Kenza eBookz
Cover art for SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 3

Post

SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 3

..... Juma said, "Also, God has not forgotten what he did to me, if he had not given me a child, you would have always put Ramata first and called her the youngest daughter, so that you will be my youngest daughter." Baffa looked at her and his face was a little sad and said, "Oh, Juma, I will make fun of you too, you say that you think so, but I did not make fun of you" Juma turned her face and ignored him. After he sat down on the mat, he opened one of the boxes he had brought and said, "Ramatu, here is the ointment, mouthwash, and other things to prepare for your return to school. She happily said, "Yes Baffana. Baffa, are you praying for me? Our exams have been postponed." Baffa said, "Didn't I tell you that I heard on the radio that the exams have been released? God will not embarrass us, Ramata. If I pray to God, you will become a pride and comparison in this town." Baffa was silent for a while and said, "Ramata, I would like that, because it is the fulfillment of my dream. But you are looking at the stamp that has been made for us in this town, because of the studies you are doing. I know if you can do this, you should stop. Alhamdillah, the beauty will pay for the soap. But

Standalone post4,284 words

SARA DA SASSAƘA AYSHERCOOL

BRIGHT PENS YOTA 002

Arewapen ayshercool

Page 3

Da sauri ya sunkuyar da kansa, sai dai saƙon da ya aika mata ta idanunsa, sun yi tasiri jikinta ya yi sanyi, har ta ɗan rasa nutsuwarta. Da sauri ya tashi ya kwashi kayan aikinsa da ya tattare, ya shige ɗakin da yake kwana ya rufo ƙofar. Gaba ɗaya sai Alina ta ji babu daɗi, a ce babba kamar wannan, Yaya Ismail ya yi masa tijara a gaban mutane, har sai da fuskarsa ta nuna yanayi na damuwa, sai ta ji sam ba ta ji daɗi ba, har ta ji dama ba ta gaya wa yayan ba.

*****

Ramata na tsugunne, tana ta aikin wanki, yayin da Juma ke ƙoƙarin tuƙa tuwo, Baffa ya yi sallama. Suka amsa masa gaba ɗaya. Ramata ta yinƙura ta tashi ta je ta karɓi kayan hannunsa. Juma ta kalle shi ta ce "Sannu da zuwa"

"Yauwwa sannu da gida"

Bayan Ramata ta ajiye kayan ta ce "Baffa sannu da zuwa"

Baffa ya ce "Yauwwa Ramatuna autar Baffa, Ubangiji Allah ya raya mini ke, ya sanya rakiyarmu ta yi tsawo tare"

"Amin Baffana" Ta yi maganar cikin murmushi.

Juma ta ce "Nima Allah ba mantawa ya yi da ni ba, da bai bani haihuwa ba, da kullum sai ka saka Ramata a gaba ka na ce mata 'yar auta, domin ka goranta mini"

Baffa ya kalle ta ya ɗan ɓata fuska ya ce "Haba Juma ya za a yi na yi miki gori ma, ke ce dai ki ke tunanin haka, amma ni ban yi miki gori ba" Juma ta tsuke fuska tare da yi masa banza.

Bayan ya zauna a kan tabarma ya buɗe ɗaya daga cikin ledojin da ya zo da su ya ce "Ramatu, ga man shafawa da man wanke baki, da sauran abubuwa na shirye-shiryen komawarki makaranta na fara sayo miki, sati mai kamawa za ki koma ko?"

Cikin farinciki ta ce "Eh Baffana. Baffa kana yi mini addu'a ko? An kafe jarrabawarmu fa"

Baffa ya ce "Ba nima na gaya miki na ji a radiyo, an sako jarrabawar ba? Ai Allah ba zai kunyata mu ba Ramata, in sha Allah sai kin zama abar alfahari da kwatance a garin nan"

Ramata ta ce "Allah ya amince Baffa. Amma Baffa zan ci gaba da karatun kuwa?"

Baffa ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ramata zan so hakan, domin shi ne cikon burina. Amma kina kallon tambarin da aka yi mana a garin nan, saboda karatun da ki ke yi. Ni na san ko iya haka ki ka tsaya Alhamdillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Amma idan Allah ya kawo damar ki yi karatun, ko bayan raina ne, zan bar wasiyya a abin da na bari, a ware wanda za a biya miki, ki ci gaba da karatu, ko ma ni ma ware da kaina.

Juma ta juyo ta zuba masa ido, daga bisani ta taɓe baki ta ce "Taɓɗi abin na yi ne ashe"

Ba su kula ta ba, Baffa ya sake cewa "Ramata ga wannan saiwoyin, ki dafa su da kyau, gobe in Allah ya kaimu zan je duba mara lafiya"

Ramata ta yinƙura ta tashi tana faɗin "To Baffa"

*****

Alina ce ta shigo da sallama, ta ɗora da cewa "Anty na dawo"

"To sannu da zuwa, ya makarantar?"

Alina ta amsa da "Lafiya ƙalau, Yaya bai dawo ba?"

"Ban da abin ki Alina, dama yana da ƙa'idar lokacin dawowa ne? Amma dai ɗazu ogansa ya kira shi, zai je ya dubo masa wasu kaya, ya ce idan bai dawo ba, mu rufe ƙofa wataƙila sai Allah ya kaimu gobe"

Alina ta ɓata fuska ta ce "Ni wannan ogan nasa ya fiye matsala, ni ba na son wannan aiken da yake yi masa"

Nadiya ta yi murmushi ta ce "Kin fiye rigima ke kuma ba. Alina shi ne babban yaronsa, duk sauran cin amanarsa suke yi. Kuma idan bai je aiken ba da me zamu rayu, tun da a ƙarƙashinsa yake nema"

Jiki a sanyaye Alina ta ce "Antynmu tafiye-tafiyen nan ne da yake yi fa ba na so"

Cikin mamaki Nadiya ta ce "Saboda me?"

"Ba na son bin manyan hanyoyin nan, ba na son ya yi hatsari"

Da sauri Nadiya ta ce "A'uzubillah, wace irin magana ce haka Alina?"

Tuni idanun Alina suka cika da hawaye ta ce "Kullum ya yi tafiya hankalina ba ya kwanciya sai ya dawo, ina jin tsoron ya yi hatsari wataran a hanya. Duk ranar da aka ce babu ke ko Yayana a duniya ya zan yi?" Ta yi maganar hawaye ya wanke mata fuska. "Na san dole hakan za ta faru watarana, amma b a na fatan ku riga ni barin duniyar nan, Allah ya sanya zamu daɗe tare"

Nadiya ta ce "Alina, shi ajali ba sai na kan titi ko na cikin ɗaki ba, yana iya faruwa a kan kowa, sai dai mu yi addu'ar Allah ya sanya rakiyarmu ta yi tsawo tare da juna, kamar yadda ki ke fara. Bari a yi sallar magariba, sai na kira miki shi ki ji muryarsa" Alina ta jinjina kai tana share hawayen fuskarta. Ta nufi ɗakinta Nadiya ta bi ta da kallo, har ta shige, sannan ta yi ajiyar zuciya ta ci gaba da abin da take yi.

Washegari da yamma, Yaya Ismail ya dawo gida, Alina ta rirriƙe shi tana murna har da hawaye. Nadiya ta ba shi labarin abin da Alina ta yi jiya, da ta dawo ta tarar baya nan.

Ya kalli Alina, cike da matsananciyar ƙaunarta ya ce "Ƙanwata, da gaske ki na tsoron na mutu na bar ki?" Ta jinjina masa kai cikin damuwa.

"Aikin gama ya gama, mutuwa dole ce Auta"

Cikin kuka Alina ta ce "Dan Allah ka daina faɗa ba na so, dan Allah ka gaya wa oganka ya daina yawan aikenka guri mai nisa ƙanwarka tsoro take ji" Rungume Alina ya yi yana murmushi tare da rarrashinta. "Babu abin da zai faru sai alkhairi, idan na zauna da ya ya zan kula da ku? Ki yi haƙuri ki din ga yi mini addu'a kin ji ko?"

Ta jinjina masa kai, ta share hawayenta ta ce "Bari na je na shirya, na gaya wa Anty zan je sayo cardboard paper, zan yi assignment"

Ya ce "To a dawo lafiya, ta baki kuɗi ko na ƙara miki?"

"Ƙara mini" Ta yi maganar tana miƙa masa hannu. Ya yi dariya ya zura hannunsa a aljihu, ya ciro ɗari biyar ya bata. Bayan fitar Alina, ya dubi Nadiya ya ce "Masoyiyya ya dai?"

"Alina fa yanzu ba yarinya ba ce ba, lokaci kaɗan ya rage ta shiga shekara goma sha biyar" Ta yi maganar tana tsuke fuska.

Cikin rashin fahimta ya ce "To meyafaru?"

Nadiya ta ce "Ina maganar rungume ta da ka ke yi, wannan ba dai-dai ba ne ba, ba abu ne da ya dace ba"

Ya ƙare mata kallo ya ce "To abin ya motsa kenan, shaiɗan zai yi miki kururuwa"

Ta girgiza kai ta ce "Shaiɗan bai yi mini kururuwa ba, ina dai gudun kai ya yi maka ne"

Ya shafa sumar kansa ya dube ta ya ce "Nadiya, ƙa'idar ba za ta canza ba, a kan Alina, zan iya lalata komai ciki har da ƙa'idar, shi kansa shaiɗai ɗin ya san na fi ƙarfin ya yi mini kururwa a kan Alina. Alina ƙaddarata ce, kuma jarrabawata. Kin san bawa ba ya gujewa ƙaddararsa, a ƙoƙarin gujewa ƙaddarar mutum ka iya halaka ba ki ɗaya. Dan haka dole ki yi haƙuri ko domin gudun halaka. Nadiya ta dube shi cikin ƙunar rai, amma ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba.

Kasancewar ba a daɗe da idar da sallar la'asar ba, rana ba ta gama yin sanyi ba, balle masu zaman majalissa su fara bin dakali da tebura su na zama.

Alina na fitowa hanya, ta tarar da shi a tsaye a bakin titi, hannunsa rungume da bagco yana ƙoƙarin tsallakawa, su na yin ido huɗu, cikin azama ya yinƙura zai tsallaka titi, dan yanzu kamar tsoron ganinta ma yake yi tun da Isma'il ya tijara shi a gaban mutane. Yana ƙoƙarin tsallakawa wani matashi ya taho a kan babur da gudu, ya buge shi. Take ya faɗi, bagco hannunsa ma ta faɗi, yalo ne fal a cikin bagcon, aikuwa ya watse a ƙasa, a kan ƙaramin titin cikin unguwar. Matashin da ya buge shi kuma, ya ja baburinsa ya zura da gudu, ba tare da ya tsaya ba Da sauri Alina ta bi yalon da gudu, ta fara tsintowa, tana sakawa a hijjabinta, saboda yadda suke ƙoƙarin shiga kwata. Sai da ta tsince su tsaf, sannan ta nufo inda yake, a ɗan tsorace ta ce "Sannu" sau ɗaya ya kalle ta, ya sunkuyar da kansa ƙasa.

Ta ɗauki buhun, ta tattare ta zuba masa a ciki. Ta sake cewa "Sun ɓaci da ƙasa sai dai ka wanke. Still ya yi shiru bai ce komai ba. Sai ta fara tunanin ko kurma ne. Sai kuma ta tuna ranar da Yayanta ya je yana yi masa faɗa a kanta ya yi magana. Ta sake cewa "Ko ba zaka iya tashi ba?" Bai ɗago ba ya yinƙura a hankali ya tashi tsaye. Sai dai ya ji rauni a babban yatsansa na ƙafa farcen ya ɗago, sai zubar da jini yake yi. Da sauri ta yamutsa fuska saboda ba ta ƙaunar ganin jini, yanzu hankalinta zai tashi. Ya miƙa hannu zai karɓi bagconsa, ta girgiza kai ta ce "Muje na kai maka" Bai sake magana ba, ya ɗaga ƙafarsa ya fara takawa a hankali. Da kyar yake taka ƙafar, saboda ya bugu, ga jini na zuba. Gaba ɗaya sai tausayinsa ya mamaye ta, da ta kalli ƙafar sai ta yamutsa fuska ta kawar da kanta gefe.

Tana tafe yana biye da ita, ta ja ta tsaya ta ce "Laa ka ga chemist ɗin Albarka ya fito, muje ya duba maka, ko jinin zai daina zuba kar jininka ya ƙare ko tetanus ta shiga ciwon, duk da kwalta ce ba ƙarfe ba. " Ta yi maganar tana nuna ƙofar shagon. Ya ɗan kalle ta, yadda take magana Allah ya hore mata iyayi. Daki-daki take maganar tana demonstration, dai 'yar siririyar muryarta mai kauɗi tamkar tsuntsuwa.

Kansa a ƙasa ya basar ya ce "Ba ni da kuɗi"

Ta ce "Mu je da kuɗi a gurina"

Bai sake cewa komai ba ya bi bayanta.

Da sallama ta shiga, mai chemist ɗin na ganinta ya hau murmushi. "Alinan Yaya, ina Yaya?"

Ta yi murmushi ta ce "Yaya yana gida. Dan Allah ka duba masa ƙafarasa babur ne ya buge shi, kuma ya gudu" Mai Chemist ya tashi yana faɗin Subhanallah.

Ya dudduba ciwon sannan ya wanke masa ciwon, ya yi masa allurai, da magunguna.

Alina ta ce "Nawa?"

"Dubu uku da ɗari biyu" ya bata amsa.

Ta waro ido ta ce "Danƙari, to ka sakawa Yaya a cikin lissafinsa"

Mai chemist ya ce "To amma ki yi masa bayani"

Ta ce "Zan yi masa in sha Allah"

Daga haka suka fito suka tafi, sai da suka je ƙofar ɗakin da yake zama, ya tsaya yana kallon kayansa da ke hannunta, bai ce ta ba shi sai kallonta da yake yi. Ta miƙa masa ya karɓa, ta ce "Ko na kawo maka baho da ruwa ka wanke?" Ya jinjina mata kai.

"To bari na je gida" Ta ajiye kayan, ta nufi gidansu. Ƙasan zuciyarsa cike da fargaba, kuma sai gargaɗinsa zuciyarsa take yi, da tuna irin abin da yayanta ya yi masa, da kuma kashedin da ya yi masa a kanta.

Ba a yi mintuna biyar ba, sai ga ta ɗauke da baho ta shaƙe shi da ruwa a ciki. Yana tsaye yana kallonta, ta ɗauki yalon nan ta juye a bahon duk ta ɗauraye su, ta zuba masa a cikin bagcon sannan ta zubar da ruwan.

Ta yarfe bahon ta dube shi ta ce "Allah ya tsare gaba"

"Amin" Har za ta tafi ta ji ya ce "Na gode" ta tsaya ta waiwaya ta kalle shi, amma jikinta ya yi sanyi, saboda yadda ya tsare ta da manyan idanunsa. Jinjina kai kawai ta iya yi, ta nufi gida.

*****

Ramata na zaune da wayarta a hannunta, ta tattara hankalinta tana sauraren radio a cikin wayar. Tana zaune hannunta riƙe da biro da takarda, ga kuma fitila a ci balbal tana haska mata littafin gabanta. Cak ta tsaya da rubutun, ta ƙara tattara hankalinta a kan sauraren bayanan da mutumin cikin radion yake yi, yadda turawa suka mamayi Afrika. Yadda suka fara zuwa African ta jirgin ruwa, su kan zo gaɓar teku domin yin cinikayya a ƙarni na sha biyar. Su na kasuwancin zinare, hauren giwa da makamatansu. Daga baya aka fara cinikayyar bayi, mussaman tsakaninsu da sarakuna, yadda suke dibar mutane daga Afrika su tafi da su ƙasashen su, su yi musu bauta. Daga bisani a ƙarni na 16 suka fara kafa sansanoninsu, da kawo coci-cocinsu, da Asibitoci da makarantu a Afrika. Suka daina tsayawa a gaɓar teku suka fara watsuwa a cikin ƙasashen Afrika. Cinikayyar bayi da yarjejeniyar bogi, tsakaninsu da sarakunan Afirka, shi ya fara kawo rarrabuwar kawuna a Afrikan tare da kawo koma baya. A ƙarni na 19 alif dubu ɗaya da tamanin da takwas, manyan ƙasashen nahiyar Turai suka yi taro, suka rarrabawa kansu ƙasashen Afirka ba tare da sanin ƙasashen Afrikan ba.

Ramata ta riƙe haɓa, jin an tafi talla. Ta dubi Baffa da yake gefenta yana sauraren radion shi ma.

"Taɓ Baffa"

"Na'am Ramata"

"Tabbas ba a taɓa cin gari har abada ba tare da ɗan gari ba. Ƙulafuci da son zuciyan sarakunan Afrika na ƙarnukan baya, na daga cikin dalilan da ya sanya muke cikin wahala haryanzu, kuma muke ƙarƙashin mulkin turawa ta wasu fuskokin"

Baffa ya yi murmushi ya ce "Ba an ce mun samu 'yanci ba? Kuma duk da haka mutanen wancan ƙarnukan ai sun fi na yanzu wadatar zuci ma da amana. Duk da ni ba wani gane kan wannan abubuwan nake yi ba"

Jiki a sanyaye ta ce "Baffa, duk da ba na nan abubuwan nan suka faru, na san Alƙawarurrukan da turawa suka yi musu, baya rasa nasaba da basu tarin dukiya, ko kuma wani abu da za su amfana ba tare da kallon makomar al'ummarsu ba. Ban da haka ya za ku din ga ɗaukar junanku ku na sayarwa mutanen da ba ma launin fatarku ɗaya ba, daga wani guri suka zo, ba ma yankinku ɗaya ba, alhalin su ba sa sayar muku da na su mutanen, tun a lokacin sun nu na ba su san ciwon kansu ba fa kenan?

Baffa ya kwashe da dariya, ya ce "Ramatu kenan. Ga shi nan sun dawo daga tallan ai, bari mu ci gaba da jin meyafaru"

"Assalamu alaikum " su ka ji an kwaɗa sallama.

Baffa ya amsa sannan ya kalli Ramata ya ce "Maza shiga ɗaki"

Ta tashi tsam ta shige ɗaki, Baffa ya sake cewa "Bismillah"

Tamkar korarre haka ya faɗo gidan, Baffa ya miƙe yana yi masa sannu da zuwa, ya nuna masa gefen tabarmar da yake kai domin ya zauna. Yana zama Juma ta fito kanta da lulluɓi, ta durƙusa ta gaishe shi ya amsa, sannan ya mayar da idonsa kan Baffa.

"Wato kai dai ba zaka taɓa hankali ba ko Jibo?"

Cikin rashin fahimta ya ce "Yaya lafiya kuwa?"

"Ka tambaye ni ko lafiya mana, to ba lau ba. Saboda tsabar ɗan kanka ne kai, mun haƙura mun zuba maka ido kana yadda ka ke so. Ban da rashin mafaɗi har dukiyarka zaka tattare idan ka mutu Ramata ta ci gaba da yahudanci ko? To baka isa ba wallahi. Babu wannan maganar na soke ta. 'ya ce dai tun da ba zaka aurar ta ba, mun zuba maka ido, a garin nan dai ka san babu mai auren ta. Ka ɗauke ta ka kai ta can wata uwa duniya ta yi kwana da kwanaki babu wanda ya san inda take da abin da take yi, babu wanda zai aure ta dan haka sai ka jiƙa ta ka sha"

Baffa ya kalli Juma, ta tsuke fuska tana kawar da kai. Ya girgiza kai ya ce "Yaya haryanzu ba ku fahimci manufata ba, ana ta samun ci gaba a duniya, mu mu na guri ɗaya duk a dalilin rashin ilimi. Ko mulkin kama karya da ikon da ake yi mana a garin Yelwa rashin ilimi ne ya haddasa mana shi."

"Ni rufe mini baki, 'yan bokon ba su ne suke kashe-kashe ba, suke mulkin ƙasar gaba ɗaya ba, wane zalunci ne su ba sa yi. Sau nawa ana kai ƙorafin abin da yake faruwa a garin nan, amma su ke goya musu baya. Wallahi idan baka yi wasa ba, yadda ka fifita yahudanci a kan aurar da Ramata, sai ka zubar da hawaye a dalilin bokon nan, sai ta zame muku masifa daga kai har ita"

Ras gaban Ramata ya faɗi, jin yadda ɗan uwan mahaifinta ke janyo musu jafa'i ga shi dattijo. Ta jingina da jikin katangar ƙasar da ke ɗakin, zuciyarta na bugawa da sauri. Baffa ya ce "Ba za a yi haka ba in sha Allah, Alkhairi za ta zame mana baki ɗaya"

"Wannan kuma matsalarku ce" Ya tashi ya kaɗe rigarsa ya fice.

Baffa ya dubi Juma ya ce "Kin kyauta, na gode sosai da sosai" Ta tashi sumi-sumi ta wuce ɗaki tana ƙunƙuni.

****

Ko da Alina ta taso daga makarantar dare, ba ta ga mutuminta ba, ta yi ta tunanin ko ya ƙafarsa, ko ya warke? Haka ta yi ta saƙe-saƙe, har ta koma gida. Daga nan sai da aka kwana biyu, sannan ta sake ganinsa. Sai dai kan ta ƙarasa inda yake ta yi magana, ya shige ɗakinsa. Duk sai jikinta ya yi sanyi.

***** Danƙareriyar mota ce ƙirar higlander take ta zuba gudu, sai dai jikin motar babu lamba. Yana zaune a bayan motar, fuskarsa a rufe da rawani, sai idanunsa kawai ake iya gani. Sai rarraba idanu yake lokaci zuwa lokaci, wasu lokutan kuma sai ya sunkuyar da kansa ƙasa yana duba agogon hannunsa. Check point suka tarar a hanya, wanda tilas direban motar ya yi slow, ya ja ya tsaya. Sojoji ne su uku a a check point ɗin, ya yin da wasu ke zaune a cikin mota, babban cikinsu ya ƙaraso, ya kalli direban ya ce "Daga ina?"

Direban ya amsa da "Maigida ne ya aike mu"

"Waye mai gida?"

"Lamba ɗaya"

A ɗan hasalae sojan ya ce "Malam ka yi mini bayani, daga ina kuma ina za ku je? Sannan suwa ka ɗaukko, ga motar ta ku babu lamba, kai ba ku da gaskiya."

A hankali ya sauke gilashin motar, ya yi wa sojan alama da ya ƙarasa. Ya ƙarasa daidai tagar yana son ganin fuskar mutumin. "Kacalla Sumale, shugaban manyan ƙungiyoyin ta'addanci na yankin nan, da ku ke nema babu dare babu rana, shi ya aike ni. Manyanku sun saka a ɗaukko ni domin wata yarjejeniya" Ya yi maganar yana ƙare wa sojan kallo, ya sauke rawanin fuskarsa, kyakykywar fuskarsa fari sol ta bayyana.

Ya sake duban sojan ya ce "Ka buɗe mini hanya zan wuce" Sojan ya ɗana bindigarsa yana ƙarewa fuskar matashin kallo. Shi ma matashin ya tsare shi da nasa idanunsa da suka da kalar ja. Ba tare da ya ɗauke idanunsa daga kan sojan ba, ya ciro wayarsa ya daddana, ya saka ta a hansfree.

Daga cikin wayar wata murya ta ce "Ya aka yi ne?"

"Ka janye mutanenku sun tsare mini hanya, ko kuma su riga rana faɗuwa" Waro ido sojan ya yi, jin muryar mai maganar, saboda duk wanda yake cikin battalion ɗin su, babu wanda bai san wannan muryar ba.

"Argungu are you with me?"

Cikin rawar murya ya ce "Yes Sir"

"Clear the road"

"But Sir"

"I said clear the road"

"Ok sir" Tamkar soko haka ya ja da baya a hankali, yana kallon motar. Ya yi wa sauran alama da hannunsa, suka buɗe hanya motar ta wuce.

*****

"Alina, wai bacci ki ke yi da la'asar ɗin nan?"

Alina ta amsa da "A'a idona biyu" ta fito tsakar gida ta ce "Saƙa nake yi, safa da hula zan saƙa idan ki ka haihu mu saka wa jaririyar"

Nadiya ta yi murmushi ta ce "Alina kenan. Kin ga gobe in Allah ya kaimu litinin ki zo ki kai wankin takaliminki, ga nawa ki haɗa da shi a yi mini round, na yi wa Yaya maganar ya manta"

Alina ta ce "To bari na saka hijjabina" Ta yi maganar tana ɗan yin hamma, sai kuma ta katse hammar da ta tuna mutumin nan da ko sunansa ba ta sani ba yana gyaran takalmi. Da sauri ta janyo hijjabin ta zura, ta ɗauki takalman ta fita. Sai dai baya gurin da yake zama, dan haka ta je ƙofar ɗakin da yake kwana cikin tsoro, ta fara bugawa.

Har ta sare ta fara tunanin baya nan, kawai ta ga ya buɗe ƙofar, sai da ta razana ta ɗan ja da baya tana kallonsa. Ya ƙura mata ido, a ɗan rikice ta ce "Ahh da..da..dama gyaran takalmi na kawo maka" Ta yi maganar tana nuna masa takalman hannunta.

Ganin ya tsaya yana kallonta, ya sanya ta sha jinin jikinta, tsoro ya ƙara bayyana a fuskarta. Kawai ta ga ya koma, ta tsaya sororo tana kallon ƙofar, har za ta juya ta tafi, ta ga ya sake buɗewa ya fito da kayan gyaran takalmin. Ta yi ajiyar zuciya ya samu guri ya zauna, ta gaya masa abin da zai yi wa takalman, sannan ta koma gefensa kan dakali ta zauna. Ya duƙufa yana wanke takalmin, ya din ga jujjuya takalmin Alina, tomes na 'yan makaranta baƙi, mai tsadar gaske. Ta ɗan zuba masa ido, haka kurum ta ji tana son ta ga fuskarsa, amma ya tara uwar ƙasumba dogon hancinsa kawai ake iya ganewa sai manyan idanunsa da suka fi komai razana ta. Bayan haka ga wata uwar hula da yake sakawa a kansa ya rufe, ga uban kwalli da yake rambaɗawa a idonsa. Kayan jikinsa sun sha jiki, dark bluen yadi ne a jikinsa, amma ya koma sky blue saboda tsufa.

"Ciwonka ya warke?" Ta yi maganar ba tare da ta shirya ba.

"Ya warke" Ya faɗa a taƙaice.

"Allah ya ƙara sauƙi, ya kiyaye gaba"

"Amin" Yayi maganar yana ci gaba da abin da yake yi ba tare da ya ɗago ba.

Ya gama gyaran takalmin, ya wanke mata nata, sannan ya miƙo mata. Ta karɓa ta ɗan yi murmushi ta ce "Kai ya naga takalmina ya koma sabo? Wannan ƙyallin ai sai na gano fuskata a ciki saboda kyau da sheƙin da yake yi" Ta yi maganar tana ɗaga takalmin tana kallonsa. Ga mamakinta sai ta ga ya ɗan kalle ta ya yi murmushi.

Ita ma murmushin ta sake yi sannan ta ce "Nawa ne?"

"A'a ki bar shi"

Alina ta ce "A'a ai sana'a ka ke yi, Yayana ya ce a duniya kar ka zalunci mai sana'ar hannu".

Ya ce "Idan kin kuma kawowa sai ki biya"

"To Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata, idan su na raye Allah ya ja kwanansu"

Ya amsa da "Amin na gode"

Ba ta kai ga tashi ba, sai ga Isma'il ya shigo layin a kan babur, idonsa na sauka a kansu, ya tsuke fuska kamar ya ga bala'i...

1k ne a telegram via 0069685771 Aisha Adam stanbic. Shaidar biya ta 08081012143 Ayshercool 08081012143.

AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.

Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..

Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.

MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN