
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 20
..... a healthy person for the privilege of parents and grandparents, he grew up a quiet child, who loves to read and ask questions. His wisdom is older than his years, as long as he is not noisy. He was five years old, suddenly in the middle of Aisha's pregnancy, he came and saw the joy of Abdul-rasheed and Yakura, their father, two months into Aisha's pregnancy, Yakura also started her own marriage. Just as Aisha got pregnant, she gave birth to a boy this time too, who looks like Abdul-Rasheed too. Ansha, a young boy named Ja'afar. After two months and two days, Ja'afar also left Yakura, and she also found a man who looked like Abdul-Rasheed, and he also said that they were called Ma'aruff. Haysam is very happy to have a younger brother who grew up like twins, and they are called twins. Su Ja'afar named Haysam for a year and sent him to school, and his son was six years old. Although before he even started school, he started taking lessons from his father and Aisha and Yakura. Abdul-Rasheed's son is standing up for Haysam's education, and there is tension between...
........Sakanni sun zama mintuna, mintuna sun koma awoyi, awoyi sun rikiɗe zuwa kwanaki, kwanaki sun haɗu sun zama sati, satittika sun dunƙule zuwa wata, wattani suka haɗa shekara. Shekaru sun cigaba da shuɗawa. Har amarya Yakura ta cika shekara uku a gidan Abdul-rasheed. Bata samu ciki ba har yanzu, hakama A'isha tunda ta yaye Haysam shekara biyu kenan bata samu wani cikin ba. Abdul-rasheed kuwa nata sake samun ɗaukaka a wajen aiki da kasuwancinsa na ɗinki, dan zuwa yanzu ya koyar da yara da yawa aikin tela, kuma Alhamdullah suma suna cin gashin kansu, ga shagon saida kayan ɗinki ya buɗe duk sati Nasiru na aiko masa da kaya daga kano. Wani lokacin kuma yaje da kansa yayo daga nan yayo zumunci ya siyama Inna kayan abinci ya dawo. Zuwa yanzu kusan duk ɗawainiyar zuri'arsa ta dawo kansa ne. Yayima su Baba yayima yayunsa da ƙannensa, yayi ma dangin mahaifiyarsa, yayima dangin matansa. Sannan ya sauke hakkin gidansa. Haysam yaro ɗan shekaru huɗu a duniya, ya tasa abinsa masha ALLAH, kyakkyawa mai lafiyar jiki ga gatan iyaye dana kakanni, ya tashi yaro mai shiru, mai son karatu da tambaya. Wayonsa ya girmi shekarunsa, damma baida surutu ne. Yana da shekara biyar a duniya kwatsam a ɗan tsakanin sai ga A'isha da ciki, ya salam zo kaga murna wajen Abdul-rasheed da Yakura dama su Baba, cikin A'isha nada wata biyu itama Yakura ta fara nata laulayin, ya rabbi, rasa ina Abdul-rasheed zai saka kansa yayi dan farin ciki, dan harga ALLAH yana matuƙar son yara. Kamar yanda A'isha ta fara samun ciki itace ta fara haihuwa, santalelen yaro namiji a wannan karon ma, mai kammani da Abdul-rasheed shima. Ansha shagali yaro yaci suna Ja'afar. Ja'afar nada wata biyu da kwanaki itama Yakura ta sauka, itama dai ta santalo nata namijin mai kama da Abdul-rasheed, shima dai yaci suna Ma'aruff. Haysam cike yake da farin cikin samun ƙanne da suka tashi tamkar tagwaye, dan kuwa ma tagwayen ake kiransu. Su Ja'afar nada shekara ɗaɗɗaya aka saka Haysam makaranta, dan kuwa ya cika shekaru shida a duniya cif. Duk da kuwa kafin ma sakashi makarantar tuni ya fara ɗaukar karatu a wajen mahaifinsa da ma A'isha da Yakura. Dan Abdul-rasheed tsaye yake akan tarbiyyar Haysam, sannan akwai shaƙuwa a tsakaninsu mai girman gaske. Akoda yaushe zaka sameshi zaune a gefen mahaifinsa yana sauraron karatun Alƙur’ani ko labaran tarihi na Annabawa da jarumai. Hakama sauran litattafai dai-dai fahimtar yaro mai irin shekarunsa. Duk lokacin da mahaifinsa ya karanta masa tarihin jarumtar Annabawa data sahabban MANZON ALLAH (S.A.W) irinsu Abubakar As-Siddiq (RA). Abokin ANNABI mafi kusa kuma khalifa na farko, mai haƙuri da sanyin hali Umar Ibn Khattab (RA). Khalifa na biyu, adalin shugaba jarumi kaifi ɗaya. Usman ibn Affan (RA). Khalifa na uku, ya tattara Al-Qur’ani cikin littafi, mai yawan ƙyauta kuma mai sadaukarwa ga bayin ALLAH mabuƙata. Aliyu ibn Abi Talib (RA). Khalifa na huɗu, kuma ɗan’uwan ANNABI, jarumi da baya tsoro sai dai kafirai suji tsoronsa, dan ya basu wuta iya wuta a filin daga, Mijin Nana Fateema ƴar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga su Abdulr-rahaman ibn Awf (RA). Irinsu Sa'ad ibn Abi Waqqas (RA). Talha ibn Ubaidullah (RA). Zubair ibn Al-Awwam (RA) ɗan uwan Ummul Muminin Khadija. Bilal ibn Rabah (RA), mai kiran salla na farko jarumi na gaske. Salmanul-farisi (RA) da ire-iren su da yawa da in lissafosu zamuyi da irin rawar da suka taka a musulunci da tsayawa kusa da MANZON ALLAH mu kammu mun san jarumai ne abin koyi da ba Haysam kawai ba ƴaƴanmu ma ya kamata ace muna basu tarihinsu domin su tashi da burin koyi da su ba zindiƙan wannan zamanin ba da yaranmu ke koyi da su koyi mara amfani da amfanarwa. A ɓangaren hikayoyi yana bashi irin nasu Iliya ɗan Mai Ƙarfi, Jatau Ɗan Mariya, Sarkin Zamani, da makamantansu. Dan a wancan lokacin, ana yaɗasu a gidajen rediyo kamar su rediyo Nigeria da jaridu irinsu Gaskiya tafi Kwabo da sauransu. Irin waɗan nan tarihi da hikayoyi sunyi tasiri matuƙa a zuciyar Haysam, dan har yana ji a ransa yana son yayi koyi da su wajen hidimtawa addini. Sai dai abinda ke saka lissafinsa ruɗewa shine zamanin da yake saɓanin nasu ne, tunda shi bai zo zamanin yaƙe-yaƙe ba. Dan haka sai yayta jerama Babansa tambaya. Abdul-rasheed kuwa baya gajiya da bashi amsa, tare da kawo masa misalai akan idan su anyi yaƙe-yaƙe a zamaninsu shi kuma zai iya zama Ɗan sanda, ko SOJA ko wani dai aikin kaki domin bama ƙasarsa gudummawa. Ba wani fahimta Haysam yake da ƙyau ba, amma hakan na sashi jin eh lallai zai iya hakan. A haka ya fara makaranta sai abubuwansa suka sake faɗaɗa. Bayan yaye ƙannensa Ja'afar da Ma'aruff iyayensa sun sake samun ciki kusan a tare, amma Yakura ma ta riga A'isha a wannan karon, dan haka ta rigata haihuwar ɗa namiji mai kama da ƴan uwansa. Shima dai yaci suna Bilal, bayan wata uku da kwanaki itama A'isha ta haihu mace. A karo na farko Abdul-rasheed ya samu mace, dan haka taci suna Halimatu mahaifiyarsa Iya kenan suna mata alkunya da (Ummie). Itama dai akasha shagalin sunanta. A wannan lokacin ma Yakura ta sa sake yin gwanne kuma, dan Bilal nada shekara ɗaya ta sake samun ciki, dole A'isha ta cigaba da shayar da Bilal da Ummie a tare, aka bar Yakura da laulayin sabon cikinta har ALLAH ya kaishi haihuwa ta haifi mace itama da taci sunan Inna wato Karimatu suna mata alkunya da (Mommy). Bayan haihuwar Mommy babu jimawa UBANGIJI ya amshi ran Baba, jiyyar kwanaki biyu rak. Wannan rasuwa ta girgiza wannan zuri'a, barema Inna data koma kamar ta ruɗe. Haka dai akasha kuka da kai-kawo kowa ya haƙura a ƙarshe. Ashe wata na tafe, dan Inna na cikin takaba itama dai ciwo yay mata tsanani, ta matuƙar sakama kanta damuwar rashin baba, ashe itama ciwo ne na tafiya, itama dai a cikar wata na shida da rasa baba tabi bayansa. Su Abdul-rasheed suka sake gigicewa da ƴaƴanta. Nan ma akasha kuka kowa kuma ya haƙura, shike nan gida ya faɗi, an bar su Abdul-rasheed daga su sai dangi. A lokacin Haysam nada shekara goma sha ɗaya a duniya. Yana primary 5, yana shirin gamawa kenan ma, tunda aji 5 ce a lokacin 1983. An gama kukan rasuwar su Baba da Inna babu jimawa itama mahaifiyar Yakura ta rasu, haka suka kwasa sai Maiduguri. Satinsu guda suka dawo ko muce A'isha da Abdul-rasheed suka dawo tare da yara. Yakura sai data ƙara kusan sati biyu ma sannan ya dawo. A lokacin A'isha ta sake samun ciki, cikin daya dinga bata matuƙar wahala, daga ƙarshe ma ta haifeshi a bakwaini, har sai da aka sakashi cikin kwalba na wasu watanni, ita kuma tasha jiyya tamkar bazata rayu ba, mafi yawan mutane idan suka je dubata gani suke kafin su ƙaraso gida za'ace A'isha ta rasu. Abin birgewa kuma Yakura ke jiyyarta kai bakace kishi bace ba sam. Haka dai tasha fama tsahon watanni kafin ALLAH ya bata lafiya ta miƙe tamkar ba'ayi ba, dan kafin cikar wata biyu jikinta ya murje sarai harta fara dawo da ƙibarta. Kamar jira sai ita kuma Yakura ta shiga nata sabon laulayin cikin. A yanzu dai Abdul-rasheed nada ƴaƴa bakwai a duniya. Haysam, Ja'afar, Ma'aruff, Bilal, Ummie, Mommy, sai autan A'isha Ammar. Family ya haɗu sai dai Alhamdullah. Ga kuɗaɗe Abdul-rasheed na samu na ban mamaki, sai dai baya tarawa kullum cikin hidimar ƴan uwa yake da ƴaƴansu, kai hatta maƙwafta da abokai cin arziƙinsa suke yi, dan mutum ne mai ƙyauta da hidima. Ga dai kuɗi ana wasa da su, amma idan ka cire gidan da yake rayuwa bai ajiye kaddarar komai ba. Hakan kuma bai taɓa damunsa ba bai taɓa kuma damun matansa ba. Ba shi kawai ba su kansu sun koya daga alkairinsa, ko baya kusa sukan yi a madadinsa da ɗan abinda yake basu da sana'o'in su duk da kuwa ƙananu ne. Abdul-rasheed bai taɓa sayen kaddara koda ta fili ya ajiye ba balle gona idan ka cire ta mahaifinsu da yake nomawa, bayan rasuwarsa kuma aka raba musu gado, daya tashi sai ya barma ƙannensa da suke ɗaki ɗaya ma kason sa. Dan a lokacin ne autan ɗakinsu ke shirin yin aure, shima dai ya gado Abdul-rasheed duk tsawon lokacin nan yana yawon karatu ne, daga ƙarshe dai zaiyi aure a yanzu cikin wannan satin. Auren daya taka rawar gani mai ban tsoro da razanin zuciya a zukatan zuri'ar Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi dama al'ummar anguwa, kai harma duk wanda yasan wannan sunan wannan aure ya kawo masa tarihin da bazai manta da shi ba.........✍🏼
Shin miya faru ne a wannan aure daya zame ma wannan zuri'a tambari da bazasu manta ba? Wane ajiyayyen tarihi wannan aure zai bari haka?🥲. Kudai kumuje zuwa dan har yanzu a shinfiɗa muke. Cakwakiyar da shagulgula na gaba🏃🏼♀️.
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 21_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp
07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________