
Post
SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 2
.....start thinking about the violence that could happen, because of that" He shook his head and said "Oh, God has brought an end to this violence, I pray to God, everything will be peaceful the next day. Are you waiting for me or what?" Ramata looked at him, a tall young man. She bowed her head and said, "After two days, did you look for me?" She turned her head away, she couldn't make eye contact with him. He put his hands together and said, "Be patient, son of God." She smiled and said, "You know, I can't be angry with you." Did he dial quickly?" He looked at the face of the phone, as if he could find something in it and said, "No, calm down, please God, I have a fight.....
SARA SA SASSAƘA...
AISHA ADAM (AYSHERCOOL) YOTA 002
Wannan littafin 1k ne a telegram via 0069685771 Aisha Adam stanbic Shaidar biya ta 08081012143
Page 2
Ganin yadda ta tsaya tana kallonsa, ya sanya shi yin gaba ya bata hanya dan ta wuce. Haka kurum ta ji jikinta ya yi sanyi, kawai ta canza hanya zuwa wata hanyar daban. Tana tafe tana waige-waige cike da matsanancin tsoro, dan gaba ɗaya ba ta yarda da mutumin ba.
Ana tsaka da assembly sannan ta shiga cikin makarantarsu, sai da ta ga ta shiga tukuna, sannan hankalinta ya kwanta ta samu nutsuwa.
****
Tana zaune ta yi shiru, ta lula a duniyar tunani, hankalinta da tunaninta ya yi nisa sosai da duniyar da muke ciki. Daga can sama-sama ta jiyo muryarsa "'Jikar makiyaya hattara, idan shanunki suka yi mini ɓarna, da ke zan tafi a maimakon ɓarnar da suka yi mini" A firgice ta waiwayo dube shi, ta yi ajiyar zuciya. Ya zauna a kusa da ita yana murmushi.
Cikin damuwa da sassanyar muryarta ta ce "Wallahi ka tsorata ni, na ɗauka da gaske ne, har na fara tunanin ɓarakar da zata iya faruwa, a dalilin hakan"
Ya girgiza kai ya ce "Haba dai, Ubangiji Allah ya kawo mana ƙarshen wannan tashin hankalin in sha Allah duk zai zama tairhi wataran. Ni ki ke jira ne ko ya ya?"
Ramata ta dube shi, dogon matashi baƙi. Ta rausayar da kai ta ce "Bayan kwana biyu ko ka neme ni"
Ya lumshe idanunsa yana kallon kyakykyawar fuskar Ramata, mai ɗauke da siririn bille "Kin san ba na son a gano mu ne, kar a samu matsala, amma ki na nan ɗi na" Ya yi maganar yana nuna mata saitin zuciyarsa.
Ta kwaɓe fuska ta ce "Ni na yi fushi" Ta yi maganar tana tura baki, tare da kawar da kanta gefe, dan ba ta iya haɗa ido da shi.
Ya haɗa hanneyensa biyu ya ce "Tuba nake yi, ki yi haƙuri dan Allah hasken rayuwata" Ya yi maganar yana murmushi.
Ta yi murmushi ta ce "Ka san ba zan iya fushi da kai ba ai" Ta yi maganar cikin ƙoƙarin faranta masa rai, duk da matsananciyar kunyar da take ji.
Ta saka hannu ta ɗaukko wayarta da take ajiye a gefenta, ta duba.
Ta dube shi ta ce "An saki sakamakon jarrabawarmu, ka ji yadda ƙirjina ya buga da sauri kuwa?"
Ya leƙa fuskar wayar, kamar zai iya gano wani abu a ciki ya ce "A'a ki kwantar da hankalinki, khairan in sha Allah, ina da yaƙinin za ki cinye duka jarrabawar"
Jikinta a sanyaye ta ce "Allah ya sa, ka san jarrabawa ikon Allah ce kawa. Aikuwa dole gobe in Allah ya kaimu in tafi cikin gari na duba."
Bukar ya dube ta ya ce "Babu wanda zai dubo miki sai kin je har cikin gari da kanki?"
Ramata ta ce "Gara na je da kaina, ba lallai wanda zai je ya iya duba mini yadda nake buƙata ba"
Bukar ya ce "To ko na jira ki a bayan gari mu tafi tare?"
Ta girgiza kai da sauri ta ce "A'a Baffa zai raka ni. Idan kuma Allah bai sanya na duba yanzu ba, sai kuma idan na koma makaranta tun da su can kafe ta ake yi gaba ɗaya, wannan kuma a computer ko waya ake dubawa. Bari na je gida na gaya masa ma, Ubangiji Allah ya sanya sakamakon nan ya yi kyau, na sanya shi farinciki" Ta yi maganar tana tashi tsaye.
Shi ma ya tashi tsayen ya ce "Amin ya rabb, Allah ya sa sauran mutanen ƙauyen nan, su yi koyi da baffanki a kan jajircewa, a yi ta samun yawan wanda za su nemi ilimi."
Jikin Ramata ya yi sanyi ta jingina da jikin bishiya ta ce "Yaya Bukar"
"Na'am Ramata" ya amsa cikin nutsuwa yana kallonta
"Duk da yadda muka shaƙu,na san babu lallai aure ya yiwu tsakaninmu, ka ga a garin nan su na ce mini karuwa, saboda Baffa ya kai ni birni makarantar kwana, kuma na kai wannan shekarun Baffa bai yi mini aure ba. Ga kuma abin da yake tsakaninmu da zuriyarku na rashin jituwa, ba za su taɓa bari mu yi aure ba ko?"
Bukar ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ramata, ki ƙarfafa zuciyarki ki yi koyi da Baffanki a kan jajircewa. Kar mu bar wata gaba da rashin jituwar da ba mu san lokacin da aka fara ba, su hana mana cikar burinmu. Sai dai ban sani ba, ko ba za ki iya aurena ba, saboda ni ba ɗan boko ba ne kamar ke"
Ta durƙusa ta ɗauki sandar kiwonta, ta kalli Bukar ta ce "Karatun boko baya cikin sharuɗan aure, kuma boko ba ta sanya na sauya da komai ba, sai abin da na san ba daidai ba ne"
Bukar ya ce "Gaskiya ne. Muje na taka miki zuwa kan iyaka" suka tafi su na ci gaba da hira.
Ko da ta koma gida, ta shigar da shanun turke, tana tsaka da yi musu hayaƙi, Baffa ya fara ƙwala mata kira.
"Na'am Baffa"
"Wai ke kina 'yar boko amma ba za ki fasa fita kiwo da shanu ba, ba kya gudun a samu matsala ma"
"Baffa ba za a samu matsalar komai ba da yardar Allah, na kula da komai yadda yakamata" Ta yi maganar tana fitowa daga cikin turken.
"Kina dai bawa 'yan boko kunya, ina ɗan boko ina yawo da nagge"
Ramata ta yi murmushi, ta ci gaba da karkaɗe hannunta.
"Idan kin gama, ki zo mu je ki raka ni zan duba marasa lafiya"
"To Baffa"
***** Matsakaicin gida ne, mai ɗauke da 'yan madaidaitan ɗakuna. Wata mace ce take ta kai wa tana komowa a tsakar gidan, tare da wasu 'yan mata su uku, biyu na ta aikace-aikace ɗaya kuma na zaune tana kallon waya tana tsifa. Ta dubi ta zaunen ta ce "Mariya, tashi ki je gidan su Bilal, ki ce idan ta haɗa ƙanzon ta baki ki kawo mini. Sai ki biya ta shagon iliyasu ki karɓo man wanke baki, ki sayo sugar sonake zuwa gobe in Allah ya kaimu zuwa jibi an gama haɗa mata kayan komawa makarantar nan"
Mariya ta tsuke fuska ta ce "Mama wannan makarantar, in dai za ta koma duk sai kin ɗaga mana hankali, kamar ita kaɗai ce 'ya" Ta yi maganar tana harar Nana da take wanke-wanke.
Naja ta yi murmushi ta ce "Kwantar da hankalinki, idan ba za ki je ba, ni idan na gama wanke-wanke na je na karɓo"
"Dama hakan aka yi, da ke da Yaya duk lokacin da ku ka zo hutu, idan za ku koma duk sai ta tashi hankalin kowa, idan kun tafi ma ba ta da aiki sai zancenku"
Ɗaya yarinyar da tun da aka fara ba ta yi magana ba, ta dubu Mariya ta ce "malama ki tashi ki je aiken da aka yi miki"
Mariya ta tura baki tana tashi tsaye.
Mama ta ce "Ai Hafsan ita ce daidai ke, tun da ni kin raina ni. Taho mini da wayata idan ina da ɗan canji na kira yaron kirki na ji ya yake"
Mariya ta fito riƙe da hijjabinta, da wayar Mama ta miƙa wa mama wayar.
Ta karɓi wayar ta daddana, ta saka a kunnenta ta ɗan yi shiru ta ce "Alhamdillah ta shiga"
A nutse ya yi sallama, fuskar Mama ta faɗaɗa da murmushi ta ce "Soja mazan fama"
Tamkar yana gabanta, haka ya risuna ya ce "Mama ina wuni?"
"Lafiya kalau Harisu, ka tashi lafiya?"
"Alhamdillah Mama, ya su Naja ya shirye-shiryen komawarta makaranta kuma?"
"Kana lissafe kenan, Alhamdillah ga shi mu na ta yi"
Harisu ya ce "Ma sha Allah, Mama ku yi haƙuri dai, haryanzu ba a biya albashi ba, na so a biya mu kan ta koma, a ƙarasa mata sayayya, amma Allah bai nufa ba. Ki ba ta haƙuri, idan na samu yadda nake so bayan salary abin da ba a saya ba zan je da kaina na kai mata har school"
Mama ta ce "A'a, ka kwantar da hankalinka ma, na haɗa mata abin da ya samu, kai ma ka kula da kanka, ku na barikin ne?"
"A'a mu na daji fa a yi mana addu'a, ban gaya miki bane kar damu kanki" Kan Mama ta yi magana Mariya ta ce "Yaya dan Allah idan an yi muku albashin ka sayo mini nama"
Hafsa ta ce "Ka ji mahaukaciya"
Harisu ya ce "In sha Allah ko ban samu zuwa ba, zan aiko da shi a saya miki. Mama bani Naja zan yi mata magana"
Mama ta miƙa wa Naja wayar, ta karɓa tare da yin sallama "Hello Yaya"
"Sallama dai ko"
"Yi haƙuri. Assalamu alaikum"
"Wa'alaikum salam, ya shirin koma wa makaranta?"
"Alhamdillah Yaya ya aiki"
Harisu ya ce "Lafiya ƙalau Alhamdillah, ki na ji na Naja, ki yi haƙuri da abin da ya sauwwaƙa, in sha Allah abin da bab zan zo har makarantar na kawo miki. Ku yi haƙuri in sha Allah wataran sai labari zai wuce, za mu zame wa Mama ababen alfahari. Duk wannan wahalar za ta wuce"
Naja ta yi murmushi cikin nutsuwa ta ce "Yaya dan Allah kar ka damu, wallahi ko ban tafi da komai ba, zan ci abincin makaranta na rayu, karatu kuma da yardar Allah ba zan baku kunya ba"
"Alhamdillah barakallah, Allah ya yi mana albarka, ba wa ƙanwata wayar" Ta miƙa wa Hafsa ita ma su ka gaisa, Mariya ma ta karɓa tana ta rashin hankali, wayar ta katse katin ya ƙare.
Soyayya da tausayin da suke nuna wa junansu ba ƙaramin sanya Mama farin ciki yake yi ba, ba ta jin tana damuwa da halin da suke ciki na babu, idan ta ga yadda Allah ya ba ta su shiryayyu.
Harisu kuwa bayan ya ajiye wayar, Suleiman ya dube shi ya ce "Wannan duk ƙannenka ne Haris"
"Eh Oga, ƙannena ne su uku ne Abbanmu ya rasu ya bar mini, su haɗu ma zan ce har da Mamanmu"
"Wow, kai kaɗai ne namiji kenan?"
"Eh nikaɗai ne"
"Allah sarki, Allah ya baka wuyan ɗauka Haris, zan zo Mama ta bani ɗaya na aura"
Haris ya yi dariya ya ce "Girmanka ne oga an riga ma an baka" Ya ƙarasa maganar yana murmushi.
*****
Tun da Alina suka rabu da su Hafsa ta nufo hanyar gidansu, kawai gabanta ya hau faɗuwa, da tuna mutumin nan da take gani, da ta fara tunanin ko mahaukaci ne, yake bin ta. Ta fara addu'a a zuciyarta, da fatar Ubangiji Allah ya tsare ta daga sharrinsa koma wane iri ne shi ɗin. Sai dai ganin har ta shiga layinsu, ba ta gan shi ba, hankalinta ya ɗan kwanta. Sai dai tana sake waiwayawa ta hango shi a ƙofar wani ɗan ɗakin langa-langa, da ke ƙofar wani gida, yana ɗinke takalmi. Ta na tsayawa, su na haɗa ido, ta ji wani irin abu a jikinta. Ya yi mata dabaibayi da manya-manyan idanunsa, da suka surka da kalar ja. A take ta hau tsuma, ta kwasa da gudu ta ƙarasa gida.
Daga cikin ɗakin Ismail ya ji Alina ta faɗo gidan ya ce "Yaya mene ne haka za ki faɗo gida haka da gudu kamar an sako shanuwa?"
Cikin fargaba ta ce "Ni wallahi Yaya wannan mutumin kullum sai na gan shi, tsoro yake bani"
Ba shiri ya fito daga ɗakin fuska a murtuke yana faɗin "Waye shi, me ya yi miki?"
Tana ɗan rarraba ido ta ce "Bai yi mini komai ba, tsoronsa kawai nake ji, kuma kusan kullum sai na gan shi"
"Mu je na ji dalilin da ya sanya yake tsorata ki" Ya yi maganar yana zura takalmansa a fusace.
Anty Nadiya ta ce "Haba masoyi, kamar ba ka san shirirtar Alina ba, ban da shirirta ya za a yi haka kurum kawai ta din ga jin tsoron mutum, ka san ta saba irin wannan rashin kan gadon, kar ka je ta saka ka ji kunya."
Sai kuma ya ɗan sassauta tsuke fuskar da ya yi, ya dubi Alina ya ce "Babu ruwanki da shi, muddin ya yi miki wani abu na rashin kyautawa, kawai ki gaya mini" ta jinjina kai, sannan ta nufi ɗakinta.
Kwanaki biyu a jere, Alina duk lokacin da za ta fita, za ta ga mutumin nan, a ƙofar shagon nan, yana gyaran takalmi. Ta din ga ƙoƙarin koyawa kanta rashin jin tsoronsa, amma ta kasa mussaman idan ta tuna idanunsa, muddin suka haɗu suka haɗa ido, sai gabanta ya yi mummunar faɗuwa gaba ɗaya sai ta rikice. In dai za ta fita har addu'a take yi, Allah ya sa kar ta haɗu da shi. Cikin sa'a yau har ta je makarantar boko, ta je islamiyya ta dawo ba ta gan shi ba, sai da aka taso daga makarantar dare sannan ta gan shi a ƙofar makarantar su. Sosai abin ya fara damunta, ga shi tana tsoron jarabar Yaya, da sai ta sake gaya masa. Ta lura gaba ɗaya yanzu mutumin a layinsu ya tare, da safe zuwa azahar ya yi gyaran takalmi zuwa yamma ta ga ya kasa wani abin daban. A daren ranar ma dai da gudun ta shiga gida, ta laɓe a bayan ƙofa ta daidaita nutsuwarta, sannan ta shiga cikin gidan, dan haka babu wanda ya gane halin da take ciki.
Da safe kuwa tamkar ta ce "Ba za ta je makarantar bokon ba, ko ta ce Yaya ya rakata. Yau ma sai da ta makara sannan ta fita, amma kamar yadda ta yi tsammani, yana jikin gidan da yake kallon nasu, ya zubo wa ƙofar gidan su ido kamar mai jiran tsammanni.
Babu shiri ta koma cikin gidan, tana ɓata fuska da rarraba ido.
Yaya ya ce "Wai me yake damunki ne? Kin makara fa mene ne haka ne?"
Kawai ta fara hawaye "Wallahi Yaya mutumin nan kullum sai na gan shi, tsoro nake ji, na fara tunanin ko gamo na yi ma nikaɗai nake ganinsa, ni tsoro nake ji"
Cikin rashin fahimta ya ce "Gamo kuma? Wai wane ne? Wane mutumin ne?"
Nan Alina ta sake yi masa bayani, tun ranar da ta fara ganinsa.
Tamkar zai dake ta ya ce "Kuma shi ne baki gaya mini ba, uban waye mu je ki nuna mini shi"
Anty Nadiya ta ce "A'a Masoyi, ka tsaya a bi a hankali"
"Ba ruwanki" ya yi maganar yana kallon Nadiya a hasale.
Ya tasa Alina a gaba suka fita.
Ko da suka fita, suka tarar da shi a zaune, yana ta kokowa da wani takalmi zai yi masa round ya gyara shi. Yaya Ismail bai jira komai ba, ya yi fatali da kayan gayarn takalimin matashin, ya damƙi kafaɗarsa ya tashe shi tsaye.
"Malam waye kai? Meye haɗinka da yarinyar nan ka ke bibiyarta?" Ya yi maganar yana nuna masa Alina. Ya kalli Yaya ya kalli hannunsa da ya riƙe shi, ya juya yana kallon Alina da ta yi tsuru-tsuru, tana rarraba ido kamar a ce kyat ta gudu.
"Waye kai malam?" Yaya ya ƙara maganar cikin ɗaga murya, yana ƙara riƙe kwalar mutunin.
"Wallahi ni ba kowa ba ne, kuma ba bin ta nake yi ba" Ya amsa da wata dakakkiyar murya, mai cike da nutsuwa da kamala, tamkar ba daga gangar jikinsa mai ɗauke da wannan yamutsatsun kayan maganar ta fito ba.
"Ƙarya ka ke yi, kusan sati biyu kenan, tana maganar wani yana bin ta, mene ne alaƙarka da ita, idan ma wani abin ne a ranka, ko mugun nufi ne da kai a kan yarinyar nan, wallahi wani abin ya same ta, sai ka zubar da hawaye a kan matakin da zan ɗauka a kanka na gaya maka"
Jiki a sanyaye ya ce "Ka yi haƙuri dan Allah, wallahi ni babu abin da zan yi mata" Ya yi maganar yana ɗaga hannunsa alamar saranda.
Tuni mutane suka fara taruwa, suna tambayar ba'asin abin da ya faru. Maigidan da mutumin yake zaune a ɗakin langa-langar da ke ƙofar gidansa, ya fito yana tambayar hayaniyar me ake yi, aka taru a ƙofar gidansa haka?
Yaya Ismail ya ce "Rana tsaka mun ga mutum yana kwana a ƙofar gidanka, ba tare da mun san waye ba, yana bin Alina, bamu san daga ina yake ba, wallahi aka yi mata wani abin daga kai har shi ba za ku ji daɗi ba. Dan mummunan mataki zan ɗauka a kanku baki ɗaya"
A rikice mutumin ya kalli matashin mai gyaran takalmi ya ce "Me ka yi mata, meyasa ka ke bin ta?"
A rikice ya ce "Wallahi ba bin ta nake yi ba, hanya ce kawai take biyo da ni, sai ta yi zaton bin ta nake yi, amma ba bin ta nake yi ba, ni wucewa kawai nake yi"
Mutumin ya sassauta muryarsa ta ce "Kana ji malam Isma'il, dan Allah ka yi haƙuri, wannan da ka ke gani, almajiri ne kawai ya ɗan zo ci rani ne, aka roƙi na ba shi dakin nan na masu gadina tun da babu kowa, ya zauna tun da yanzu ba ni da masu gadi, kan ya samu gurin zama, amma ina da yaƙinin mutumin kirki ne, ba zai cutar da kowa ba. Ɗalibin Alqur'ani ne"
Yaya Ismail ya sakar masa wuya, yana zazzare ido, tare da yi masa wani irin mugun kallo. Yana sakinsa matashin ya durƙusa yana tattaro kayan gyaran takalminsa, da Isma'il ya yi fatali da su. Gaba ɗaya sai jikin Alina ya yi sanyi, ta yi dana sanin gaya wa Yaya Ismail, ba ta ji daɗin yadda ya ɗauki abun da zafi har haka ba. Sai ta ga kamar mutumin ya muzanta da yawa. Ya ce "Gara dai da na yi magana, tun da mu bamu san wane iri bane kawai ka kawo shi ka ajiye, babu bayani. Wallahi duk abin da ya faru ba zan lamunta ba"
Alhaji Sadi ya ce "Da yardar Allah babu ma wani abu da zai faru sai alkhairi, in sha Allah" Ismail yadube ta ya ce "Wuce muje" ya riƙe hannunta suka yi gaba, ta waiwaya ta ga maƙwabcin nasu na yi wa mai gyaran takalmin magana, yayin da shi kuma yake ƙarasa harhaɗa kayan sa da Yaya Ismail ya watsar, Ya ɗago suka haɗa ido ita , ta yi saurin kawar da kanta suka shiga gida.
MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN.
Ayshercool 08081012143
AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.
Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..
Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.