Kenza eBookz
Cover art for KOMAI YA YI FARKO  HAUSA NOVEL 6

Post

KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 6

....."You're welcome." He answered his eyes of the street. When she saw him take the road to their house, she said; "Won't you drop us home first?" He kept quiet and continued driving, she kept her mouth shut and turned her eyes to the road. When they got close to the house before he corrected his voice, he said; "Yesterday I wasn't in a good mood that's why I did that to you, but I truly regretted my actions.' He was silent for a while, then he continued to say; "Mami is angry because of what I did, and she said you are the only one who will make her impatient, that's why I'm taking you to her, give her patience. Intisar smiled and said; "God is king, my sweet Mami." Hunaif was parking in the parking lot of the house, Inti and her friend started to get down, Inti put her head through the window and said; "If you're taking someone out next time, don't come directly from the stadium, go home and sprinkle water before then." She quickly moved forward, so that he didn't even follow her, Zee followed her behind saying; "What did you say to him again?" "Nothing." She answered laughing. Hunaif's body began to tremble, he felt the smell of what he had put on Inti when she said this, but h

Standalone post1,863 words

KOMAI YA YI FARKO

PAGE 6

Babban shopping mall Hunaif ya kai su Intisar, yana parking a harabar mall ɗin, ya ciro ATM card ɗinsa daga aljihunsa, ya miƙawa Intisar, yace; "Zan jira ku a nan, go and get what you want."

Kallon ATM card ɗin ta yi, sai ta saka hannu ta karɓi katin, tace; "Nawa za mu cira?"

"Not more than 1.5M." Ya ba ta amsa.

Zee ta zaro ido jin kuɗin da ya ambata as if is nothing, 1.5M for just few hours shopping, "This guy must be damn rich." Ta ayyana a ranta.

Intisar ta ɗan juyo baya ta kalle Zee, tace; "Let's go Zee." Hunaif ya kalle wacce Intisar ta referring to as Zee ta mirror, sai ya kawar da kansa, ya ɗauki wayarsa ya fara latsawa.

Su Intisar kuwa, suka shiga shopping mall ɗin, shopping sosai suka yi, sun ɗauki almost an hour a mall ɗin kafin suka fito, biyu daga cikin ma'aikatan mall ɗin na biye da su da ledodin siyayyar su. A bag seat gefe ɗaya suka ajiye kayakin, Zee kuma ta zauna a ɗayan gefen. Suna fita daga mall ɗin, Intisar ta kalle shi, tace; "Thanks Yaya."

"You're welcome." Ya amsa idonsa na titi.

Hanyar gidansu ta gan ya ɗauka, sai ta ce; "Won't you drop us home first?"

Shiru ya yi mata ya ci-gaba da driving ɗinsa, baki ta taɓe ta mai da idonta kan titi. Sai da suka kusa da gidan kafin ya yi gyaran murya, yace; "Jiya I wasn't in a good mood shiyasa na yi miki hakan, but I truly regretted my actions.' ya ɗan yi jim, sai ya cigaba da faɗin; "Mami is angry saboda abinda na yi, and she said ke kaɗai za ki bata haƙuri ta hakura that's why I'm taking you to her, ki ba ta haƙuri. Murmushi Intisar ta yi, tace; "Allah sarki my sweet Mami."

Hunaif na parking a parking lot na gidan, Inti da friend ɗinta suka fara sauka, ta window Inti ta saka kanta tace; "If you're taking someone out next time, don't come directly from stadium, ka jeka gida ka watsa ruwa kafin nan." Ta yi sauri ta yi gaba, don kar ma ya biyota, Zee ta bi ta a baya tana faɗin; "Me kika tsaya faɗa masa mishi kuma?" "Babu komai." Inti ta amsa tana dariya.

Hunaif kuwa sunsuna jikinsa ya fara yi, ya ji ko wari yake da ya saka Inti ta yi wannan maganar, aikuwa ya yamutsa fuska. Buɗe ƙofan motar ya yi. Ta ƙofar baya ya bi ya shiga gidan, ya haura ɗakinsa direct. Bathroom ya shiga, ya shiga cikin jacuzzi ya kwanta cikin ruwan ɗumi da ya tara, yana kwance har sai da ya gaji, don kansa ya tashi, ya buɗe hanyar fitar ruwan, ruwan ya fita, sannan ya yi wanka, ya shirya cikin wandon jeans da baƙin T-shirt, ya fito falo yana baza ƙamshi. Ƙamshin da ya ziyarci falon ne ya saka Zee ɗago kanta, aikuwa idonta ya sauka a cikin na Hunaif, kafesa da ido ta yi, ganin irin kallon da take mishi lostly ya sa ya kau da kansa, ya fara takowa zuwa cikin farin, a gefen Mami ya zauna, ya riƙe hannunta ya ɗan matsa, yace; "Hajiya Mami na mu, Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon rai."

Murmushi Mami ta yi, tana jin daɗin irin addu'ar nan da Hunaif ke yi mata, cikin ƴaƴanta duka babu wanda is as caring as Hunaif, idan yana gari akai akai yake shigowa ɗakinta dubota, duk fitarsa kuma sai ya yi mata tsaraba, and he's very observant, a duk lokacin da yanayinta ya canza shine mutumin farko dake ganewa, idan kuma ta shiga baƙin ciki sai ya nema hanyar da zai sakata farinciki, idan dai tace she's the luckiest Mom on earth ma ba ta yi ƙarya ba, don kuwa samun ɗa irin Hunaif is a blessing. Matsa hannunta Hunaif ya yi, yace; "Tunani me kike yi?"

"Ina tunanin wacece za ta zama very lucky ta aure miji irinka, ina picturing family ɗinka a zuciyarsa, Hunaif...I know you will be a good husband and father, Allah ya nuna mini aurenka."

Murmushi ya yi, yace; "Aameen Mami, I'm really working on that, ko don na saka ki cikin farinciki."

Inaya dake kwance tana danna wayarta ta yi gyaran murya, reminding them cewa ba su kaɗai bane a falon, Hunaif ya ɗan harareta, yace; "I can smell jealousy."

Zumɓura baki Inaya ta yi, tace; "Idan wannan ne ai ba yau muka fara gani ba, we're all used it, so their is no jealousy anywhere."

Zee ta rinƙa kallon happy family ɗin da ido, tana admiring ɗinsu a zuciyarta, especially Hunaif da ta gan mua'amalarsa da mamansa da kuma ƙanensa, he's unlike sauran maza da ta saba gani, his is a unique guy.

Miƙewa Intisar ta yi, tace; "Mami za mu tafi, yamma ya yi, Zee needs to go home."

Mami ta ce; "Hakane, kar Maghrib ya yi mata a waje. Thanks for the visit, Yayanki kuma na yafe masa tunda kin nuna min ke mai ɗan uwa, Allah ya yi muku albarka baki ɗaya." Ta juyo ta kalle Hunaif, tace; "Kai za ka kai su?" Girgiza kai ya yi, yace; "Driver ya kai su kawai, Ni na gaji sosai."

"Ok hakan na ya yi." Cewar Mami, ta raƙa su Inti zuwa farfajiyar gidan, ta kira Driver ya zo ya kai su gida, Zee ba ta ji daɗin haka ba, she wished Hunaif ne zai kai su, saboda ta ƙara kallonsa da kyau.

_________________

Humaira na ɗaki ta ji su Bilki na Ihu suna faɗin "Oyoyoyo Ya Kausar." Da sauri ta diro daga kan gado, ta fito tsakar gidan a guje daga ita sai t-shirt da zani, babu kallabi a kanta, kitson calabar da Inna Habi ta yi mata sun sauko har gadon bayanta, ta wani yi tsalle sai jikin Kausar, rungumeta sosai kausar ta yi tana faɗin; Oyoyo Humairan Inna." Humaira jinta a jikin ƴar uwarta sai ta zama very emotional, kawai sai ta fashe da kuka, Kausar ta fara bubbuga bayanta a hankali tana faɗin; "Ya isa hakan, ki daina kukan." Da kyar ta iya lallaɓata ta yi shiru, sannan suka ƙarasa ɗakin Inna, Kausar ta gaisheta kafin suka tafi ɗakin Mama Hafsatu, daga nan suka tafi ɗakin Mama Lantana, a ɗakin suka ya da zango, suka fara hirarakin su. Bayan Sallar La'asar Mama Hafsatu suka fita da Inna, za su shiga maƙwabta taya su aikin biki, gidan ya rage daga Humaira sai Kausar, da su Bilki, Ya Kausar ta kori su Bilki waje su je su yi wasa, ya rage su biyu kawai a ɗakin, ta juyo ta kalle Humaira, tace; "Na ji abinda ya faru dake Humaira, amma ban samu daman zuwa ba sai yanzu, Allah ya sa ba ki yi fushi da ƴar uwarki ba, don na san definitely za ki buƙace Ni kusa dake a lokacin."

Murmushin ƙarfin hali Humaira ta yi, tace; "Ta yaya zan yi fushi dake, bayan ba san ki damu da damuwata, na san tabbas wani abun ne ya hana ki zuwa, kuma yayyun mu maza where by my side." Rungumeta Kausar ta yi, ta fashe da kuka, cikin kuka ta ce; "Amma me yasa kika biyewa su Abba aka yi shiru akan maganar, ya kamata a ɗau mataki akan yaron."

Murmushin da ya fi kuka ciwo Humaira ta yi, tace; "Ba ki kaini son ganin an ɗauki mataki akan shi ba, amma ba mu da wannan ƙarfin, Baban shi mai kuɗi ne, mu kuma talakawa ne, ta yaya za mu fara Shari'a da su?"

Tsaki Kausar ta ja, tace; "It still doesn't matter, mu gwada sa'ar mu, mu kai karar shi, tunda mutanen anguwa da ake tsoron su sani ma duk sun sani yanzu."

Humaira ta sa hannu ta goge guntun hawayen da ya gangaro mata, tace; "Ya kausar ina ganin zai fi idan muka bar shi da adalin sarki, mu bar shi har sai mun je gurin da kuɗin su ba zai yi amfani ba, saboda idan muka yi wani ganganci yanzu ina da tabbacin ɗaya daga cikin mu zai ƙare rayuwar shi a gidan yarin, kife maganar za a yi ace sharri muke masa, idan kuma wani abu ya sami wani a gidan nan ta dalilina ba zan iya yafewa kaina ba."

"Yanzu tsakani da Allah an zalunce mu, kuma bamu da ikon ɗaukar wani mataki." Kausar ta faɗa a sanyaye.

Humaira ta ce; "Babu komai, Allah zai saka mana."

Kausar ta goge hawayenta tace; "Amma babu abinda ke damunki yanzu ko?"

Numfashi Humaira ta sauke, tace; "Idan na ce miki babu abinda ke damuna ma na yi ƙarya." Sai ta ɗan yi jimm, ta kama hannun Ya Kausar, tace; "Wallahi har yanzu na kasa yadda da abinda Kamis ya yi min, yanzu ba damar na fita sai a rinƙa nuna ni, wasu ma suna zargin ba batun rape, daman na saba hulɗa da maza ne kawai yanzu na zo ina wani ƙarya wai an yi min fyaɗe. Ya Kausar... Wallahi ina ji kamar zuciyata za ta fashe, amma bisa dole nake ɓoye damuwata da murmushi saboda kar na rinƙa ta wa su Abba da hankali."

"Ki kwantar da hankalin ki, komai zai wuce kamar ba a yi ba, mutane za su gaji da yin maganar, the won't talk about it forever, ki daure ki cigaba da building rayuwarki yadda zai yi kyau nan gaba." Kausar ta faɗa cikin ƙarfafa gwiwa.

Kai Humaira ta gyaɗa mata, tace; "Nagode."

Kausar ta kuma rungumeta, tace; "Kwana biyar zan yi, idan zan koma sai mu tafi tare, har sai maganar ta daɗa lafawa."

A ranar da Ya Kausar za ta koma, ta yiwa Abba magana akan tafiya da za ta yi da Humaira, da farko bai yarda ba, amma ganin itama Humairan tana son bin ta, sai ya yarda su tafin.

Da Yamma suka iso Nasarawa inda gidan Kausar yake, a lokacin da suka shigo gidan mijin Kausar Lawal na shirin tafiya masallaci, da fara'a ya tarɓe su, ya kalli Humaira cikin zolaya yace; "Iyye su Humaira an zama ƴan mata." Humaira ta ɗan zumɓura baki ta ce; "Shiyasa bana son zuwa gidan nan fa, sai ka yi ta zolayar mutum."

Lawal ya ɗaga hannun sama, yace; Na daina to, idan abinda ya saka ba ki son zuwa gidan kenan."

Murmushi Kausar ta yi, tayi gaba abinta ta bar Humaira da Lawal.

Lawal is a very simple man, bai da damuwa ko kaɗan, kuma yana da son wasa da zolaya.

Tunda Humaira ta dawo gidan Ya Kausar ta fara healing daga damuwarta, saboda sam Kausar ba ta bata damar yin wani tunani, kuma idan ta fita babu wanda ya san abinda ya faru da ita a nan balle su yi gulmarta, sai ta ji kamar kar ta koma gidansu, amma ta san wannan ba mai yiwuwa bane, ba za ta cigaba da zama a gidan ƴaruwarta ba, iyayenta ba za su yarda ta zo ta ƙara zama burden wa Lawal da ba wani ƙarfine dashi ba, he's just a school teacher, a hakan kuma yana da responsibilities ɗin ƙanensa akansa don shine babba, don haka ya zama dole Humaira ta koma gidansu bayan ta ɗan sha iska.

#Jikargarba✍️