
Post
HIYAAM HAUSA NOVEL PAGE 6
..... on her face, her hair was red and she was shaking like a madwoman, she was screaming and scratching her claws on her body, blood was coming out wherever she put her fingernails, so blood was coming out. Lami's back quickly said, "Hey, I'm going to go in three, we are very damaged!" Dikko shook his head worriedly and said, "Batty, what's wrong with you, Batty boy?" He said in a low voice because his body was shaking because he was afraid of the girl's condition and his heart was broken. She slowly raised her head and opened her colored eyes, seeing the way his eyes were red and protruding as if they were the eyes of people, he put them in Lami's stomach. "I don't hear that from her, Lami." Then he went straight to where Batty was kneeling and he also knelt there and put his hand and took her hand calmly and carefully and said "What happened to this girl?" She opened her mouth to speak and they heard the cry of the mage filling the room, a kind of unpleasant cry and a loud noise came out, the urine was already filling Lami's pants and her body was trembling. "Speak, Batty, what?" This time Batty's alternative voice came out and she cried too.....
*H I Y A A M*
Page 6: Haunted by Blood
Bright pens Yota/001
“You are a blessing, and I pray happiness never leaves your side.” Nazeefah Sabo Nashe
A firgice ta farka daga mummunan mafarkin data afka a cikinsa, wani irin nishi take yi numfashinta yana yin sama ƙirjinta na ɗagawa, kaf-kaf kuma haka duka ilahirin jikinta ya shiga rawa da kakkarwa zufa sai yanko mata take yi, ta kasa buɗe idanunta saboda tsoran daya gama gigita mata nutsuwarta tunanin abin da ya faru da inda taga kanta ya tsayar da tunanin ƙwaƙwalwar Batty cak waje guda. Ta jima a haka kafin ta saki wata iriyar ƙara me firgitarwa tana yin baya tare da kakkare jikinta tana ganin kamar mutanen zuwa za su yi su kamata.
"Ƙarya nake yi, ba sunana Fatima ba" Gabaɗaya ta ruɗe ta fita daga hayyacinta
"Bani ce wacce kuke nema ba, don Allah kar ku bari ya yi mini abin nan bani ce ba" da wani irin sauri aka ɗaga assabarin bukkar tare da shigowa ciki, Lami ce ta haske fuskar Batty sai taga kamar ba Batty ɗin ba, lokaci guda ta sauya ga fuskarta ta yi jajur sumar kanta ta kunce ta hargitse kamar mahaukaciya sai ihu take yi tana karta faratanta a jikinta jini na fita a duk inda ta saka farcen hannun nata haka jini yake fitowa. Baya Lami ta yi da sauri ta ce
“Kai ni kam na shiga uku, mun lalace ƙwarai!” Dikko ya girgiza kai cike da damuwa ya ce
"Batty, kai yaro Batty meke damunka?" Ya yi furucin cikin sarƙewar murya domin shi kan shi jikinsa rawa yake yi saboda tsoron yanayin yarinyar daya gama gitta masa zuciya. A hankali ta ɗago kanta tare da buɗe rinannun idanunta, ganin yadda idanun ya yi wani irin jaa ya firfito waje kamar bana mutane ba, ya saka cikin Lami juyawa ta yi saurin saka hannunta ta dafe cikin ta ce
"Ko dai Batty nada iska Dikko?"
"Bana jin haka daga gare ta Lami" Sai ya yi gaba daidai inda Batty ke durƙushe shima ya durƙusa a wajan ya saka hannunsa ya kama hannunta cike da nutsuwa da kulawa ya ce "Mene ya samu ɗiyar nan?"
Baki ta buɗe za ta yi magana sai suka ji kukan mage ya cika ɗakin, wani irin kuka mara daɗin ji wani amon sauti na fita, tuni fitsari ya cika wandon Lami jikinta sai rawar ɗari yake yi. "Yi magana Batty menene?" Wannan karon ma madadin sautin muryar Batty ɗin ya fita sai kukan mage ya sake karaɗe wajan, kafin kuma tif su ji ƙarar saukar abu a gadon bayan Dikko, wani irin hantsilawa Lami ta yi tare da yin allandugure ta kifa, zanin jikinta ya yi gefe guda bata tsaya ɗauka ba ta yi waje fitsari na bin cinyoyinta, a hanya ta haɗu da Sadiatu data fito da sauri tana kiran Dikko ta faɗa masa cewa Allah Ya yi wa yaron Kulu rasuwa, suna haɗuwa da Sadiatu a hanya ta yi gefe zata shige ɗakinta. Sadiatu ta ce
"Lami yaron Kulu ya koma" Kafin Lami ta yi magana sun ji yo ihun Dikko daga cikin bukkar Batty wani tsalle suka yi tare da rungume juna suna salati da ƙarfi, suna rungume da juna Dikko ya fito a guje yana faɗin ya shiga uku zata kashe shi ta cinye masa hannu, tun kafin ya ƙarasa fitowa Lami da Sadiatu sun rugasa ƙarasawa cikin bukkarsa kafin ya ƙarasu sun rufe yana ganin haka ya yi kwana ya nufi ɗakin Kulu wacce take rusa kukan rashin jaririnta.
Yana zuwa ya tarar itama ta rufe ɗakin nata, sai kawai ya fashe da kuka ya kama bukkar Kulu ya haye saman bukkar, yana hawa kamar an ce ya juya suka yi ido huɗu da wata baƙar mage jibgegiyya da ita idanunta jajur sai haki take yi tana zaro harshe waje. Cak numfashin Dikko ya tsaya a ƙirjinsa daga nan bai sake sanin abin da yake faruwa ba.
Dikko na fita daga bukkar Batty sai ta yi saurin miƙewa tsaye idanunta rufe ta fito farfajiyar gidan shiru babu kowa, sannu a hankali ta dinga takawa har ta isa banɗaki ganin babu me ganinta ya saka ta tsugunawa waje guda ta cure jikinta, tana daga durƙushen ta fara wata kalar rawa da girgiza ta kafe yatsun ƙafarta a ƙasa tana kartar ƙasa dasu, a hankali halittar jikinta ya fara sauyawa zuwa suffar mage bata ɗauki lokaci ba, ta koma wata baƙar mage me jajayen idanun ta yi tsalle tare da haure kewayen banɗakin ta yi waje abin ta. Tafiya magen take yi hankali kwance da idanunta na huɗun take cin karo da kurwar jama'a dake yawo a duniya a cikin sakaliyar daren.
Dake yawanci sai dare yayinda gangar jikin mutum ke kwance yana samun nutsuwa a wannan lokacin ne kuma kurwa take tashi ta shiga duniya ta dinga yawo, wannan dalilin ya saka idan ka haɗu da mutum a zahiri sai ka fara tunanin kamar ka san shi, kuma ka rasa inda ka taɓa ganinsa. Hakan ya faru ne dalilin kurwarku data haɗu da daddare a hanya. Wasu kuma na cewa
Ruhi ne yake tashi yabar gangar jiki.
Tunda Batty ta yi arba da Mado ta ji ranta ya biya, domin yana da kitse sosai jininsa da namansa masu kyau ne za su yi daɗi a baki. Wannan dalilin ya saka ta biyo dare ko za ta iya cimma burinta a wannan karon, wannan ne lokaci na farko da take jin ba zata iya haƙura da abin da take ji ba akan Mado ba. Har cikin gidan Moddibo ta kutsa kai cikin sa'a ta samu ɗakin Mado ta haye rufin ɗakin ta shiga rera masa kuka a cikin kunne mara daɗin ji saboda wani amo da yake fita a ciki
"Mado... Mado... Mado..."
Haka magen ta dinga kiran sunansa.
A firgice Mado ya farka jin abin ya yi kamar a mafarki, ya zabura ya miƙe tsaye yana juyawa ya ci karo da Moddibo yana tsaye, Mado ya nufi wajan mahaifinsa yana faɗin
"Baka ji ba?"
Ya girgiza kai. "Baka ji kukan mage ba?"
"Sunana na ji ana kira" Moddibo ya kalli Mado, a wannan lokacin da Mado ya nutsu zai iya hango ƙwayar idanun Batty a cikin idanun Moddibo zai fahimci Batty ce bawai mahaifin nasa ba. Moddibo ya miƙa hannu kamar zai riƙo Mado sai kawai ya kai hannun zuwa wuya Mado ya shaƙe masa wuya, Mado ganin Mahafinsa ne sai bai shiga ramawa ba, ya dinga kokawar ƙwace kan shi amma ya kasa, sai da aka kai Mado ƙasa baya ko motsi kafin Moddibo ya bar ɗakin daidai nan magen ta yi sauri ta fice daga cikin gidan gabaɗaya.
Sama-sama ya ji ana kiran sunansa, gabaɗaya jama'ar gidan sun cika ɗakin Mado saboda ihun daya dinga yi, a hankali ya buɗe idanunsa sai yaga ƙannensa da sauran ƴan'uwansa, salatin da ya ji ana yi ne da tofin da ake yi masa da sautin muryar Moddibo ya saka Mado ƙoƙarin juyawa amma ya kasa saboda kasalar data saukar masa a jiki, ga wuyansa daya kumbura.
Sai ya mayar da idanunsa ya lumshe.
***
Bayan sallar issha'i duk suna zaune a ƙasan bishiyar da Iftihal ta shimfiɗa musu babbar tabarmar da suka saba zama akai wajan cin abinci da hira. Jadid da Jaheed na zaune suna hira sai Iftihal data gama jera musu kwanikan da aka kwasa tuwo da miya a ciki haɗe da babban tire da babban jug, Innti na saman darduba tana azkar. Jadid da yake ta jin sauyin yanayin da yake tabbatar masa ciwonsa zai tashi yaja idanuna ya lumshe a ƙasan zuciyarsa yana addu'ar Ubangiji ya sauƙaƙa masa wannan jarrabawa ya kawo masa da sauƙi. Babban yaya ne ya shigo ciki hannunsa ɗaya cikin aljihu ɗaya kuma riƙe da wayarsa farar Jallabiya ce a jikinsa wacce tabi fatar jikinsa ta kwanta yana da buɗaɗɗan ƙirji tsayi da faɗi a tsaye yake sosai, bai saka hula ba, sai kyakkyawar sumar kan shi data bi fatar wuyansa ta kwanta sai ɗaukan idanu take. Sun san dole zai yi sallama duk da basu ji ba, amma haka suka haɗa baki wajan amsawa. Ya nemi waje ya zauna.
Iftihal ta ƙarasu inda yake ta durƙusa har ƙasa ta ce "Barka da dare Babban yaya, ya aiki?" A nutse ya dubi Iftihal kafin ya ɗan lumshe idanunsa, gargasar idanunsa suka sauka a fatar idanun nasa ya sakarwa Iftihal murmushi. Ta ce "Babban yaya za mu fara exam ta shiga Ss 1 a makaranta gobe"
Ya zuba mata ido, sai ya miƙa hannunsa kaɗan ya riƙe nata ya ɗan matse kasan
Alamar "I wish you all the best" Cikin jin daɗi ta ce
"Thank you Babban yaya" Wajanta ta koma ta zauna, Babban yaya kuma idanunsa ya dinga juyawa yana neman inda zai hango Ana amma bata tsakar gidan. "Ƴan'matan Innti ana ta girma wasa-wasa daga secondary school sai University sai kuma aure, ina ka gane mini fuskar tagwaye a ɗakin miji? Musamman ke" ya ƙare maganar yana kallon Iftihal.
Iftihal ta ce "Kai Yaa Jaheed, aure kuma?"
Ya ce "Shi fa, ai kece bakya damun mu da maganar saurayi ko miji. Ita kuma tattabara kullum maganar Allah ya bata kyakkywan miji take yi koda maye ne ba ruwanta"
"Ko kuma Aljani ba" cewar Jadid.
Babban yaya ya watsa ƙwayar idanunsa a fuskar Jadid jin ya ce Alljani sai ya ɗauke kai.
Innti data kammala azkar ta ce "Ƙuruciya dangin hauka, mazan yanzu ya ka ƙare dasu balle ka dinga yi wa kan ka mummunan alkaba'i? In sha Allah mazaje nagari Ubangiji zai muku tukuci dasu, kuma za ku samu mataye na gari da za su zame muku abin alfahari. Bani da addu'a wacce ta shige taku"
"Muna godiya uwar arziƙi irin albarka, Allah Ya yi mana arziƙin da za ki ji daɗi a duniya Babarmu"
Ta ce "Arziƙi na tsoran Allah in sha Allah"
Iftifal ce ta ce "Innti shalele bata fito ba?"
"Ƙyale Ana kin ji Iftihal miskilancin ne ya motsa tun ɗazo take ta ƙunci, kin san an yi tuwo" suka kwashe da dariya abin su.
Ɓata fuska Iftihal ta yi ta ji itama abincin ya fita a kanta tunda mahaɗinta haka zata kwana da yunwa, gashi yau ta fahimci akwai abin da yake damun Innti taƙi nuna musu ne. "Innti nima na ƙoshi, bari na jira ki yi mana tatsuniya kawai kafin na kwanta"
Innti ta zubawa Iftihal idanu kafin ta numfasa zuciya babu daɗi murya a karye ta ce "Ina son ku dinga haƙuri da abin da kuka samu kuke dashi a rayuwa, ni ba kowa ba, ban banda ajjiya ba, ba'a bani ba, bamu da wani gata ɗaya shige na Ubangiji. Ku dinga haƙuri da abin da kuka samu wasu suna nan a daren ko tuwon basu samu ba, mu hakan ni'ima ce a gare mu kin ji?" Iftihal ta jinjina kai ta ce "Kece gatanmu a nan duniya Innti, bamu da haufi akan kulawarki, ba kuma takaicin cin tuwon nake ba, ina samu kaina da rashin sukunin zuciya idan naga mahaɗita tana cikin damuwa ki yi haƙuri"
"Mahaɗinki halinta dabanne da naki, ta fiki jarumta da taurin zuciya, ki barta da masifar son da take miki da Inntinta ta gargajiya, wannan soyayyar da take mana ita ce jarrabawarta" Murmushi Iftihal ta yi ta ce
"Ban san ya zata yi ba idan na yi nisa da ita" Jaheed ya ce "In sha Allah brothers za ku aura tagwaye, da suka fito ciki guda suma"
"I hope so bro.....
Jadid ya ɗan yatsuna fuska ya ce
"Turawan zamani, daman a Government school ana koyar turanci har haka Innti?"
Innti ta ce “Education is a gift; muddin ɗalibi yana da fahimta, they can achieve anything. Kuma ya danganta da koyarwar Malami"
"Innti ni dai kece Malamata, kowa yana jin daɗin koyarwarki kafin ki daina teaching"
Abinci suka fara ci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da soyayyar juna, a ƙa'ida idan suna cin abinci babu wanda yake yin magana har su kammala. Yanzu ma haka ne, Babban yaya ne ya fara kammalawa ya ɗauki ruwa ya sha yana kammala sha Ifti ta ɗauka ta sha, sauran ma duk suka sha, bayan sun wanke hannunsu tas Ifti ta kwashe kayan ta ajjiye wajan da suke ajjiye marasa kyau. Akan shimfiɗar suke zaune ta fara yi musu tatsuniya kamar yadda ta saba me cike da hikayoyi da alamar, bayan ta kammala zata tambayi kowa abin da ya koya na darasi daga tatsuniyar. A hankali ta ɗaga kai ta kalle su, zuciyarta cike da fargaba da kuma soyayyar yaranta, an ce dukkan yaran da suka yi nasara a rayuwa, akwai jajirtattun iyaye a bayansu, ita a rayuwar yaranta ita kaɗai ce tsaye a bayansu, ita ce ta ɗauki responsibilities na uwa, kuma ta haɗa tana uba, ta sake ɗaukan ɗawainiyyar dangin uba, bata gajiya da dukkan ɗawainiyyar dake kanta ta sake haɗawa dana dangin uwa. Ta dubi hannunta babu komai sai farcen sosa, bata da komai sai dattin alijuhu. A ƙarƙashin tsoron daya cukukuye zuciyarta harɗa bauɗaɗɗan halin Ana, yarinya ce mafi soyowa a ranta, yarinyar da take matuƙar so fiye da sauran.
A ƙarƙashin wannan son, ta koyi yadda zata sarrafa shi ba tare da mahaɗin haihuwarta ta gane ya haddasa mata damuwa ba, a madadin ta nuna soyayyar Ana a fili sai ta danne tsaf. Ita ce ma wace tafi Addabawa da faɗa a ciki. Gyaran murya ta yi gabaɗaya suka kalle ta, kaifafan idanunsu masu huda zuciyarta da ƙauna ne ke kallon ta. "Ina sake tuna muku ku ba kowa bane a duniya, ba kowa bane a dangin mahaifinku, ku iya talaucinku, ku ɗauke ranku tsam daga kan abun wani, ku yi rayuwa da abin da kuke dashi, watarana sai labarin... Ko ba yau ba, ko ba yanzu ba, za ku ji daɗi za ku zama kune masu ƙarfafa wasu da taimakon su, kun ji me ma ce ko?"
Murmushi Jaheed ya yi cikin ladabi ya ce "Idan hadda ce wannan da tuni mun sauke mun sake ruɓanya saukar sau shurun masaƙi uwar arziƙi. Kalamanki kai tsaye umarni ne ba kawai wa'azi ba. Mu masu biyayya ne a gare ki, Allah Ya bamu ikon kulawa dake" nauyayyiyar ajjiyar zuciya Innti ta sauke, tana jin dole ta sake zage damtse tare da humɓasawa akan sana'ar da take saboda yaranta musamman matan. Yanayin fuskar Jaheed ya sauya zuwa damuwa kafin ya ce "Bana son arziƙin da zan yi wanda Daada zai amfana dashi..,"
Marin da Innti ta ɗauke Jaheed dashi ne ya hana shi ƙarasa faɗar abin da yake ƙwarzabar zuciyarsa, ya yi saurin dafe kuncinsa da hannun dama idanun ya yi jajur duk da duhun dare ya yi ba'a ganin fuskarsa balle cikin idanunsa. Raɗaɗin da ƙonar marin da Jaheed ya ji ya sauka a zuciyar abokin haihuwarsa Jadid, shima runtse idanun nasa ya yi a hankali kuma ya miƙa hannunsa ya ɗora akan na Jaheed
Alamar rarrashi.
"Dukkan arziƙin da ɗayanku zai samu wanda mahaifinku ba zai amfana dashi ba nima ya zama haramiyata, bana buƙata bana muku addu'ar ku samu, ƙwara mu zauna cikin babu ko ƙasa za mu ƙwaba mu dinga ci saboda yunwa na aminci da hakan" da ƙyar take maganar tana jin raɗaɗin marin da ta yi wa Jaheed yana sauka a ƙasan zuciyarta yana cinta. Ta yi saurin yin ƙasa da kanta tare da goge hawayen da yake zuba daga cikin idanunta. Ta ɗora da
"Hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, ko baku ƙaunaci Daada a Matsayin uba ba, ba za ku hana duniya faɗar cewa ku ƴaƴansa bane. Ko muguwar kalma ɗaya daga cikinku ya yi masa, ko ina raye ko bana yare ko akan idanuna ko a bayan idanuna wallahi tallahi ban yafe ba, biyayya a gare shi umarnina ne, shi mijina ne, garkuwata kuma uban ƴaƴana, duk yadda zai kai da addaba mini ko aibata ku, haka zan cigaba da yi masa addu'a, haka kuma kullum cikin addu'oinku umarni ne akan ku yi masa addu'a" a karo na farko Jadid ya kalle ta.
Ya ce "Innti rawar zata sauya zani ne?" Muryarsa shima a raunace take sosai
"Kin san kallon da jama'a suke yi mana akan Daada? Kin san raɗaɗin da muke ji a cikin zuciyarmu? Kin san yadda muka sha bambam da sauran yara a duniyar nan?" Ya runtse idanunsa yana jin yadda komai baya yi masa daɗi, yana ƙoƙarin fidda rai da rayuwa me tsayi yana da yaƙinin ciwon nan ba zai bar shi ba. A fusge ya ce "Innti mutane basu da adalci, sun kasa yi mana adalci cewa, bamu da laifi ko saka hannu a cikin al'ummaran Daada, ya za mu yi ne? Ya za mu yi da ranmu, a wajanki kawai muke jin iska me daɗi, a wajanki muke samun inuwar da za mu raɓa mu ji sa'ida. Na karaya na fara karaya ina tsoron in ji cewa kamar ba mu yi sa'ar uba ba....,"
"Jadid!"
Ta dakatar dashi da ƙarfi ta hanyar kiran sunansa, ya yi ƙasa da kan shi a hankali yace. "Ki yafe mini Innti kar ki yi fushi damu, ke kaɗai muke da ƙwarin gwiwar buɗe ba ki mu faɗawa halin da zuciyarmu take ciki, ina tsoron kar matsalolin Daada ya yi wa'adin ɗaya daga cikin zuri'arki, dauriya kike, na sani na san da wannan Innti shiru bashi ne ba" Ta zubawa Jadid idanu, sai yanzu ta lura da sauyawar da ya yi, wanda ya ci tun a jiya ta gane saboda bata da wasa wajan fahimtar yanayin yaran nata. Ta ja numfashi ta sauke ta kasa cewa komai sai ƙirjinta da ya yi mata nauyi, wani abu ya tsaya mata.
Wayar Jaheed ce ta fara ƙara alamar shigowar kira, number wanda ya gani ce ta saka shi yin murmushi, murmushin daya saka Jadid sauke ajjiyar zuciya me nauyi ko babu komai ganin abokiyar haihuwarsa cikin farinciki ya sauƙaƙa masa ciwon da yake ji a jikinsa. "Mutumin rigimammiya ne"
"Yaa Sam?" Inji Iftihal tana dariya.
"Haysaam, kin canka masoyiya"
Jaheed ya bata amsa, yana miƙa mata wayar ya ce "Jeki kai mata, na san dai ita yake nema" Iftihal ta amshi wayar da hannu biyu cike da ladabi ta juya zuwa ɗakin nasu. "Wannan wayar da suke yi da Haysaam da Ana babu damuwa a cikinta dai ko? Kun san irin maganganun da suke yi a tsakaninsu?"
Jadid ya ce "Babu in sha Allah, hirar dai ba zata shige ta masoya ba idan ta yi ƙamari"
"Soyayya? Sonta yake yi?"
Yadda Jaheed ya yi tambayar ya bawa Jadid dariya ya ce "Kusanci idan ya yi yawa tsakanin mace da namiji ai soyayya ce kawai, wata rigimar da Shalelen Innti Babban yaya da Innti sai shi Haysaam ɗin kawai ne suke tanƙwara mana ita, kafirin taurin kai kamar matar kuturu da iyayin tsiya kamar jikar ƙaruna. Ga yauƙi kamar kuɓewa" Innti ta girgiza kai tana murmushi ta ce "Allah Ya shirya ka Jadid ya shirya mini zuri'a baki ɗaya, ka je ka sha maganinka ka kwanta haka nan" Kamar zai ce mata maganin ya ƙare sai kawai ya yi shiru ya miƙe tare da cewa "Mu kwana lafiya Sahibata" ta jinjina masa kai. Jaheed miƙe ƙafafuwa ya yi yana bawa Innti labarin shago, gabaɗaya ya mance da abin da ya faru na sharrin da aka yi wa Shalelen Innti.
Babban yaya daman kamar baya wajan, wayarsa kawai yake dannawa ba tare daya san mema yake yi dannawa ɗin ba, tunaninsa kamar ba nasa ba, hatta shi ɗin jinsa yake kamar ba shi ba. Sai ya dinga gani ko ji a ran shi cewa; yana da bambanci da ƴan'uwansa. Bambancin da yake sake nisanta shi da al'umma, baya samun nutsuwa muddin zai jisa a cikin mutane. Wannan rayuwar jejin da yake tsintar kan shi a ciki idan ya yi bacci tafi masa daɗi.
Iftifal da fara'a ta shiga ɗakin tana saukar da ganinta a shimfiɗarsu, domin ta ɗauka mahaɗinta ta jima da yin bacci.. turus ta yi ganin Ana zaune a ƙasa a inda ta yi sallar issha ko tashi ba ta yi ba, ta zubawa waje guda idanu. Har Ifti ta ƙarasu inda take ta tsuguna bata sani ba, alamar ta yi nisa cikin tunaninta. "Ana!" Ta kira sunanta da ƙarfi.
Tana jijjigata kafaɗunta biyun.
"Tunanin me kike yi mahaɗita?"
A hankali taja manyan idanunta ta lumshe su bata jima ba ta ware su a fuskar Ifti ba tare da ta ce komai ba. Ajjiyar zuciya Ifti ta sauke a sanyaye ta ce "Ba damuwa Daada kika sakawa ranki ba ina fata rabin rai?"
"Daada....?
Yadda ta yi furucin da yadda ta ambaci sunan Daada zaka ɗauka bata taɓa jin sunan ba sai a lokacin. Furucin da Ana ta yi ya daskarar da jinin jikin Ifti da wani irin sabon tashin hankali ta ce "Kin san me kika ce? Kin san abin da kalmominki ke nufi?"
Ana ta girgiza kai ta ce "A'a"
"Waye Daada? Da gaske ban waye shi ba?" Iftihal ta ce
"Ina tunanin Sunanki Ayshatul-Haleeym Ana Daada, wannan sunan da yake maƙale da sunanki kamar rai da ajali, wannan sunan da idan babu shi ba ki gama zama cikakkiyar ƴar sunna ba, wannan sunan da zai ta bibiyarki har yaranki da za su amsa sunan jikokin Daada.. wannan Daada mahaifinki"
Ana ta bubbuɗe idanunta kafin ta juya ƙwayar idanun ta ce "Oh! Idan na fahimta wannan mutumin mai dukan matarsa, wannan dai mutumin me shigo mana gida tsirara cikin talatainin dare, hakazalika wannan mutumin me bin manta banza wanda yake da karuwa me suna Tani, wannan dai mutumin me yin caca shi kenan nufi? Shine Daadan da kike magana akai?"
"Ana!"
"Iftihal....
Ta kira sunanta itama cikin sanyin muryarta mara son hayaniya da rashin ɗaukan raini.
"Ana mahafin naki kike faɗawa haka? Babu kyau fa ki tuna abin da Innti take faɗa mana akan Daada. Ni dai ina son Daada ina matuƙar son shi sosai a cikin zuciyata"
Ana ta sake ware idanunta da mamaki ta ce "Kai haba? Shine mahaifin nawa kenan ashe?" Iftihal bata iya bawa amsa ba. Ana ta ɗan cije lips a hankali ta ce
"Kuma kin taɓa ji na saka muku baki idan kuna batu akan shi? He's never been headache wallahi"
"Kinga Iftihal, za ki iya son Daada har ƙarshen rayuwarki idan kin so, amma ba'a tilasta Ana yin abin da ba ta yi niyya ba. Idan ba ki ba sani ba, bari yanzu ki sani. Mahaifin Ana ya jima da rasuwa tun tana cikin Innti"
Tana faɗin hakan ta miƙe zata je ta kwanta cikinta na yi mata wani irin ciwo saboda azababbiyyar yunwa, amma data ci tuwo ta gwammace ta kwana da ƴar gusau.
"Yaa Sam ke kiranki a waya"
Wayar ta amsa fuska ba walwala ta kara a kunne da wannan sanyin muryarta ta ce"Uhm...
Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Yaa Sam ya sauke tun ɗazo yana jin yadda take surutu na masifa saboda ta yi niyya. "Dawa kike?"
Ta yi masa shiru ta yatsar fashi.
Shirun da yake azabtar da zuciyarsa wanda baya so baya buƙata shi ta yi masa. Ba zai jure sai ya tattaro dukkan nutsuwarsa ya sake fesar da numfashi da ta ji sautinsa ya shiga kunnenta ya saukar mata a zuciya, ta ƙanƙame wayar tana lumshe idanunta tana jin wani abu yana yi mata motsi a ƙirjinta.
"Nanaah"
Ta yi masa shiru wannan karon ma. "Zan koma Lagos gobe idan rai ya kai mu, naso ganinki kafin hakan ta kasance kin ji?" Sai ta yi shiru tana sake saka ƙarfi wajan riƙe wayar da kyau, Lagos ke ta yi mata kai komo a kunne, ba yau ta saba jin sunan Lagos a bakin Haysaam ba, ba yau bane kawai, wannan bai zama na farko ba, babu tabbacin zai zama na ƙarshe. Akwai wani abu da take ji game da sunan Lagos, da duk sanda ya furta a kunnenta, menene shi? Menene abin? Bata sani ba, ko wuƙa aka saka a wuyanta akan sai ta faɗi me take. Tabbas sai dai a ɗauki ranta.
"Na.......
Ya kasa ƙarasa kiran sunan nata.
Kamar yadda ta yi shiru shima shirun ya yi, duk wani bugun zuciyarta yana tafiya daidai da bugun tasa zuciyar. Ta ɗauka ya kashe kiran sai ta ce "Yaa Sam.....
"Na'am"
"Zaka tafi dani? Ka tafi dani Please" ta ce kamar za ta yi kuka
"Nanaah, ya zan tafi dake garin da babu dangin uwa balle na uba, ke ba matata ba?"
Ta ɗan narke masa ta cikin wayar "To ba sai ka ce ƙanwarka bace ni, ka yi maganin munafukai ko?" Ya yi jim sai kuma ya ce "A baki kike jin Lagos Nanaah, ba irin garinku Kano bane, kuma inda nake ɗaki ɗaya ne da Banki suka bani, ko zan dinga kwana dake muna using one bedroom?"
"E, na yarda nikam"
"Ba za ki ji komai ba, mu kwana tare?" A hankali ta ce
"Me zan ji to?"
"Think dear, yi tunani ko?"
"Na yi, ba zan ji komai ba"
Sai kawai ya share ta, yaja matsagaitan idanunsa ya lumshe.
"Yaa Sam"
"Nanaah"
"Kai za ka ji?"
Ya ɗan murmusa, sautin murmushin nasa ya saka ta sakin nata kyakkyawan murmushin da zuciya ke ayyana masa kamar ya ji ɗumin bakinta ne a fuskarsa.
"E, zan ji" ya bata amsa.
"To faɗa mini me zaka ji ɗin, na ji ko nima zan ji irin shi mu yi anko ni da kai abokina"
“Abokina” ya maimaita sunan a ran shi.
"Please Yaa Sam, say it"
"Zan faɗa, not now"
Ta ce "Sai yaushe?"
"Sanda Shalelen Innti ta girma"
"Yaa Sam.. Yaa Sam...
Ƙit ya kashe wayar. Bayan ya kashe wayar juyi kawai yake yi a saman ƴar yaloluwar katifarsa, yaja idanunsa ya lumshe ya sake buɗe su, ya ƙara rufe su ji ya yi zuciyarsa na yi masa motsi. Ya zai yi ne? A aboki ta ɗauke shi Madam, kuma kamar she's too young ta fahimci abin da yake ji, wata ƙilama ita bata jin komai ma. Yaushe ya san Ana ne? Kamar zai iya tuna sanda ya ganta? Idan ya rufe ido tsaf zai ga tarihin daya shuɗe akan Ana
Sanda ya fara ganinta a duniya.
***
Rediyo take saurara amma taƙi tsayar da hankalinta waje guda, daga ta danna nan sai kuma ta danna nan cikin sa'a takai inda ake maimaicin labarai. Ta yi shiru tana saurara. Sai ji an ce
"Wannan kenan. A yau ne wani rikicin kishi tsakanin matan Malam Sani dake Gandun Albasa ya barƙe, barƙewar data tashi barƙewa ta haɗa da jaririn da aka haifa wanda yake a shaƙi iskar kwana ɗaya a duniya, inda kishiyar Maryama wato uwar gida ga Malam Sani ne suna Talatuwa ta yi juyin waina a tanta da jaririn Maryama a ruwan zafin, kai ka ce kaza ake shirin figewa wajan yin tagomashin arziƙi a baki" me yin labaran ta ɗan yi shiru ta ɗora da; "Duk yadda gidan rediyon bright Fm yaso ganawa da Maryama abin ya faskara, ga abin da ya faru a taƙaice daga bakin wanda idanunsu ya gane musu"
Muryar wata mata aka sako tana kuka sosai ta ce "Ban taɓa ganin azababben kishi fara fa'ida irin wannan, akan idanuna ta ɗauki jaririn amaryar ta cilla a ruwa, Talatuwa ta yi haka ne da gayya da tunanin hukuma ba zata ɗauki mataki ba, sun auro yarinyar suna gallaza mata hatta mijin bayan Talatuwa yake bi shi ya hana Maryama ta kai ƙara. Alkur'anin Allah akan idanuna komai ya faru"
Ɗif aka ɗauke muryarta. "To daman kowa ya sai rariya ai ya san zata zubda ruwa, Allah kasa mufi ƙarfin zuciyarmu. Me rahoto Yussrah Yassar Yakasai"
Sai aka ɗan sako take da muryar namiji a background sound ana faɗin "Labaran rana kuka Saurara daga bakin Yussrah Yassar Yakasai....," bata bari ya ƙarasa faɗa ba ta yi cilli da rediyon hankali tashe ta fito tana faɗin "Malam malam fito ka ji muryar Asabe a rediyo ta yi bayani dalla dallah mun shiga uku Malam" fitowa ya yi daga ɗakinsa domin shima yanzu yaga ma ji ya kalli Talatuwa data rushe da kuka daidai nan Maryama ta fito tana kuka sosai "Malam na rasa ɗaya ya rasu na shiga uku, an kashe mini yarona"
A fusace ya ce "To allahamdulilah da hakan ma, maza tattara kayanki da gawar ki fice mini a gida na sake ki saki uku cif kar na sake ganin me kama dake. Ba za ki ja mini masifar zaman gidan yari ba billahi"
Cak kukanta ya tsaya ta zubawa Malam ido jikinta duka rawa da ɓari yake yana zata da gawa cikin daren nan? Ina za ta yi? Ba zata iya komawa gidansu ba, ta shiga uku. "Ka tausaya mini Malam na yarda ka sake ni amma kabar ni na zauna a gidan nan don Allah, na shiga uku. Ka tuna ɗan nan na kane ko jana'iza ayi masa"
Talatuwa ce ta shiga ta ɗakko jaririn a hannu, Malam ya shiga jan Maryama tana turjewa sai da ya kai ta bakin ƙofa Talatuwa ta ajjiye mata gawar ƙasa suka ja ƙofa suka rufe babu ko mayafi a jikin Maryama.
*** Juyi kawai Ahlam take yi a saman gadon dakinti, ta ɗauki a ƙalla awa ɗaya da daƙiƙo a haka tana juyin da bashi da amfani, idan ta yi niyyar bacci baya samo, maganganun MD da suke neman saka mata ciwon zuciya kawai take tunawa a cikin kanta, ga matsalar baiwar Allah da bata san halin da take ciki Bama, ga matsalar Yussy da kanta.
"Na shiga uku! Ko dai bani da rabo ne a aikin jarida?" Ta saka hannu ta dafe kanta.
Da sauri ta miƙe zaune tana faɗin "No! Ba zai yiwu ba, dole na ɗaukaka akan aikina, ɗaukaka nake so ko ta wacce fuska wacce zata saka tauraruwar Yussy ta disashe" ta saka tafin hannunta wajan goge hawayen idanunta, shanyayyen hannunta ta kalla. "Ko nakasata ce silar komai? Ko ita ce ta hanani ɗaukaka ni Ahlam?" Sannu a hankali ta miƙe tsaye bayan ta sakko daga kan gadon, safara da marwa ta shiga yi a cikin bedroom ɗinta. "Anees" ta kira sunan.
Wayarta ta ɗauka ba tare data duba lokacin kiran ba, idanunta rufe ta fara neman number. Kira biyu ta yi ba'a ɗauka ba, ana ukun aka ɗauka sai aka yi shiru.
"Hello....
Babu martani. "Hello...
Nan ma shiru sai ta ce
"Anees, akwai matsala ina buƙatar taimakonka Please" babu raddi ko numfashi balle sauti a ɓangaren Anees ɗin. Wayar ta ciro daga kunnenta tana ƙoƙarin sake kira, da firgici ta yi baya tana zaro ido ganin number MD ta makawa kira a cikin daren.
***
Wajejen gotawar uku da kwata na dare, Innti na zaune saman laddumar da ta yi lafila hannunta riƙe da carbi tana azkar. Ta jima zaune iska na kaɗata. Hannunta ta ɗaga sama bayan ta ajjiye carbin da karyayyiyar murya me raunin gaske, buɗaɗɗiya me cike da buƙatu a wajan Ubangiji ta ware hannayenta wajan furta. "na sani Ubangiji, ina da masaniyar babu abin da zai faru da rayuwar bawa face abin da ka ƙaddara masa, na amshi jarrabawata da hannu bibbiyu, burina, fatana addu'ata akan ƴaƴana ne da mijina. Mijina shine gatana ƴaƴans sune farincikina, Ubangiji ka shirya mini zuri'a, ka shirya mini su. Allah ka haɗa su da alherin da yake cikin wannan duniyar, ka nisanta su da sharrin dake cikinta.. Allah ga autata nan Ubangiji ka shiga cikin rayuwar Ayshatul-Haleeym, ka shirya mini ita, ka shirye ta ka tausashi zuciyarta, ka cire mata zafin zuciya da taurin kai. Ka daidaita tsakaninta da mahafinta" taja ajjiyar zuciya me ƙarfi ta sauke ta ce "Mijina...
Wani irin hawaye masu zafin gaske ne suka shiga sunturi a saman fuskarta, jikinta ya shiga rawa da ɓari a wahalar ce ta shiga faɗin. "Mijina Ya Allah. Ya zan ce bana son mijina? Gyara naka ne, shiriya taka ce, Allah ka shirya mini mijina ka dawo dashi hanyar tsira kar ya koma gare ka cikin wannan mummunan tufar, bana riƙon shi a raina bana jin zafinsa. Allah ka dawo dashi kan tafarki madaidaici, ka kiyaye masa alƙalaminsa daga aikata mugun abu akan kowacce ɗiya mace ko don tsoron dawowa gare ka. Ko don tarihin zuri'arsa.....,"
Bam! Ta ji ƙarar buɗe ƙofar da ya yi ya shigo, wata faɗuwar gaba ta saukar mata. Kafin ta yi yunƙurin matsawa ta ji saukar ita ce a gadon bayanta, azaba, raɗaɗin da bata taɓa jin irinsa ba ya saka ta saki wata ƙara haɗe da kiran sunan Allah. Daman niyyar tashi take yi saboda nishin da ta ji a ɗakin samarin yaranta wanda babu tantama Jadid ne ciwonsa ya tashi, ciwon ƙodar da yake fama dashi. Ƙarar da ta yi na farko ya fito da Jaheed daga cikin ɗaki dai-dai lokacin ma Ana ta fito ta kafe Daada da ido, yau ma tik yake haihuwar uwarsa babu kaya a jikinsa. Jaheed na ƙoƙarin janye Innti, Daada ya sake ɗaga icen hannunsa ya sake makawa Innti a gadon bayanta. A hargitse Jaheed ya nufi Daada zai ture shi. "Idan ka sake hannunka ya sauka akan mahafinka zan maka Allah Ya isa Jaheed. Mahafinka ne"
Cak Jaheed ya tsaya jikinsa na wani irin rawa da ɓari hawayen daya cika idanunsa ya shiga bin fuskarsa ya durƙushe a wajan.
"Daada ka yi haƙuri, ka ji tsoron Allah ka tuna mu da Innti amana ce a gare ka, matarka ce. Kar hakkin Innti ya bimu har gidan aurenmu" Iftihal ce ta furta hakan bayan ta fito daga ɗakin. "Daada ka tuna faɗar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, dukan mata rashin adalci ne, idan ya zama tura da bakin riga ake dukan su, haka Mu'allim ya ce mana. Muna son ka muna kwaɗayin rayuwa da kai, kar ka kashe mana Innti" kallon Ifti ya yi zai kai mata duka sai ya tuna yarjejeniyar cacar da yake kanta, zai samu miliyan ashirin cif saboda ita, don haka a yanzu ita kallon kuɗi yake mata. Ya kalle su sama da ƙasa kafin ya ce
"Na tsani haihuwa, me ya saka ta saki jiki duk ta haife ku kamar wata dabba, uwarku bata da amfani ita da dabba ɗaya suke a wajena. Jaka ce, daƙiƙiyya mara amfani"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"
Iftihal ta furta tana fashewa da kuka, tana jin kamar zuciyarta ce zata fito waje.
Daada ya sake kallon Innti take durƙushe ya ce "Wallahi Tani ta fita armashi da garɗi, ta sani bana son haihuwa me ya saka ta haife ku har haka? Ku duka tsinannu ne ba za ku yi albarka ba. Allah wadaran....," a zabure Innti ta miƙe tana girgiza kai kafin ta ce
"Kar ka aibata mini zuri'a Daada, kar furucinka ya zame musu Harshen wuta, ka yi wa girman Allah Daada...," bai bari ta ƙarasa ba ya ɗauke ta da mari ya nuna ta da manuniyya "Na faɗa, Allah Ya tsine musu dake dasu gabaɗaya, zuri'ar da bata da wani amfani kema ba ki da amfani bare su, sai sun watse sun bi duniya. Allah ya tsine musu, Allah ya farraƙu gabaɗaya na huta"
"Allah Ya tsine maka dai Daada da kai da Tani Allah Ya tsine muku" muryar Ana ta sauka akan kunnuwansu....
Akwai page 7,8,9&10 available at ArewaPen. Free Chapters ku shiga ta website ku yi searching ArewaPen.com a Chrome kenan ko application na ArewaPen kuna yin searching HIYAAM za ku gani.
Idan kana buƙatar littafin nan ka yi magana ta waɗannan numbers ɗin via WhatsApp. 08082101373 08164069385