
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 25
.....don't you know? Do you have to tell them that I have a wife and a son so that they can divorce me?" Zahra laughed scornfully, "Oh wow." She said, waving her hand, "So now you came to my house because of this?" "Answer the question." He interrupted her. "What is wrong with you Zahra?" She immediately rolled her eyes. "What is wrong with me?" "Yes." He answered. "Why do you keep entering people's lives, I have to live alone?" Zahra laughed, a frustrated laugh "Khalil, are you sure you want this interview?" "Very much." He answered "Good" She nodded her head "Well I also have one question." "Ask." He said while folding his hands, "What is the reason for a married man to follow her outside like a bunsuru" Khalil raised his eyebrows, very much her words saying "Don't start Zahra son, we will have big issues wlh" "No." She raised her hand "Let's start, I'm ready for it" He sighed. "You love drama so much, but don't believe that I said something that will make you cry" "Drama? I'm not afraid, Ibrahim." He said, "Okay.. I see you're not afraid, but you're almost regretting it." Zahra smiled. A smile that didn't reach inside. Khalil continued. "I'm warning you to get out of my case wit
*FARASHIN IZZAH*
Book 1 Chapter 25
Ya miƙe tsaye daga inda yake zaune
“Finally.” Ya faɗa yana kallon agogon hannunsa.
Zahra ko kallonsa bata yi ba, ta cire key ɗin kofar ta nufi hanyar stairs kai tsaye, kamar ma ba ta gan shi ba haka tayi pretending
Da mamaki reacton ɗinta ya bita da kallo, sai data kai kusa da matakalar ne ya ɗaga murya
“Malama, dakata anan.”
Sauke kafar nata tayi, sannan a hankali ta juya, wani irin kallo ta watsa masa. Kallon da ya nuna bata cikin yanayin da za ta iya ɗaukar rashin hankali, she’s ready to exchange words with him
“Me kuma?” Ta tambaya a taƙaice
Khalil ya yi wata irin dariya. “Nine zan tambaye ki me kuwa”
Ya taka zuwa gabanta
“Wane dalili ne zai sa ki dinga bin girlfriends ɗina kina tayar musu da hankali?”
Zahra ta ɗaga gira
“Au” ta faɗa tana gyara tsayuwarta
“Ita Lovie Dovie ɗinka ta faɗa maka kenan?”
Fuskarsa ta ɗan canza. “Whatsoever Zahaaaaa…” ya kare maganar da karfi kamar zai dake ta
“Abin da ya dame ni shi ne, me yasa kike bin mutanen da ba su san ki ba? Dole sai kin fada musu Ina da mata dan su rabu da ni?“
Zahra ta yi dariyar rainin hankali
“Oh wow.” Ta fada tana tafe hannu
“So yanzu kai ka zo gidana ne saboda wannan?”
“Answer the question.” Ya katse ta.
“What is wrong with you Zahra?”
Nan take ta zaro ido. “What is wrong with me?”
“Yes.” Ya amsa.
“Me yasa za ki dinga shiga rayuwar mutane, dole sai nayi rayuwa da ke kadai ne?”
Zahra ta yi dariya, dariyar takaici
“Khalil, ka tabbata kana son wannan hirar?”
“Very much.” Ya amsa
“Good” Ta gyada kai
“Toh ni kuma ina da tambaya guda ɗaya.”
“Ask.” Ya fada yana folding hannaye
“Wane dalili ne zai sa married man ya dinga bin mata a waje kamar bunsuru”
Khalil ya haɗe gira, sosai maganar ta dake sa “Don’t start Zahra dan zamu samu big issues wlh”
“No.”Ta ɗaga hannu “Let’s start, I’m ready for it”
Ya furzar da iska. “Kina son drama sosai, amma kar ki yarda nayi maganar da zaki yi kuka”
“Drama? Ai ni bana tsoro Ibrahim”
Ya ce “Okay.. naga alama Baki da tsoro amma kina dab da nadama kuwa”
Zahra ta yi murmushi. Murmushin da bai kai ciki ba
“Interesting.”
Khalil ya ci gaba. “Ina miki warning ki fita harka ta da Duk wacca ta raɓe ni, kuma idan kina son zaman Lafiya stop touching my phone”
“Your business?” Ta katse shi “Really?”
“Yes.” Ya amsa
“Toh ka daina kawowa har cikin gidana shi harkan naka, taɓa waya kuma ai na daina tunda ba alkhairi kake shukawa ba”
Nan take ya yi tsaki “Waye yake causing matsala a tsakanin mu idan ba ke ba, a dole sai kin duba wayata kuma ko sau dari zaki duba ba zamu daina samun matsala ba”
“Because you are the problem.” Ta mayar masa ba tare da tunani ba
“Excuse me?”Ya matso kusa da ita “Repeat that.”
“I said you are the problem.” Ta maimaita tana kallonsa kai tsaye
“Khalil, ka daina acting like victim.”
“Victim?” Ya yi dariya. “So yanzu ni ne victim?”
“A’a” Ta gyara masa “Kai ne culprit.”
Wani irin shiru ya biyo baya Kallon juna kawai suke yi
Khalil ya girgiza kai.
“Unbelievable.”
“Ai ni ma abin da nake gani yanzu unbelievable ne” Ta mayar.
“Imagine married man yana defending girlfriends ɗinsa, just imagine fah….”
“Watch your mouth Zahra” Ya faɗa da gargaɗi
“No” Ta amsa nan take. “You watch your actions first”
Ya ɗan yi shiru kafin ya ce, “At least they respect me.”
Nan take fuskar Zahra ta canza. “What?”
“Kin ji ni ai” Ya amsa
“At least they know how to talk.”
Zahra ta ji wani abu ya tsaya mata a maƙoshi, na wasu daƙiƙu ta kasa magana, sai daga ƙarshe ta yi murmushi, murmushi mai cike da ciwo
“Oh” Shi kenan kawai ta faɗa Ta gyada kai a hankali “Oh, I see.”
Khalil wani kallo yake mata
Ita kuwa ta ɗauki jakarta a zuciye “Congratulations then” Ta faɗa
“What?” Ya tambaya
“Congratulations” Ta maimaita. “If they make you that happy, good for you.”
Sai ta juya.
Khalil ya ɗaga murya. “Zahra!”
Amma ko juyowa bata yi ba. Kai tsaye ta hau stairs.
“Zahra I’m talking to you!” Ya sake maimaitawa
Ku waiwayowa bata yi ba balle yasa ran zata kulasa
Tana isa sama ta buɗe ƙofar ɗakinta da ƙarfi, ta shiga ciki tare da banke ƙofar a bayanta
Khalil kumq ya tsaya a parlorn ƙasan, hannayensa a aljihu, yana huci saboda takaici
Ita kuma Zahra bayan ta shiga daki tana tsaye bayan ƙofar ɗakinta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi tsabar bakin ciki
Ba saboda maganar girlfriends ɗin ba, sai saboda kalmar da ya jefa mata. “At least they respect me.”
Kalmar ce kaɗai ta isa ta sake karya wani ɓangare na zuciyarta.
Daga ƙarshe shima Khalil ya haura sama zuwa dakinsa.
Yana shiga ya banke ƙofar a bayansa da ƙarfi. Wani irin takaici yake ji kamar zuciyarsa zata faso. Har yanzu kalaman Zahra na yawo a kansa
Ya cire agogonsa ya jefa kan side drawer.
Tsaki ya ja.
A rayuwarsa bai taɓa tunanin wata rana za su kai ga irin wannan matsayi da Zahra ba
A gefe guda kuma, Zahra na zaune kan gadonta.
Hawayen da take hana kanta ne tun a parlorn suka sake kubuce mata, sosai take kuka
Kukan da take yi tun daga zuciya ce, a hankali ta dafe cikinta Saboda wani ciwo da yake mata
“Wallahi na gaji…” Ta furta a hankali.
“Na gama zama da Khalil as miji…”
Tafi awa tana kuka, tunawa tayi bata yi sallar isha’i ba yasa ta share fuskarta da sauri, miƙewa tayi ta nufi toilet
Alwala tayi cikin nutsuwa sannan ta dawo ɗakin, sallaya ta shimfiɗa, ta tada kabbarar sallah
Dogon lokaci tayi tana addu’a bayan ta idar.
Addu’o’in da ita kanta bata san lokacin da ta dauka tana yi ba, tana yi ne tana kuka
Daga ƙarshe ta jingina da bango tana kan sallayar, tunanin rayuwarta kawai take yi.
Can ba tare da ta sani ba bacci ya fara rinjayarta. A haka bacci ya ɗauke ta.
Misalin karfe biyu na dare, wani irin yunwa ne ya farkar da ita, ta buɗe idanunta a hankali
Da farko bata ma gane inda take ba. Sai can sannan ta tuna, Akan sallayan bacci ya dauke ta
A hankali ta miƙe tana jin jikinta babu ƙarfi, ga ciwon da maranta yake yi, ta gyara hijabin kanta sannan ta fito daga ɗakin
Ta nufi hanyar stairs domin ta sauka zuwa kitchen
Sai dai tana wucewa ta lura da wani abu… Ƙofar ɗakin Khalil a buɗe take.
Ta tsaya tana mamaki, toh ko ya shiga dakin ne jiya daya fita sai bai kulle ba?
Har ta yi niyyar wucewa, sai kuma wani abu ya sa ta waiwaya A hankali ta ƙarasa bakin ƙofar, ta leƙa ciki
Nan take mamaki ya bayyana a fuskarta Khalil yana cikin ɗakin, yana bacci
Ba fita yayi ba kamar yadda zuciyarta ta ɗauka ba.
Fitilar bedside lamp ce kawai ke kunne
Kayan da ya sa tun na daren ma bai canza su ba, ya ana kwance gefe ɗaya, wayarsa a ajiye kusa da shi
Alamar dai ya yi bacci ne ba tare da ya shirya ba
Zahra ta tsaya tana kallonsa.
Wani sashe na zuciyarta ya tuna mata kwanakin da suka yi farin ciki.
Kwanakin da ko minti ɗaya baya son ta ɓace daga ganinsa.
Sai dai tunanin daren yau ya dawo mata. Nan take ta kawar da idanunta. Ta haɗiye miyau.
“Tunani kawai nake yi…” Ta faɗa a ranta.
Wani tunani ne yazo mata rai, hakan yasa a hankali Zahra ta ƙarasa cikin ɗakin, har yanzu yana kwance yana bacci, tsayawa tayi tana kallonsa na ɗan lokaci
Tunawa da yadda ta yanke hukuncin cewa ba zata iya ci gaba da rayuwa da shi ba yasa zuciyarta sake zama cikin kunci
A hankali ta ɗauki wayarsa. Numfashinta ya fara sauri.
Allah ya bata sa’a, tana ɗaukar hannunsa ta daura yatsarsa kan fingerprint ɗin wayar.
Nan take wayar ta buɗe. Ta saki ajiyar zuciya.
Da sauri ta fito daga ɗakin zuwa nata.
Zaunawa tayi bakin gado tana riƙe da wayar, abu na farko da ta fara yi shi ne shiga gallery
Folder ɗinsu ne ya fara buɗewa, hotuna, videos, selfies, da duk abin da ya taɓa nuna akwai soyayya tsakaninsu
Idanunta suka cika da hawaye Sai dai wannan karon bata tsaya tunani ba
Ɗaya bayan ɗaya ta fara gogewa, har sai da ta tabbatar babu ko guda da ya rage
Daga nan ta shiga wasu folders tana duba ko akwai wani abu da ya rage.
Bayan ta gama, sai ta shiga Instagram.
Ta yi logging account ɗinsa a wayarta.
Ta san idan gari ya waye kuma ta samu sarari, zata shiga ta goge duk wani abu da ya haɗa su.
Ta sake komawa gallery domin ta tabbatar da komai ya tafi.
Sai kawai idanunta suka sauka kan wani hoto, da farko bata gane ba.
Sai da ta buɗe shi, nan take zuciyarta ta buga
Saudat ce… Kawarta Saudat da Khalil
A cikin ɗakinta ne suka yi wannan hoton shi da ita, jiri ta fara ji ta fara nanata innalillahi wa Inna ilahir rahiun
Hannunta ya fara rawa
Khalil zallan three-quarter ne a jikinsa. Saudat kuma sanye take da half vest da bombshort.
Mirror selfie ne.
Kuma daga yadda suke tsaye babu shakka suna cikin sakewa sosai, Dan Saudat a kirjinsa take a kwance
Zahra ta sake buɗe wani.
Sai wani, sai wani, duk su biyun ne.
Wasu tana kwance a jikinsa, wasu suna dariya
Numfashinta ya ɗauke na wasu daƙiƙu. Ta ji wani irin zafi ya ratsa ta.
Hawaye suka fara zuba ba tare da izini ba
Da sauri ta tura wa wayarta duk hotunan.
Bata ma san tsawon lokacin da ta ɗauka tana yin hakan ba.
Da ta gama, ta yi minimizing gallery ɗin.
Ta goge duk wata app da ta shiga. Ta miƙe da niyyar fita.
Sai kuma taji muryarsa. “Bani wayata.”
A razane ta ɗaga kai.
Khalil yana tsaya bakin kofar Idanunsa a buɗe yana kallonta
Zahra ta haɗiye miyau.
Amma ta daure bata nuna masa komai ba.
Ta miƙa masa wayar, ya karɓa
Sai ya yi murmushin gefen baki. “Maganin ki da bincika min waya.”
Zahra ta haɗe fuska Bata ce komai ba
Zai fita ta samu kanta da ce masa “Duk abun da kayi Kai da Allah ne”
Ya juyo yana murmushi ya ce “Na ga ko uban naki ma bada mace daya yake tare ba”
Nan take Zahra ta ɗago “Enough Khalil” Ta faɗa da ƙarfi
“Wasa-wasa kar ka sa ubana cikin maganar nan.”
Kallon kallo suka shiga yiwa juna Sai Zahra ta juya ta wuce ta gefensa ba tare da ta sake cewa komai ba
Kai tsaye kitchen ta nufa.
Tana tafiya tana jin zuciyarta kamar zata faso saboda zafi
Shi kuma ya bita da kallo Sai daga ƙarshe ya girgiza kai, ya juya ya koma dakinsa, yana shiga ya kwanta, ba jimawa bacci ya sake ɗaukarsa
A kitchen kuwa Zahra ta jingina da kitchen cabinet tana kukan mai tsuma zuciya Kuka irin wanda mutum yake yi idan ya kai ƙarshe, ta rasa me zata yi, ta rasa wanda zata faɗawa, ta rasa yadda zata ci gaba da ɗaukar wannan rayuwar
How on earth kawarta wacca suke tare tun day one ta kalli picture dinta tare da mijinta for that matter, kuma a ɗakinta, Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, when? How? Itama bata sani ba
Daga ƙarshe ta fito ta koma ɗakinta.
Wayarta ta ɗauka ta kira Firdausi.
Sau ɗaya, sau biyu, sau uku.
Ba a ɗaga ba, ta kalli lokaci
Kusan ƙarfe uku na dare ne. Nan take ta kashe kiran.
“Bari…” Ta faɗa a hankali
“Kar na tashe ta.” Ta ajiye wayar
Sai dai bacci ko kadan kuma bata ji, Dan ya kaurace mata
A haka ta zauna har aka kira sallar asuba tana aikin kuka
Da ƙyar ta iya miƙewa saboda wani ciwon mara da ya sake sakota gaba
Ta yi alwala, ta yi sallah Bayan ta idar kuma ta daɗe tana addu’a
Duk da ciwon da ke zuciyarta, abu ɗaya ya bata ɗan sauƙi
Ta tuna cewa ta riga ta goge duk wani abu nata a wayarsa, komai ya tafi
Ta daɗe tana zaune kan sallaya Hawayenta na zuba lokaci zuwa lokaci, har gari ya fara waye wa
Wayarta ne ta fara ringing, ta ɗauka a hankali, ta kalli screen ɗin sai taga sunan Firdausi
Numfashi ta ja sannan ta yi receiving.
“Hello?”
Firdausi ta fara magana tun kafin Zahra ta ce wani abu.
“Lafiya Zahra? Zahra, what happened? You called me around 3 a.m. Please talk to me. I’m really worried Zahra”
Zahra ta rufe idanunta, ta ji wani irin ƙulli ya sake tokare mata maƙoshi.
Firdausi na can tana jiran amsarta gaba daya hankalinta a tashe
“Zahra?”
A hankali Zahra ta buɗe baki ta ce “Firdausi…” Sai kuma muryarta ta karye
Hawayen da take rikewa suka sake gangaro mata
Firdausi ta tashi zaune daga kan gadonta.
“Me ya faru? Zahra, talk to me.”
Shiru. Sai sautin kukanta kawai.
Firdausi ta fara firgicewa.
“Wallahi kina bani tsoro. Me ya same ki? Talk to me please Zahra”
Da ƙyar Zahra ta samu ta furta. “Firdausi…”
“Na’am.” Ta ce
“Zan mutu.”
Nan take Firdausi ta miƙe tsaye. “What!”
“Zuciyata zafi take yi…” Tana gama faɗin haka ta fashe da kuka. Kuka mai ciwo.
Kafin Firdausi ta sake cewa wani abu, Zahra ta kashe wayar.
“Hello?”
“Hello Zahra?”
“Hello!”
Firdausi ta sauke wayar tana kallo, gabanta ya faɗi dabas ta zauna a kasa
A rayuwarta bata taɓa jin Zahra a irin wannan yanayin ba
Ba tare da bata lokaci ba ta miƙe tsaye Ta fara neman hijab ɗinta.
Da sauri ta saka, ta ɗauki wayarta, ta fito daga ɗakin.
A kitchen ta samu Mama tana bakin murhu tana girki.
Da alama dama yanzu ta gama zikirin asuba.
Mama ta ɗaga kai tana kallonta.
“Firdausi lafiya kuwa?”
Firdausi ta ƙarasa wajen.
“Mama zan tafi gidan Zahra.”
Mama ta ajiye cokalin hannunta.
“Me ya faru?”
Firdausi ta girgiza kai.
“Ban sani ba. Yanzu na kira ta, ta ɗauka amma kamar kuka take. Bata iya magana ma.”
Nan take fuskar Mama ta nuna damuwa.
Duk da ƙarfin halin da take yi, bata ji daɗin maganar ba.
“Allah ya sa lafiya.”
“Ameen.”
Firdausi ta amsa.
Mama tace,
“Ki gaishe ta. Ki je ki ga yadda take.”
“Toh Mama.”
Ta juya zata fita.
Sai kuma ta sake komawa ɗakinta.
Ta ɗauko handbag ɗinta.
Hijab ta gyara sosai.
Har zata fita sai kuma ta tsaya tana kallon Mama.
“Mama zaki iya ko?”
Mama ta yi murmushi.
“Eh mana. Ki tafi.”
Firdausi ta gyada kai.
Ta juya.
A tsakar gida ta hango Abdul yana wanke-wanke.
“Abdul.”
Ya ɗaga kai.
“Na’am Addah.”
“Ka taya Mama idan ka gama da wanke wanken .”
“Toh Addah.”
Sai ya ƙara cewa, “Sai kin dawo.”
Firdausi ta gyada kai.
Daga haka ta buɗe gate ta fita, gabanta na ci gaba da faɗuwa
A ranta addu’a kawai take yi Allah ka sa Zahra lafiya.
Saboda yadda muryarta ta kasance a wayar, ba ƙaramin tsoro ta bata ba
#Jiddatulkhayr writes #08110615256