗe da aka yi wa Humaira, ya kuma faɗa masa akan ana ma zargin ƴar iska ce kawai fakewa take yi da an yi mata fyaɗe. Alhaji Sani kamar an dasa shi a wajen saboda mamaki, he just can't believe abubuwan da kunnuwarsa ke ji akan Humaira, amma idan gaskiya ne me yasa suka zaɓi su ɓoye mishi gaskiya, meyasa ko da bakin wasa ba su taɓa nuna masa ko da alama ne, kawai sai ya ji a zuciyarshi bai yarda da saurayin ba, zai gudanar da bincike akan abinda ya faɗa masa, idan kuma ƙarya ne sai ya ɗauki mummunar mataki akansa.
Humaira kuwa tana shiga gida ta gan Inna ta fito tsakar gida, tana zaune da matan gidan suna aikace-aikacensu suna hira, a gaban Inna Humaira ta ajiye babban ledar dake cike da kayyaki, tace; "Inna gashi ya kawo min."
Inna ta janyo ledar, ta fara fitar da kayakin ciki, tana faɗin; "Allah sarki bawan Allah, Ubangiji ya biya shi duniya da lahira, amma kamar hidimar nan ta yi yawa fa." Provision ne sosai, sai da waya Tecno spark 4, da kuma ƙaramar envelope, buɗe envelope ɗin Inna ta yi, kuɗi ne a ciki naira dubu hamsin, Inna ta cire ten thousand a kuɗin ta bawa su Mama Lantana dubu biyar biyar tana faɗin; "Gashi ku siya sabulu, kuma ku mori arzikin ƴar ku." Humaira kam ciki ta shiga ta bar Inna da kayakin a gabanta tana ta suburbuɗawa Alhaji Sani albarka.
Washegari da sassafe Kabir ya raka Humaira har gidan Mallam Sadi abokin Abba, wanda a nan ne za ta zauna tana tafiya makaranta Daga nan, saboda makarantar is trekkable daga gidan. Mallam Sadi ɗan kasuwane, yana siyar da materials da kuma takalma. Matarsa Umma A'i ta rinƙa yi musu Maraba da fara'a, ɗayar Umma Rabi kuma tana zaune daga gefe ko ɗaga ido ta kallesu ba ta yi ba.
A ɗakin ƴanmata aka sauke Humaira, Mallam Sadi na da yara ƴan mata uku, Laurat, Aisha da Hannatu, sai samari biyu; Ahmad da Yunusa, babbar ƴarsa Latifa ta yi aure tana da yara huɗu.
Kabir bai wani zauna ba ya juya baya, aka bar Humaira ita kaɗai a ɗakin da kwanon abincin da Umma A'i ta kawo mata a gabanta. Ƴan matan gidan duk sun tafi makaranta, matan gidan kuma suna aiki a tsakar gida. Wayar da Alhaji Sani ya siyo mata ta ciro daga cikin jakarta, ta kunna ta fara buga game don ya ɗauke mata kewa. Few minutes da kunna wayarta sai ga kira ya shigo, jiya da daddare Yaya Kabir ya kaita aka siyo mata, lambar ƴan gidansu kawai take dashi, mamakin wanda ke kira ta yi saboda lambar is not saved a wayarta, a hankali ta yi picking call ɗin kamar mai tsoron taɓa wayar, ta yi shiru bayan ta saka wayar a kunne. "Hello sarauniyar kyau." Ta ji muryar Alhaji Sani daga cikin wayar. "Ina wuni." Ta faɗa a hankali.
"Lafiya ƙalau Humaira, ya gajiyan hanya?"
"Alhamdulillah."
"Masha Allah, a yi karatu fa."
Gyaɗa kai Humaira ta yi kamar yana gabanta, sannan tace; "In Sha Allah, thanks for everything."
"Don't mention dear."
Shawarwari Alhaji Sani ya ba ta na zama gidan mutane da kuma yanayin rayuwar jami'a kafin ya katse kiran, ko da wasa bai nuna mata akan ya ji komai game da ita ba. Humaira na ta zaune ita kaɗai har bacci ya ɗauketa.
____________
A ɓangaren Hunaif kuwa shirye-shiryen tarɓar amaryarsa yake yi babu kama hannun yaro, da farko iyayen Zee sun buƙaci a basu watanni huɗu su yi mata kayan ɗaki da gyaran jiki, amma ɓangaren Hunaif suka nuna ba su buƙatar amaryar ta zo da komai, don haka suka ba ta wata guda na gyaran jiki, a cikin wata guda yanzu saura kwanaki uku. Gidansu Hunaif za a fara kaita ta yi kwana biyu kafin ta ɗaga zuwa Brazil. Yau aka zo aka fixing masa sabbin furnitures a ɗakinsa, carpenters din na tafiya ya kira Zee video call; "Hello Mrs Hunaif." Murmushi Zainab ta yi, tayi wani fari da ido wa Hunaif dake kallonta ta cikin waya tace; "Masoyina da fatan kana lafiya."
"Lafiya ƙalau my wife, na kira ki gan ɗakinki ne." Hasko mata ɗakin ya yi, Zee ta wani zato ido, tace; "Wow! Don't tell me this is our room?" Gyaɗa mata kai ya yi, yace; "It is dear."
"It's so beautiful, I love it, can't wait to be there with you."
Murmushi Hunaif ya sakar mata, ya ɗaga mata gira ɗaya ya ce; "What can't you wait for?"
"To be in your arms, na ji ni akan ƙirjinka."
Ɗaga mata gira ya yi, yace; "And what again?"
Hararar shi Zee ta yi, tace; "Stop thinking far bad boy."
Murmushi Hunaif ya yi, su ka cigaba da hirar su na soyayya.