
Post
HIYAAM HAUSA NOVEL PAGE 4
.....I gave birth? Do I see my own son in front of me?" Sadiatu said, "God is in control." "That's right, Yaa Sadiatu." Slowly she turned and looked at the baby again, and it was as if his breathing was not going as it should, not like a stick gave birth to him. She took him, she felt his body tremble, her eyes turned white, she looked at the sky. "Oh my God, look at this child." Her body trembled with fear I didn't give birth to him..," she couldn't finish. "He came into the world in perfect health," she said at the same time bursting into tears. Sadiatu was very changed around the baby but she didn't want to confuse Kulu in her care. She said, "Oh Kulu, does God not tempt a servant? I told you it was a suggestion...
*H I Y A A M*
Page 4 Bright pens
Yota/001
*"A resilient heroine;* Nazeefah Sabo Nashe
Ganin rana ta buɗe ya saka ta ƙara ɗaure bakin zaninta inda ta ƙulle kurwar jaririn tana tafe tana juyawa har ta ɗauki hanyar shiga rugar Fulaninsu da ake cewa Rugar Yari, idanun nan nata jajur babu kyan gani sai motsa bakinta take, tana yin tiƙar baki.
Daga can cikin gidan Kulu na zaune da jaririn a hannunta sai murmushi take yi yau Allah ya azurtata da samun ɗa, bayan shafewar wasu shekaru da aurenta, mai rai baya fida tsammani a rayuwa, a wajan Kulu har ta cire rai da ganin jininta a duniya, banda gorin haihuwa, dana kishiya da kuma dangin miji, ana kiranta da juya babu kalar cin kashin da bata gani ba. Duk tafiyar minti guda sai ta juya ta kalli jaririn da zuwa yanzu ta kwantar dashi akan ka katifa. "Kulu kallon yaron ya isa haka" In ji Sadiatu
Murmushi ta yi can kuma ta ce "Yaa Sadiatu ji nake kamar ba daka cikina ya fito ba, me zan yi na nuna wa Ubangiji godiyata daya share mini hawayena? Yau ni na haihu? Ɗana na kaina nake gani a gabana?" Sadiatu ta ce
"Haka Allah yake ikonsa"
"Haka ne Yaa Sadiatu"
Sannu a hankali ta juya ta sake kallon jaririn sai taga kamar numfashinsa baya tafiya yadda ya kamata, ba kamar sanda ta haife shi ba, ta dinga kallonsa gabanta na faɗuwa, jinin jikinta na daskarewa saboda tsabar fargaba da zullumi, bata son dukkan abin da zai gitta a jikinsa da sunan ciwo ko wata damuwa, a hankali ta ja numfashi ta fesar, sai kuma ta miƙa hannunta ta ɗauke shi, sharf haka ta ji jikinsa ya saki, yana wani ƙanƙandarewa, ƙwayar idanunsu ta yi fari tas tana kallon sama. "Na shiga uku, Yaa Sadiatu duba mini yaron nan kamar bashi da lafiya, wayyo Allahna" jikinta ya ɗauki rawa da wani irin kakkarwa na fargaba.
"Ki nutsu Kulu, shawara ce ta shige shi" da ƙarfi Kulu ta ce
"Shawara?"
Kulu ta maimaita a kiɗime.
Sai kuma ta girgiza kai idanunta na cika da hawaye ta ce "Ba haka na haife shi ba..," ta kasa ƙarasawa "Da cikakkiyar lafiya yazo duniya" ta furta a lokaci guda tana fashewa da kuka sosai.
Sadiatu taga sauyi sosai a tattare da jaririn amma bata so ta ruɗa Kulu cikin kulawa ta ce "Haba Kulu, shikenan Ubangiji baya jarabtar bawa? Na faɗa miki shawara ce ba wani abu ba, yara kuma suna yi, bari na fitar dashi waje yanzu zan aika a amso mini magani" ta faɗa tana miƙewa tsaye, bata son rawar da jikinta ya ɗauka ya ankarar da Kulu cewa ba lafiya ba, don haka cikin sauri ta fice da jaririn tana sallallami a zuciyarta.
Batty dake rakuɓe tana wasa da wani zakara data kama tana fiffige gashin jikinsa yana cara da kuka amma duk basu ji ba, ganin jini na fita a jikin zakaran ta yi saurin rungume shi kamar mutum yunwa ke ƙoƙarin zautar da ita. Da sauri ta zubawa Sadiatu manyan idanunta da nan take suka sauya daka fari zuwa ja, ba Sadiatu take kallo ba, jinin dake gudana a jikinta shi take bi da idanunta guda huɗu, jikinta ya ɗauki rawa, sai ta yi saurin yin ƙasa da idanunta zuwa ƙafafuwan Sadiatu ta zubawa kurwar Sadiatu dake yawo a ƙasan ƙafafuwan idanu, idan ta yi kamar zata kame kurwar sai ta fasa, cikin hanzari ta yi cilli da zakaran ta fice daga cikin gidan ta fara tafiya idanunta na shigewa ciki ya yi jajur bata ganin ko gabanta, sai data nausa ta shiga cikin gonaki kafin ta samu gefen wata ƙorama da ruwa ke gudana a wajan ta zauna, zanin Fulanin dake jikinta ta ɗan kuntu kaɗan sai ga baƙar leda ta bayyana, ɗanyen barkono ne a ciki jajur dashi, ta saka fararan hannunta ta ɗamki barkonon ta watsa a bakinta ta shiga taunawa kamar zata ci babu, sai data kusa cinye sannan ta ji abin ya faɗa mata a hankali.
“Baffana, Innata ku cire mini abin nan bana so bana so a cire mini bana so” ta ce a hankali. Tana yi tana ƙoƙarin yage kayan jikinta.
Sai kuma ta kwanta a gefen ƙoramar tana sakin wani irin kuka mara sauti tare da shura ƙafafuwanta tana riƙe cikinta. Idan ta tuna mutanen da suka shigo har rugarsu suka yanka Innarta wani irin abu take ji yana yawo a ƙirjinta, burinta na son yin karatun boko yana ƙaruwa a ranta.
*** Yana daga zaunen da yake a saman kyakkyawar kujerar ofis ɗinsa tana ɗan juyawa dashi cike da nutsuwa ya ɗaga kai ya kalle ta kafin ya ce "You again? Na ɗauka na kawo ƙarshen matsalarki? Ina nufin zuwa yanzu ba ki da wata damuwa akan aiki?"
Murmushi ta sakar masa tana ɗan juya jikinta da kwainane ta ce "Kasan buƙata haifar kanta take yi sir, kuma sai ina da buƙata zan zo wajanka tunda ka sabar mini?" Ta ƙasan idanunsa yake kallon ta ya yi shiru alamar yana sauraranta.Sai ta yi ƙasa da murya ta ce "Akan recorded ɗin dana tura maka ne wanda Ahlam ta yi, kuma ni ce wacce zan gabatar dashi a labaran rana. Labarin me kyau ne idan aka cire sunan Ahlam a matsayin wacce ta kawo labarin aka maye gurbinsa da nawa zan samu ƙarin ɗaukaka sosai Sir, zan ƙara farin jini a idanun mutane kuma kasan an kusa taron ƙarshen shekara zan iya samu award, shine requesting ɗina"
"Amma kin san wannan labari ne me kyau da zai ƙara kawo mana audience a gidan rediyon nan, daga zuwan Ahlam kawo yanzu kin san muhimman labaran data kawo ake saka sunanki a madadinta saboda kawai ki samu ɗaukaka da fashion. Shekara nawa da kafa gidan rediyon nan wanne irin Appointment letter ne bamu turawa Sayyadi Baffa ba, amma ko sau ɗaya daga Office ɗinsa na Hisba Shari'a ba'a taɓa responding ba, amma tun wani program da Ahlam ta yi akan rigingimu addini da ake da Malaman Ɗari'a da jama'ar Shi'a sau ɗaya ya amshi gayyatar ta ɓoyayyiyar hanya, madadin a tura Ahlam ke aka tura, ban san ta ina ya fahimci cewa ba Ahlam bace sai office ɗinsa suka cancelled program ɗin ma, last last ma ashe bada shi za'ayi hirar ba da yaronsa ne. Kin ja mana asara babba, da Ahlam ta yi hira da Sayyadi Baffa Allah kaɗai ya san mabiyan da Bright Fm zata samu da irin ɗaukakar da yarinyar za ta yi"
Cikin sigar damuwa ta ce "Ka kwantar da hankalinka sir zan nemo Sayyadi Baffa zan yi program dashi a wannan gidan radiyon" wani kallo ya yi mata na kamar bata san me take ba, a baki kawai take jin Sayyadi Baffa ɗin, ko Hisba bata da ikon shiga balle Office ɗinsa. "Kar ki wahalar da kan ki, kamar yadda bai taɓa shiga kowacce kafar yaɗa labarai ya yi magana ba, to ke ba ki isa ki saka shi ba, duk wa'azinsa da yake yi har gidansa ake zuwa a ɗauka" "Ok fine. Yanzu yaya ake ciki?" Sai ya miƙe tsaye ya zago inda take yana kallon ta a tsanake. "Kenan a kamilalliyar ƴar jarida ake kallonki duk wannan uban rawar kan da kike dashi da yadda kika gama rabawa manya jikinki saboda kawai ki samu damar program dasu" murmushi ta yi kawai tana jin yadda ya ɗan rungumeta ta baya yana hura mata iska a kunne ta yi saurin jan numfashi.
"Sir.....
"Can I?"
Idanunta a lumshe ta kasa motsi muryarta na rarrabewa ta ce "What?"
"Kiss you"
"Can I kiss your lips?" Ta fara gajiya amma kuma tana buƙatar cigaba da ɗaukaka a matsayinta na ƴar jarida ta jinjina kai. Kissing ɗinta ya fara na wani lokaci kafin ya sake ta ya yi baya ya ce "Approved"
"Thank you sir"
"Amma da sharaɗin za ki saman a hotel yau mu kwana ko?"
Ta yi ɗan jim sai ta ce "Amma me zan ce a gida?" Ya ce watsa mata harara "Ɗan jarida ai yafi kowa iya tsara zance. Ki nemi abin faɗa kawai ko ki ce dutyn dare ne dake suwa safiya, ita Ahlam ki mance da ita bata biyo layin ɗaukaka ba" har zata fita ya ce "Taken ki, hankaka me da ɗan wani naka, idan kin zo hotel ɗin haka za ki ce ina da shadols da yawa"
"Ok sir" ta faɗa tana ficewa.
*** A hankali take takawa kamar bata son shiga ciki, sanye take da abaya purple wacce take da feshin stones daya kasance baƙi, ta yi rolling kanta da baƙin mayafin abayar, hannunta ɗaya riƙe da jakarta da wayarta, ɗaya hannun maƙale a wajan hammatarta wanda ya kasance shanyayye. Addu'a ta yi kafin ta sako ƙafafuwanta cikin reception ɗin BRIGHT FM. Wanda a ƙofar shiga aka rubuta da babban haruffa da golden colour da feshin milk. “BRIGHT FM 116 KANO”
"Bulala hamsin ta makara"
Ta ji an furta a bayanta, cikin murmushin da baya taɓa barin kyakkyawar fuskarta ta murmusa kaɗan cike da ladabi tana yin baya kaɗan ta ce "Baba driver ina kwana" ya washe baki ya ce
"Lafiya lau Alam"
"Alarm?" Ta faɗa tana marairace fuska. Ya ce "Sunan naki ne na ƴan gayu, akwai wahalar furtawa a saman harshe musamman wajan irinmu tsofaffi wallahi" Ta lumshe idanunta ta buɗe, har ƙirji ta ji ƙamshin turarensa ya saukar mata, kafin sannu a hankali ta ji takun tafiyarsa ya ratsa ta gefenta ya shige, sai ta ji kamar ya shige da komai nata ne, nutsuwa, farinciki, da sauran kuzarin daya ragu a jikinta komai ba. Idan ta ce komai, tana nufin everything!
"Barka da shigowa MD"
Ta ji Baba driver ya faɗa, bata da tabbacin ya amsa, domin a karkashinsa ta san tuni ya yi kwana ya shige sashin da yake. Idanunta ya ɗan yi rau-rau wani ruwa na kwanciya a cikinsu, idan akwai abin da take da rauni ko yake nuna saurin gazawarta, bai shige kuka ba. Ko fitar hawaye daga cikin idanunta.
"Ahlam ne baba" sai ta ɓata fuska.
"Idan ka ce Alarm kana nufin abin agogo" Baba ya ce "Ba ki da sunan gaskiya ne?"
"Akwai, Haleemah"
Ya ce "kice kakata ce, bari na ce tsohuwa"
"To shikenan, na gode baba"
Ta furta tana jan ƙafafuwanta zuwa ciki, kai tsaye sashin sashen Labarai (News Department) ta dosa, office ɗin Director of News ta fara shiga, ta yi sa'a yana zaune yana duba wasu ayyuka a computer gabaɗaya ya tattara hankalinsa zuwa ga abin da yake yi . "Sai yanzu?" Ya furta a hankali.
"Sir, na tashi da ciwon kai ne"
"Opps, wish you a very quickly recovery"
"Thank you, Sir"
"Zauna mana, have a seat please"
Jin shiru kuma bata zauna ba, ya sanya a karon farko ya ɗago idanunsa da suke cikin farin glasses ya zuba a saman fuskarta kamar ba zai yi magana sai kuma ya ce.
"Ahlam"
"Na'am"
"Nemi waje ki zauna, ya akai?"
A sanyaye ta ja kujera ta zauna, yau ɗin ba kamar yadda ya saba ganin karsashi a jikinta ya ruske ta ba, sai ya ji a ran shi tabbas akwai damuwa, duk da ɗabi'arta ce zuwa gaida kowa a gidan rediyon muddin ta shigo. "Kin yi shiru? Kamar da matsala ko?"
"Sir, akan rahoton dana tura maka jiya ne"
"Oh; Yes, na duba komai ya yi kyau kin yi aiki me kyau kuma me muhimmaci, ni kaina hankalina ya tashi dana saurara ban yi ƙasa a qwiwa ba na tura shi bayan na tace komai" ya ce yana yin baya da juya kujerar.
Ahlam ta fiddo idanunta wajan faɗin.
"Ina ka tura shi Sir?"
"Editor-in-Chief, is there any problem?"
Shiru ta yi har zata miƙe tsaye ta ce "Sir ka gyara zaman tea cup ɗin zai iya faɗuwa ya zube maka a ƙafa, idan ka ƙone ai muna cikin wani hali" kallon cup ɗin ya yi sai ya kalle ta.
"Babu wani faɗuwa....," bai ƙarasa faɗa maganar ta tsaya masa ta dalilin rikitowar cup ɗin da shayin zuwa ƙasa, Ahlam ta hangame baki cike da tsoro ta yi baya tana faɗin
"Sannu sir, bari na...,"
"Hold on please Ahlam, ki faɗa mini gaskiya ya akai kika san cup ɗin zai faɗi da shayin? Da faɗar da kikai ko minti uku ba'ayi ba ya kifo mini a ƙafa" kai ta shiga girgiza wa da alamar jarumta a tattare da ita ta ce "Kawai na faɗa ne bana nufin hakan" Wani kallo ya yi mata wannan shi ne karo na uku tana musu a gidan rediyon nan yana faruwa wani abu kamar camfi "kina nufin bakya tsafi?"
Ta girgiza kai sai kuma ta yi saurin tashi tsaye ta yi masa godiya ta fita, cikin sassarfa bata ganin ko gabanta ta nufi office ɗin Editor-in-chief, tana ƙoƙarin yin corner ta ji ta yi ƙaro da ƙirjin mutum, a kiɗime ta yi baya tana rarraba idanunta, tare da dafe goshinta, ya tsaya cak daga tafiyar da yake yi yana juya idanunsa a kanta, wacce take biye dashi ce ta yi siririn tsaki wajan furta "Kin fita daga cikin hankalinki ne da za ki dinga tafiya anyhow, duk yadda zuciya ta raya miki kamar a filin gidanku?"
Ahlam ta zubawa Yusraah idanunta, kamar da biyu take mata faɗan, kamar bata lura cewa abin da ya faru unexpected ne ba, ba da gangan ta yi ba, ta ya ya zata tsara buge mutumin daya girme mata, ya zama sama da ita a gidan rediyon, yake sama da kowa ma. Dukkan su ai suna ƙarƙashinsa ne, a ƙasan MD suke shi kuma yake ƙasan Founder, kamar bata lura shima ya yi mata rauni da buɗaɗɗan ƙirjinsa ba, ko ita Yusraah bata gani ne, bata kuma fahimta.
"I'm very sorry Sir"
Shine abin da ya suɓuce daga cikin bakinta, ba tare data lura daya jima da barin wajan ba. "Ga iyayi ga nakasa, a dole sai an ɗaukaka wai, mu zuba mu gani ni dake babu wani cigaba da za ki kawo wanda zai iya moving level ɗinki daga yadda kike ɗaukaka sai dai ki ga ana yi wallahi"
"Yussy, ai ban ɗauka kina halitta ba" Yusraah ta ce
"Kar ki mini rashin ɗa'a yanzu na miki illa"
Ahlam ta yi murmushi tana cije bakinta tana kallon Yussy ta ce "Bayan rashin aji dake ɗawainiyya dake ashe hadda rashin ilimin addini ne ke damunki Yussy."
"Ni kike faɗawa haka"
"Na faɗa miki ki saka mini gas idan za ki iya, wacece ke da za ki fara mini ihu a saman kaina, da faɗan zan ji ko da muryarki dake neman tarwatsa dodon kunnena, maganar nakasa da kike, na yarda ina da nakasa, amma nakasata bata taɓa zama kasawa a gare ni ta zama hujjar zama raunin Ahlam ba, kina ji kina kallo da wannan nakasar Ahlam zata kafa tarihin da har abada Yusraah bata kafa ba, kuma ki faɗawa me sama cewa bai iya halitta ba, ƙarshe kenan"
Tana faɗin hakan ta shige office ɗin Editor-in-chief ta bar Yussy tsaye shanye da baki."Kamar fa daƙiƙiya take ƙoƙarin haɗani da kalmar, kan uba, yaushe tazo gidan rediyon?" Ta saka hannunta a baki tana ciza sai kuma ta yarfe hannun, ba zata taɓa zuba idanu Ahlam ta shigo ta fita farin jini ko ƙoƙari a cikin BRIGHT FM, Radio ba, wacece Ahlam yaushe ta fara koyan aikin? Ta tuna ranar data fara zuwa gidan rediyon, ranar data saka idanunta akan Ahlam sai ta ji kamar wacce zata kawo ƙarshen farin jininta a gidan rediyon ce tazo. Tabbas ta tuna, ta tuna komai.
Daga office ɗin HR ta fito sukai karo a hanya
"Sunana Ahlam Abdallah Kurmi, matashiyar ƴar Jarida me koyan aiki yau na fara aiki" Ta ce da golden voice ɗinta tana kallon Yussy, wacce ta yi tsaye tana kallon ta, bafa mata ƴan jarida ne bata saba gani ba, ana yawan yin mata masu koyan aiki, kuma ta dalilin Yussy suke barin BRIGHT FM ɗin.
Sai dai me? Akwai bambanci.
Tarin bambancin dake tsakaninsu da Ahlam, a suffa, kyawun sura, nutsuwa da kamala, da zallar kyau irin na kanuri. Da farko, muryarta ita ta fara ruɗa Yussy, irin muryar dake hawa da kowanne kalar program a gidan rediyon, News, interview, Boardcast, kowanne kalar abu muryar Ahlam zata ɗauka. Hakan ya bawa Yussy tabbacin Ahlam za ta yi nasara na shiga kowanne kalar program, ita kuma za ta yi ƙasa ne. Hujjar farko daya zama dalilin tsanarta da Yussy ta yi, hujjar da bata zama ƙwaƙƙwara ba, bata zama dalili babba ba. Tana da kyawun da za'a so ta, sai dai tana da tabbacin ko kallo bata ishe MD ba, kamar yadda burin Yusraah shine maza matar MD ɗin.
Sai ta kalle ta sheƙeƙe ta watsar, tana taunar chewing gum, ƙas ƙas ƙas ƙas.
Al'amarin da ya yi wa Ahlam zafi kenan.
"Ina fatan na samu ƙawa, wacce zata koya mini abubuwa da ya kamata na sani game da aikin daya kawo ni ko?".
"Sai da bana abota da nakasasshe, da zan ba ki shawara da kin koma gida kin ɗauki roba ki bi sawun mutanen gefen titi, amma wannan aikin bana mutane masu nakasa bane irinki" ta faɗa tana watsawa Ahlam harara, har zata juya sai kuma ta tsaya ta ce
"Yusraah Yassar Yakasai, shine sunana, matashiyar ƴar jaridar da ake ji da ita"
Tana faɗin hakan ta juya tana rangaji kamar wacce zata bi iska ta yi sama, siririya ce sosai, irin masu shafaffan ɗuwawun zaman nan, ga ɗamammun kaya da take son sakawa, wanda ke fitar da jemammen kwankwason nata a fili, zanƙaleliya ta ita tana da yalwar ƙirji da kyan fuska sosai
Ahlam sai ta fito da hannunta data ɗan rufe da mayafi, ta kasance me duhun fata, irin me hasken nan sosai da akewa laƙani da
'Chocolate colour'
Bata da tsayi can, kuma ba gajeriya bace, tana da kakkuran jiki ko'ina a murje kamar ita ta zaɓin yadda zata kasance, abu uku dake fito da asalin kamarta da Kanuri shine, manyan idanunta farare tas, sai jajayen laɓɓanta wanda suke koyaushe kamar ta shafa musu lips lamp peach kuma. Hannun daya shanye take ta kallo, yatsun hannun wani yafi wani, wani dogo wani gajere, sai ɗan kaifi da suka yi, wanda ya kasance manuniyya shine ya yi zabgege a ciki, sai fatar hannun da ta yi yaushi da tattare waje guda, bata taɓa iya motsa hannun yana maƙale kodayaushe, da hannu guda take yin komai na rayuwa, wanda ya zama na damanta, bata samun gazawa na yin abu.
To ai ita ma ba haka aka haife ta ba.
Kamar cutar ƙyanda ta yi.
"Baby na kusa rasa ki, fara ce ke sosai, ƙyandar nan da kikai ta saka kin yi baƙi"
Cewar Engineer.
Yussy ta sauke ajjiyar zuciya bayan Ahlam ta shige cikin office ɗin Editor-in-chief, ta yi ƙwafa tana bin bayan MD zuwa office ɗinsa.
TJ ya kalli Ahlam ya ce
"Golden voice ya akai ne?"
"Sir, na je wajan Director of News akan batun rahoton dana tura masa jiya da daddare, shine ya ce ya turo maka ai"
"Rahotan matar da aka ƙonawa jinjiri?"
Cikin rawar murya Ahlam ta ce.
"Yes Sir, shi nake magana"
"Ok ya akai Golden voice?"
"Sir Tj akwai matsala ne akan rahoton, ina buƙatar a dakata wajan ɗora shi, kar a gabatar dashi Please don Allah sir Tj"
Ya yi baya ya ce "A dakata?"
Ta ce "E, don Allah"
"Na riga na turawa News editor, zai wahala idan ba'a kammala ba, domin a labaran 12 za'a saka shi, sai dai ki je can ki duba muga...," bai ƙarasa faɗa ba, ta yi saurin miƙewa jikinta na rawa ta fita ta nufi office ɗin News editor, a hanya ta haɗu dashi, tun kafin ta ƙarasa ya dinga yi mata kyakkyawan murmushi yana lumshe idanunsa tare da daidaita tsaiwarsa yana jiran zuwan nata, daman wajanta zashi sai kuma gata tazo.
"Baby ya aka yi?"
Ya furta kamar yadda Engineer yake faɗa, sai ta kwaɓe fuska idanunta ya yi rau rau muryarta na rawa domin bata so ya dinga ce mata baby sam.
"Shikenan, Ahlam"
Ya ɗan matsa kusa da ita yana jin numfashinta na sauka. "Anees, rahoton dana turo yana ina? Ka cire a cikin rahotanni da za'ayi ina cikin matsala ne sosai Please"
"Problem?"
Ta jinjina masa kai.
"11:52 fa baby"
Anees ya faɗa yana duba agogon hannunsa.
"News Anchor tana studio yanzu haka, ki yi haƙuri ki bar shi baby, ai labari ne me kyau"
"Na shiga uku"
Shine abin data samu zarafin faɗa tana jingina da jikin bangon. Anees ya ɗan matsa kamar zai riƙe hannunta daga bayansa ya ji an furta "Kana iya ɗaukanta zuwa hotel, nan bai zama dandalin yin iska ci ba" kafin su juya tuni ya bar wajan, ƙirjin Ahlam sai ɗagawa yake yi kamar wacce Asthma ɗinta ke ƙoƙarin tashi, ta dinga riƙe ƙirjinta, bata san zirga-zirgar da MD yake yi yau ɗin nan ba, tana lura sai shige da fice suke yi shi da Official & Professional department, tare da Events & Outside Broadcasts (OB) Unit.
"Anees ka taimaka mini, idan aka saka abin nan ina cikin matsala ba zan yafewa kaina ba, ka taimaka mini" Anees ya zuba mata idanunsa da sukai ɗan laushi da kalaman da MD ya jefe shi da su, da ƙyar ya iya cewa
"Baby bana shiri da Yussy kin riga kin san hakan"
"Yussy ce zata gabatar da labaran?"
Ya ce "Yes, Zainab Alƙali bata shigo ba"
Ta sulale a wajan tana dafe kanta, daidai nan messenger ya shigo da sauri yana faɗin "Golden voice kin yi baƙuwa a reception" bayan messenger tabi tana zuwa ta hango matar, wacce kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci Bafullatana ce, da kuma ɗanyen jikin dake tattare da ita na haihuwa.
Tana ganin Ahlam ta zabura tana durƙushewa ta ce "Ki taimaka mini kar ki saka abin nan a iska yabi duniya, ki taimaki igiyar aurena kar a sake ni, idan ya rabu dani wallahi yanka ni za'a yi a gida, ki tausaya wa rashin gatana nasan ke macace, ba za ki so na wulaƙanta ko aurena ya mutu ba, na haƙura na bar komai a wajan Ubangiji don Allah kar ki saka na roƙeƙi" baya da baya Ahlam ta fara ja, jikinta na rawa da kakkarwa ta juya a guje zuwa studio wanda aka rufe ko'ina gudun kar iska ta shiga, tuni Yussy ta shirya komai gabatarwa kawai ya rage, tana ƙoƙarin buɗe ƙofa ta ji an buga mata uwar tsawa a firgice ta juya idanunta ya sauka akan Md ɗin.
***
Ƙafarsa ta ɗora ɗaya kan ɗaya idanunsa zube cikin farin glasses da kaya na shan iska a jikinsa, ƙasaita kamala da ilimin zamani da gogewa ta shiga cikin manyan mutane ya gama zama a jikinsa. Labarai yake kallo a Aljazira girman parlourn kaɗai abin kallo ne. Wayarsa ce ta fara ƙara alamar shigowar kira ya juya kaɗan, sai ya miƙa hannunsa me ɗauke da gargasa zuwa kunnensa ya gyara zaman Bluetooth.
"Indabawa ya ake ciki?" Ya furta a tausashe yana sake lumshe idanunsa.
"Abin da kake jira ne, Government house ta fitar da sabbin forms na ɗaukan matasan da suka kammala University babu aikin yi, an fitowa da tsarin Allowance for the other students da basu samu Form na aikin ba da za'a dinga musu shi monthly" ya yi jim.
Indabawa ya ce "Kana jina?"
"Wane ya akai wannan buƙar ga Shugaba? Wa aka bawa damar rabawa local government forms ɗin da Reps?"
"Actually ban sani ba, amma kai aka bawa duka forms ɗin ta hannunka za su fita" sai a lokacin ya saki ajjiyar zuciya ta samu nutsuwa ya ce "Ina ga abin da za'ayi, zan ɗan rabawa rukuni sai ku bawa familys naku, za'a sanar a Internet dama ga masu son aiki su je Government house a tantance aiki ne kyau ga wanda suka kammala University suka fita da first class, sauran aikin zan sanarwa da Kalido yadda za'a tsara, ba za'a raba ko ɗaya ba, duk me buƙata siyar masa za'ayi, idan mata ne a tura su office ɗin P.A na, idan sun ji jarrabawar da ya yi musu sai a basu"
"Yadda ka ce haka za'ayi, Allah Ya taimake ka, na hannun daman Shugaba ƙasar taku gwamnati taku" ɗan murmusawa kawai ya yi kafin ya kashe kiran.
***
Iftifal ce ke tafiya daga aiken da Innti ta yi mata na karɓo kuɗin adashi, tun daga nesa ta hango majalisar dasu Daada suke zama, kamar koyaushe yana zaune suna karta sai busa sigari Daada yake yi yana fesarwa tazo dab dasu ta durƙusa har ƙasa tana wasa da yatsun hannunta da suke farare tas abinsu.
"Ina yininku?"
Ta ce a sanyaye da murya me laushi.
Alhaji Baita ji ya yi wani abu ya yi masa zillo ya tsarga masa, kamar tsohon maye haka ya shiga suɗe bakinsa yana washe haƙoransa masu jan goro, nan da nan ya rasa nutsuwarsa sai riƙe wando yake yi.
"Lafiya lumi Iftihal, unguwa za'a ne?" Garbati ya amsa mata yana zungurin Alhaji Baita. Jinjina kai kawai ta yi, shi kuma Alhaji Baita ya karkace yana zaro kuɗi sabbin ƴan dubu dubu har dubu biyar ya ɗauka ya bawa Ifti. "A'a Baba, na gode"
"Ke Iftihal amshi, don ubanki"
Ta ji muryar Daada.
"Daada Innti ta hana mu amsar kuɗi wajan wanda bamu sani ba, babu kyau ta ce" Alhaji Baita ya ce
"Ayya ayyya, ban ji daɗi ba nine ba ki sani ba Alhaji Baita? Abokin mahaifinki ne ni ƴar nan"
"Wallahi ban sanka ba"
Ta faɗa a tsorace, tsawar da Daada ya yi mata ita ce ta saka ta amshi kuɗin tana yin godiya kana ta miƙe ta tafi. Bayan ta shige Garbati ya ce "Daada kaga irin arziƙin da yake tattare da yara mata? Wallahi ko sabon gari ka kai su, ka kama musu shago kaga yadda za'ayi taruruwar tayin su, kamar nama a miya haka Ana da Iftihal za su zama, ka amince da wannan cacar Dada"
Daada ya numfasa yana kallon Alhaji Baita, kafin ya ce "Baita ka tabbatar Miliyan ashirin zaka saka a wannan cacar? Ka tabbata ko?"
"Haba Daada, ba ƙaramin mutum bane ni, kaf unguwar nan waye kullum ake miya da nama a gidansa idan ba ni ba? 20 Millions ne cash" Daada ya shiga lissafin dokin Rano, rayayye da matacce, hango kan shi cikin daula da arziƙi yake, hango yadda zai gina tangameman gida, ya siya mota da abubuwan mure rayuwa, yadda zai ƙara aure ya ajjiye mata har huɗu, ga Tani a gefe biyar cif kenan. "Na amince, na amince"
"Na amince wallahi, da gaske na amince"
"Ka amince dame?"
"Na amince da saka Ayshatul-Iftihal, Ifti a cikin cacar, ina da yaƙinin ni zanci" wani irin shu'umin murmushi Garbati ya yi ya juya ya kalli Alhaji Baita kafin ya ce
"Sai a yi komai a rubuce ai"
Suka ɗakko takadda kowa ya yi rubutu.
"Ni Alhaji Baita na saka Naira miliyan ashirin a wannan cacar, idan Daada ya ci, zan bashi kuɗin, kamar yadda sharuɗan cacar yake"
Shima Daada ya rubuta.
"Ni Daada, na amince da saka ƴata Ayshatul-Iftihal Ifti, a cikin wannan cacar, idan Alhaji Baita ya ci, zan mallaka masa ƴata Iftihal da hannuna"
Aka saka kwanan wata, da saka hannun kowa dana shaidu suka tsayar da ranar da za'ayi wasan kamar yadda aka tsara.
Da saurin daya rage a jikinta ta nufi gidan nasu, kanta a ƙasa tun kafin ta ƙarasa ta hango shi tsaye ya harɗe hannunsa a ƙirji, milk ɗin shadda ce a jikinsa ta haska farar fatarsa ya ɗora zanna bukar a kan shi, sajen gefe da gefen fuskarsa sun yi kwance yana da tsayi da buɗewar ƙirji babu alamar wasa a tattare dashi. Ta durƙusa har ƙasa ta ce
"Yaa Sam, ina yini"
Daga sama har ƙasa yake kallon ta ya yi shiru har sai data sake maimaita kanta. A hankali ya ce
"Lafiya" ya faɗa da ƙyar.
"Bari na faɗawa Ana ka dawo, ƙila bata sani ba....," bata ƙarasa faɗa ba, ta hangu su, su huɗu jere sanye da Jallabiya a jikinsu suna tafe suna rangaji da yarfe hannu zuwa gefe, sai karairaya suke yi kamar babu ƙashi a jikinsu, babban cikinsu ya saka ɗankwalin atamfa wajan ɗaure ƙugunsa dashi ya rataya baƙar jaka a kafaɗa, suna tafe suna hira sai su yi shewa su tafa. Ganin haka ya saka ta yi saurin cewa "Yaa Sam bari na shiga na kira maka ita yanzu yanzu" ta yi saurin shigewa ciki gudun kar su same ta.
Yana ganin sun ƙarasu ya shige gidan dake kusa da gidansu Ana abinsa.
Ana na zaune tana duba ɗinkin da Innti ta yi tana mai yaba rigar wajan faɗin
"Gaskiya ɗinkin nan ya yi kyau Innti, irin shi za ki yi mini da ƙaramar sallah kin ji uwata"
"Allah Ya nuna mana Indo, yasa muna raye"
"Innti ga Baba Bala nan"
Iftifal data shigo ta faɗa a ruɗe, kamar walƙiya haka Babban yaya ya shige ɗakinsu.
"Gafaranku dai"
Suka furta a tare suna shigowa cikin gidan, Ana da Iftihal suka yi saurin komawa waje guda, Innti ta amsa da "Allah yai mana"
Suna shigowa tsakiyar tsakar gida, suka yi shewa "Ahayye... Riiiii" suka game kwankwaso waje guda ana karya kai gefe guda. Hakan ya faru bayan ido biyu da sukai da rigar Maman Innti dake shanye a igiya.
"Yaya ga abar fa"
Ƴar Beauty ya ce yana saka dariya
Ya maƙale hannu a kafaɗa kamar mai shan inna yana tauna cimgam ƙas ƙas. "Sai dana fito naga wannan na tuna ashe tsirara na fito" wanda aka kira da yaya ya faɗi hakan
"Kai Yaya, haka maza suka ƙare miki kallo a hanya ashe?" Cewar Abar ƙauna.
Sukunbiya ya rangwaɗar da kai. "Bari kawai, shi ya sa na jini tantsan tantsan, ba tsiya ba arziƙi ki ce a ɗaiɗaice na fito" ƙas ya faɗa yana bada sauti.
Tiƙa-tiƙan maza ne, wanda akewa laƙabi da ƴan daudu suke maganar a tsakaninsu.
Ita dai Innti ɗinkinta kawai take yi.
Ƴar Beauty ya kalli Sukunbiya ya ce. "Yaushe duniya ta yi tunbuɗi na fitar da sabbin ƙinƙisa a gidan nan Yaya?"
Sukunbiya ya ce
"Ke uwar gane gane, ƴaƴana ne su fa, ɗan yayanka ai ɗanka ne bana son haka"
"Baba Bala ina yini"
"Kinga yini akan ki Ana, ni za ki kalla ki kira da Bala, ina mace ƴar'uwarki ta ina na yi miki suffa da namiji, shi yasa bana son shigowa cikin gidan nan wallahi aikin kawai"
Ana ta tura baki gaba ta ce
"Ai shi ya sa naga nono a ƙirjinka, wallahi mugun duka ne baka ci ba, da sauri zaka dawo asalin namiji ina faɗa maka"
Iftihal ta buɗe baki da mamakin Ana. Innti ta ce "Ana, wacce magana ce haka?"
"Innti ki bari na faɗa masa gaskiya, sai ya dinga yawo yana zubar mana da rigar mutumci, waye zai aure mu idan yaga ƙanin babanmu ɗan daudu ne, ni da nake burin auren kyakkywan miji, kuma kin san kyakkywan maza yawanci masu kuɗi ne"
Innti ta kasa magana.
Ana ta murguɗa baki ta ce
"Wallahi walakiri ba zai maka da kyau ba idan ka mutu a haka, jibgarka za'ayi kamar jaki, ai sai ka auri namiji ƙarshen daudu kenan"
Bala Sukunbiya ya ce "Ni kike faɗawa haka? Kamar a bakin Daada wallahi, sai na ja miki masifa za ki san kin yi da watsastse"
Caraf Ana ta ce "Kaga watsewa a kan ka, da kai da Daada duk ku kaga duhu, wlh sai na yi addu'a in sha Allah nono ya fito maka har ciki, wai Sukunbiya?" Sai ta sheƙe da dariya
"Mahaɗita yau miyarmu da Sukunbiya za'ayi" takaici ya kama Sukunbiya.
Sai ya yi ƙwafa kawai.
"Daɗin ciwo nishi, inda me maka sannu"
Inji Ƴar Beauty.
Caraf Abar ƙauna ya amshe da faɗin.
"Ni dai ki yi sauri yaya, ina da aikin suyar waina zani yinin suna kuma, kar a yi mini asarar haɗuwa da ƙawayena masu capacity"
"Heeee riii" suka sake saka shewa da haɗe kwankwaso waje guda abinsu.
Sukunbiya ya ce "Daman kuɗin adashi na kawo gashi, ina neman alfarma a bani zubi na gaba, saboda bikin ƴar aminiyata za'a yi"
Ya ranƙwafar da hannu wajan miƙa mata kuɗin, ganin Innti bata amsa ya dire kuɗin ya ce "Na rasa ta cewa, wai uwar gulma ta yi cikin shege, sai aron rigar mamakin za ki bani zani suna yau, naga size ɗinmu ɗaya dake matar Daada, kema dai tubarakallah"
Abar ƙauna ya riƙe zancen da faɗin.
"Kallabi tubani, wai anwa uwar kwarto fyaɗe ya ce mama riƙe mini wando ina zuwa"
"Riiiii!" Suka sake yin shewa.
"Ya naga kina mini kallon hadarin kaji, abin fa duk the same me, wai Ali ya ga Ali"
Cewar Sukunbiya.
Innti ta ce "Bala ka yi haƙuri, bana bada kayan sawata, kar ka sake mini haka"
Ya riƙe haɓa ya ce "Oh ni Sukunbiya abin zubawa a miya, ina ruwan gayyar tsiya arna a idi abin arziƙi bai amshe ni ba ni dai kam"
Ƴar Beauty ya ce.
"Yaya muje don Allah, na ji kamar al'adata ce take bin ƙafafuwana, muje muje ni"
Suka rankaya tare da ficewa suna sakarwa Innti habaice-habaice ita dai bata kula su ba. "Mahaɗita Yaa Sam ya dawo fa"
"Me ƙarya?"
"Ɗan aljanna, yana waje ma"
Cikin sauri ta zura hijab ɗinta, rabon data fita waje har ta manta makaranta ke fitar da ita, kuma kwana biyu bata je kwata-kwata.
Sanda ta fita bata same shi a waje ba, sai ta shiga gidansu ta tarar da Mama zaune tana suya gyaɗa ta ce "Barka da yamma mama?"
Mama na dariya ta ce "Ana manya, muddin naga ƙafafuwanki a gidan nan mutuminki ne ya dawo, yanzu ya fita yana shagonsu na waje ai" murmushin kawai Ana ta yi ta nufi waje, a bakin shagon ta tsaya tana bubbugawa, yana jinta bai amsa ba, ta gaji ta bugawa ta leƙa sai taka ya miƙe tsaye yana gyara rigarsa ya fito.
"Yaushe ka dawo?"
Ya dube ta tsam ta grey eyes ɗinsa ya sake yin fresh fuskarsa na ɗaukan ido sai ya ce "ban sani ba"
"Au sorry faɗa muka yi ne? Naga ka yi fari ko bilitin ɗin ka fara ne, ina yini ya hanya?" Bakinta kawai yake kallo.
Ƙafarta ya kalla yaga takalminta ya lalace sosai kafin ya ce " kin rame"
Kamar me jira ta shawagaɓe masa fuska blue eyes ɗinta ta juya ta ce "To ba kai bane"
"Ni?" Ya nuna kan shi da yatsa.
"Baka sake kirana a wayar Yaa Jaheed na duk na damu"
A kasalance ya ce "Ban niyya ba"
Sai ta fara yarfe hannunta tana shirin yi masa kuka abin da ba ɗabi'arta ba, ya tsuke kyakkyawar fuskarsa ya ce "Kar ki mini banso" sai ta yi ƙasa da kanta kawai.
"How many times zan ce ban son shawagaɓar nan Nanaah?"
Ita dai ba ta yi magana ba, ya ce
"Muje"
Ta ce "Ina?"
"Siyar dake"
***
A gurguje Gana ta shige cikin bukkarta tana sakin assabari, ajjiyar zuciya ta sauke kafin ta sunkuya ƙasan ƙaramin gadonta ta janyo wani kasko ta fito da baƙin ƙyalle a hankali ta kuntu gefen zaninta ta ciro ƴar tsokar kurwar jaririn ta ɗaure da baƙin ƙyallen, sai kuma ta saka a cikin kaskon ta zura cikin wata kwarya ta rufe. Wani kwano ta ɗakko me ɗauke da mai fal ciki, ta saka yatsa ta lashi man a bakinta tana jin garɗi da daɗin man na ratsa cikin kunnuwanta saboda daɗi
"Allah ka sake haɗani da mai maiƙo a jiki kamar Hansai, wayyo daɗi wayyo daɗi"
Ta sake laso man ta kai bakinta.
"Kamar na sayarwa da Alhaji kurwar nan, kamar na yi watanda a kanta" ta fara tunani.
Sai kuma ta ɓata fuska sosai
"Ina son kuɗin kuma"
Can ta yi tsaki ta ce "Ina son jaririn ma"
***
A bakin shagon Ana ta tsaya Yana Sam kuma na can gefe yana yin waya hannunsa cikin alijuhu yana daga inda yake yana hangota. Ita bata saba tsayuwar shagon katin nan ba, gashi ko ta kira sunan Jaheed ba ji zai ba. A cikin cunkoson wajan ta ji an zura hannu ana shafo ta, sai ta yi banza ta sake jin an shafo bayanta cikin sauri ta juya idanunta na rinewa ta kalli yaron ta ce "Ajjiyar me ka yi a jikina da kake shafani, ɗan iska ne kai? Uban me kake nema?"
Gabaɗaya mutanen wajan suka juyo suna kallon Ana, kamar basu taɓa ganin mace ba sai a kanta musamman yadda take juya manyan idanun nan nata, sai ya ce
"Ni za ki wa sharri?"
Tai wani irin luu da idanunta kamar za ta yi bacci ta buɗe su akan shi, fuskarta ta haɗe ta watsa kamilallun idanunta akan shi.
"Ashe ban ji sanda kake taɓa ni ba"
Ta sake faɗa kamar bata son magana.
Wani ya ce "Ke yarinyar nan me zai taɓa a jikin naki, ko dai ba ki ji dai-dai bane?"
"Me namiji yake taɓawa a jikin mace?"
Caraf yaron ya ce "Sharri ma take yi mini"
Wani irin haske ne ya bayyana a idanun Ana ya sauka akan yaron jikinta har wani irin rawa yake yi ta ce "Ban taɓa yi wa wani sharri ba, ban yafe ba ɗan iska kawai, in sha Allah sai kaga abin da zai same ka"
Wani irin ɗaci take ji a maƙoshinta, ta tsani a ƙaryatata, ta sani a nemi cin zarafinta, gata da wata baƙar zuciya da riƙe abu a rai
"Kake cewa na maka sharri?"
Ta runtse idanunta, ta sake ware idanun wannan hasken me kama da magic ya sake sauka akan yaron "Zaka gani"
Ganin abin na neman zama rigima aka ce yaron ya tafi zuwa wani kantin, ita kuma ta cije a wajan jikinta sai kakkarwa yake yi.
Yaron na ƙoƙarin juyawa kawai ya faɗi a wajan yana murɗewa idanunsa suka kakkafe, cikin sauri ta kalli yaron domin itama ta tsorata sosai sai ta juya caraf wani ya riƙe hannunta ya ce "Mayya ina za ki bayan ki kama yaron mutane shine za ki gudu?" Da rashin fahimta Ana take kallon cikin idanun mutumin ranta ya sake ɓaci ta rasa abin cewa, da alama yau bata da sa'a. Wani ya ce "Daman ta ce zai gani"
"Kuma zai ga abin da zai same shi" in ji wani.
Mutumin ya ce "Bidiri kashin rana da kiɗa, gashin nan tun ba'a yi nisa ba ta kame shi"
Nan da nan wajan ya cika ana faɗin.
"Mayya ce Mayya ce"
Mene kuma mayya? Wani abu ne hakan da bata san dashi ba har ake jifanta dashi?
Gabaɗaya sai ta rasa fahimta ta zama confused lokaci guda, ta haɗiye wani abu mai ciwo a ƙirji taƙi barin ruwan daya taru a cikin idanunta zuba, wanda ya sake sawa idanun nata suka sake zama manya.
"Ni ba mayya bace, me na yi masa?"
"Ai wallahi babu inda za ki sai kin tsallaka shi" cewar yayan yaron daya ƙarasu.
Jaheed bai san meke faruwa ba, domin ko da wasa bai taɓa tunanin Ana zata fito ba, balle har ta ƙarasu kantin nasu.
"Kul, kurwata kur ina faɗa miki" mutumin ya sake furtawa yana jefa wa Ana harara
"Idan kun su ko kashe ni, babu wanda ya isa na tsallaka yaron nan, ku kuka san wata mayya kamar wani man shafawa aikin banza" sannu a hankali Yaa Sam ya ƙarasu wajan saboda hayaniyar da ta yi yawa, kuma ya hango Ana a tsakiyar mutanen, ya dubi mutanen kaf ya kalli Ana sai ya ce "Menene?" Cikin rawar murya ta ce
"Wai ni ce Mayya zai na tsallaka yaron nan"
"Mayya?" Yaa Sam ya nanata sunan a ƙasan ranshi. Sai ya kalli mutanen wajan ya ce
"Kun yi kuskuren fahimta, ba ita bace"
Yayan yaron ya ce
"Wallahi sai ta tsallaka ƙanina sau uku, ko mu ƙone ta da taya a wajan nan a rage iri, wato a bari ta tafi gida, idan yaso ta cinye shi a can ko?" Ana ta kalle shi sosai.
"Idan baka ƙona ni baka cika ɗan halak ba"
Yaa Sam kallon ta ya dinga yi
Daman ana cin mutum ne?
Ganin al'amarin ya zama babba ya saka Yaa Sam sassauta murya yana kallon Ana
Ya ce
"Tsallaka shi, ki goge shakkun ransu"
Sai a lokacin ne ruwan idanunta ya yi kamar zai sauka da sauri ta haɗiye hawayen ta ce
"Kaima kallon mayyar kake mini? Wallahi tallahi sai dai su kashe ni amma ba zan taɓa tsallaka shi ba....
A yi hutun ƙarshen mako lafiya. Mu haɗu daku ranar Monday in sha Allah. Ga mai son cigaba daga kan chapter 4 zuwa 10 akwai A ArewaPen. Ka yi searching sunan littafin zai fito In sha Allah. Idan baka da application na ArewaPen ka shiga ta chrome ka yi searching website. ArewaPen.com sai ka yi login ko register.
For more information about the book contact us via WhatsApp. 08082101373 08164069385