Kenza eBookz
Cover art for KOMAI YA YI FARKO  HAUSA NOVEL 10

Post

KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 10

.....success." Even before Humaira said something, he turned around and went back to his car, Humaira also entered the house without taking the letter he had left. As she was entering the house, Inna followed her with a look and said; "Is he gone yet?" "Bilki took a hijab and went out the door, she said; "I saw a big lady at the door of our house "It's not your fault. Bilki went and brought in the leather." Bilki went back and brought in the leather, it was her daughter's rubbish inside, like grease, grease, soap, perfume, pink, ginger and all the other rubbish. Mother shared Bilki's things without leaving a single piece for Humaira, Humairan even in her stomach, because even if it was removed from her, she would not use it......

Standalone post2,017 words

KOMAI YA YI FARKO...

Page 10

Tunda Alhaji Sani ya kawo Humaira gida ya samu wajen zuwa, duk bayan kwana biyu yake zuwa wajenta, a takaice dai Humaira ta gudu bata tsira ba, wasu lokutan idan yazo ta kan yi ɓurus dashi a wajen ta ƙi fita. Har gida Alhaji Sani yazo ya same Abba ya yi masa magana akan Humaira, Abba ya bashi damar ya nemi soyayyarta, wannan dalilin ya saka idan har Inna ta san yazo sai ta tursasawa Humaira ta fita.

Rai a ɓace Humaira ta fita daga gida tana gunaguni, ta tsane wannan matsa mata da Inna ke yi, daga bakin ƙofar gidan ta ja ta tsaya, ta jingina da bango ta yi folding hannunta a ƙirjinta, Alhaji Sani ya sauke girman kansa ya fito daga motar, cikin nutsuwa ya tako zuwa gabanta, yace; "Barka da war haka sarauniyar kyau."

Humaira da babu rahama ko kaɗan akan fuskarta tace; "Ina wuni."

"Lafiya ƙalau gimbiyata, yau dai kamar ranki a ɓace yake?"

Kawar da kai gefe ta yi ba ta kulasa ba. Alhaji Sani ya ajiye ledar hannunsa a gefenta, yace; "Zan tafi tunda yau ɗinma babu nasara."

Tun kafin Humaira tace wani abu ya juya ya koma motarsa, Humaira ma ta shige gida ba tare da ta ɗauki ledar da ya ajiye ba. Tana shiga gida Inna ta bi ta da kallo, tace; "Har ya tafi kenan?" Kai Humaira ta gyaɗa mata, ta nemi waje ta zauna. "Ko dai kin nuna masa baƙin halin naki?" Humaira kamar za ta yi kuka tace; "Nifa ban yi mishi komai ba."

Inna ta kalle Bilki dake ɗaurayewa Imrana kwanuka, tace; "Bilki duba min idan ya tafi da gaske."

Bilki ta dauko hijjabi ta saka ta fita ƙofar gidan, ta ɗan lelleƙa sai ta dawo ciki, tace; ''Inna ya tafi, sai dai na gan wani ƙaton leda a ƙofar gidanmu.''

Inna ta kalle Humaira da ta wani haɗe fuska, tace; "Humaira kar dai kice min yau ma barin kyautar da ya yi miki kika yi a waje?"

Zumɓura baki ta yi, tace; "Nace masa bana so ba sai ya haƙura da kawowa ba."

Inna ta kaɗa kai tace; "Ba laifinki bane. Bilki je ki shigo da ledar."

Bilki ta koma ta shigo da ledar, tarkacen ƴanmata ne fal ciki, kama daga man shafawa, na kitso, sabulun wanka, turare, hoda, janbaki da dai sauran tarkacen, Inna ta rabar da abubuwan wa su Bilki ba tare da ta bar wa Humaira ko guda ba, Humairan ma ko a cikinta, don ko da an cire mata ba amfani da shi zata yi ba.

Bayan kwana biyu, result ɗin JAMB ɗin su Humaira ya fito, result ɗinta ya yi kyau sosai inda take da 275 as JAMB point ɗinta, yanzun jiran sakamakon WAEC take sai ta fara shirye-shiryen tafiya jami'a ko Alhaji Sani zai fita harkarta.

Alhaji Sani kuwa duk wulaƙancin da Humaira take mishi hakan bai saka ya fasa zuwa wajenta ba, kuma a duk zuwan shi sai ya yi mata tsaraba, tun tana barin tsarabar a waje Inna ta tura Bilki ta ɗauko, har ta fara ɗauka tana yi masa godiya. Ranar farko da ta amsa kyautar har ta yi godiya Alhaji Sani ya yi godiya ga Allah saboda ya san ya fara ɗaukar hanyar yin nasara kenan.

_____________

Instead of ƴan kwanankin da Hunaif ya shirya zai yi a Saudi sai da ya yi sati guda da kwanaki saboda Abba ya ƙi yarda ya koma, sai ranar da su Abba za su koma Nigeria kafin ya bar Hunaif ɗin shima ya ɗaga zuwa Brazil. Ɓangaren shaƙuwarsa da Zee kuwa kullum ƙaruwa abin yake, ta kai ta kawo da a rana sai su yi waya fin sau uku, har Zee ta haɗa shi da mahaifiyarta a waya sun gaisa.

Watan Hunaif uku da komawa Brazil ya kira Abba akan yana son aje a nema masa auren Zee a gidansu, saboda ya riga da ya gamsu cewa Zee is the type of woman he have been patiently waiting for. Mami ta yi murna sosai da ta ji wannan maganar, duk da ta so Hunaif da Intisar ne, amma tana fatan hakan shine mafi alkhairi.

Hunaif ya idar da sallah, yana kan darduman ya ɗauki wayarsa ya kira Zee video call. Zee da fitowarta daga wanka kenan ta ji shigowar kira wayarta, tana dubawa ta gan Hunaif ke kira, Hijjab ta ɗauka ta saka akan towel dake ɗaure a ƙirjinta, tana picking call ɗin ta sakar masa murmushi, tace; "Barka da warhaka masoyin Zee."

"Abin ƙaunata da fatan kina lafiya?"

"Lafiya ƙalau alhamdulillah, sai kewarka da ta hanani sakat."

Murmushi Hunaif yayi, yace; "Kar ki damu, kin kusa zama mallakin Hunaif, za ki kasance a duk inda yake, Kinga babu batun kewa kenan."

Hannu Zee ta daga sama, tace; "Allah ya nuna min wannan rana."

"Aameen." Hunaif ya amsa, sai yace; "Zee, na kirane don na yi miki wani albishiri."

Zee ta mayar da full attention ɗinta kanshi, yana kallon fuskarsa da kyau ta screen ɗin wayarta, tace; "Ina sauraronka masoyina."

"Iyayena za su nema min aurenki gobe a gidan ku."

Ƴar harara Zee ta yi masa, tace; "Saboda ka gan ina sonka sossai shine harda zolayata ko?"

Girgiza kai Hunaif ya yi, yace; "Zee kenan babu batun zolaya, tunda ina sonki, kuma na tabbatar kema kina sona, to me ya rage da ya wuce mu yi aure mu kasance tare, wannan dalilin ne yasa na tura a zo a nema min aurenki."

Wani ihu Zee ta sakar na murna, ta yi cilli da wayarta akan gado, buɗe hannunta ta yi ta fara jujjuyawa a ɗakin tana faɗin; "alhamdulillah, Allah na gode maka, mafarkina na neman zama gaskiya."

Hunaif na jinta, can sai ya ji shiru, kawai sai ya katse kiran, ya miƙe don shirya tafiya stadium, yau bai da match, amma yana son ya tafi kallon na wasu.

__________

Yau da gobe asarar mai rai, WAEC result ɗinsu Humaira ya fito, tana da eight credit, dukka recommended subjects na karantar LAW da take so tana da shi. Tun tasowar Humaira take son ta karanci law, da farko dai outfit ɗinsu ne ke burgeta, amma daga baya bayan duniya ta gogeta, sai ta sauya mata tunani, ta ji tana son ta karanci law ko don ta zama wata babbar judge ta rinƙa yanke munanan hukunci akan azaluman mazaa su yi wa ƴaƴa mata fyaɗe.

Result ɗin Humaira ya yi kyau, amma samun admission shima wani abune mai zaman kansa. Inna na tsakar gida tana dakan garin kunun tsamiya wa Humaira da ta tashi da zazzaɓi yau, yaro ya shigo da sallama, yace wai ana kira Humaira a waje.

Inna ta shiga ɗaki ta tarar da Humaira a ƙudundune cikin bargo, sai ta fito tacewa yaron; "Ka ce a shigo."

Alhaji Sani ya yi mamaki da aka ce ya shigo, saboda Abba ya ba su zaurene matsayin wajen hira, amma sai ya yi sallama daga bakin ƙofar shiga, Inna ta amsa tace; "Shigo." Alhaji Sani ya shiga cikin gidan, Inna ta leƙo daga ɗakinta, ta nuna mishi ƙofar falon Abba tace; "Shiga nan ka zauna, tana zuwa." Da ƙyar Inna ta lallaɓa Humaira ta tashi ta saka hijjabi, ta fita zuwa fakon Abba. Alhaji Sani na shiga falon ya zauna a ɗaya daga kujerun dake falon, ji da ya yi kamar ya zauna akan abu ya sa ya tashi, papern da ya gani da hoton Humaira ne ya saka ya ɗauka, WAEC result ɗinta ne aka pinning da JAMB slip ɗinta, ya na duba slip ɗin ya yi murmushi yace; "Ashe tana da ilimi shiyasa take son karatu."

Labulen dakin Huraira ta daga, ta shigo a hankali kamar mai tsoron taka ƙasa, a ƙasa ta zauna ta kwantar da kanta a jikin cushion, da kyar ta iya furta; "Ina wuni."

Alhaji Sani dake lura da yanayinta, yace; "Lafiya kuwa Humaira?"

"Zazzaɓi nake ji." Humaira ta faɗa a hankali.

"Sannu, kin sha magani?"

Kai kawai ta gyaɗa mishi hawaye na bin fuskarta.

"Subhanallah, jeki ki kwanta kawai, Allah ya ƙara sauƙi."

A hankali Humaira ta miƙe ta fita daga falon, Alhaji Sani ya tashi shima ya fita daga ɗakin, tsakar gidan shiru kamar babu mutane, daman Inna da Humaira ne kawai a gidan, sai ya sa kai ya fice, yaro ya samu a wajen ya bashi ledan tsarabar da ya yo wa Humairan ya shigar mata da shi.

Washegari Humaira na kwance a cinyar Inna tana zuba mata shagwaɓa wai kanta na ciwo Ya Kabir ya shigo, ya kalle Humaira dake ƙananan rikici kamar wata ƙaramar yarinya, yace; "Wannan kuma me ke damunta? Ko dai zazzaɓin ne har yanzu?"

"Kanta ke ciwo?" Inna ta faɗa tana shafa kan Humairan da babu kallabi.

"Allah ya sawwaka. Daman na zo ta bani slip ɗin JAMB ɗinta da WAEC ne, wannan Alhajin dake zuwa wajenta wai zai nema mata admission a Jami'ar Bayero."

Inna ta ɗaga hannu sama tace; "Alhamdulillah, Allah abin godiya, ashe dai wannan bawan Allah da alkhairi ya zo, amma Humairata kike ta wulaƙanta shi, gashi tun ba a kai ko ina ba kin fara ganin ranar shi."

Humaira da ta nemi ciwon kai da take yi ta rasa, ta ɗago daga cinyar Inna, tace; "Yaya don Allah da gaske kake?"

"Daman na saba yi miki ƙarya ai."

Kai Humaira ta girgiza, tace; "Yaya kira min shi idan kana da lambarsa please."

Ciro wayar Kabir ya yi daga aljihunsa ya dialing lambar Alhaji Sani ya miƙawa Humaira.

Alhaji Sani na daga kiran instead of ya ji muryar Kabir sai ya ji sallamar Humaira da siririyar muryarta.

Numfashi ya sauke yace"Wa'alaikissalam gimbiya, ya ƙarfin jiki?''

"Jiki da sauƙi Alhamdulillah."

"Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi."

''Aameen." Shiru ne ya biyo baya, can Humaira ta daure tace; "Da gaske za ka nema min admission?"

Murmushi Alhaji Sani ya yi, yace; "Humaira kenan, ribar me zan ci idan na yi miki ƙarya?"

"Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya sa ka fi haka."

"Aameen Humaira."

Alhaji Sani ya karɓi photocopy na credentials ɗin Humaira ya ba wa abokinshi wanda yake Deen students affairs na Bayero University Kano akan ya nema mata admission, abokin ya karɓa ya ba shi assurance akan In Sha Allah suna Humaira zai fita a first list of admission.

_____________

Hunaif na stadium Abbansa ya rinƙa kiransa, message ya turawa Abba; 'Im in the stadium, idan na fito zan kira ka.' Immediately reply ɗin Abba ya shigo; 'Ka fita yanzu, we need to talk.'

Hunaif na ganin reply ɗin ya miƙe ya fita daga stadium ɗin, yana shiga motarsa ya dannawa Abba kira, ringing ɗaya Abba ya ɗauka, yana ɗaukawa yace; "Congratulations Son."

"Tha...nk...you." Hunaif ya amsa sounding confused.

"Daga tafiya gaisuwa muka buƙaci a baka auren zainab, iyayenta kuwa suka yarda da hakan, a take muka bayar da sadaki aka ɗaura muku aure, yanzun haka maganar da nake yi maka kai ɗin angon Zainab ne." Jin maganar Abba Hunaif ke yi kamar a shirin film, ya san yanzu ana ɗaura aure daga kai kuɗin gaisuwa, amma ai da sanin ango ake yi, je just can't believe an ɗaura masa aure yana stadium, is this a movie or what? "Errm Abba you mean ni ɗin aka ɗaurawa aure yau?"

Abba ya yi murmushin manya, yace; "Yaushe kake son a kawo maka matarka?"

"Wait first Abba, I need to talk to Zee right away." Hunaif ya katse kiran Abba, immediately ya kira lambar Zee, tana ɗagawa yace; "Zee wai abinda nake ji gaskiyane, shin ke ɗin mata tace?"

Confusingly Zee dake gidan su Inti tace; "Ban fahimceka ba?"

"Baƙin da ba zai taɓa yi min ƙarya ba ya sanar da ni cewa an ɗaura mana aure, ya aka yi ba ki sani ba?"

"Wait, wait, wai me kake nufi ne, daga zuwa tambaya kana nufin aka ɗaura auren?"

"Yes my wife." Hunaif ya faɗa yana doka murmushi.

Katse kiran Zee ta yi, ta fisgi mayafinta da handbag ɗinta, ta fita a guje, Inti ta bi bayanta, tana faɗin; "Wai lafiyarki Zee?" Amma ina Zee ta riga da ta yi gaba.

IYYE, SU HUNAIF AN ZAMA ANGO

SU HUMAIRA ZA A TAFI UNI

#JIKARGARBA