
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 31
.....the phone in the bag and she continued walking. When she arrived at the parking lot, she headed towards her new car. Abbah changed it for her after everything calmed down. She went in and turned it on without waiting for some of her friends. She was a little tired and wanted to go home and rest. On the way, another Kira is slowly rising. And she is driving calmly for the first time in months, she feels very peaceful in her heart. She would have reached home. The guard opened the gate for her and she entered the car, she parked, then she came out with her handbag on her shoulder, she went straight to the parlor downstairs. "Peace be upon you." She said. Mummy replied. "Greetings." Then she looked, "Did you finish the iddah yesterday?" Zahra smiled. "Yes Mummy." Mummy nodded. "Well done." Then she adjusted her posture. "Now another husband has come out." Zahra was silent and listening to her. Mummy continued. "But Fatima, stop and make a choice, don't remarry, even if you don't get married in two months, you will be divorced again, you are a girl now, you will be called a little widow" Zahra smiled a little. "I know for us Mummy." She said. "But everyone goes according to their
*FARASHIN IZZAH*
Book 1 Chapter 31
Watanni suka shuɗe... A hankali rayuwa ta fara dawowa Zahra yadda take a da. Ta gama iddarta lafiya.
Ta ci gaba da karatunta ba tare da wata matsala ba, yanzu ma kusan komai ya ƙare
External defense kaɗai ya rage mata, idan ta gama shi kuwa sai jiran sakamako.
Daga department ta fito, a hankali take tafiya, handbag ɗinta riƙe a hannu, gaba ɗaya a gajiye take
Tun safe take zirga-zirga tsakanin offices da supervisors, da ƙyar ta sauko matattakalar department ɗin.
A dai-dai lokacin wayarta sabuwa da Abbah ya siya mata ta yi ƙara, alamar shigowar sako, ta ciro ta daga jaka
Da farko ta yi tunanin wani ne daga classmates ɗinta, amma da ta duba sai ta ga alert ne na ₦1,500,000. Duba Wanda ya turo kudin tayi taga daga Abbah.
Murmushi ya suɓuce mata, ta girgiza kai.
"Wato saboda jiya na gama iddah kenan, Kai Abbah" Ta faɗa a hankali.
Ta san halin Abbah, duk lokacin da ya ji daɗin tayi wani abu mai kyau , sai ya nemo wata hanya da zai faranta mata rai. Ta saka wayar cikin jaka sannan ta ci gaba da tafiya.
Da ta isa parking lot, ta nufi wajen motarta sabuwa. Wadda Abbah ya canza mata bayan komai ya lafa
Ta shiga, tare da kunna shi Ba tare da ta jira wasu ƙawayenta ba, dan gajiya ya mata yawa a jiki, gida take son ta koma ta huta.
A hanya kuwa wani Kira'a ne ke tashi a hankali. Ita kuma tana driving cikin nutsuwa
Karon farko cikin watanni da suka wuce, tana jin salama sosai a zuciyarta.
Da ta isa gida. Mai gadi ya buɗe mata gate ta shiga da motar, ta yi parking, sannan ta fito
Jakar hannunta a kafaɗa, kai tsaye parlorn ƙasa ta nufa Tana shiga ta hango Mummy zaune Batoul na gefenta.
"Assalamu alaikum." Ta faɗa.
Mummy ta amsa. "Wa alaikumussalam."
Sai ta kalleta "Ashe jiya kika gama iddah?"
Zahra ta yi murmushi. "Eh Mummy."
Mummy ta gyada kai. "Toh yayi."
Sai ta ɗan gyara zamanta. "Yanzu kuma saura wani mijin ya fito."
Zahra ta yi shiru tana saurararta.
Mummy ta ci gaba. "Amma Fatima ki tsaya ki yi zaɓe, kar ki sake aure ace ko wata biyu ba zaki cika ba a sake sako-ki, kinga yanzu ke yarinya ce, Karamar bazawara za a fara kiranki"
Zahra ta yi wani ɗan murmushi.
"Na sani mana Mummy." Ta ce.
"Amma ai kowa akan ƙaddararsa yake tafiya ba wanda ya isa ya tsallake abin da Allah ya rubuta masa."
Mummy ta gyada kai. "Eh! Haka ne."
Sai Batoul ta yi wata yar dariya.
"Iyeee! Yau ke ce da wa'azi?" Ta faɗa tana kallon Zahra.
"Ina anan saboda za ki rigani aure kike yin abin da kika ga dama, Har a family ban tsira ba, ana cewa kanwata ta rigani aure. Yanzu kuma me amfanin auren wata biyu wanda ko cika bai yi ba?"
Nan take murmushin Zahra ya ɗan ɓace.
Ta kalleta.
"Whatever, Batoul" Ta faɗa a nutse
"Haka Allah ya ƙaddara min. Sannan ke ma ba ki fi ƙarfin haka ba. Mind you..... Kullum kina gaya min magana. Ina ɗauke kai ne kawai."
Nan take Mummy ta zaro ido tana kallonta da mamaki, kamar ba ita ba
Batoul ta miƙe tsaye.
"What?!" Ta faɗa.
"Batoul zaki kirani?"
Zahra ta ɗan ɗaga gira.
"Dama kin riƙe girman ne? Ai idan ba ki sani ba, yanzu na girme ki a yanayin rayuwa. Ask everyone saboda da kanki kin fada nayi aure kinga ko anan ai na dara miki"
Batoul ta matso kusa da ita "Wallahi zan fasa bakin ki yar iska, shegiya!"
Zahra kuwa dariya kawai ta yi "Dadin abin kin san ubana balle ki kirani da shegiya, sannan kuma gani a gabanki, ki fasa, wallahi kina taba ni zan Rama"
Batoul ta tsaya cak, ta kasa magana na wasu daƙiƙu. Domin ba ta taɓa jin Zahra ta mayar mata da magana haka ba.
Zahra kuwa ta juya tana dariya ta nufi staircase.
Mami da ke saukowa daga sama ta haɗu da ita.
"Zahra." Ta kira.
Zahra ta tsaya.
"Na'am Mami."
"Meyasa zaki biye musu?" Mami ta tambaya.
Zahra ta saki murmushi. "Mami ki ƙyale su. Kullum sai sun gasa min bakar magana. Ina kyale su. Kuma Abbah yace Duk Wanda ya gaya min magana Akan aure na yana baya na dari bisa dari na mayar musu da bakar magana, hakan ne kawai zai sa su rabu da ni"
Mami ta girgiza kai tana murmushi. Ta lura Zahra ta canza fiye da yadda take tunani, ko kadan mutuwar aurenta bai dameta ba kuma ta cire damuwar komai dan har wani haske da kiba ta kara
"Toh je ki cire kayan nan, ki watsa ruwa, sannan ki zo ki ci abinci"
Zahra ta gyada kai.
"Toh Mami."
Daga haka ta juya, ta wuce zuwa ɗakinta
Yayin da Mami ke kallonta tana murmushi a hankali.
A zuciyarta kuwa tana gode wa Allah. Domin duk da abin da Zahra ta fuskanta... Ta sake tashi tsaye.
Mama na zaune a parlorn tayi tagumi, idanunta na kan Ibrahim da ke zaune a gabanta yana danna wayarsa ba tare da wani kuzari ba.
Tun bayan rabuwarsa da Zahra abubuwa suka sauya masa.
Mutanen da a da suke yabonsa a media kuma suke masoyansa, sun juya suna sukarsa. Followers ɗinsa sun ragu sosai. Deals da yake samu ma sun fara raguwa.
Mama ta girgiza kai.
"Ai Ibrahim kai ne ka lalata komai."
Ya ɗago ya kalleta.
"Mama kamar ya kuma?"
Ta ɗan matso gaba.
"Baka iya buga wasan bane. Ni mace ce amma wallahi har na fi ka iya yadda zaka buga"
Ibrahim ya saki ajiyar zuciya.
"Haba Mama. Da na yi yadda kike so ma ai da yanzu wani maganar ake yi ba wannan ba."
Mama ta miƙe tsaye.
"Toh shikenan. Source of income ɗin ya kare ai kenan."
Ibrahim ya yi murmushi.
"Ba komai. Zan koma, zaki kuma sha mamaki"
Mama ta tsaya tana kallonsa sai kuma ta girgiza kai.
"Ai bana jin hakan me yuwa ne, kana tunanin ita ɗin da ka sani ce har yanzu?"
Shiru ya yi.
Mama ta juya ta wuce, ta bar shi da tunaninsa.
A ɓangaren Zahra kuwa... Weekend ne yau
Ita da Ya Umar suna zaune a parlon sama suna hira
Ya Umar na ta ba ta labarin wani abin dariya da ya faru an office. Har dariya take yi tana rike cikinta
Can sai ya kalleta.
"By the way."
Ta ɗago kai "Na'am?"
Yace, "Yaushe kika fita solo date na ƙarshe?"
Ta yi dariya. "Solo date kuma?"
"Eh mana. Kawai ki fita ki yi shopping, ki ci abin da kike so, ki more rayuwarki."
Ta ɗan yi tunani "Gaskiya na daɗe."
Ya Umar ya ciro wayarsa.
"Good." Ya ce, sai kuma ya danyi danne danne
Wayarta ta yi ƙara, ta buɗe, ta bude ido sosai tana kallon alert din ₦500,000
Ta ɗaga kai tana kallonsa "Yaya!"
Yana dariya yace, "Go and enjoy yourself, ki tabbatar kin kashe dukka wannan umarni ne."
Murmushi ya cika fuskarta, ta tashi da sauri ta rungume shi
"Thank you Yaya naaa!"
Ya Umar ya yi dariya. "Get lost."
Washegari da safe Tun da wuri Zahra ta fara shiryawa
Bayan ta yi wanka Ta shafa body mist mai sanyin ƙamshi, ta ɗauki wani elegant wine-colored abaya mai sauƙin ƙyalli, veil dinsa tayi rolling Wani ƙaramin gold wristwatch a hannunta, da matching handbag.
Babu wani make-up mai yawa Sai light gloss da powder kaɗan.
Amma kyau... Kamar an fito da ita daga magazine, ta koma ainahin Famous Zahratyyn ta
Da ta sauko ƙasa. Mami har sai da ta tsaya tana kallonta
"Masha Allah Zahra" Ta faɗa.
Zahra ta yi dariya.
"Thank you Mami, zan tafi solo date, Ya umar ne ya bani 500k na fita wai"
"Anya Zahra? Solo date ne ko bikin aure?"
Zahra ta yi dariya. "Kaiii Mami."
Mami ta karaso ta gyara mata gefen veil dinta
"Allah ya kiyaye hanya, make sure kinyi addua"
"Amin. In shaa Allah" Ta amsa.
Tana shiga parlor taga Abbah, Sai ta sunkuya ta gaida shi da ke zaune yana karanta wani file.
Abbah ya ɗago ya kalleta.
"Enjoy yourself." Ya faɗa.
"Kuma don't be home too early."
Zahra ta yi dariya. "Kai Abbah!"
Ya ɗaga hannu.
"I'm serious. Go have fun."
Ta gyada kai. "Toh."
Tana fita compound ɗin Mai gadi ya yi saurin buɗe mata gate.
Ta nufi sabuwar motarta. Black Lexus ɗin da Abbah ya saya mata bayan ta gama iddah.
Ta buɗe ƙofa, tana shiga ta zauna sai ta ɗan sauke numfashi.
A hankali ta kunna motar. Sai wani murmushi ya bayyana a fuskarta.
A hankali ta fice daga gate, ta hau babban titi.
Wani cool music mai sanyi na tashi a motar, yayin da take driving, Idanunta na kan hanya, amma zuciyarta cike take da wani irin salama
Ta tsaya a wani boutique ta siya wasu kayan
Ta shiga wani store ta ɗauki turare Sai kuma ta wuce wani bookshop.
Domin duk da komai har yanzu son karatu novels na nan a ranta. BBayan ta gama yawon
Sai ta nufi wurin da take son ta zauna Wani upscale garden restaurant, wurin yana da kyau sosai
Flowers a ko'ina, korayen bishiyoyi Da ƙananan fountains da ke zubar da ruwa cikin nutsuwa
Ta yi parking ta fito daga motar.
Iskar wurin ta kaɗa gefen veil ɗinta, wani an murmushi ya sake bayyana a fuskarta.
Ta shiga ciki, wata ma'aikaciya ta tarbe ta cikin mutunci da fara'-
Ta nuna mata wani wuri mai kyau kusa da garden ɗin.
Zahra ta zauna, ta cire wayarta ta ɗora kan table.
Ta yi order na abinci da fresh juice. Yayin da take jiran a kawo mata.
Sai ta jingina da kujera, tana kallon mutanen da ke kai-komo
Ga wani soft music na tashi a hankali tana jin wani irin nutsuwa, lumshe ido tayi
Sai taji kamar an kira sunanta, da farko ba ta kula ba
Sai kuma muryar ta sake zuwa mata
"Zahra..."
A razane ta ɗago kai, hadi da bude idanunta dan jin voice din da ba zata taba mantawa da shi ba
Wani saurayi ne ke tahowa zuwa gare ta
Zaro idanunta tayi waje, ta miƙe tsaye, tana kallonsa
Lips ɗinta suka motsa a hankali "Ahmad...?"
Saurayin ya yi wani irin murmushi "Zahratyyy..."
Yana ƙarasowa gabanta.
Wani irin bugun zuciya ya kama ta, ba tare da ta yi tunani ba
Ta juya da sauri, ta fara tafiya...
"Zahra!" Ya kira
"Please tsaya!"
Amma ta kasa saurarensa, ta ci gaba da tafiya da sauri
Yayin da Ahmad ke bin bayanta yana ƙoƙarin kiranta...
Sai kuma wani abu da ta ji daga bakinsa ya sa ƙafafunta suka fara yin sanyi, ta tsaya cak
Numfashinta ya ɗauke na ɗan lokaci, a hankali ta fara juyowa...
Sai kuma kamar Wanda aka tsikara ta juya ta fita daga wajen da sauri, kamar wadda ta ga abin da zuciyarta ba ta shirya ba
Ahmad ya tsaya a baya yana kiranta, "Zahra! Please just listen to me..."
Amma ko da wasa bata tsaya ba, ta yi sauri zuwa inda ta faka motarta
Hannunta na rawa ta buɗe ƙofa, ta shiga, ta zauna ba tare da ta duba baya ba
Numfashinta na fita da sauri, ta danna start Motar ta yi karan kunnawa, ta fice daga wurin cikin gaggawa
A hanya kuwa... Duk abin da ke cikin motar kamar ya koma nisa, Idonta na kan hanya amma zuciyarta ba ta nan, wani nauyi take ji a ƙirjinta, kamar wani abu ya tashi ya tsaya a maƙoshinta
A hankali ta rika driving har ta shiga cikin unguwarsu Mai gadi ya buɗe mata, ta shiga ta yi parking kai tsaye, ba tare da ta duba ko ina ba Ta fito daga motar da sauri, ta nufi cikin gida
Tana shiga parlorn ƙasa babu kowa, tayi handalah, ta wuce kai tsaye staircase
Ta hau sama da sauri, har zuciyarta na bugawa da ƙarfi
Tana isa ƙofar ɗakinta ta buɗe, ta shiga ciki da sauri
Ta rufe ƙofar da baya, ta jingina da ƙofar
A hankali ta lumshe idanunta Numfashinta na hawa da sauka, ta ɗora hannunta a ƙirji. Zuciyarta na bugawa kamar zata fito waje, tayi shiru sai karar agogon bango kaɗai ke ji
A wannan shiru ɗin ne ta fara jin tunanin Ahmad yana dawowa mata a hankali
Kalaman da bai ce ba, a autin muryarsa da ta yanke mata wata nutsuwarta
Ta buɗe idanunta a hankali.... Sai kuma tunanin abubuwan da suka faru a baya ya shiga zuwa mata, hawaye ne suka shiga tsintiri a fuskanta
Wasa-wasa abin ya zama kamar al'adarsa Kusan kullum sai Ahmad ya zo gidan, amma Zahra ko sau ɗaya ba ta fito ta gan shi ba
Har idan ya haɗu da Ya Umar ma, kasa haɗa ido yake yi da shi shima
Yau ma kamar kullum, Zahra na zaune a parlon ƙasa, wayarta a hannunta tana scrolling Instagram.
Bayan ta gama iddah ne ta fara posting hotunanta a page ɗinta. Ganin yadda ta ƙara lafiya da kiba, ba ta son mutane su ci gaba da tunanin tana cikin damuwa ko kunci, bayan ta rubuta caption din ne ta sake hoton
Sai dai ga mamakinta, tana duba notifications ɗinta ta ga: Ibrahim khalil liked your post.
Tsaki ta ja. Nan take ta shiga profile ɗinsa, ta yi unfollow dinsa. Daga nan kuma ta cire shi daga cikin followers ɗinta.
Wayar ta ajiye gefe.
A dai-dai lokacin Farida ta shigo.
"Anty." Ta kira
Zahra ta ɗago kai "Na'am?"
"Kinyi baƙo."
Ta haɗe gira "Baƙo kuma?"
Farida ta gyada kai. "Eh."
Kai ta gyada "Toh, ina zuwa."
Farida data fita, Zahra ta gyara zamanta sai kuma ta dauki wayanta ta shiga pdf tana kallon chapter 5 na project dinta da classrep ya turo mata
Har kusan minti 15 Zahra tana zaune, har kusa manta da maganar baƙon tayi
Can sai ga Mami ta shigo parlorn, ta tsaya tana kallonta.
"Ana jiranki fa." Ta faɗa.
Nan take Zahra ta ɗago kai sai ta miƙe ba tare da ta ce komai ba, ta haura sama, ta shiga ɗakinta ta ɗauki hijab.
Bayan ta saka shi ne ta fito, a hankali ta nufi parlon baƙi, tana isa bakin ƙofar, ta tura ta ta shiga
Kawai idanunta suka sauka a kansa, zuciyarta ta buga.
Ta juya da nufin fita.
Sai ta ji muryarsa. "Please... ki tsaya."
Kawai ta tsaya cak
"Let's talk."
A hankali ta sauke idanunta ƙasa Hawayen da ba ta san suna taruwa ba suka fara zubo mata, ta ɗaga hannu tana share su
Sai ta ji muryarsa a karo na biyu
"Zahra..."
Shiru ya biyo baya.
Kafin ya sake cewa,
"Zahra, zaki aure ni?
Alhamdu Lillah!! Anan muka kawo karshen book 1 na littafin nan me suna FARASHIN IZZAH
Me son book 2 sai ya biya kudi ta wannan account details din; 7084571222, Hauwa Jibrin, OPay. Shaidar biya ta wannan 08110615256. 500 ne kacal ba tsada
Ko kuma a karanta a arewapen, Nagode.