Kenza eBookz
Cover art for KOMAI YA YI FARKO  HAUSA NOVEL 8

Post

KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 8

.....r." Inara went and knocked on the bathroom door. "Why are you knocking on my door?" Inaya said in a fight. "I'm not going to follow you and let's be stupid, it's because Yayane wants to talk." Hunaif smiled at their drama. They fight more than ten times a day, but if you look at them, you'll think they'll never fight. She quickly took her phone out of Umar's hand and said, "Hello, I miss you, when will you come back?" Hunaif left the room with the phone in his ear and went to the kitchen to look for something to eat. the second time, as if he was about to change his mind, he put the phone on his ear and said, "Hello, where are you?" He wanted to raise his voice, but he said directly.

Standalone post1,992 words

https://chat.whatsapp.com/CGm8zTMQDDO1e9sf3BmDKQ?mode=hqctcla

KOMAI YA YI FARKO

PAGE 8

Hunaif na sauka a apartment ɗinsa dake Rio de Janeiro ya fara shiga waka, da warm water ya wanke jikinsa tass yana jin gajiyar da ya debo na raguwa, yana fita daga bathroom ɗin ya goge jikinsa tsaf, ba tare da ya tsaya shafe-shafe ba ya shiga closet ya ciro boxers da daguwar wando, wandon ya saka, ya feffesa body spray kawai sai ya hau gado, lumshe ido ya yi yana wani jin kewar gida, a haka bacci ya ɗauke shi.

Baccin two hours ya yi, yana farkawa ya shiga bathroom ya yi alaula, a ɗakin ya shimfiɗa darduma ya yi sallah, bayan ya iddar da sallah sai ya ɗauki wayarsa ya kira Inaya, tana bathroom lokacin da kiran shi ya shigo, Inara dake kwance ta janyo wayar, tana ganin mai kiran ta tashi daga kwancen da take ta yi picking ɗin call ɗin, "Hello Yaya ka kai isa lafiya?" Inara ta faɗa farin ciki fal muryarta.

Murmushi Hunaif ya yi, yace; "Lafiya ƙalau my darling Inara, ina masoyiyata?"

"Bari na ba ta wayar."

Inara ta tafi ta kwankwasa ƙofar bathroom. "Wai me hakane za ki zo kina ƙwanƙwasa min ƙofa?" Inaya ta faɗa cikin faɗa

"Ni kam ba zan bi ki mu yi rashin hankali ba, daman Yayane ke son ya yi magana dake."

Hunaif kam sai murmushin dramar su yake, a rana sai su yi faɗa fin sau goma, amma kallo ɗaya idan ka yi musu zaka ɗauka ba za su taɓa yin faɗa ba. Inaya ba ta gama uzurinta ba, amma ta tare ruwa ta tsarkake jikinta ta fito da sauri, fisge wayarta ta yi daga hannun Umar, ta saka a kunne tace; "Hello Yaya, I miss you, yaushe za ka dawo?"

Hunaif ya fita daga ɗakin ɗauke da wayar a kunne da yana hira da su Inaya, ya nufi kitchen don neman abinda zai ci.

Bayan kwana biyar da tafiyar Hunaif, yana kwance a cushion na falonsa yana kallon wani match wayarsa dake gefe ya ɗau tsuwa, ɗaukar wayar ya yi, ya duba ya gan new number ne, sai ya ajiye wayar kawai, aka sake kira for the second time, kamar zai ignoring sai ya canza ra'ayi ya ɗauki wayar da har kiran ta kusa katsewa, yana saka wayar a kunne ya ji an ce; "Hello Yaya, ina wuni, ya hanya?"

Shiru ya yi, yana son ya ɗago mai Muryar, amma ya kasa, sai ya ce; "Who's it." Kai tsaye.

"Zee ce, Ƙawar Intisar da ka kai su shopping a week back." Aka faɗa daga cikin wayar.

Hunaif ya ce "Ok."

Zainab dake expecting yace more than ok, sai ta ɗan yi shiru ta ji ko zai tambaye ya take da su Mama. Ganin shirun ya yi yawa, sai tace; "Mun tafi gidanku ɗazu, shine Mommy ta ce ka koma Brazil that's why I called na yi maka ya hanya."

Hunaif da hankalinsa ke TV yace; "Nagode."

"Ok bye-bye, my mom is calling me."

Hunaif ya riga ta katse kiran, ya mayar da full attention ɗinsa kan match da yake kallo.

_____________

Washegarin ranar da su Humaira suka tafi kasuwa, da sassafe suka ji ana buga musu ƙofar gida, Lawal da kan shi ya tafi ya buɗe ƙofar, da mamaki ya kalle Alhaji Sani dake tsaye ɗauke da leda a hannunsa, Alhaji Sani ya miƙa masa hannu yana faɗin; "Assalamualaikum Malam Lawal." Lawal ya miƙa masa hannu shima suka yi musabaha, yana mamakin me ya kawo Alhaji Sani ƙofar gidan shi da sassafe. Alhaji Sani ya yi gyaran murya, yace; "Juya na tarar da matarka da wata ƴar budurwa a hanyar kasuwa, budurwar ba ta da lafiya sosai, shine na gan dacewar na zo na yi mata ya jiki kafin na wuce wajen aiki."

Lawal da Kausar ta riga da ta faɗa masa taimakon da Alhaji Sani ya yi mu su juya, kawai dai bai yi tunanin mutum kamar Alhaji Sani zai damu har ya zo dubiya ba shine ya ba shi mamaki, sai ya ce; "Allah sarki, jiki kam da sauƙi, shigo, shigo daga ciki ku gaisa."

Alhaji Sani ya bi bayan Lawal zuwa cikin gidan, a ƴar falonsu da suka decorating ɗinsa da set ɗin cushion dai-dai ƙarfinsu, da ƴar ƙaramar TV ya ba wa Alhaji Sani wajen zama, sannan ya shiga ɗakin Kausar, ya ce Humaira ta fito an zo gaisheta. Hijabin Ya Kausar dake rataye a ƙofa Humaira ta saka ta bi bayan Mallam Lawal tana tunanin waye ya zo gaisheta. Tana shiga falon idonta ya sauka akan mutumin da ya taimaketa jiya, a ƙasa ta zauna, kanta na ƙasa ta gaishe shi. Alhaji Sani yace; "Masha Allah, jiki ya yi sauƙi, Allah ya ƙara lafiya."

"Aameen." Humaira ta amsa a hankali.

Alhaji Sani ya miƙe, ya ajiye ledar hannunsa, yace; "Ga wannan babu yawa." Sannan ya nufi ƙofa, bai ma tsaya jin godiyar da Humaira ta yi ba, Mallam Lawal ya bi bayansa, ya ƙara yi masa godiya.

Da yamma Humaira na ɗebo ruwa a borehole ɗin gidan Alhaji Sani, ta ji horn na mota, ko da ta juyi ba za ta iya tantance wa ke cikin motar Ba saboda tinted glass ne a motar, juyowa tayi abinta ta kashe ruwan don robarta ta cika ko, tana ɗan waige-waigen duba wanda zai ɗora mata ruwan a kai, ta ji Maigadi na buɗe gate, motar da aka yi horn sau ɗayan nan ya shiga gidan. "Masu kuɗi na sha'aninsu, gate ɗin ne sai an buɗe musu" ta faɗa a zuciyarta. Wani Almajiri zai wuce, ta kira shi ya aza mata ruwan.

Alhaji Sani kuwa a nashi ɓangaren, da ya yi horn Humaira ta juyo, sai ya ƙura mata ido ba tare da ta san yana yi ba, a zuciyarsa yake faɗin; "Allah ya yi halitta a nan." Buɗe masa gate da maigadi ya yi ne ya dawo da shi daga duniyar kallon da yake mata, ya ja motarsa ya shiga ciki.

Tunda Alhaji Sani ya fahimci Humaira na zuwa ɗebo ruwa a borehole ɗin gidansa da yamma, ya mayar da lokacin, lokacin dawowarsa daga aiki, idan ya shige cikin gida kuma, sai ya haura sama zuwa dakinsa, ya tsaya daga bakin window ya rinƙa kallonta har sai ta gama ɗeba ruwanta kafin ya bar bakin windown.

Yau yana karya kwanar gidansa ya hango Humaira tana zuwa da bokiti a hannunta, ɗan kallon anguwar ya yi, ya gan ko ina silent, babu sahun mutane, parking ya yi ba tare da ya yi horn ba, ya buɗe ƙofa ya fito.

"Ƴan mata." Ya furta da ya ƙaraso bayanta, a firgice Humaira ta juyo jin magana a bayanta, da mamaki ta kalle Alhaji Sani, shi kuwa murmushi ya yi mata, yace; "Ko dai matar aure ce?"

Girgiza kai ta yi, ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

"Ina da magana dake, yaushe za ki ba ni dama na zo gidanku mu tattauna?"

Ɗago dara-daran idanunta ta yi, tace; "Allah ya sa ba laifi na yi ba?"

Murmushi ya yi, yace; "Ba ki yi laifi ba, wata magana mai muhimmanci nake son mu yi."

"Idan zai yiwu, ka faɗawa mijin Yayata ko menene, shi zai sanar da ni."

Alhaji Sani ya yi murmushi, yace"Ok, hakan ma zai fi sauƙi."

Humaira na kallonsa ya koma ya shiga motarsa, ya danna horn, Maigadi ya buɗe masa ya shiga, ta rinƙa mamakin dama nan ne gidansa.

Da daddare bayan sallar Isha tana kwance a cinyar Ya Kausar suna hira, Mallam Lawal ya yi sallama ya shigo, bayan Humaira ta gaishe shi ta miƙe za ta fita, sai ya katse mata hanzarin ta, yace; "Wajen ki ai na zo ƴan mata." Humaira ta ce; "Ƴan mata kuma Yaya?"

Lawal yace"Eh mana."

Komawa Humaira ta yi ta zauna, ɗakin ya ɗauki shiru, sai Kausar tace; "Mu na jin ka." Harararta Lawal ya yi, sai ya mayar da dubansa ga Humaira, yace; "Alhaji Sani met me akan ki, ya ce ke kika turo shi wajena, hakane?"

Kai Humaira ta gyaɗa mishi, ta ce; "Eh haka ne."

"Toh ya zo min da batun yana sonki, kuma bayan na yi waya da Yayanki Kabir, na bashi daman ya rinƙa zuwa hira wajen ki ko za ku daidaita."

Wani irin faduwar gaba Humaira ta ji lokaci guda, soyayya? Duka-duka yaushe ta gama warkewa daga raɗaɗin abinda wanda take kira da masoyi ya yi mata? Wai don an gan tana farinciki da walwala ana tunanin ta manta duk abinda ya faru a rayuwarta ne? She's only trying to move on with her life, ba soyayya bane a gabanta yanzu, karatu take son ta yi, ta zama babba a ƙasar nan ta yadda za ta rinƙa kwatarwa wanda aka zalunta ƴanci, don haka Mallam Lawal bai ma zo da maganar da za ta iya dauka ba, wannan shine abubuwan da suka fara yawo a zuciyarta.

__________

Tun daga ranar da Zee ta samu lambar wayar Hunaif, ta saka shi a gaba da kira duk bayan kwana bibbiyu, daga tace ta kira ta gaishe shi ne, sai tace ta kira ta ji lafiyarsa, and so on, tun Hunaif na tsaki idan ya gan kiranta, har ta kai da idan bai gan kiranta a lokacin da ta saba kira ba ya rinƙa duba wayarsa kenan, a hankali wani irin sabo ya shiga tsakaninsu, idan ma ba ta kira shi ba, shi zai kirata, har ta kai da every blessed day sai sun yi waya. Shi zuciya daman tana son mutum mai nuna mata kulawa, hakan ya saka Hunaif ya fara son Zee ba tare da ya fahimci hakan ba. Yana kwance akan gado, bacci yake ji amma ya kasa yin baccin yana jiran kiran Zee, ya kirata ya fi sau uku amma lambarta ba ya shiga, tun yana jiran kiranta har ya fara gyangaɗi sai ya ji ringing ɗin wayarsa, ɗaga wayar ya yi, ya saka a kunnens, bacci fal idonsa, murya ƙasa-ƙasa yace; "Assalamualaikum Zee."

"Na'am Yaya, shine ko ka neme ni ko" Zee ta amsa itama muryarta ƙasa-ƙasa.

Gyara kwanciyarsa ya yi, yace; "I called har sau uku, amma lambarki ba ta shiga."

"Na kai wayar caji ne, ba mu da wuta."

Hunaif ya ce; "I will send you money a installing muku solar, saboda wannan rashin wutar naku yana damuna."

Zainab ta ɗan yi murmushi, tace; "Solar kuma Yaya, sai in cewa Baban mu na samu kuɗi a ina?"

Ɗan dafa goshinsa Hunaif ya yi, yace; "Zan kira Intisar sai mu san yadda za a yi."

"Ba damuwa Yaya, how was today's match?"

"Alhamdulillah, mun yi nasara, but I sustained a minor injury." Hunaif ya furta a hankali.

"Subhanallah!" Zee ta faɗa sounding very worried, tace; "Ya jikin? A ina ka ji ciwon?"

"Taka Ni aka yi a cinya, an yi mini massaging but I'm still feeling slight pains, but idan na ɗan huta zan kira a ƙara massaging wajen sai na shafa man zafi, the pain will subside In Sha Allah."

Zee ta zumɓoro baki kamar yana kallonta, tace; "Kuma mace ce za ta yi maka massage ɗin ko?"

Murmushi Hunaif ya yi, yace; "Is that jealousy?"

"Jealous for what?" Zee ta tambaya tana wani zaro ido.

"Kar dai ni kaɗai nake son ki?" Hunaif ya tambaya.

Wani sanyi kalamar Hunaif suka sanya a zuciyar Zee, yau tana jin kamar she's the luckiest person on earth,ba ta taɓa tunanin za ta iya samun soyayyar Hunaif easily haka ba. Hunaif ya kuma ce; "Ba ki ce komai ba Zee." Zee ta yi wani juyi akan gado, ta kwantar da murya tace; "Yaya kunyarka nake ji."

Murmushi Hunaif ya yi, yace; "Iya kunyar ne ko harda soyayya?"

Murmushi Zee ta yi, tace; "Har da soyayyar, amma kaɗan"

"Ba damuwa, ko cikin cokali ne Alhamdulillah."

Hira sosai su Hunaif suka yi kafin suka yi sallama. In less than ten minutes da katse kiran bacci ya ɗauke Hunaif saboda gajiyar da yake ji da kuma baccin da ya cika idanunshi.

GA HUMAIRA GA ALHAJI SANI.

GA HUNAIF GA ZEE.

#Jikargaraba 07048694211