Kenza eBookz
Cover art for KOMAI YA YI FARKO  HAUSA NOVEL 7

Post

KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 7

.....yes, she drove them to the airport, Hunaif was sitting next to her, the Twins were sitting in the backseat, Mami was parking in the parking lot, she turned and looked at Hunaif, she said; "If you have a match with him, please fine time to go and see your father before he comes back to Nigeria." He shook his head at her and said; "I Shall God." She gave him a side hug and said; "God protect me, protect me from the front and the back, please do not play with worship." "May God bless you, Mami." They opened the door of the car and got down. Hunaif hugged the twins at once and said; "I will miss you little ones." "We will miss you too." They said together. Inaya, who was closer to him, started moving the ball, Hunaif pulled her nose and said; "If you cry, it will be a long time before I come." He looked at Inara and said; "If she cries, don't tell me." Inara nodded. At exactly seven o'clock in the morning on Monday, the British Airway flight took them from Hunaif to London, where they will board a flight to Brazil. Mami saw the departure of the plane and felt as if she was crying and how Inaya was doing. This is not the first time that Hunaif is going to Brazil, but every time he

Standalone post2,061 words

KOMAI YA YI FARKO

PAGE 6

Shirye-shiryen komawa Brazil Hunaif ya fara yi, ya kasance yana mai buga ƙwallon ƙafa wa Flamengo football club Brazil, a matsayin midfielder, shi ɗin kwararrene kuma sanannen ɗan kwallon kafa da ba Brazil da Nigeria kaɗai ba, duniya gabaki ɗaya ta san da shi. Mami na zaune a gefen shi tana taya shi arranging kayakinsa a box, sai tace; "Allah ya sa next zuwanka ya zama aurenka ne."

Murmushi Hunaif ya yi, yace; "Aameen Mami, ki taya ni da Addu'a Allah ya bani mace ta gari da za ta iya hakuri da Ni, mu zauna lafiya cikin so da ƙaunar juna."

"Ina yi maka addu'ar nan kullum, kuma ina da tabbacin Allah zai amsa."

Suna gama shirya kayan, Mami ta miƙe, tace; "Sai ka kwanta yanzu, saboda gobe ka tashi da wuri tunda flight ɗin sassafe zaka bi.

Washegari da sassafe Hunaif ya fito janye da trolley ɗinsa, Mami na biye dashi a baya, twins kuma na ƙasa suna jiran saukowar su, Inaya ce ta karɓi trolley ɗin hannunsa suka yi gaba, Hunaif ɗin da Mami na biye da su a baya.

Mami ce ta yi driving ɗinsu zuwa airport, Hunaif na zaune a gefenta, su Twin kuma na zaune a backseat, Mami na parking a wajen da aka tanada don parking, ta juyo ta kalle Hunaif, tace; "Idan ka yi match da kake da shi, please fine time ka je ka duba Abbanku kafin ya dawo Nigeria." Kai ya gyaɗa mata, yace; "In Sha Allah." Side hug ta yi masa, tace; "Allah ya tsare, ya kare min kai gaba da baya, don Allah kar ka rinƙa wasa da ibada."

"In sha Allah Mami."

Buɗe ƙofar motar suka yi, suka sauka, Hunaif ya rungume twins lokaci ɗaya, yace; "I will miss you little ones."

"We will miss you too." Suka faɗa a tare. Inaya da ta kasance more close to him ta fara matsar kwalla, jan hancinta Hunaif ya yi, yace; "Idan kika yi kuka sai na daɗe kafin na kuma zuwa." Ya kalle Inara, yace; "Idan ta yi kuka ki faɗa min." Gyaɗa kai Inara ta yi.

Ƙarfe bakwai daidai na safiyar Monday jirgin British Airway ta daga da su Hunaif sai London, inda a nan ne zai dai jirgi zuwa Brazil. Mami na ganin tashin jirgin ta ji kamar ta yi kuka itama yadda su Inaya ke yi, ba wannan ne karon farko da Hunaif ke tafiya Brazil ba, amma duk tafiyarsa sai ya bar su da kewa, saboda a duk lokacin da yake gari ya kan ɓata su da excess caring and love. Da ƙyar Mami ta iya danne nata damuwar, ta fara consoling su Inaya da hankalin mutane ya fara dawo kansu, Inaya was crying seriously saboda ita ɗin ce abokiyar hira, shawara, zolaya da kuma faɗar Hunaif, she's more closer to him than Inara, saboda Inara is the type da ba ta ɗaukan komai serious, while Inaya mutum ce da ta value duk abinda take da opportunity ɗin samu, she don't play with her education at all dama duk abinda take da shi, hakan ya sa ta zama more close to him, Mami ta kama Inaya ta shigar da ita mota, Inara ma ta shigo tana goge hawayenta, Mami ta kalle su, tace; "Haba, sai ka ce wanda ba zai ƙara dawowa ba, your brother will come back to you anytime he is oppurtuned, kuma ai ya ce ba zai ƙara daɗewa kamar last time ba, so now ku share hawayenku, ku yi mishi addu'ar nasara a duk abinda ya saka a gaba, that's the only thing he need from you, ok?" Kai suka gyaɗa mata, kowa na ƙoƙarin mayar da hawayenshi.

Hunaif na shiga jirgin shima ya ji jikinsa ya yi sanyi, tun bai bar ƙasarsa ba ya fara jin kewarta, ya fara kewar hirar Mami, addu'o'inta da kuma zolayarta, ya fara kewar rigimar su Inaya, unnecessary billing ɗinsu, da kuma yin musu shari'a kullum. It's always like that anytime he is going back to Brazil, sai ya ji kamar ya bar komai ɗinsa a Naija, amma da zaran ya yi kwana biyu a can sai ya ware ya dawo normal, at some point he believes there's no place like home, da ba don so da yake da shi wa football ba, da babu abinda zai saka ya bar ƙasar haihuwarsa.

A London Hunaif ya kwana, the next morning ya shiga flight straight to Brazil. A Brazil a cikin garin Rio de Janeiro Hunaif ya ke da zama, yana da gidan kansa a wajen, da kuma business da yake running bayan buga ƙwallo. Yana sauka a airport, chauffeur ɗinsa dake airport ɗin yana zaman jiransa, ya zo ya karɓe trolley ɗinsa ya saka a booth, Hunaif na ƙarasowa bakin motar ya buɗe masa back seat ya shiga, shi kuma ya koma gefensa na dreba. Lumshe ido Hunaif ya yi yana jin gajiya a jikinsa, wayarsa ne ya fara vibrating a aljihunsa, hannu ya saka ya ciro wayar, murmushi yayi gani Mami ce mai kiran, ya picking wayar ya saka a kunne, yace; "Assalamualaikum Mamina."

Mami dake kishingide a falonta ta lumshe ido, tace; "Wa'alaikum Salam, Hunaif ya hanya?"

"Alhamdulilla Mami, yanzun haka ina hanyar Rio de Janeiro ne, ban riga da na isa gida ko ba."

"To Allah ya kiyaye hanya, idan ka isa sai mu yi wayar." Mami ta faɗa tana ƙoƙarin cire wayar daga kunnenta.

"Where's Inaya?" Hunaif ya tambaya kafin ta kai ga cire wayar.

"Tana ɗakinsu, tunda ka tafi ta kasa walwala, amma she will be fine, ta saba."

Murmushi ya yi yace; "I miss you guys Mami."

Mami ta ji wani hawaye ya gangaro mata, amma sai ta daure ta yadda ba zai gane ba, tace; "We miss you too, please don't stay long kafin ka zo."

Gyaɗa kai ya yi kamar tana gabansa, yace; "In Sha Allah."

__________ Yau su Kausar sun tashi babu ko ƙwayar hatsi a gidan, gashi har ana neman sha biyu Lawal bai dawo gidan ba, wanda hakan ke nuni cewa bai samo abinda za a dafa bane, Ya Kausar ta shiga damuwa sosai don ta fi kowa sanin yadda Humaira ba ta da juriyar yunwa, tun Humaira na daurewa har ya shige uwar ɗaka ta fara kuka, tana jin shigowar Kausar ta yi sauri ta goge idanunta, amma ta makara saboda Kausar ta riga da ta ganta. Duk da yadda abubuwa suka yi yawa akan Lawal bai taɓa gazawa ba wajen ciyar da iyalinsa, yanzun ɗinma akasi aka samu, wajen aikinsa ba su yi musu biya ba na wata biyu kenan, shiyasa abincin gidan ya ƙare gabaki ɗaya. Kausar ta kalle Humaira dake kwance, tace; "Humaira tashi ki rakani wajen customer ɗinmu a kasuwa, ta auna min bashin shinkafa kafin a yi wa su Lawal albashi."

A hankali Humaira ta miƙe saboda yadda take jin kanta kamar ba za ta iya miƙewa ba, cikinta har wani ɗan murɗa mata yake, Ya Kausar dake kallonta tace; "Ko za ki jirani a gida ne, na tafi na dawo." Humaira tace; "Mu tafi kawai."

Suna hanyar tafiya kasuwa Humaira da ta kasa riƙe abinda ke cikinta tace; "Ya Kausar me zai sa ba za ki kira su Yaya Kabir su taimakeki ba? wallahi zama da yunwa babu kyau."

Kausar ta ce; "Humaira ba mu taɓa yin rashin abinci a gidana ba, this is the first time kawai sai na kira gida? Ashe dai ba zan iya rufawa mijina asiri ba kenan? Wannan jarabawace, zan yi ƙoƙari wajen ganin na cinyeta." Har sun kusa da kasuwa Humaira ta ji wani sharp pain a cikinta, durƙusawa ta yi, ta riƙe cikinta, Ya Kausar ta ji wani irin tashin hankali, ta kamo Humairan ta zaunar da ita a dakalin wani shago, tana faɗin; "Sannu, don Allah ki ɗan ƙara daurewa Humaira, yanzu zan samo mana abinda za mu ci, ki zauna a nan ki jira Ni, ina zuwa yanzu." Da sauri Ya Kausar ta ƙarasa cikin kasuwar, Humaira kuwa Ya Kausar na juya baya ta ji ciwon cikin kamar an kunna shi, a dakalin shagon dake rufen ta kwanta tana birgima riƙe da cikinta, wani mutum da ya parking motarsa ta wajen ya tafi siyan kaya a shagon dake across, ya dawo riƙe da kayan zai shiga mota kenan ya gan mutum a kwance tana birgima, ƙarasowa kusa da ita ya yi, ya tsaya a kanta yana faɗin; "Baiwar Allah lafiya?" Hannunta da take riƙe da cikinta dashi ya bi da kallo, yace; "Ciki ke miki ciwo?" Kai Humaira ta gyaɗa mishi hawaye na bin fuskarta.

"Ina gidanku yake?" Ya kuma tambaya.

Da ƙyar Humaira ta iya faɗin; "Babu kowa a gida."

"Mu je pharmacy na siya miki magani to." Mutumin ya faɗa out of sympathy.

Girgiza kai Humaira ta yi, ta cigaba da juye-juyenta. Mutumin nan ya rinƙa kallonta for some seconds sai kawai ya juya ya shiga motarsa, don ya fahimci tsoron bin shi yarinyar take.

Humaira na kwance a wajen ya tafi ya dawo, yadda ya barta haka ya sameta, ledar hannunsa ya ajiye mata a gefe, yace; "Ga magani na siyo miki, na yi tunanin ƙilla ba ki ci abinci ba sai na haɗa miki da abinci. Humaira ba ta ko ɗago kai ba, balle ta nuna ta ji abinda ya faɗa, A hakan Kausar ta dawo ta same su, da sauri ta ƙaraso ganin Humaira a kwance tana riƙe da cikinta, riƙo Humairan ta yi, tace; "Tashi mu tafi gida, na samo mana abinda za mu girka, yanzu za ki saka wani abu a cikinki In Sha Allah." Ledar dake gefen Humairan ta kalla, sai ta ɗago kanta ta kalli mutumin dake tsaye daga gefe yana kallon su, a hankali ta furta; "Ina wuni."

Mutumin ya ce; "Lafiya. Kamar matar Malam Lawal, ko ba ita ba ce?"

"Ita ce." Kausar ta amsa tana ƙoƙarin tuna inda ta san mutumin. Kamar ya san abinda ke ranta sai ya ce; "Makwabcinku ne ni, Alhaji Sani mai bore hole."

"Oh." Kausar ta faɗa don ta gane shi. "Shigo na kai ku gida." Ya faɗa yana kallon Humaira dake kwance, Ya Kausar ba ta yi musu ba, don ba ta da kuɗin abun hawa, kuma ta san Humaira ba za ta iya tafiya gida a ƙafa ba da wannan raki da take yi, ɗago Humairan ta yi, ta ɗauki ledar da ta gani a gefen Humairan, suka bi bayan Alhaji Sani zuwa wajen motarsa, ya buɗe musu backseat suka shiga, shi kuma ya koma driver's side ya shige.

A ƙofar gidansu ya sauke su, Ya Kausar ce ta yi masa godiya, Humaira kam fita ta yi a guje saboda yadda take ji kamar za ta yi amai, Ya Kausar ta biyo bayanta, ta tsuguna kusa da ita tana shafa mata baya, ta kai almost ten minutes a wajen amma aman bai zo ba, sai ta miƙe kawai a hankali ta fara tafiya zuwa ƙofar shiga gidan. Ya Kausar ta koma ta ƙara yi wa Alhaji Sani godiya sannan ta bi bayan Humaira zuwa cikin gidan.

Abincin da Alhaji Sani ya siyawa Humaira, Kausar ta fara bata ta ci, ta sha magani, tana kwanciya bacci ya ɗauketa, numfashi Kausar ta sauke tace; "Alhamdulillah."

A lokacin da Humaira ta farka daga bacci har Kausar ta gama girki, ta kwanta daga gefenta, Kausar na ganin ta buɗe ido ta saki murmushi tace; "Humaira sarkin raki." Murmushi Zahra ta yi, ta rufe fuskarta da hannunta. Kausar tace; "Allah ya baki mijin mai wadata."

Humaira ta ce; "Kin san me Ya Kausar?"

Kausar ta girgiza kai tace; "Sai kin faɗa."

Saukar da ido ta ta yi, muryarta ta yi sanyi, tace; "A lokacin da na shiga damuwa tsantsa, wallahi sai da na yi kwana biyu ban ci abinci ba, amma ko yunwa ban ji ba, ashe dai da gaske damuwa na hana mutum jin yunwa?"

Kausar ta ɗan rungumeta tace; "Tabbas damuwa na kawar da jin yunwa, nuna shaida ce, lokaci da su Ya Kabir suka ce ba zan auri Lawal ba, sai da nima na shafa kwanaki ban ci abinci ba saboda damuwar da na shiga."

Lumshe ido Humaira ta yi, tace; "Allah ka yaye mana dukkan damuwar mu duniya da lahira."

"Aameen. Tashi ki ci abinci kafin ki sume min." Ya Kausar ta ƙarasa maganarta cikin zolaya. Dariya suka fashe dashi a tare kamar ba su ne a cikin wani hali some hours back ba.

#Jikargarba