
Post
HIYAAM HAUSA NOVEL PAGE 3
...., what about the alcohol you drank? How can I do it, Daada, where can I do it?" "In the way Tani is to me" The answer did not confirm to her that it was a conversation of the heart that was clear, she knew that it was bothering her on her right fingers, but the pain that she feels in her heart every day, always your weakness that finds her trunk, is a long time, it is not new to her, what about her children? She hears. Her five children! from hearing the sound of the four voices that were rising, calling her 'Innti', she would have done that, but she was not lucky enough to fail. "Happiness".
*H I Y A A M*
Page 3 Bright pens
Yota/001
Stay blessing as always; Nazeefah Sabo Nashe
A gigice Innti ta miƙe tsaye ganin yana shirin yi mata tsirara a tsakar gidan, cikin tashin hankali da kiɗima tana ja da baya da wani irin tsoro
Ta ce "Ka dubi girman Allah Daada...," yana layi da tangaɗi ya ce "Wata can a waje wacce ba matata ba, ta iya bani komai da Ubangiji Ya yi mata na ɗiya mace, sai ke da kike ƙarƙashin ikona, za ki mini iyaka da jikinki? Jikin da nake maleji dashi, jikin dashi da babu duk uwarsu ɗaya, wai gayyar ta ahoo. Tani da muke dadiro ta fiye mini ke sau dubun du bata wlh Innti"
Ciki maye yake furta hakan, yana tangaɗi a tsakar gidan ya yi tik haihuwar uwarsa, zafi da raɗaɗin da zuciyar Innti take yi, kamar ana rura wutar ƙona biredi haka nan take jin yayyafin wutar azaba na dirar mata a cikin zuciyarta, ance mace ta gari ni'ima ce.
Ashe miji na gari ma rahma ce. "Ta ina zan iya mu'amala da kai a tsakiyar tsakar gida? Ta ina zan iya mu'amala da kai a lokacin da kake a buge, na barasar da ka sha? Ta ina zan iya, Daada ta ina zan iya"
"Ta yadda Tani take mini"
Amsar daya bata ya tabbatar mata cewa, zancen zuciya ne ya fito fili, ta san ya yi mata targaɗe a yatsunta na dama, amma ciwon da yake ji mata a zuciya a kullum, a koyaushe yafi rauninka da yake samun gangar jikinta, wahala mudu ce, ba'a taɓa sabo da ita, tarbiyya fa? Yaranta take ji.
Yaranta biyar!
Ta sassauta muryarta zuwa ƙasa sosai, da tana da iko na toshe kunnuwanta daga daina jin sautin muryoyi huɗun da suke tashi, suna kiran 'Innti' suna kiranta, da ta yi hakan, amma bata da sa'a sam ta gaza.
"Shikenan, na fahimta"
Ta furta a sanyaye tana tsayawa a gabansa, ba tare da shikenan ɗin ta zama “Everthing” ba, ba tare da “Everything” ɗin ya zama “Solving” ba ko da ya zama, baya nufin abubuwan zun shuɗe, sun jingina zuwa ga kalmar "Ending“ ba balle a samu “Happiness”
"Mu shiga daga ciki mu yi magana, saboda kunnuwan zuri'arka Daada, akwai Babban yaya, Jadid, Jaheed, Iftihal da Ana, zan yi dukkan abin da kake so, umarninka biyaya ne a gare ni, amma ka tuna mune makarantar waɗannan halittu biyar ɗin mune allon kwaikwayonsu"
"Za ki bani abin da Tani take bani?" Ya furta yana layi tana riƙo shi ita kuma zuwa gabanta, idanunta cike da hawaye.
"Ko ban baka ba, zan yi iya ƙoƙarina na faranta maka"
Ya ɗan suɗe leɓansa da harshensa.
"Gaskiya Tani duniya ce, ita kamar kankana ce me abin alheri, ke kuma tamƙar murhun gasa nama ce saboda azabar zafi Innti"
"Ya Rabbi!"
Innti ta furta a ƙasan zuciyarta, domin ta fahimci abin da gurɓatattun kalmominsa suke nufi. Ta cire kallabin kanta ta ɗaurawa Daada a ƙugunsa wajan suturta al'aurarsa, kana ta riƙe hannunsa suka nufi ɗaki, suna zuwa bakin ƙofa ya saka mata ƙafa nan take ta yanke jiki ta faɗi akan hannunta, ya shiga taka mata ruwan ciki tana kuka da ihu da kiran sunan Allah, har numfashinta ya fara ƙoƙarin tsayawa, can kuma ya shiga sheƙa mata amai me azabar wari a fuskarta, sai da ya amayar mata da duka barasar daya sha kafin ya tsallake ta ya shige cikin ɗaki abinsa ya zube a ƙasa yana rufda ciki sai bacci, cikin sa'a ya shiga mafarkai da Tani.
***
A hankali take juyi saman makeken gadon nasu, ƙirar royal bed tana sanye da kayan bacci ruwan huda, amma idanunta ya gaza ɗaukan bacci ko kaɗan balle ta runtsa kamar kowanne me rai da ke bacci a wannan lokacin.Motsinta ne ya yi yawa, ya saka shi ɗan juyowa daga bayan daya bata kaɗan.
"Madam" ya kira sunanta a sanyaye yana me kallon ta
Ta kasa amsawa sai lumshe idanunta kawai da ta yi. "Ya aka yi? Mene Madame?"
Engineer ya tambaya yana tashi zaune tare da miƙa hannunsa ya kunna hasken kusa dashi yana ƙarewa fuskarta kallo sosai.
"Yanayin garin? Damuwa? Ko buƙatar kai da kai Jiddo?"
Sai ta ɗan girgiza masa kai kawai alamar babu ɗaya daga ciki.
"Kar ki ce mini ban canka ba?"
A sanyaye ta ce "Eh"
Sai ya ɗan birkitota saman cinyarsa yana kama hannunta ɗaya ya riƙe cikin nasa.
"Kamar Abdallah zai fi kowa sanin halin Jiddah, shikenan faɗa mini mene ya hana idanunki runtsawa ya kuma hana zuciyarki sukuni har haka?" Sannu a hankali ta juyo da fuskarta zuwa kan tasa, ta zuba masa idanunta masu cike da buƙata, wanda hakan ya nuna ta bugun zuciyarta da yadda ƙwayar idanunta take nuna alamar buƙata. Ta sauke numfashi "Akan Ahlam ne fa" Ya ɗan yi jim na nazari
"Ahlam?"
Ya faɗa a zuciyarsa.
"Ahlam!"
Wannan karan a fili ya furta.
Ta ce "E, akan ta Yallaɓai"
"Ta miki wani abu ne?" Sai ta yi shiru ta kasa bashi amsa
"Tear out, me ta yi miki?"
Sai ta girgiza masa kai, tana aro murmushi ta aza a saman fuskarta "Ko kallon banza Ahlam bata taɓa yi mini ba, balle saɓani ya shiga tsakanina da ita, yarinya ce me nutsuwa da sanin ya kamata, ba kowa ne zai yarda ita rainonka bace, tun kafin mu yi aure kake kulawa da tarbiyyarta, a dalilinta ka aure ni domin tana ganin saboda ita ne kaƙi aure, na yarda she's talkative, wannan kuma a dalilin aikinta ta zama kamar aku"
"Baby nada surutu sosai"
Ya furta yana murmushi.
"Kar ki mini shiru, bani labari sauyin yanayin na lokaci guda" Jiddah ta kalli mijinta, shima kallon ta yake yana murmushi kamar wanda ya riga ya san abin da zata furta ta hanyar karantar yanayin fuskarta da kyau.
"Me zai hana ta goge recorded ɗin matar can ta yi, tun kafin a saka a Redio?"
Ya ce "Me ya sa?"
"Saboda gujewa matar shiga matsala, ina tausaya mata ƙwarai, a budurwa ya aure ta, kuma tashin ƙauye ce, mene zai faru aurenta ya mutu ta dalilin Ahlam? Ina Ahlam zata kai hakƙin matar? Mutane da yawa ba za su fahimci akan aikinta take yi ba, wasu ma za su ga saboda ita bata da aure ne ya saka ta yi mata ƙyashi na farraƙa na matar"
Ya girgiza kai "Wannan bai zama hujja ba"
"Engineer!" Ta kira shi da sunan da mutane suke kiran shi da mamaki a fuskarta.
"Wannan bai zama hujjar da za'a tauyasawa matar nan ba? Aure fa Engineer?"
"Auren fa"
Ya ce yana ɗage mata girarsa biyu. "Faɗa mini wani abu Hawwa'u , idan na yi aure, sai wata mace ta yi wa Mufeed haka ya za ki ji raɗaɗin abin a zuciyarki? Idan daka side ɗina na nuna kar ki ɗauki mataki ya raɗaɗin zai ruɓanya kan shi a zuciyarki?"
Sai ta yi masa shiru.
"Adalci take nema wannan yarinyar, wanda kuma shine ya yi ƙaranci a wannan zamanin a cikin al'ummarmu, da shuwagabanni, da jami'an tsaron, a kowanne ɓangare ba'a fiya samun adalci ba, ban ce duka ba, yawanci. Human rights ce zata iya bi mata haƙƙinta ba tare da fargaba ba, ko kuma WRAPA (Women’s Rights Advancement and Protection Alternative) ƙungiya ce dake kare hakƙin mata da yara, taimakon shari’a (legal aid) Yaƙi da auren dole, duka, da cin zarafi. Idan rayuwar ɗanta ya salwanta bata da tabbacin dana da wani ƙwan na haihuwa, zata iya sauya miji idan ƙaddararsu ba za ta zo ɗaya ba, amma zuri'a Rahma ce Jiddah"
Ya ɗan lakaci hancinta "Da ina da iko da tuni na shiga maganar, amma tunda baby tana da dama me ya sa zamu daƙushe ta? Ita ƴar jarida ce, bana son tun yanzu ta kafa aikinta akan tsoro, dole zata fuskanci ƙalubale, amma idan ta yi haƙuri komai zai shige, da ɗan jarida, da lauya da marubuci suna da hanyoyin daya haɗa su, na san wasu za su iya yi mata bazarana kuma da yawan lokaci matsoraci ake yi wa, ina son wannan karan ma ta yi abin da za'a bata award a girmamata ko hakan zai rage mata raɗaɗin zuciyarta musamman akan nakasarta"
Ta sauke ƙarfaffar ajjiyar zuciya a hankali.
"Na fahimta Engineer, daman saboda halin da Ahlam za ta iya shiga ne ya sa na damu"
Bai magana ba sai murmushi kawai yake.
"To dariyar ta mece?"
"Taki mana"
Ta ce "Ni kuma?"
Ta nuna kanta da yatsarta zuwa fuska.
"Na san matata, kar ki ce mini ban fahimci cewa akan abin da Ahlam ta ce mini bane"
"Ahlam? Ta ce maka?"
Yadda ta yi maganar da yadda ta kira sunan Ahlam kamar a lokacin ne ta taɓa jin sunan.
"Yes, saboda ta ce zan auri yarinyar idan aurenta ya mutu saboda ita?" Ta buɗe baki za ta yi magana ya yi saurin ɗora yatsarsa akai ya ce "Shhhh, mu kwanta" yana faɗin hakan ya jata zuwa jikinsa suka kwanta.
*** Batty kasa runtsawa ta yi a wannan daran, bata tsoron a gaban kowa ta ce ita mayya ce ita da Innarta, bata sani ba ko ana yarda da ita ko akasin hakan, tunda mayen gaskiya ba zai fito ya nuna kan shi ba. Taja idanunta da sukai laushi ta lumshe su, a hankali bacci ya fara ɗaukanta tana daga zaunen da take.
"Hiyaam....
"Hiyaam....
"Hiyaam!"
Haka ta ji wata kamilalliyar murya na shiga cikin kunnenta, muryar me taushi ce, da nutsuwa da kamala, sautin me muryar yana nuna neman agaji domin murya ta nuna a wahale yake, bata me yake nufi da Hiyaam ba, suna ne, ko kalma ce, ko sunan wani gari bata da tabbacin me yake buƙata. Yana cikin duhu a kuma ɗaure yake da wasu igiyoyi. A hankali ta fara tafiya zata ƙarasa inda yake domin ya juya mata baya ne bata ganinsa.
"Hai Batty, kai yaro Batty" muryar Gana ta ratsa cikin kunnenta, a ɗan firgice ta farka daga baccin da ɗan jujjuya kanta ko za taga mutumin sai ta fahimci mafarki take yi. Yau bata yi mafarki da Innarta ba sai da wani bawan Allah.
Gana dake tsaye ta kalli Batty ta ce "Tashi ki je maza ga Saleh can a bayan bukka yana jiranki na ganshi da ƙunshin leda a hannunsa, maza tashi Batty ki je" Sai ta ɗan turo bakinta gaba cikin yanayin ƙuruciya ta ce. "Saleh ƙirji yake matse mini Yaaye, kuma ina jin zafi sosai"
"To don ubanki da yake matse miki ƙirji ba abin daɗi yake kawo miki ki laƙume ba" Batty kallon Gana kawai ta yi idanunta da ya yi damshin hawaye, hasken fatar fuskarta sai ƙyalli yake ta cikin aci balbal ɗin da Gana ke haske ta dashi.
"To idan kina bani abinci kuma ina shan kindirmon nagge ba zan ji yunwa ba. Kuma ki faɗa mini su waye suka shigo rugarmu suka kashe jama'a suka tafi da wasu har da Innata aka kashe saboda taƙi shiga wani addinin daba Musulunci ba. Yaaye ina son yin karatu sosai ki saka ni a bokoko don Allah"
"Ƙaniyarki da karatu, bokokon a wuta da Allah Ya tsinewa masu makarantar bokoko kike so? Za ki shige ki samu Saleh ko sai na ɗaure ki a turke" ta girgiza kai a hankali tana haɗiyar zuciya don bata son kwanan cikin dabbobi. Sosai take fargabar zuwa wajan Saleh tsoro yake bata ma. Har ta yi gaba ta dawo ta ce. "Kin san mutanen da suka shigo rugar Yari? Idan kin sani ki waɗe mini su Allah sai na cinye kurwarsu tunda suka yanka mini Innata. Kuma ki faɗa mini kin san mene Hiyaam? Idan abinci ne ko kayan daɗi ki bani kin ji"
Gana ta ce "Na boni, na sani yana wajan Saleh. Kuma duk ranar da kika kuma cewa Innarki mayya ce sai na yanka ki a gidan nan, tunda Baffanki ba lafiya gare shi ba" Batty ta yi wa Gana ƙuri da ido. "Saboda kar a ce kema mayya ce tunda ke ƙanwar Innata ce ko?" Sai ta washe bakinta tana lumshe idanunta ta ce "Idan aka tambaye ni kam zan faɗe musu gaskiya"
Zangarniyyar kara ta ɗakko ganin haka ya saka Batty zabura tana zura yatsarta a baki ta fara tsotsa ta yi waje. Gana ta fara tunanin dole ta raba Batty da rugar Yari tun kafin taja mata masifa.
Idanunta lumshe tana tsotsar yatsa a bakinta jikinta sanye da kayan saƙi na Fulani farare tas, hatta ƙarfta sarƙa ce da wuyanta, fararan ƙafafuwanta a bayyane a haka take tafiya har ta ƙarasa inda Saleh ke laɓe yana jiranta. Yana ganinta ya washe bakinsa sosai ya ce "Masoyiyata Batty ki yi murmushi mana ko zan ji daɗi haba Batty" ta kau da kai zuwa gefe guda tace
"Ni dai mu kunce, na daina kulaka kuma ba zaka sake taɓa mini ƙirji ba, tunda ka fara taɓa mini suke zama kamar balo wacce ka taɓa kawo mini daka je birni"
Saleh ya gyara tsaiwa ya ce "Yanzu ma biredi da lemo ja na ruwa na kawo miki Batty duba kiga"
"Ce Allah rantse in ji"
"Da gaske nake duba"
Hannu ta miƙa zata amsa ya yi baya da hannun ya ce "To bani na taɓa kaɗan kin ji? Gana da kanta ta ce na dinga yi" shiru ta yi alamar tunani sai ta ce "Amma sau ɗaya ko?"
Ya kada bakinsa wajan faɗin "Kayya Batty, Gana fa Innarki ce ta san ba zan cece ki ba ki buɗe kawai kuma ni zan aure ki" da sauri ta ce "A'a walle, ɗan boko nake so kyakkywa dogo wanda zai dinga goyani yana shillani"
"To na ji buɗe mini"
Tattare rigar ta yi sama jikinsa har rawa yake yi wajan yin abin da ya saba na taɓe mata matasan ƙirji, data fara jin zafi yaga zata gudu sai ya manneta da bangon ya shiga murzawa da ƙarfi ihu ta saka ta fashe da kuka tana yarfe hannunta.
"Wayyo... Wayyo shikenan ya cire mini kindirmona wayyo kindirmona na barinkaɗi na lalashe"
Gana na jinta ta yi iska da ita, addu'a take yi dama zai lalata mata rayuwa a wajan ta wuta da bala'in yarinyar. Dan haka ta ɗauki niyya gari na wayewa zata fice da Batty daga rugar Yari.
***
Sun daina jin kukan Innti! Sun daina jin sautin muryarta! Sun daina jin hargagin Daada!
“Mene ya faru?”
Jadid, Jaheed, da Iftihal suka shiga tambaya a ƙasan zuciyoyinsu, banda Yaya wanda tunda ya yi ƙasa da kan shi bai ɗago ba, bai kuma motsa ba, ya gaza sakin rezar data murmushe a tafin hannunsa, jini sai zuba yake kamar a lokacin rana ta take.
Ƙirjinsa ne ya shiga harbawa da yi masa rawa, wani abu ya tsaya masa a ƙahon zuciyarsa, baya ko motsi.
"Suma ta yi" cewar Jadid.
Sai ya durƙushe a wajan da jikinsa da bashi da ƙwari saboda lalurar dake damunsa, hawaye na bin farar fuskarsa. Jaheed daskarewa ya yi daka tsayen da yake jinin jikinsa ya daina gudana na wani lokaci, idan akwai wani abu da ake kira da tsoro, sun riga da sun gama shiga, tsoran rasa Innti shine abin da zai wa zuciyoyinsu wahalar ɗauka, ba balle ƙwaƙwalwarsu ta yarda zasu iya rasa ta. "Ka kira sunanta, zata amsa"
"Ba zata amsa ba" Jadid ya bawa Jaheed amsa nan take yana riƙe kan shi.
"Babban yaya!"
Suka kira sunansa a gigice ganin jini na zuba a hannunsa, bai ji kiran ba, saboda ya shiga cikin tunaninsa ne sosai,kama hannunsa da suka yi ne ya dawo dashi cikin zahiri. Ya kalli Jadid da Jaheed, ya dubi hannunsa da suka riƙe, fararen idanunsa da suka rine da ja ya buɗe musu sosai, curarriyar girarsa na haɗewa waje guda.
"Babban yaya hannunka"
Ya sake buɗe musu idanunsa. Sai suka yi saurin sakinsa, daya motsa idanunsa ya basu tabbacin umarni yake basu da su je su kwanta jikinsu a sanyaye suka koma shimfiɗarsu tare da kwanciya.
Shima kallonsu kawai yake yi, ganin da gaske ba za su yi bacci bane ya saka shi miƙewa tsaye, ya ɗauki bakin rigarsa ya yi musu firfita, duk yadda sukai ƙoƙarin juyawa suka gagara, saboda wata iska me daɗi data ratsa fuskokinsu, wacce basu taɓa jin irinta ba, nan take ta mantar da su abin da ya faru da halin da Innti take ciki, wani nauyayyen bacci ya ɗauke su. Babban yaya ya ja numfashi ya cika bakinsa da iska ya fesar, sannu a hankali ya zare rigar jikinsa duhun fatarsa me ɗaukan idanu ta bayyana, da yawan lokaci jikin mutum na yin ɗumi amma koyaushe sanyi ne a jikinsa idan tsautsayi ya saka ka raɓo da jikinsa, sai ka ji kamar ka taɓa ruwa me sanyi ne don haka ba kasafai yake gogayya da mutane ba. Sumar kan shi har ƙasan wuyansa.
Baƙa suɗik da ita, idanunsa da surkin blue blue sak irin na Ana komai da komai.
Jikin bango ya zubawa idanu, a hankali ya matsa sai bangon ya buɗe masa ya fice, yana zuwa tsakar gidan yaga Innti kwance a ƙasa babu numfashi ya durƙusa dab da ita yana kallon ta sosai, tamkar zai mai data ciki saboda soyayyar uwa haka yake ji a ƙirjinsa.
Ta cikin idanunsa ya hango ƙashin hannunta daya goce, ga jini nan yana gudana a wajan, sai daya fara saka ta nauyayyen bacci kafin ya yi bisimillah a zuciyarsa ya shafi hannun, tsananin azaba ya saka Innti firgita zufa ta jiƙe mata jiki amma iskar da yake hura mata ta baki ya hanata farkawa ko yunƙurin motsa bakinta, ya saka farin zare wajan naɗe hannun ya shafa mata magani, kana ya saki hannunta. Shi kaɗai yake iya ganin zaren kuma. Haka yaja yatsunta sukai ƙara ya daidaita musu zama, sai ya miƙe tare da Innti a hannunsa ya tsallake Daada ya kwantar da ita saman katifar ɗakin kafin ya miƙe ya fita. Har zai fice waje, ya ji sautin kukan Ifti, tabbas ita ce, yasan Ana ba zata taɓa kuka ba, suna da saɓani ta nan.
Kamar walƙiya ya ratsa ƙofar ya shige, Ifti na durƙushe tana rera kuka da muryarta da bata fita sosai saboda kukan data sha. Ana kuma na tsaye jingine da bango ta zubawa waje guda ido, yana hango yadda jikinta yake rawa da kakkarwa idanunta kamar su fita waje, jijiyoyin kanta sun yi reras a saman goshinta sai fuskar numfashi take yi. Babban yaya ya motsa.
"Yaya" Ifti ta kira sunansa.
Da sauri ta miƙe ta nufi wajansa tana riƙe shi "Mene ya samu Innti? Me Daada ya yi mata, yaya mun shiga uku idan muka....,"
Bai bari ta ƙarasa ba ya saka hannunsa ya shafi kanta yana mata tattausan murmushi.
Ajjiyar zuciya ta shiga saukewa sanda ya bata tabbacin Innti lafiya ƙalau take."Me ya sa Daada yake dukan mahaifiyarmu? Me ya sa yake shan giya? Me ya sa yake zuwa wajan karuwa, haka kowanne mahaifi yake Yaya?" Ta sake fashewa da kuka.
Jikinta har wani ɓari yake.
"Innti ta ce za mu yi aure watarana, muma haka mijinmu zai dinga yi mana? Ya dinga shigowa gida tsirara babu tufafi a jikinsa?"
Bashi da amsoshinta, daman shi bai taɓa amsa ko tambaya ɗaya ba a rayuwarsa idan ya shige tambayoyin jarrabawa, iya su kawai. Zata sake yin magana ya ɗora yatsarsa a saman ƙaramin bakinta alamar "Ya isa"
Sai ya matsar da bakinsa dab da fuskarta ya hura mata iska, nan take idanunta ya fara lunshewa jikinta ya saki murus ta yi kamar zata faɗi ya taro ta a tafukan hannunsa tare da kwantar da ita ya lulluɓe mata jikinta. Ganin baccinta ya yi nisa ya saka shi juyawa zuwa inda Ana take tsaye, tunda ya shigo ɗakin ko yatsar hannunta bata motsa, ya matsa dab da ita yana ɗan kallonta taƙi yadda ta kalle shi, tana da taurin kai kafiya da zuciya, tana da sauƙin hali da shiga rai kamar kuɗi, da daɗin zama da baiwa ta karatu, bata taɓa shiga sabgar mutane.
Ya saka hannunsa ya juyo da fuskarta. Sai a lokacin ta kalle shi da blue eyes balls ɗinta, sai wani haske ya fita kamar magic.
Da idanunsa ya yi mata alamar "Menene?"
Sai yaga ta yi murmushi, har dimples ɗinta suka lotsa ta lumshe idanunta gashin idanun suka bi fatar wajan kwanciya suma.
Kuka ya dace ta yi kamar sauran ƴan'uwanta, amma sai yaga akasin hakan, suna da kamamceceniyya na hali, shi da ita. A hankali ta dube shi ta ce
"Babban yaya ka je ka kwanta"
Ɗas! Yatsunsa suka bada sautin magana
"Ke kuma fa?" Haka ƙarar ta bayyana.
"Bana jin bacci"
Sai yaga tana ta murmushi jikinta ya shiga rawa sosai, ya sani idan zai kwana a tsaye yana hura mata iska ba zata taɓa ɗaukanta ko aiki a jikinta ba, sai ya kama hannunta kamar tana jira ta lumshe idanunta ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi tana sakin wata ajjiyar zuciya, duk yadda take ƙoƙarin taga hawaye ya fita a idanunta amma ya ci tura, wani irin raɗaɗi na azaba ƙirjinta yake yi mata. Gani take idan suka rasa Innti sai tafi kowa shiga damuwa a wannan duniyar.
"Ya......yaaaa" ta kasa magana.
"Zafi ƙirjina yaya....
"Ka danna mini ƙirjina"
Ta faɗa a rarrabe, jikinta na kakkarwa.
"Ba zan iya taɓa ƙirjinki ba Shalelen Innti"
Haka numfashinsa ya bata amsa, ganin da gaske ƙirjinta ciwo yake yi ya jata jikinsa ya rungumeta daga tsayen da suke, tafin hannunsa ya ɗora a bayanta ya dinga shafawa har sai da ya ji ta yi gyatsa ciwon ya faɗa mata. Tana jikinsa ta ce "Kamar na mutu, bana son Daada, bana son ganinsa" ta rufe idanunta da ƙyar numfashinta na sarƙewa ta ce
"Ko dai ba babanmu bane?"
Yaya ya yi mata shiru.
"Ɗan iska ne fa, yana zuwa wajan karuwa"
"Iskanci yake yi da Ta....,"
Bai bari ta ƙarasa ba, ya danna jijiyar wuyanta sai ta tafi luu ya yi saurin rungumeta, bai san me ya sa yake jin soyayyar Ana fiye da komai ba, banda Innti mahafiyarsa ce, wani lokacin har tsoro yake kar soyayyar Ana tafi ta Innti yawa a ƙirjinsa, yana ƙoƙarin dannewa kar ya nuna fifiko ita da mahaɗinta, shi ya saka yafi hukunta Ana fiye da Iftihal ɗin.
Ya ɗan sumbaci goshinta kana ya kwantar da ita kusa da ƴar'uwata ya yi musu addu'a shima ya fice daga cikin ɗakin ta jikin bango.
Ya zauna a tsakar gidan, iska na kaɗa shi tana tafiya da duk wata damuwa dake ƙasan zuciyarsa, bayan ya lumshe idanunsa na wani lokaci, sai ya ji sanyin jikinsa ya yi masa yawa, iskar ma haka, ga wani haske dake shigar masa ido sosai, sannu a hankali ya buɗe ido, ya shiga ƙarewa wajan ido, ba tsakar gidan Innti bane, tsakiyar dokar daji ne, gefen ƙoramar dake gudana a wajan.
Cikin bacci Jadid da Jaheed suka ji muryar Innti tana kiran sunan su, a hankali suka buɗe ido, bakinsu ɗauke da addu'ar tashi daga bacci. "Innti?" Jadid ya furta a hankali "Har an kira sallah kuna bacci? Wannan baccin na magani da mene ban saba ganin irinsa ba" Jaheed ya miƙe zaune.
"Ban san ya aka yi mukai nauyi ba yau"
"To ku tashi, kar ku rasa jam'i"
Ta faɗa tana miƙewa tsaye, kaɗan kaɗan hannunta yake mata ciwo, gefen fuskarta a kumbure haka ta fita, ta dubi Iftihal ta ce
"Ana bata fito ba?"
Kafin Iftihal ta yi magana Ana ta fito daka cikin banɗaki kan nan babu ɗankwali, Innti ta yi sak ganin kan Ana kamar bishiya saboda tsabar yawa da tsayi, Iftihal ma kallon Ana take yi da mamaki a fuskarta.
"Allah Ubangiji ka shirya mana zuri'a, Ubangiji ka shirya mini Aysha, da asubar nan ki shiga banɗaki babu kallabi kamar kuntacciya, haba Ayshatuna, me ya sa kike so na dinga yaƙi da baki akan ki ne, haka ki kaga ƴar'uwarki na yi? Kin manta abin da ya same ki ne jiya a cikin bayan gida?"
"Fitsari nake ji sosai Innti"
"Sai ya ba ki damar fitowa haka? Ki raba kan ki da Aljanu Ana, ina rabaki da Aljannu"
"Ni ina ruwana da wasu Aljanu" ta faɗa tana kumbura baki
Innti ta ce "Au haka kika ce?"
"Nifa Innti zan so ganin Aljanun ma idan akwai, ko matar dana gani kawai mafarki ne, babu wasu Aljanu a duniya, kuma Innti ki yi shela, masu yi mana kashi da asuba kamar masu cikin fara don Allah su daina" kasa magana Innti ta yi idan ta biyewa Ana bata san wacce kalma zata iya amfani akan yarinyar ba. Ganin ta yi shiru ya saka Ana ta yi murmushi tana kashe idanunta "Allah Ya yi mini arziƙi na kai ki Umara da Hajji Sahibarmu abar ƙaunarmu walwala da jin daɗinmu idan bake babu gida lantarkin gidanmu baya goya marayu na karya miki ɗan kwali Babarmu"
Murmushi Iftihal ta yi tana kallon mahaɗinta gabaɗaya ita babu Daada a lissafinta, gashi ita kuma a duniya tana masifar son mahaifinta yarinya me nutsuwa bata da hargagi ko ɗaya, saɓaninta ɗaya da Ana, ita Ana data saka ƙafa waje dukkan farincikinta zai kau ta haɗe fuska bata buƙatar kowa sai iya su kawai, miskila ta bugawa a mujalla a rubuta taurin kai da kafiya akwai barkwanci amma. Iftihal yawan fara'a da murmushi duk wanda ya yi mata magana babu ruwanta, she's so friendly to everyone. Akan wannan matsalar har daina magana suke yi na minti biyar, Ana tana ganin kaf duniya Iftihal kawai take da ita matsayin ƙawa, idan kuma tana kula wasu shikenan sun ƙwace mata nutsuwar zuciyarta masifar kishin yan'uwanta gare ta.
Dai-dai nan Babban yaya ya fito yana gyara zaman Jallabiyar jikinsa, ya dubi Innti jin tana maganar Aljanu, kana ya dubi Ana, Innti ta yi mamakin ganinsa domin data shiga ɗakin baya ciki, dai-dai nan ma Jadid da Jaheed suka fito, Babban yaya ya yi waje suka bi bayansa.
Alwala Ana ta yi haka Iftihal daman tuni Innti ta yi, a tsakar gida sukai sallah bayan sun idar sukai azkar suka ɗora da tilawar Kur'ani. Innti ta kunna wuta ta fara ɗora ɗumamen tuwon da suka yi jiya, gaban Ana sai faɗuwa yake kar dai ɗumamen za su ci yau ma, sun manta da abin da ya faru jiya banda Ana da Innti da Babban yaya.Abin yana zane a zuciyoyinsu raɗau.
Suna idar da karatun, Iftihal ta fara share tsakar gidan, Ana kuma ta fara wanke-wanke. Ƴan mazan na dawowa suka fara nasu aikin, Jaheed jan ruwa a rijiya ya cika ko'ina, Jadid na zaune yana karatun Alqur'ani saboda bashi da lafiyar yin aiki. Babban yaya kuma ya haɗa kayan Innti dana Ana dana Iftihal ya wanke tas ya shanya, Jaheed ya wanke nasa dana Jadid.
Bayan sun gama kowa ya yi wanka ya shirya weekend ne, Babban yaya sai 11 zai tafi farm center, Jaheed kuma sai 12 zai je shago Ana da Iftihal kuma babu makaranta. Suna zaune a tsakar gidan iska na kaɗawa gwanin sha'awa, sun shimfiɗa tabarma a ƙasan bishiya suna jiran Innti ta kawo musu ɗumamen tuwon. Ana ta miƙe ta nufi ɗaki babu jimawa ta dawo hannunta ɗauke da waya tana ta murmushi a fuska
Jadid ya ce "Yau kuma kin tashi daga mafarkin zama marubuciya kin ɗauki burin Iftihal na zama ƴar jarida Allah Ya shirya mutum muna ganin ta kanmu a gidan nan" murmushi kawai ta yi masa bata ce komai ba.
"Muna ɗaukan rahoto kai tsaye daga gidan rediyon Innti, me rahoto Ayshatul-Haleeym Ana"
"Ƴar jarida kika zama yau?"
Ta kashewa Jaheed idanunta.
"Yaya Jaheed, me zaka iya cewa akan ɗumammen tuwon da Innti take yi yau?"
Yana murmushi sosai ya ce "Ɗumammen tuwo duniya ne, ba'a bawa yaro me ƙiwa"
Ta juya idanunta ta koma kan Iftihal ta ce "Mahaɗita ke mene ra'ayinki?"
Iftihal na murmushi ta ce.
"Kai mahaɗita, ɗumame akwai daɗi"
Tun kafin ta ƙarasa kan Jadid ya ce
"Kina zuwa inda nake zan kwarfeki, da wasu idanunki kamar na mage wasu koraye"
A hankali Babban yaya ya juya nasa idanun da suke blue akan Jadid sai kawai ya ɗauke yana cigaba da danna waya. Ana ta koma kan Innti ta ce "Hajiya Inntinmu ta gargajiya, me za ki ce akan wannan ɗumamen da kika yi mana yau don Allah"
"Allah Ya cika miki burikanki na alheri Aysha, ya shirya mini ke". Ta lumshe idanunta kamar yadda ta saba kamar me jin bacci can ta buɗe su akan Babban yaya tana ƙarasawa kusa dashi.
"Babban yaya magajin uba, me zaka ce kai kuma"
Kamar ba zai motsa ba, sai kuma ya ɗago kan shi ya sauke mata fararan idanunsa masu launi a cikin nata, bai san me ya sa ba, sai ya ji murmushi yana shirin suɓuce masa, ya kawar da kan shi zuwa gefe guda.
Duk yadda Innti taso Ana ta ci tuwon fafur taƙi ci, ta tsani tuwo kamar mutuwa.
Bayan sun gama ci, Innti ta samu Yaya a cikin ɗakinsu ta ce "Yaya, Ana taƙi cin abinci fa tun jiya, na rasa yadda zan yi mata"
Ya jinjina kai, bayan ta fita ya miƙe shima ya fita zuwa waje, babu jimawa ya dawo hannunsa ɗauke da leda, ya ɗauki kwano ya saka tuwo da miyar ya shiga ɗakinsu Ana, ita kaɗai ce Ifti ta fita aike zuwa maƙota. Ya zauna saman ƙafafuwansa irin zaman raƙuma ya ja kwanon gabanta, tun kafin ta yi magana ya zura yatsunsa ya ciro tuwon ya saka mata a baki, ta ɓata fuska haka ya dinga bata tuwon a bakinta da hannunsa ganin kamar za ta yi amai ya wanke hannunsa ya miƙa mata ledar, indomie ta gani dafaffiya tun kafin ta yi magana ya fice daga cikin ɗakin yana rufe idanunsa. Daman tun asubar fari Daada ya fice nasa waje, su kaɗai ne a gidan.
***
Ƙuri ta yi wa jaririn da yake kwance jikinsa kamar kwando saboda saɓulewa da ya yi, bata iya taɓa shi an baɗe masa jiki da wani garin magani. A hankali ta kai hannunta zuwa fuska ta share hawayen idanunta, bata taɓa ganin aure irin wannan ba, ko da ta taɓa gani nata yana da tarin bambanci, mijin ya aureta amma kamar kishiyarta ce ke riƙe da igiyoyin auren, da ƙuruciyarta da komai amma baƙincikin aure da zaman kishiya ya sako rayuwarta gaba, haihuwa ta yi ko kunun kanwa wannan bai ga cikinta ba, balle ƙaurin da ake yi wa me jego. Ɗan kara kunnenta ta yi sai ta ji numfashin babyn na fita da ƙyar.
Labulen ɗakin aka ɗago yana daga tsaye ya ce "Wato Maryama ba za ki je ki hana me rahotan can sakawa ba, wallahi Allah muddin ta saka a bakin aurenki makira munafuka" kasa motsi Maryama ta yi, jikinta ɗanye ne sosai abarka da farar mace ta sake yin fari shar kamar mara jini a jika, gefe da gefen fuskarta duk gashi ne kwance haka ma girarta kyakkywa ce sosai bata shige 21 ba gabaɗaya.
Cike da tsoro ta ce "Ai ban santa ba, bani na faɗa mata ba. Kar ka sake ni don Allah wallahi za'a iya kashe ni a gidanmu"
Da hargagi ya ce "Ai gwara su kashe ki tunda gashi za ki jazamin shiga masifa da zarar hukuma ta ji na kaɗe har ganyena"
Wacce take gefensa ta yi ƙwafa "Malam burinta ba a rufe ni na bar gidan ya zama daga kai sai ita, na faɗa maka ba ƙaunata take yi ba, da zaka sake ta da yafi" sai ya yi mursisi da idanu saboda yana ƙaunar tarayya da ita "A'a bata kai ga haka ba, ki duba duk ayyukan gidan nan Maryama ce ke yi miki idan ta bar gidan yaya kenan"
Wani irin malalacin kallo ta watsa masa "Na fahimci kamar son ta kake, bana hanaka ce mata Maryama ba idan ba zaka ce ƴar aiki ba kawai ka yi shiru kaima fa Malam jarababbe ne" tusa ƙeyarsa ta yi suka fice daga ɗakin. Maryama ta bisu da idanu tana fashewa da kuka a hankali ta ce "Ubangiji ka kawo mini mafita ta alheri"
*** NIGER/MINNA.
Jihar Niger tana Arewa ta Tsakiya (North Central Nigeria). Ita ce jiha mafi girma a faɗin ƙasa wanda babban birninta ya kasance Minna, suna maƙwabtaka da Zamfara, Kebbi daka Arewa, sai Kaduna, FCT Abuja daga Gabas, sai kuma Kogi, Kwara daga Kudu, Benin Republic daga Yamma.
Akwai mabanbanta mutane a jihar Niger zuwa Minna, Nupe a ɓangaren Bida, Lavun, Agaie. Sai Gwari/Gbagyi daka ɓangaren Suleja, Tafa, Minna. Sai Hausa Fulani a yankin Kontagora, Rijau, Wushishi, haka sauran ƙabilun kamar Kamuku a yankin Mariga, sai Kambari a yankin Agwara, sai Basa a yankin,Katcha haka kuma Dukawa a yankin Borgu. Niger na daga jihohin da suka fi kabilu haɗuwa a Najeriya.
BIYA. Wani yanki ne a Nijer ƙauye ne sosai, wanda mutanen ƙauyen suka dogara da Noma, farauta da kiwo sana'ar hannu, suna da ɗan yawa gasu da soyayyar juna ta mutunci.
"Wai har yanzu bata sauka bane?"
Lami ta yi tambayar tana kai komo hannunta riƙe da zaninta saboda tashin hankali. Jin an yi mata shiru ya saka ta sake cewa
"Sadiatu, magana nake yi"
"Kika ce me Lami?"
Sadiatu ta yi maganar tana ɗago labule daga ɗakin da take ta fito fuskarta babu walwala saboda damuwa.
Lami ta ce "Har yanzu bata juye bane?"
"Sai dai Allah Ya saukar da alheri, ban taɓa ganin naƙuda irin wannan ba Lami, abu tun jiya? Har hantsi ya fara kawo kai?" Sadiatu ta faɗa idanunta cike da hawayen halin da Kulu take ciki, suka yi jingum jingum. "Ai Malam ne da kalar tasa masifar, a kira me karɓar haihuwa amma bafur yaƙi ba dole ba" Sadiatu ta ce "Kin san shi da kafiya kamar kuturu haka yake".
"Ai har gwara kuturu dashi"
"Gafaranku dai"
Suka ji an yi sallama daga bakin ƙofa.
"Maraba lale da Gana, yau kece a tafe?" Cikin fara'a da walwala Gana ta ce "Wallahi, ai tafiyar dole ce shi ya sa na yi babu sanarwa" ta ƙare maganar yanayin fuskarta yana sauyawa zuwa damuwa can kuma ta juya a fusace ta ce "Ba za ki shigo ba ƴar kusun uwa, munafuka makira me ido a tsastsaye, mahaukaciyar banza da wofi"
Lami da Sadiatu suka shiga leƙawa zuwa bayan Gana domin ganin dawa take sai suka hangota tsaye rakuɓe da jikin katanga. Tana zazzare idanu, tare da murza gashin kanta dake tufke tana wasa dashi, sai murmushi take yi tana girgiza kai da nunna abu a sama, ita kanta bata san me take yi ba, ba kuma tana yi saboda hauka bane bata son ganin matan gidanne
"Au wai Batty ce, ince dai lafiya yaushe ta fara hauka kuma ni ƴar nan?"
Gana ta yi ƙwafa cike da takaici ta ce
"Ina lafiya? Ai Baffan Batty ne ya ce a dawo da ita gabanku, wataƙila za ta yi hankali, ta dage sai an sata a makaranta" mamaki ya wanzu a fuskokinsu. "To ina Fulani ina zuwa wata makaranta, arna ne kawai suke zuwa bokoko, ya yi mini daidai ai"
"Wata sabuwa ni Lami" ta sake faɗar haka Gana taja kujera tana zama.
"Me ta yi ne? Me ya sa Baffan Batty ya ce a kawo ta Biya wani abu ta aikata a can yarin?"
Cikin fillatanci Gana ta ce “Ko Batty woni jokka waɗude jango mo, sabu ɗum jokkaare makko.” ma'ana a yaren Biya ana nufin “Batty ce ta fara ɗauko masa zance, ai iskanci ne ke tuka ta.” Lami ta shiga salati
"Na boni, me ta ɗakko?"
"Zuwa ta yi ake taɓa mata matasan ƙirjin saboda iskaci, shi ya sa shekarunta be ɗakko ba, zuciyarta ta ɗakko nan da nan ƙirji ya haye" Sadiatu ta girgiza kai kawai.
"Yanzu ni da aka kawo mini ita nan na yi yaya da ita? Salon ta dinga ɗaukar mini zance, Biya fa ba kamar can yari bace"
Gana ta ce "haka za ki haƙuri Lami"
Sai ta juya ta kalli Batty wacce kanta yake sama tana ta murmushi, a nutse yarinyar take sosai, idan ka ɗauke ƙuruciyar dake addabar kanta kayan saƙi na fulani ne a jikinta an ɗaure sumar kanta kamar alkaki.
"Shai Baffan daya turo ta nan me za'ayi mata? Kiwo zata dinga yi ko farauta?"
"Idan an samu me son ta a bayar da ita sadaƙa" sai a lokacin ta ɗago dara-daran idanunta ta zuba akan Gana tana jin duk abin da suke cewa, da sauri kuma ta faɗo cikin gidan, a hankali kuma ta kalli Sadiatu, ba ita take kallo ba, jinin da yake gudana a jikinta yana kai kawo take kallo, da kuma kwantaccen kitsan da yake cikinta, ta zubawa cikin idanun sai ta hango dafaffiyar masarar da Sadiatu ta ci ɗazo wacce bata gama narkewa ba, wani irin numfashi ta fuska idanunta yana rinewa saboda ja da kuma abin da ya motsa mata, tana ta kallon abin da yake yawo a ƙasan ƙafafuwan Sadiatu. Kafin su yi magana sun jiyo kukan jariri cikin sauri Sadiatu ta nufi ɗakin Gana kuma ta ce "Waye zai haihu?"
"Kulu ce"
"A'a tubarakallah ma sha Allah, kulu Allah ya yi kenan" Gana ta ce tana washe bakinta. Suna zaune aka gyara jaririn mutane suna ta yi wa Kulu murna haihuwar da har ta fitar da rai da ita. Gana ce ta shiga cikin ɗakin tana ƙifta idanunta, bayan ta ɗauki jaririn da yake fari tas ƙato dashi, sai motsa baki take, can dai ta miƙe tana faɗin "Allah Ya raya Kulu sai mun dawo raɗin suna, sannu kin ji haihuwa me daɗi" Kulu na murmushi
Ta ce "Yaya Gana har za ki shige?"
"Wallahi, Batty na kawo ai"
Tana faɗin hakan ta laso bakinta kamar za ta yi magana sai ta haɗa da kurwar jaririn ta yi sauri ta fito. "Gana tsaya mu yi magana"
"A'a Sadiatu, zan dawo ai in sha Allah"
Ta faɗi hakan tana ficewa, sai data je waje ta tsaya ta ƙulle kurwar a bakin zaninta....
Akwai page 4,5,6 a ArewaPen. Ku yi searching sunan littafin HIYAAM chapters ɗin zai fito sai ku yi following domin samun notification idan an yi update.
More information 08164069385 08082101373
Share fisabilillahi