
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 11
.....for the privileged few, then the blacks also belong to the privileged few. Here comes the colorful sauces and drinking bowls. Then when we are grown up, the mother's daughter is separated from the side of God, the mother is separated from her mother. Each corner is covered with beautiful carpets, then curtains. Then it was a good harvest and the fulanis who had drunk tarde and the women were put in ropes and hanged, and the land was also given to Allah. You don't talk, the bride's roommate hears everything, you look at the bride's room. The only thing that God knows is the one who saw it. You're all jealous when you see that this room is filled with Ai'shatu's clothes. They were finishing up at night and the bride was brought back, and her family all came back and the celebration continued after they were fed two big lambs in a row. The next morning is the opening day, and the day of the festival will start, all the guests will pass, especially the little ones. The white rice was cooked, and the bride took a bath today. Since she was brought, she did not change her clothes. She did not take a bath. She still hasn't put Abdul-Rasheed in the eye of tobacco, so he didn't see her.
......Washe gari an cigaba da shan biki a Bauchi, dan anyi wankan ango da ajo ɗinsa. Amarya kuwa babu wanda zai ce yaga fuskarta sam dan ko wajen wankan ango da ajo bata leƙo ba tana ɗaki ƙunshe. Hakan kuwa shine dai-dai kuma shine ɗa'a. A ranar kayan amarya suka iso dan su sai washe gari aka taho dasu. Gidanta dake nan jikin gidan sirukanta da sauran ƴan uwansa aka sauke, sauran kayan gara kuwa gidan su abdul-rasheed. A take danginta suka koma can aka hau jere, aka barta da ƙawayenta ita kuma anan gidan. Ɗakin amarya yayi ƙyau. Iyayenta sunyi ƙoƙari sosai. Gado ne guda biyu, babba mai rumfa na miji, sai ƙarami nata. Mai rumfa yasha ƙatuwar katifa da zanin gado harda rumfarsa ta sama da filo har goma sha biyu ciff, aka saka masa labule da ake kira (Zarge shige🤣). Dan haka gadon yay ɗas kamar ka zauna kaita kallo. Itama dai natan an saka katifa da zanin gado mai ƙyau, sai kabot da ya sha jeren fantekoki a sama da kwalloli, sai kanta a cike da tasoshi ƴar girke dake ta ƙyalli da ɗaukar ido na ƴar gata, sai tangarare suma na ƴar gata. Ga languna tuwo da miya kala-kala da kwanon sha. Sai kumbo manya anyi nasu dankin uwa ta raɓe suma a gefe masha ALLAH, ga uwa ta raɓe ta fantekoki masu murtala. Kowace kusurwa an buga darduma masu ƙyau, sai labule. Sai gansarwa na garar kaka da ƙoran fulani da suka sha tarde da ludaye a cikin an sakasu a ragaya aka rataye, ledar ƙasa ma an baza masha ALLAH. Kai abunfa ba'a magana, dan ɗakin amarya sai sambarka komai yaji, kaida ka gani kaga ɗakin ƴar gata. Abin dai masha ALLAH sai wanda ya gani. Dan duk hassadarka kai kana ganin wannan ɗaki kasan an zubama Ai'shatu kayan ƴar gata. Suna kammalawa zuwa dare aka dawo da amarya nan, suma dangin nata nan duk suka dawo aka cigaba da shagalin biki bayan an dire musu raguna manya guda biyu na jere. Washe gari buɗar kai, ranar kuma biki zai tashi, baƙi duk zasu wuce musamman ma ƴan kano. An dafa farar shinkafa, sannan amarya tayi wanka yau, dan tunda aka kawota ko kaya bata canja ba, batayi wanka ba kuma, idan kaga ruwa ya taɓa jikinta sai na alwala. Har yanzu bata saka Abdul-rasheed a idon taba shima haka bai ganta ba. Tunda safe aka fara mata kitso ƙana-ƙana masu ƙyau, sun jima sunayi dan har zuwa azhar sannan suka kammala aka haɗa mata ruwa da yaji turarruka da addu'oi ta shiga wanka da kanta. Bayan wani lokaci ta fito, an bata kaya ta canja, atamfa mai tabarma da akaima ɗinki mai ƙyau irin na wannan zamanin, yau dai gyale aka bata ta yafa ba zani ba, sabon takalmi sai tsakiyar wuya mai ƙyau tanata sheƙi. Sosai hankalinta a tashe yake, dan yan uwanta duk sun kammala shirin su, ana gama buɗar kai zasu wuce. Gida ya cika taf, dangin ango duk sun dawo nan suma. An fara yin rabo irin na al'ada ga dangin miji, bayan kammalawa ne aka fito da amarya dake lulluɓe cikin gyalenta, har yanzu dangin miji dama ƴan gari babu mai cewa ga kamaninta. Sabuwar tabarma aka shimfiɗa aka ɗora sabuwar kujerarta ƴar tsugunno a kai, ta zauna. Shinkafar nan da aka dafa fara sai gishiri kawai a cikinta, amma fa tasha mangaɗa ƙyallan aka juyo a ƙaton bangaji aka ajiye gabanta. Tana lulluɓen aka kamo hannunta biyu aka fito da su, ta haɗesu waje guda kamar mai addu'a aka cika mata shi da shinkafar nan taf. A baki ta saka, sai dai babu batun taunawa ta furzar a gefenta na dama, ta ƙara cika baki ta furzar a gefenta na haggu, ta karshe ta furza a gaba, sauran ta watsata baya. Daga nan ne fa aka shiga rangaɗa guɗa, masu kiɗan ƙwarya suka fara. Bayan an gama cashewa da kiɗan ƙwarya koma muce ana cikin cashewar iyaye a cikin dangin ango suka kwashi kayan da aka basu na baye suka koma gida, aka sake shirya amarya itama aka bisu da ita can hannunta riƙe da ƙwarya mai ƙyau. An fara kaita ɗakin Inna dake matsayin uwar mijinta a yanzu. Inna tayi addu'ar zaman lafiya, ta kawo kuɗi jaka biyu ta saka mata a ƙwaryar, danginta sukai godiya aka fito, daga nan sai ɗakin marigayiya mahaifiyar Abdul-rasheed, inda danginta suka fanshi nata, ba'a nan aka tsaya ba, sai da akabi iyaye kaf, dangin uban miji dana uwa. Kafin kace mi sai ga kuɗi shimili amarya ta tara a wannan ƙwarya, dan har makwaftansu da ake zumunci irin na mutuntawar mutanen da, makwata iyaye ne ba abokan gaba ba, nan ma sai da aka kai amarya, daga nan ne aka sake baidata gidanta inda yara da ƴammata ke cigaba da cashewa da kiɗan ƙwarya. An maidata ɗakinta, aka saka wasu cikin ƙannen ango suka zauna da ita, suko ƴan kano cikin hikima suka zare jikinsu duk suka gudu batare da amarya daketa kukanta ta farga ba. Balle kuma masu kiɗan ƙwarya na wasansu har magriba. Sai bayan sun tashi ne gida ya fara komawa tsit A'isha ta fahimci da kaf yan uwanta babu. Sosai ta ƙara ƙarfin kukanta, ƙannen ango dake tare da ita har lokacin na lallashinta. Zuwa bayan sallar isha'i an tafi an bar amarya ita kaɗai a ɗakinta tanata kuka, sai daga baya aka turo mata wasu ƴammata huɗu su zauna da ita saboda zuwan anguna. Babu jimawa kuwa ango da abokansa suka yo masa rakkiya cikin girma. Ƙawayen nan sune suka amsa, dan amarya na can ƙarshen bango ta rakuɓe ƙudundune cikin gyale. Anyi gaisuwa tsakanin ƙawayen amarya da abokan ango, ƙawayen amarya suka gabatar musu da abinci. Kwanika ne guda biyu dake a saman tire ɗin kwano da kwanon sha dake cike da ruwa an rufesu da tuma ƙasa (😂Azo gaya min minene tuma ƙasa akwai kyauta). Gefe suka koma su kuma abokan ango suka naɗe hannayen riga suka fara ɗibar girki, gefe kuma suna hira da ƙawayen amarya. Bayan sun kammala akai sayen baki, anyi ƴar jayayya akan kuɗi, daga ƙarshe dai suka ajiye musu jaka huɗu. Ita dai amarya na nan a gefe kamar ma bata san bikin da ake ba a ɗakin, kukanta take dai kawai. Abokan ango sunyi nasiharsu ga amarya da ango, tare da addu'a. Daga haka suka miƙe tare da ƙawayen amarya sukai musu sallama suka wuce. Abdul-rasheed ya miƙe dan rakasu Nasiru ya maida shi ya zaunar yana faɗin, “In dai mune mun huttasheka, zauna ka lallashi min ƙanwa sai munzo maka tausa”. Daga haka suka fice suna dariyar kalmar shaƙiyancin Nasiru. Abdul-rasheed ya bisu da kallo kawai yana murmushi. Bayan fitar tasu ɗakin ya kasance shiru na fin mintuna uku, dan haka kawai shima Abdul-rasheed ɗin sai yake jin kansa wani iri tamkar ba shi ɗin ba. Yau ALLAH ya cika masa burinsa ga shi ga masoyiyarsa dai a tare da shi. Itako har yanzu kukanta take mai fita da sauti kaɗan da shashsheka. A hankali ya miƙe yana mai tattare babbar rigar jikinsa ya cire gaba ɗaya, saman gadon mai rumfa ya ɗaga labulensa ya ajiyeta sannan ya taka zuwa inda take zaune a maƙure tsakanin gado da bango. A nan ma ɗan tsayawa yay kanta yana kallo na sakkanni, kafin ya kai tsugunne gabanta ya ɗaura hannunsa kan nata dake riƙe da gyalen da take lulluɓe a ciki. Ɗan zabura tai na tsorata, dan haka ya saki hannun nata, sai kuma cike da tausasawa ya furta, “Ha Giwar mata, kukan ya isa haka mana. Yau fa rana ce irin ta farin ciki gaki ga Abdul-rasheed ɗinki, kwana da kwanaki an hana min ganinki kewa na neman kaini ƙasa. Bana son kukan nan yana ɗaga min hankali da sukar zuciyata, kiyi haƙuri ki daina yinsa. Ina sha ALLAHU na miki alƙawarin zan kwatanta daga ƙoƙari irin na Inna a gareke, bazan barki kiyi doguwar kewa ba ko yin kukan rashinta a kusa dake. Zan yi ƙoƙarin maye miki gurbin su Bashir, haka kuma zan maye miki gurbi na ƙawayenki. Zan zama adali mai ƙoƙarin sauke nauyin da ALLAH ya ɗora masa na maye gurbin damuwarki da farin ciki, kukan ki da dariya. Kin san ina sonki matuƙa A'ishatu, ba kuma zan daina ba har na koma ga UBANGIJI na in sha ALLAHU”. Sosai kalamansa ke tasirantuwa a zuciya da gangar jikin ta, dan haka a hankali ya fara sassauta kukan nata. Da wannan damar yay amfani wajen bata umarnin miƙewa. Babu musu ta miƙe ɗin, dan a nasihar da tasha an tabbatar mata biyayya ga miji shine nasararta kuma wajib ne in har ba akan saɓon ALLAH ba. Sai dai fuskata na rufe a gyalen baya gani komai na jikinta sai hannu da ƙafafu ta ƙasa. “Je kiyi alwala muyi sallar godiya ga UBANGIJI”. Nan ma bata musa ba akan umarninsa. Haka ta nufi hanyar fita waje ta ɗauki buta a ƙofar ɗaki, tsaidata yayi tare da takowa ya miƙa mata Torchlight ta ƙarfe da ake ma zubin batira. Ganin ba ganinsa take ba ya kamo hannunta ya saka mata a ciki, kamawar data sakata ƴar zabura kamar ɗazun. Har ma abin ya saka Abdul-rasheed sakin murmushi. Sai kuma cike da zolaya ya matsa jikinta sosai, cikin raɗa a saitin kunenta ya raɗa mata, “Ayi haƙuri a buɗe fuskar kar amarya ta ɓige da faɗuwa ko bige goshi a bango”. Murmushi ta saki a karo na farko, sai dai bai gani ba dan ba ganin fuskata yake ba. Amma yanda ta juya da sassarfa yaji a ransa ta murmursa ɗin. Shima sai yay murmushin sosai yana binta da kallo. Kafin ya koma cikin ɗakin yana bin jeren da aka tsantsara musu da kallo daki-daki. Komai ya masa ƙyau, ya kuma ƙayatar da shi. Yana nan a haka harta dawo, baiyi magana ba ya amsa fitilar shima ya ɗauka butar ƙarfe ya fita domin yo alwalar..........✍🏼
*_Ayi haƙuri da jina shiru kwana biyu, an yi mana haihuwa ne bana samun zama shiyyasa. Naga kuma zan raba hankalina biyu sai kawai nace bara dai ayi suna sai mu dawo gaba ɗaya.😀🙏_*
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 12_
__________________
https://chat.whatsapp.com/Kf6jd57OsXHCG7cODNAje6
*_Kowace mace na matuƙar son taga ta gyara kitchen ɗinta kodan ta kalla itama taji daɗi 💃_*
*_Dunƙule kuɗin ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_*
*_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_*
*_To kwantar min da hankalinka ƙawata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sauƙi da rahusa._*
_Ta buɗe adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da daɗi, akan farashi mai sauƙi, kaya ƴan zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._💃💃
*_Za'a fara zubi 25th October in sha ALLAH 💃_*
20k monthly kayan 100k 10k monthly kayan 50k
*_Arha tafi bashi, hakama adashe yafi bashi. 💃 Ga sauƙi abaka tamkar ƙyauta 💃💃😀_*
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________