
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 23
.....I thought it was her. She'd better do that, or else she'll make him sad. She was very sleepy and started to lose her strength, so she set the alarm for ten o'clock and went to bed. Suddenly she fell asleep again. On Umar's part, it is not said that he was able to sleep. He spent the whole night in thought. In the morning, Abba had to wake him up to pray. In his mind, he feels as if they did not give Zahra a gift when they married Ibrahim. At breakfast time, they all sit in the dining room and lie. Mami noticed that Umar was not with them. "O Umar, are you okay?" she asked. He looked quickly, then looked at Mummy and Abbah. He instantly created a smile. "It's okay, Mom, it's just my head that hurts a little." Abbah said, "It looks like you didn't get any sleep yesterday. You hardly even got up to pray." Mami shook her head. "Well, you should see a doctor before the pain gets into your body." He replied, "Toh Mami." Mummy was sitting and listening to them, but she didn't say a single word. So they finished the breakfast, but it was Zahra's thoughts that refused to leave Umar's life. Until he finished eating, his heart was on his sister and what he would do to make Ibrahim realiz
Book 1 Chapter 23
Daren ranar haka Zahra ta gagara bacci. Sai can wajen asuba bacci barawo ya ɗauke ta. Ibrahim kuwa ko zuwa gidan bai yi ba, a waje ya kwana.
Wajen ƙarfe shida na safe alarm ɗinta ya fara bugawa, hakan yasa ta farka da ƙyar. Addu'ar tashi daga bacci tayi, sannan ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Brush tayi tare da alwala, daga nan ta fito ta shimfiɗa sallayarta ta yi sallah.
Bayan ta idar, azkar ɗinta ta fara yi a hankali. Da ta gama, ta zauna kan sallayar tana kallon wani waje, hawaye na bin kuncinta. Jin kamar bacci zai sake ɗaukarta yasa ta koma kan gadon, domin bata jin zata iya zuwa makaranta a ranar.
Can cikin baccin da take yi ne ta ji ƙarar shigowar message. A hankali ta buɗe idanunta, ta ɗauki wayarta. Firdausi ce.
Da sauri ta buɗe message ɗin.
"Ki shirya yau. In Sha Allah yau zamu haɗu da Lovie Dovie."
Tsaki Zahra ta ja tsaki tana juyawa gefe.
"Bana jin zan sake yaƙi da wata saboda Ibrahim."
Ta faɗa a hankali.
Sai kuma ta sake buɗe idanunta da sauri. Wani tunani ya faɗo mata. Gwamma ta yi hakan, ko ba komai zata cusa masa baƙin ciki ne.
Bacci sosai ya fara cin ƙarfinta, hakan yasa ta sa alarm na ƙarfe goma sannan ta kwanta. Nan da nan bacci ya sake kwashe ta.
A ɓangaren Ya Umar ma ba a ce ya samu bacci ba. Gaba ɗaya daren jiya ya kwana cikin tunani. Asuba ma sai da Abbah ya tashe shi zuwa sallah. A ransa yake jin kamar ba su kyauta wa Zahra ba da suka aura mata Ibrahim.
Lokacin breakfast, dukkansu suna zaune a dining suna karya. Mami ce ta lura hankalin Ya Umar kamar baya tare da su.
"Ya Umar, lafiya dai?" ta tambaya.
Da sauri ya kalleta, sannan ya kalli Mummy da Abbah. Nan take ya ƙirƙiri murmushi.
"Lafiya lau Mami, kawai kai na ne yake ɗan ciwo."
Abbah ya ce,
"Daga gani ma kamar baka samu bacci jiya ba. Da ƙyar ma ka tashi sallah."
Mami ta girgiza kai.
"Toh ya kamata ka ga likita kafin ciwon ya shiga jikinka."
Ya amsa da,
"Toh Mami."
Ita dai Mummy tana zaune tana saurarensu, amma ko kalma ɗaya bata ce ba.
A haka suka gama breakfast ɗin, amma tunanin Zahra ne ya ƙi barin ran Ya Umar. Har ya gama cin abincin, zuciyarsa na can wajen ƙanwarsa da kuma abin da zai yi wanda zai sa Ibrahim ya gane kuskurensa.
Shi ne ya fara miƙewa daga dining ɗin ya wuce ɗakinsa. Yana shiga ya ɗauki wayarsa ya yi dialing number ɗin Zahra wanda ya yi saving da Our Angel ❤️.
Kiran na shiga, sai ya ji muryarta cike da bacci.
"Hello Yaya."
Nan take ya sauke ajiyar zuciya. Wani irin relief ya ji ya mamaye shi.
"Kina lafiya?"
"Alhamdulillah."
"Sorry na tashe ki a bacci ko?"
Kallon agogon da ke gefen gadonta Zahra tayi. Ganin saura mintuna goma ƙarfe goma yasa tace,
"A'a Yaya, dama ƙarfe goma nake son na tashi."
"Alright. Amma zaki shiga school yau ko?"
"Eh."
"It's good. Ki samu ki tafi, ki zama so lively."
Wani ƙaramin murmushi tayi.
"Thank you."
Ya Umar yace,
"If there's anything, just let me know baby."
"In Sha Allah."
Daga haka suka yi sallama.
Zahra ta ajiye wayar sannan ta wuce toilet. Wanka tayi, tana fitowa ta shafa lotion tare da fesa turare mai sanyin ƙamshi. Daga nan ta nufi wardrobe ta ɗauko wata baƙar abaya mai matuƙar kyau ta saka.
Ba ƙaramin kyau tayi ba.
Ta ɗauki tot-bag ɗinta ta zuba wayoyinta a ciki, sannan ta sanya baƙin flat shoe a fararen ƙafafunta.
Sauka tayi ƙasa.
Farida na mopping parlorn lokacin.
Da ganin Zahra sai ta miƙe tsaye.
"Ina kwana Anty."
"Lafiya lau Farida, ya aiki?"
"Alhamdulillah."
Kai ta gyada kawai sannan ta nufi hanyar fita.
Da sauri Farida tace,
"Amma Anty baki yi karin kumallo ba ne?"
Zahra ta juya ta kalleta.
"Bana jin yunwa ne."
Farida ta haɗe fuska.
"Amma fa rabonki da abinci tun jiya. Wallahi yadda na ajiye abincin jiyan nan haka nake zuwa na same shi."
Murmushi kawai Zahra tayi.
"Idan na dawo zan ci."
Daga haka ta juya ta nufi ƙofa.
Farida ta bita da kallo har ta fita.
Sai kuma ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta juya da sauri ta nufi ɗakinta.
Wayarta ta ɗauka.
Ganin missed call yasa ta yi saurin kiran number ɗin.
Ana ɗagawa tace,
"Afuwan, ina aiki ne."
Ta yi shiru tana saurare.
Sai kuma tace,
"Eh, yanzu ta fita."
Bayan wani ɗan lokaci ta sake yin shiru.
"Amma ana ganinta ansan ba lafiya ba. A yadda ta fita kam"
Ta sake sauraron mai maganar sai kuma ta ce
"Toh In Sha Allah."
Sai kuma ta ɗan yi murmushi.
"Amma zata yi dare fa, dan yanzu idan ta fita makaranta tana daɗewa kafin ta dawo gidan."
Daga haka ta kashe wayar tana kallon screen ɗin na wasu daƙiƙu kafin ta ajiye ta ta koma bakin aikinta
Lokacin da Zahra ta isa makaranta, har an gama first lecture. Duk da ta yi sauri a hanya, hakan bai hana ta tarar da ɗalibai suna ta fita daga hall ɗin ba.
Motarta tayi parking a inda ta saba, sannan ta sauka a hankali. Ba tare da ta damu da shiga neman kowa ba, ta nufi wani cool down da ke kusa da department ɗinsu.
Zama tayi a ɗaya daga cikin kujerun wajen tana kallon ɗaliban da ke wucewa.
Wayarta ce ta fara vibrating. Ciro wayan tayi taga Firdausi ce sai ta ƙyale kiran.
Bayan ƴan mintuna kuma sai ga wani. Tsaki Zahra taja sannan ta ɗaga.
"Hello."
"Madam, ina kike ne?" Firdausi ta tambaya.
"Ina makaranta mana."
"Na sani. Ina a makarantar?"
Zahra ta kalli wajen da take zaune "Ina cool down ɗin kusa da department."
"Okay, ki zauna nan. Gani nan zuwa."
Kafin Zahra ta ce wani abu, Firdausi ta katse kiran.
Bata jima sosai ba sai ga Firdausi ta iso.
Tana zuwa ta zauna kusa da ita "Kinga fa, tun safe nake ta kiranki."
Murmushi Zahra tayi. "Bacci nake yi."
Firdausi ta kalleta sosai. "Kin yi kyau yau wlh"
"Thank you." Tace a takaice
Sai dai kafin ta ƙara magana, Zahra ta dafe cikinta a hankali
Firdausi ta kalleta da sauri, ta ce "Lafiya?"
Zahra ta sauke numfashi "Wallahi yunwa nake ji."
Firdausi ta zaro ido. "Yunwa? Shine kike zaune bayan kin dan condition dinki?"
Kai ta gyada "Har kamar zan yi amai."
Da sauri Firdausi ta miƙe tsaye. "Toh tashi mu je cafeteria yanzu."
Ba gardama Zahra ta mike Ita kanta ta san jikinta na buƙatar abinci
A tare suka nufi cafeteria ɗin makarantar Wajen cike yake da ɗalibai, kamar kullum
Da ƙyar suka samu waje suka zauna.
Wata ce ta ƙaraso wajensu
Firdausi ta kalli Zahra. "Me zaki ci?"
Zahra ta ɗan yi tunani kafin tace, "Ina son jollof rice da grilled chicken."
"Abin sha fa?"
"Fresh orange juice." Ta ce
Firdausi ta gyada kai. "Ni kuma fried rice kadai, sannan bottled water."
Bayan sun gama order, suka zauna suna jiran a kawo musu.
Firdausi na kallon Zahra lokaci zuwa lokaci.
Ita kuma Zahra hankalinta yana kan abincin da ake shiryawa Domin yunwar da take ji a lokacin ba kaɗan ba ce.
Bayan sun gama cin abincinsu, suka miƙe suka nufi hall ɗin next lecture.
A wannan karon Zahra ta yi ƙoƙarin mayar da hankali kan abin da lecturer yake koyarwa, amma duk da haka zuciyarta ba ta gama kwanciya ba sbd Lokaci zuwa lokaci sai ta tsinci kanta cikin tunani
Firdausi kuwa tana lura da ita, amma bata ce komai ba.
Bayan lecture ɗin ya ƙare, suka fito tare da sauran ɗalibai.
A ranar lectures biyu kawai suke da shi, saboda haka kowa ya fara kama gabansa
Firdausi na shirin yin sallama da friends dinsu ne, sai Zahra ta riƙe hannunta
"Zo muje can."
Ba tare da ta jira amsarta ba, ta fara jan ta zuwa wani cool down da ba ya da hayaniya sosai.
Da suka isa, suka zauna.
Na ɗan lokaci babu wacce ta ce komai.
Firdausi ce ta fara magana.
"Like seriously, me yasa kika kawo ni nan?"
Zahra ta sauke numfashi. "Kamar kar na koma gida."
Firdausi ta kalleta. "Why?"
Zahra ta yi shiru, sai ta kalli wani waje kamar tana kallon wani abu da babu shi
Firdausi ta lura da hakan ta ce "Zahra?"
Shiru tayi ba tare data kulata ba
"Menene?"
A hankali Zahra ta ce, "Ina so na rabu da Ibrahim, shiyasa ɗazu nace ba sai munje can din ba"
Firdausi ta ɗan zaro ido tana kallonta sai dai bata katse ta ba.
Zahra ta ci gaba. "Wallahi Firdausi ban damu ba ko duniya zata min dariya."
Muryarta ya fara rawa "I don't care.... Firdausi"
Sai ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi
"Kuma zan je na bawa Mami haƙuri."
Firdausi ta haɗe gira "Mami kuma?"
Kai Zahra ta gyada.
"Eh."
"Me yasa?" Firdausi ta tambaya
"Saboda ina jin kamar harda hakkinta a kaina."
Ta sauke numfashi mai nauyi, sai ta lumshe idanunta
"Kullum sai na ga kamar har yanzu Mami tana jin haushin abun daya faru"
Kafin Firdausi ta ce wani abu, Zahra ta fashe da kuka nan take
Firdausi ta matsa kusa da ita da sauri
"Hey..."
Amma Zahra ta kasa tsagaitawa, kawai kuka take yi
Firdausi ta riƙe hannunta. "Ki kwantar da hankalinki."
Ta girgiza kai. "Na gaji Firdausi, Na sani komai, Wallahi na gaji"
Da ƙyar Firdausi ta lallabata har kukan ya fara raguwa.
Sannann ta ce, "Listen to me."
Zahra ta share hawayenta.
Firdausi ta ci gaba.
"Auren Ibrahim yana cikin ƙaddararki. Abin da ya faru ma yana cikin ƙaddararki, kuma babu wanda zai iya canza abin da Allah ya rubuta"
Zahra ta yi shiru tana saurarenta
Firdausi ta matsa kusa da ita "Yanzu ba lokacin yanke hukunci bane Kin ji ni?"
Bata amsa mata ba, ita dai wani wajen take kallo
Sai Firdausi ta sake cewa
"Ba lokacin da mutum yake cikin fushi da ciwo yake yanke manyan hukunci ba."
A hankali Zahra ta ɗaga kai ta kalle ta
Firdausi ta ci gaba "Ki bari zuciyarki ta huce. Daga nan sai ki yanke shawarar da zata fi miki alkhairi"
Ta ɗan yi murmushi.
"Kuma game da Mami, wallahi na san tana sonki, don haka kar ki ɗora komai a ranki, tuni ma idan Mami Dana sani ne ta yafe miki Zara"
A hankali Zahra ta share sauran hawayenta, sai ta sauke numfashi
Duk zuciyarta bata huce gaba ɗaya ba, amma kalaman Firdausi sun rage mata wani ɓangare na nauyin da take ji
A haka suka ci gaba da zama a wajen na wasu mintuna kafin suka miƙe suka kama hanyarsu
Da ƙyar Firdausi ta samu Zahra ta sake murmushi kafin suka yi sallama. Daga nan Zahra ta nufi motarta ta kama hanyar gida
A hanya ma tunanin abubuwan da suka faru ne ke yawo a ranta, amma ba kamar da safe ba. Kalaman Firdausi sun ɗan kwantar mata da hankali
Da ta isa gidan, mai gadi ya buɗe mata gate. Ta shiga compound ɗin a hankali tare da yin parking.
Tana sauka daga motar ne kuwa ta hangi wata mota tana shigowa
Ta tsaya tana kallo. Ya Umar ne.
Yana ganinta ya yi parking shima sannan ya fito daga motar.
"Wai Zahra!" Ya faɗa da murmushi.
"Yaya." Ta amsa tana murmushi
"Kin dawo kenan?" Ya ce
"Eh."
Ya matso kusa da ita yana kallont
"Alhamdulillah. Yau kam kin fi jiya kyau, ko ke fah"
Dariya ta yi ta ce "Yaya kenan."
"Da gaske nake." Ya karɓi bag ɗinta daga hannunta
"Zo mu shiga."
A tare suka shiga cikin gidan
Sosai ma Mami ta jata a jiki Yau, ganin kamar Tana cikin damuwa. Haka ma Ya Umar ya ƙi yarda ta zauna ita kaɗai. Ko yaushe sai ya samo wani abin hira ko wasa.
Bayan ya dawo a masallaci suka zauna a parlorn suna buga game a wayarsa
"Daga nan zaki mutu." Ya Umar ya faɗa yana dariya
"Yaya cheating kake yi."
"A'a ke ce baki iya ba"
"Wallahi ka yi cheating"
Daga can Mami tana kallonsu. Da ta ji Zahra na dariya sai itama ta yi murmushi
Tun jiya take lura da cewa zuciyar Zahra ba a kwance take ba, sai dai bata so ta matsa mata da tambayoyi
Hakan yasa ita ma ta shiga jan Zahra a jiki fiye da kullum
"Wai ku biyu ba zaku bari a huta ba ne?" Mami ta faɗa tana fitowa daga kitchen.
"Shi ne fa Mami" Zahra ta kai ƙara "Yaya ya hana ni cin game ɗin."
Ya Umar ya yi dariya ya ce "Ai ke ce baki iya ba."
Mami ta girgiza kai tana murmushi.
"Ku dai kuna nan har yanzu kamar wasu yara"
Ta zauna kusa da Zahra sannan ta dafa kafaɗarta
"Kin ci wani abu kuwa?"
"Eh Mami."
"Da gaske?"
Kai Zahra ta gyada.
Sai Mami ta kalleta da kyau. "Toh shikenan."
Amma duk da haka ta miƙe ta koma kitchen.
Ba jimawa ƙamshin gwate ya fara tashi a parlon
Ya Umar ne ya fara cewa,
"Hmmmmm Mami."
Mami ta yi dariya ta ce, "Kar ka fara."
Zahra ta kalli kitchen ɗin. "Gwate ne?"
"Eh." Mami ta amsa daga ciki "Na dafa miki da kaina"
Zahra ta yi mamaki "Danni Mami?"
"Eh mana."
Mami ta fito da plate ɗin tana ajiye wa a gabanta "Tunda na san kina son shi."
Wani abu ya motsa a zuciyar Zahra, ta kalli Mami
Sai kawai ta ji idanunta sun cika da hawaye, amma ta yi saurin mayar da su baya
Mami kuwa ko kaɗa bata nuna ta lura ba. Kawai tace, "Ki ci kafin ya huce."
Murmushi Zahra ta yi "Nagode Mami naa"
A wannan yammacin, tsakanin hirar Ya Umar, kulawar Mami da kuma zaman gidan, Zahra ta ji wani sashe na damuwar da ke zuciyarta ya ɗan sauka, Ko da yake ciwon na nan, amma a karo na farko cikin kwanakin nan, ta samu kanta tana dariya ba tare da ta tilasta wa kanta ba
#08110615256 #Jiddatulkhayr writes