Kenza eBookz
Cover art for FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 22

Post

FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 22

..... she looked at Ibrahim. "What!!?" Ibrahim lowered his eyes, "Listen..." "No, be quiet, because silence suits you" Zahra interrupted him, her voice shaking. O Umar folded his leg and leaned on the body of the car, looking at the power of God. The woman opened her eyes. She looked at him, "Wait... do you have a wife?" Abraham felt as if the earth had opened and he entered. But instead of being calm... He started to get angry and embarrassed, because of the way people look at them "Zahra!" He raised his voice and said to him "Don't stop yelling at people in the street! Is it your bad behavior that you want to display here?" A frustrated laugh escaped her and she said, "Shout? Bad behavior?" "Yes, I said," He pointed to "Look at how you gathered people!" "Am I gathering people? Or is your injustice gathering people?" "Yes! You are gathering people!" He began to speak in pain. "You are standing and insulting people outside!" O Umar, who didn't say anything at first, said, "You hit me since you have a heart." The woman looked at Ibrahim in surprise. He pointed to Zahra, "Since she got out of the car, she didn't give me a chance to speak, except what she was saying." Zahra felt tears

Standalone post1,474 words

Chapter 22

Kallon kallo suka shiga yiwa juna, Matar ma kallonta take yi daga sama har ƙasa Na wasu daƙiƙu babu wanda ya ce komai.

Sai dai yanayin wajen ya canza gaba ɗaya

Ibrahim ya ji gabansa ya faɗi. “Zahra…” Ya kira sunanta cikin kashedi.

Amma ko kallonsa bata yi ba Ta ci gaba da kallon matar.

“Wacece ke?” Ta faɗa cikin ɓacin rai

Matar ta ɗan haɗe gira “Excuse me? Har kin isa kimin wannan tambayar?”

“Wacece ke?” Zahra ta kuma tambayarta cikin ɓacin rai

Matar ta ɗan taɓe baki ta ce “Da alama kin san wanda nake tare da shi ai.”

Wani irin dariya Zahra tayi ta ce “Eh na sani. Shi yasa nake tambayarki”

Ibrahim ya fito daga motar da sauri. “Enough Zahra”

Ta juya da sauri ta kalle shi, nan take Idanunta suka canza “Enough…? Zaka ce….?

Ta maimaita “Ni zaka ce wa enough?”

Mutane suka fara fitowa a balconies da bakin gate saboda hayaniyar.

Matar ta kalli Ibrahim. “Who’s she?”

Gagara magana yayi, Zahra tayi folding hannayenta ta matsa jikin kofar ta ce

“Matarsa.”

Nan take matar ta juya da sauri ta kalli Ibrahim. “What!!?”

Ibrahim ya runtse ido “Listen…”

“A’a ka yi shiru, saboda shirun ne ya kamace ka” Zahra ta katse shi, muryarta har tana rawa.

Ya Umar ya nade kafarsa ya jingina jikin motar yana kallon ikon Allah

Matar ta zaro ido Tana kallonsa “Wait… kana da mata?”

Ibrahim ya ji kamar ƙasa ta buɗe ya shige shi.

Sai dai maimakon ya natsu… Fushi ne ya fara hawa kansa da borin kunya, Saboda yadda mutane ke kallonsu

“Zahra!” ya ɗaga murya

Wani banzan take masa

“Kar ki tsaya kina yi wa mutane ihu a titi! Ko banzan halin naki ne kike son displaying anan?”

Wata dariyar takaici ta kufce mata ta ce

“Ihu? Banzan hali?”

“Eh ihu na faɗa” Ya nuna wajen

“Duba yadda kika tara mutane!”

“Ni na tara mutane? Ko kuma rashin adalcin ka ya tara mutane?”

“Eh! Ke kika tara mutane!” Ya fara magana cikin zafi.

“Kina tsaye kina yi wa mutane rashin kunya a waje!”

Ya Umar da tun farko bai ce komai ba yace “Ka bugeta toh tunda Kaga mai zuciya”

Matar ta kalli Ibrahim cikin mamaki “Rashin kunya kace take maka?”

Ya nuna Zahra “Tun da ta fito daga mota bata bani damar magana ba sai abun data ga dama take fada”

Zahra ta ji hawaye sun cika idanunta, ko karin mayarwa ta fara, sosai Ibrahim ya bata mamaki sai kawai ta tsaya tana kallonsa

Ibrahim ya cigaba “Kuma ai baki da right ɗin da zaki tsaya kina tuhumata!” Ya faɗa cikin fushi

Zahra ta zuba masa ido. “Bani da right?”

“Eh!” Ya faɗa da karfi

“Kina fita yadda ranki yake so! Kullum kina gidanku! Kullum kina can! Kullum wani ƙato ke kawo ki gida”

Matar kuwa… Sai kawai ta fashe da dariya harda tafe hannu ta riƙe cikinta.

“Wow!” Ta ce, ta kalli Ibrahim.

“Seriously?” Ta nuna Zahra.

“Wannan matar taka ce?”

Ibrahim ya haɗe gira, matar ta sake dariya.

“Wallahi ka bani mamaki.” Ta girgiza kai.

“Wai kana da mata irin wannan sannan kana yawo kana neman mata? Me anfanin boyewar cewa kana da mata? Lemme tell you bana son makaryaci hakan na nunawa kayi disqualifying kan ka”

Yanzu kam fuskar Ibrahim ta canza.

Matar ta cigaba “Ka dube ta mana.”

Ta nuna Zahra.

“Innocent, Beautiful, classy, respectful.”

Sai ta yi masa kallon raini “Yadda ka mata Nima haka zaka min ko da na shigo Ibrahim, dan haka kazo ka karbi kayanka na gidan mu”

Wannan maganar ta dake shi sosai

Jin furucinta yasa Zahra ta fara ganin bibbiyu, Ya Umar ya karaso wajenta ganin yadda Zahra ta tsaya kamar mutum-mutumi

Hawaye kawai ke zuba a fusakanta, Ya Umar ya ji zuciyarsa Tana tafasa

Kai tsaye ya kama hannunta “Mu tafi.”

Zahra bata motsa ba, har sannan idanunta na kan Ibrahim

Ya Umar ya sake matse hannunta “Zahra.”

Still bata amsa ba

Kamar ma bata jin me yake cewa

Ya Umar ya Kama fuskanta “Kanwata.”

Sai a lokacin ta ɗan kalle shi.Idanunta sun yi ja.

Ya Umar ya girgiza kai

“Mu shiga ciki.”

Sai hawaye suka fara zubowa kamar an kunna pampo

Ba tare da ta ce komai ba Ya Umar ya jata a hankali

Kawai binsa take yi Kamar an cire mata lakka

Yayin da suka shiga cikin gidan ne, matar ta sake kallon Ibrahim.

Ta girgiza kai cikin takaici.

“Wallahi ka ci sa’a da ka samu irin wannan matar, idan nice abun da tayi sai na ninkasa sau duba” Sai ta shiga motarta ta rufe ƙofa, taja motar da gudu ta bar layin

Ibrahim kuwa ya tsaya kamar Wawa…..

Ya Umar na duƙe a ƙasa gabanta, yayin da ita ke zaune kan kujera tana kuka kamar zuciyarta zata fito

Da farko yana ƙoƙarin lallashinta ne da magana, amma da ya ga kukan nata na ƙaruwa maimakon ya ragu, sai ya ji zuciyarsa ta kasa ɗauka

Hawayen da take yi ba irin na fushi bane, kukan ciwo ne

Ya Umar ya sauke numfashi mai nauyi, sai ya miƙe tsaye ya zauna kusa da ita. Kafin ya janyo ta jikinsa

Nan take Zahra ta sake fashewa da kuka, ta rike rigarsa tana kuka kamar ƙaramar yarinya

Ya Umar ya lumshe idanunsa, da ƙyar yake danne kansa, a ankali ya fara bubbuga bayanta

“Shhh… Ya isa haka.”

“Wallahi Yaya…” ta ce muryarta na rawa

“Sai ya dinga cewa bai da mata? Ni fah?”

Ya Umar ya runtse idanunsa, wannan kalmar ce ma ta fi masa ciwo. Ba wai dan Ibrahim ya kula wata mace bane

Abin da ya fusata shi shi ne yadda ya tsaya a gaban wata mace yana nuna Zahra kamar rayuwarta ba komai ba ce, valueless, Kamar ba ita ce matarsa ba

A hankali ya sake bubbuga bayanta ya ce “Kalle ni”

Da ƙyar ta ɗago kanta daga kafaɗarsa, Fuskarta cike da hawaye, Idanunta sun yi ja

Ya Umar ya ji tausayinta ya ƙara cika zuciyarsa

“Kina ji ni da kyau?”

Kai ta gyada masa.

“Zahra kina da gatanki, bai isa ya sa wannan gatan naki ya gushe ba”

Sabbin hawaye suka zubo mata.

“Ko Yau kika dawo gida sai ma sabbin gata da zaki gani, infact kin fisa gata ta ko wani angel ma”

Sai ya share mata hawayen fuskarta

“Kin yi fiye da abin da ya kamata mace tayi, kinyi hakuri tun ba Yau ba nasani. Kin yi ƙoƙarin gyara abubuwa”

Sai ya girgiza kai

“Saboda haka kar ki zauna kina zargin kanki, shine kawai ba nagari ba”

Zahra ta sauke numfashi tana ƙoƙarin tsayar da kukanta

Ya Umar ya ci gaba da magana cikin tausasawa

“Kuma dan Allah…” Ya dafa kanta

“Saboda cikin jikinki, Saboda lafiyarki, Ki kwantar da hankalinki”

“Kar ki bari wannan damuwar ta cutar da ke” Sai ya ɗan yi murmushi mai ciwo

“Idan ba saboda kanki ba, toh saboda jaririn da ke cikinki” Zahra ta lumshe idanunta, a hankali kukan nata ya fara raguwa

Ya Umar ya ce,

“Na yi miki alkawari.” Ta ɗago ta kalle shi.

“Zan ɗauki mataki”

“Amma ba yanzu ba har sai kin gama gama defense. Yanzu abin da nake so shi ne ki huta, kin ji ni?”

Da ƙyar ta gyada kai. Ya sake tambaya.

“Kin ji ni?”

“Eh Yaya.”

“Good.”

Sai ya miƙe tsaye Zahra ma ta share fuskarta

“Yaya…”

“Naam?”

“Ina so na kwanta”

Ya Umar ya gyada kai.

“Hakan ma ya fi” Sai ya tsaya yana kallonta

“Amma ki yi min alkawari.”

Ta kalleshi

“Kar ki kwanta kina kuka, kar ki zauna kina tunanin ki hana kan ki bacci”

Zahra ta gyada kai a hankali.

“In Sha Allah, Nagode Yaya”

Ya Umar ya san ba ta cikin yanayin da zata iya magana sosai, har mamakin dauriyarta take yi

Saboda haka bai ƙara mata wata magana ba, ya raka ta har bakin staircase. Yana kallonta har ta haura sama

Har ta ɓace daga ganinsa Sai a lokacin ya sauke wani dogon numfashi Tausayinta fal a ransa

Bayan ya tabbatar ta shiga ɗaki, Ya Umar ya fito waje

A can gefen gate ya hango motar Zahran, ya girgiza kai

A hankali ya nufi motar, ya buɗe ƙofar driver’s seat ya shiga

Na ɗan lokaci ya jingina da kujera yana tunanin abin da ya faru

Sai kuma ya tada motar, a hankali ya juyata ya shiga da ita cikin compound

Ya yi parking ɗinta a inda aka saba ajiye motocin gidan, ya kashe motar ɗin, ya zarekey ɗin ya fito

Da ya rufe ƙofar motar, ya ɗaga kai ya kalli saman gidan, Inda ya san dakin Zahra, maybe tana kwance tana kuka

Wani irin fushi ya sake cika masa zuciya, amma ya haɗiye shi

Saboda yanzu…

Abin da ya fi muhimmanci a wajensa shi ne lafiyar kanwarsa.

Kar na barku sakayau ne shine na sakuro Wanda nayi editing, ban wuni gida bane Yau afuwan