
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 21
.....emotion. And that is what is causing him trouble again. After they had breakfast, Farida made them tea, bread and an omelette. "Do you have a lot of lectures today?" Ibrahim asked looking at his tablet. "Yes," she answered briefly, "Don't trouble yourself." She just nodded. After they finished they came out together. In the compound, he stopped and looked at her. "She cares." "You too." She answered him calmly and got into his car. He stood looking at her until she left the car. A kind of uneasy feeling came over him again. At school, Zahra parked in front of their department as usual, some students greeted her as she was getting off. "Anty Zahra is dead?" "Thank God." She answered with a smile, "Long time?" She just smiled at them as she passed. From a distance she saw Firdausi and Asiya sitting at the corridor and chatting. Suhaima saw her standing up quickly. "Here Madam!" Asia laughed. "By God, she is glowing today." Firdausi realized from the first look that Zahra was not in a perfect mood. But today she is more controlled. When they entered the hall, the first lecture began. Today is the Statistics Lecturer, he is explaining on the board but half of the students are tire
Book 1 Chapter 21
Washegari sun makkara wajen tashi da asuba, Zahra ta tashi tun kafin Ibrahim ya farka
Na ɗan lokaci ta zauna bakin gado tana kallonsa cikin bacci. Fuskar nan tasa dake cike da nutsuwa kamar babu wata damuwa tare da shi yasa zuciyarta yin wani irin nauyi.... Sai dai yau bata yi kukan data saba ba
A hankali ta miƙe ta shiga toilet tayi alwala, daga baya ta tada shi suka yi sallar asuba tare.
Ko bayan da suka idar babu wata hira tsakaninsu kamar yadda kwana kin baya suka fara
Shi dai Ibrahim yana kallonta lokaci zuwa lokaci kamar yana son ya ce wani abu, amma ya kasa
Zahra kuwa ta mayar da hankalinta kan addu'o'inta.
Da gari ya gama waye wa Zahra ta shirya cikin wata simple but elegant outfit black fitted skirt da milk colour top mai matuƙar kyau, sai hijab ɗinta daya ƙara fito da kyawun fuskarta.
Tun tana shiryawa Ibrahim ke kallonta ta mirror, yau kam akwai wani abu tare da ita . Too calm
Ba irin Zahra ɗin da zata tsaya tana masa hira ko shagwaɓa ba ko kuka bane cikin emotion. Shi kuma hakan ne ke sake dagula masa lissafi
Bayan sun sauka breakfast, Farida ce ta haɗa musu tea da bread tare da omelette.
"Yau kina da lectures sosai?" Ibrahim ya tambaya yana duba tablet ɗinsa.
"Eh" ta amsa a takaice
"Kar ki wahalar da kanki."
Kai ta gyada kawai.
Bayan sun gama suka fito tare. A compound ya tsaya yana kallonta. "Take care."
"You too." Ta amsa masa calmly sannan ta shiga motarsa
Ya tsaya kallonta har ta fita da motar. Wani irin uneasy feeling ne ya sake ratsashi.
A makaranta kuwa, Zahra ta yi parking a gaban department ɗinsu as usual, tana saukowa wasu students ne suka fara gaisheta.
"Anty Zahra ya jiki?"
"Alhamdulillah." Ta amsa da murmushi
"Long time fa."
Murmushi kawai ta musu tana wuce
Tun daga nesa ta hango Firdausi da Asiya zaune a bakin corridor suna hira. Suhaima na ganinta ta miƙe da sauri.
"Ga Madam!"
Asiya ta yi dariya. "Wallahi yau ma glowing take yi."
Firdausi kuwa tun kallon farko ta gane Zahra ba cikin perfect mood take ba. Sai dai yau ta fi controlled
Da suka shiga hall, lecture na farko ya fara. Lecturer ɗin Statistics ne yau, yana ta bayani a board amma rabin students ɗin ma sun gaji saboda lecture ɗin na safe ne, gashi Uban calculations ne
Firdausi na rubutu tana ɗan kallon Zahra lokaci zuwa lokaci.
Zahra kuwa notebook ɗinta a buɗe yake amma gaba ɗaya hankalinta baya wajen lecturer ɗin
Sau biyu lecturer ya kira sunanta saboda tambaya.
"Zahra?"
Sai Firdausi ce ta taɓa hannunta a hankali.
Da sauri ta ɗago. "Yes sir?"
Class ɗin suka yi dariya kaɗan ganin ta yi lost.
Lecturer ɗin ma yayi murmushi. "You seem distracted today."
"Sorry sir." kawai ta iya cewa
Daga haka lecture ya ci gaba, bayan first lecture suka fita break.
Cafeteria suka wuce tare da su Asiya.
Suhaima na ta hira akan wani lecturer da ya kama wata student tana cheating a test, Asiya kuwa na ta dariya.
Sai dai Zahra yau bata wani shiga hirar sosai ba.
Firdausi ce kawai ke lura da ita.
"Ki ci abinci mana," ta faɗa tana tura mata juice.
"Ok." A hankali Zahra ta fara sha.
Can kuma Asiya ta kalleta. "Amarya lafiya dai? Yau kin yi shiru."
Murmushi Zahra tayi. "Just tired."
Suhaima ta ce "Babyn mune ke wahalar mana da ita"
Zahra dariya kawai tayi, daga nan suka wuce masallaci suka yi sallar zuhur tare.
Bayan sun idar ne suka zauna a harabar masallacin ƙarƙashin bishiya saboda iska, dan wannan cikin Zahra nan kamar na son wajen ne
Students na ta wucewa suna hayaniya amma Zahra gaba ɗaya zuciyarta na wani waje daban.
Firdausi ta ɗan matsa kusa da ita. "He texted you?"
Kai Zahra ta girgiza.
"Kin ga? Relax then."
Sai Zahra ta sauke numfashi. "Firdausi... ban san me nake ji ba."
Firdausi ta riƙe hannunta a hankali. "Ke dai ki ci gaba da observing ɗinsa. Mun gama da first step kamar kin dawo daidai shine zaki sake komawa gidan jiya" Zahra bata kuma cewa komai ba
Da lecture na gaba ya shiga Duk suka miƙe suka koma hall.
Har aka gama lectures ɗin ranar, Zahra tana trying sosai ta haɗa kanta, amma duk lokacin da ta tuna messages ɗin wayarsa... sai zuciyarta ta sake yin nauyi.
Bayan sun gama last lecture ɗinsu, Zahra da Firdausi suka fito tare daga hall ɗin.
Yau rana ta gajiyar da students sosai, kowa na ta neman hanyar gida a gajiye suke sosai
A hankali suka isa parking lot ɗin.
Zahra ta buɗe motarta suka shiga.
Tun tana tada motar tayi shiru na wasu mintuna kafin daga ƙarshe ta kasa haƙuri.
"Firdausi..."
"How far?"
"Kin samu wani abu akan Lovie Dovie?"
Firdausi dake danna wayarta ta ɗago ta kalleta.
"Not yet."
Zuciyar Zahra ya tsinke
Sai Firdausi ta ƙara da, "But ina working on it."
"Ta yaya?" Zahra ta tambaya
Murmushi Firdausi tayi. "Ke dai ki bari idan na gama zamu yi magana."
Wannan answer ɗin bai gamsar da Zahra ba, amma ta ga yadda Firdausi ke avoiding magana sosai, hakan yasa ta yi shiru.
A haka ta kai Firdausi gida. Kafin ta sauka, Firdausi ta riƙe hannunta a hankali.
"Please ki kwantar da hankalinki."
Kai Zahra ta gyada mata.
"Text me idan kin isa."
"Toh."
Firdausi ta fita daga motar ta shiga gida.
Zahra kuwa ta ja motarta a hankali ta wuce. A hanya zuwa gidan su, gaba ɗaya tunanin ya mamaye ta.
Ko red light data tsaya bata ma san tsawon lokacin data yi a wajen ba sai da wata mota ta yi mata horn, sai ta ɗan firgita ta tada motar.
Kalaman Pretty suka fara dawo mata kai
"Ni ma dama ba aurensa zanyi ba..."
Sai kuma yadda Ibrahim ke kallonta da soyayya kamar babu wata mace a rayuwarsa. Ashe wasu can yake tare da su
Wani numfashi ta sauke tana jin zuciyarta na mata nauyi.
Lokacin data isa gidan su, mai gadi ya buɗe mata gate cikin girmamawa.
"Sannu da zuwa Hajiya."
Ta amsa masa da murmushi kafin ta shiga ciki da motarta tayi parking
Yau gidan yayi mata wani irin comforting, kamar duk lokacin data zo gida tana samun sauƙin numfashi, sauka tayi Tana sauke ajiyar zuciya
A parlorn ta tarar da Mami zaune tana gyaran wasu kaya yayin da tv ke kunne yan aiki
Da ganin Zahra, Mami ta ɗan yi mamaki
"Zahra?"
Zahra ta ƙarasa ciki tana gaidata. "Ina wuni Mami."
"Lafiya lau." Mami ta ajiye kayan hannunta. "Yau kuma da rana haka Baby?"
Ta zauna kusa da ita tana gyara hijab ɗinta. "Na yi missing ɗinku ne, shine nazo gaishe ku"
Mami tayi murmushi. "Toh ai muma mun fi missing dinki babu yadda muka iya ne"
Da sauri Zahra ta kalleta sosai, sai kuma ta sauke kai kasa
Akwai wani abu tattare da Zahra yau da bai mata ba, wani rin sanyin hali.
"Lafiya dai ko?" Mami ta tambaya
Da sauri Zahra ta gyada kai. "Lafiya kalau Mami"
"Kin ci abinci?"
"A'a."
"Toh tashi ki je kitchen ɗin ki duba abinda zakici."
Murmushi tayi sannan ta miƙe .A kitchen ɗin ma ma'aikatan gidan suka fara gaisheta da fara'a.
Abincin ta zuba, zama tayi ta ɗan ci abinci kaɗan sannan ta dawo parlorn, ta zauna kusa da Mami tana jingina da cushion
Zahra na zaune kusa da Mami tana sauraron hirarta, lokaci zuwa lokaci tana amsawa da murmushi, duk da cewa zuciyarta na wani waje daban
Wayarta na hannunta, tana jiran message daga Firdausi. Can sai suka ji karan buɗe ƙofa
Mummy ce ta fara shigowa parlorn.
Tana riƙe da handbag ɗinta, daga gani yanzu ta dawo daga wani waje.
Da ganin Zahra, ta ɗan tsaya sannan ta yi murmushi.
"Toh toh, amarya ta zo mana ashe?"
Zahra ta miƙe cikin girmamawa.
"Sannu da Zuwa, Ina wuni Mummy."
"Lafiya lau." Mummy ta amsa tana zaunawa "Yau kuma da yamma haka? Kamata yayi tun safe ne zaki zo mana mu wuni"
Murmushi Zahra tayi. "Na yi missing ɗinku ne, amma zan zo na kwana ma idan na gama da project"
"Yauwa, haka nake so. Kar dai mijin ya kwace mana ke gaba ɗaya."
Mami ta yi dariya.
Zahra ma ta yi murmushi. Sai ga Ya Umar ya shigo
Wayarsa na hannunsa, amma yana shigowa ya ajiye ta a gefe
Da ganin Zahra ya ɗan yi mamaki.
"Lallai kuwa... yau muna da babban bakuwa"
Murmushi ya sakar mata "Kanwata."
Zahra ta miƙe. "Ina wuni Yaya."
"Lafiya kalau."
Ya ƙaraso ya zauna a kusa da su sannan ya kalleta.
"Ya school?" Ya tanbaya
"Alhamdulillah."
"Ya lectures ɗin?"
"Alhamdulillah" ta sake basa amsa
Ya Umar ya ɗan haɗe gira."Alhamdulillah kawai?"
Mummy ta yi dariya. "Umar kenan, me zata ce idan ba Alhamdulillahn ba?"
Shima ya yi murmushi ya ce "Ai na saba da ita yadda take bada amsa ne. Da idan ka tambayeta lectures ɗinta sai ta ba ka labari daga farko har ƙarshe"
Murmushi Zahra tayi tace "Lectures muke sha fafa. Mun gama presentation ɗinmu kuma supervisor ya yi mana gyara kaɗan"
"Good." Ya Umar ya gyada kai. "Final semester ɗin nan dai ki dage sosai."
"In Sha Allah."
Ya Umar ya jingina da kujera yana kallonta. "Ya jikinki kuma?"
"Da sauƙi."
"Magunguna fa?" Ya kuma tambayarta
Kai ta gyada. "Ina sha."
"Yauwa."
Mami ta kalle shi. "Tun da ta shigo kai ma tambayoyi kawai kake yi"
Ya Umar ya yi dariya. "Toh Mami ai ina son na san yadda take" kai ta gyada masa
Shi dai kallon Zahra kawai yake yi,gaba daya ta canza a Zahran daya santa, ko hawa online ma ta dena
Ya ce "Ai Yau tunda kika zo gida Banda aikin yi kin shiga uku da magana kuma"
Nan take Mummy ta yi dariya. "Wallahi nima abinda nake tunani kenan, naga bata son magana kaii kuma sai takura mata kake yi, taga ta kwanta yau"
Zahra kuwa murmushi kawai tayi tana girgiza kai. "A'a Yaya, stress ne fah"
"Da kyau." Ya Umar ya faɗa yana ɗan taɓe baki. "Dan idan 'yan maganarki suka dawo ko kallona kar kiyi dan ba zan kula ki ba"
Mami ta ce "Ahtoh tunda shareka ka ma tayi ba!"
Dariya suka yi gaba ɗaya
Mummy na gama dariyar, ta miƙe tana gyara mayafinta.
"Toh ni bari na haura sama, tun ɗazu nake ta zirga -zirga"
Mami ta gyada kai "Ki huta Lafiya"
Mummy ta juya tana kallon Zahra. "Kar ki gudu fah, yau kina nan har dare"
Murmushi Zahra tayi. "Toh Mummy"
Daga haka Mummy ta juya ta haura sama
Bayan tafiyarta, hirar ta cigaba tsakanin Mami, Ya Umar da Zahra.
Ya Umar ne ke bata labarin wasu abubuwan da suka faru an office ɗinsu, lokaci zuwa lokaci Mami na tsokanar sa.
Har Zahra ta samu kanta tana dariya da gaske. Lokaci guda taji damuwarta na vanishing a hankali
A karon farko tun bayan abubuwan da suka dame ta, ta ji zuciyarta ta ɗan sauƙa.
Can bayan la'asar, Mami ta sa aka kawo musu tea da snacks.
Suka zauna a parlorn suna sha suna hira. Ya Umar ma daya dawo a masallaci ya cire takalmansa ya miƙa ƙafafunsa yana jin daɗin yadda yasa Zahra ta sake
"Wallahi gidan nan ya yi shiru idan baki nan," ya faɗa yana kallon Zahra.
Mami ta gyada kai. "Hakane kam, musammam Abbahn ku babu mai damunsa"
Zahra tayi murmushi. "Toh ai zan dinga zuwa kullum idan na gama da school"
Mami ta ce "Halan baki da hankali ne" Dariya sosai Ya Umar yayi, yace once in a while muke son ganinki Malama"
"Yauwa." Mami ta faɗa. "Ko da sau ɗaya ko sau biyu a sati biyu"
Ita dai shiru tayi, can data gaji ta kwanta a kafan Mami, a haka lokaci ya tafi kuma abin mamaki, Zahra bata ma lura yadda lokaci ya tafi ba
Ta manta da damuwar da take ciki na ibrahim da wata lovie Dovie.
Wajen magrib ne aka ji karan buɗe gate, ba jimawa kuwa Abbah ya shigo
Da sallama ya shiga parlorn. Mami ta amsa masa
Ya Umar ya miƙe ya gaishe shi. Zahra ma ta miƙe da sauri.
"Abbah nah"
Murmushi ya yi sosai har ana ganin hakoransa
"Baby na"
Ta sunkuyar da kai tana gaishesa. Ya amsa cikin kulawa kafin ya zauna.
"Yanzu kika zo ?"
Mami ta amsa masa. "Ta zo mana tun bayan lectures dinsu na 12pm"
"Madallah."
Abbah ya kalleta. "Hakan yayi kyau. Kar ki manta gidan nan gidan ki ne ko yaushe kina da ikon zuwa idan da izinin mijinki"
Wani irin taɓuwa zuciyar Zahra tayi. "Na gode Abbah."
Can bayan Insha'i
Aka kawo musu fruits, tea da snacks
Abbah ya shiga ba su labaran wasu abubuwan da suka faru yayin tafiyarsa.
Ya Umar kuma lokaci zuwa lokaci na saka dariya cikin hirar ganin yadda zahra ta fara tafiya duniyar tunani
Har Mami ma ta kasa daina dariya.
Ita kanta ma tana enjoying companyn su but tunaninta ya fara komawa gida, amma kuma tana jin daɗin kasancewa a wajen
Lokaci ya tafi ba tare da ta lura ba. Har karfe 8
Bayan sun gama dinner ne Abbah ya kalli agogo sai kuma ya kalli Zahra.
"Amarya, yau dai kin manta da gidan mijin naki ko?"
Dariya Mami tayi "Wallahi kuwa."
Ya Umar ya ƙara da,
"Ni kam tun ɗazu nake tunanin ko kwana ne tazo mana"
Dariya ta ƙara tashi a parlorn Zahra ma ta yi dariya
Sai dai a zuciyarta... Da gaske ne bata son komawa.
A nan tana jin nutsuwa, a nan babu wayoyi da zata duba da dare, babu messages da zasu karya mata zuciya, babu tunanin inda Ibrahim yake ko wa yake magana da ita
Abbah ya lura da shiru da tayi, ya ɗan kalleta cikin kulawa.
"Lafiya dai ko?"
Da sauri ta murmusa. "Lafiya lau Abbah."
Ya gyada kai tare da fadin "Madallah." Amma ba kadan ba hankalinsa ya tashi
Sai ya jingina da kujera ya ce, "Duk da haka dai, ina ganin lokaci yayi da zaki koma kafin dare yayi sosai."
Wani sanyi ya ratsa zuciyar Zahra. Sai dai ta ɓoye komai da murmushi.
"Toh Abbah na"
Zahra ta koma parlorn ta ɗauki handbag ɗinta
Mami tace, "Toh Fatima, Allah ya tsare hanya."
"Ameen Mami." Ta rungume Mami sannan ta ma Abbah sallama
Abbah yace, "Ki kula da kanki."
"In Sha Allah."
Tana shirin fita ne Ya Umar ya miƙe yana ɗaukar key ɗin motarsa.
"Mu tafi."
Da sauri Zahra tace, "A'a Yaya, ai nazo da mota na"
Yace "Okay, bari na Kai ki"
Nan ma ta girgizaza masa kai
Ya Umar ya harare ta. "Me yasa?"
"Yaya dare yayi ne."
"Dama ni ba dare nake fita ba?"
Murmushi Mami tayi. "Ku tafi kawai."
Zahra tace, "Amma Yaya idan ka kaini ya zaka dawo?"
Ya Umar ya ɗaga kafaɗa. "Zan kira Bolt."
"Yaya..."
"Zahra." Yadda ya kira sunanta yasa ta yi shiru.
"Zo mu tafi."
Daga haka ta bi bayansa har suka sauka.
A hanya kuwa Ya Umar ne ke hira ita kuma tana amsawa lokaci zuwa lokaci.
Sai dai duk da tana ƙoƙarin shiga hirar, zuciyarta na wani irin nauyi.
Tun da safe Ibrahim bai kira ta ba. Bai turo message ba. Bai tambayi inda take ba.
Wannan ne ya fi ɗaga mata hankali, this shows that baya gidan
Ko kuma yanzu ma yana wajen waccan? Ta girgiza kanta tana ƙoƙarin korar tunanin.
Bayan kusan mintuna talatin suka isa layinsu.
Ya Umar ya rage gudu.
Sai dai kafin ya ƙarasa parking a bakin gate ɗin gidan, wata baƙar mota ta shigo layin.
Da farko Zahra bata kula ba.
Amma da motar ta matso ƙarƙashin fitilar layin...
Sai gabanta ya buga da karfi, Numfashinta ya tsaya.
Ibrahim ne zaune a gaban motar. Kuma mace ce ke tuƙa motar.
Wani irin jiri ya ɗan ɗibeta, ta ƙura musu ido.
Matar tana magana, tana dariya har da shafa masa fuska
Ibrahim ma biye mata yake dan ko lura da motar Zahra bai yi ba
Kafin ya ɗago idanunsa, Idonsa ya sauka kan motar Zahra, tare da Ya Umar
Sannan ya ganta Na daƙiƙa guda fuskarsa ta sauya, amma sai ya kau da kansa da sauri, kamar bai ganta ba
Wani abu ya tokare zuciyar Zahra
"Tsaya." Ta faɗa cikin murya mai sanyi.
Ya Umar ya kalleta "Calm down Zahra?" Dan yaga abun data gani
"Tsaya Yaya, ko na sauka"
Da sauri ya taka birki, bai ma gama tsayawa sosai ba, Zahra ta buɗe ƙofa ta fito
"Zahra! Don't gooo" Ya Umar ya fadi da karfi
Amma bata tsaya ba, kai tsaye ta nufi motar
Ibrahim yana ganin tana zuwa, da sauri ya ce 'ki tada motar' ga matar.
Amma kafin hakan ta faru, Zahra ta isa. Ta kai hannu, ta buɗe ƙofar driver ɗin
Matar ta dago da sauri Tana kallon Zahra
Eid Mubarak! Taqabbal Allahu minna wa minkum, Allah maimaita mana. Kar a manga a cinye goron Sallah a jiye 500 na FARASHIN IZZAH