Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 19

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 19

.....Iba in the country of Hausa. But everyone prayed for the holy Haysam, and then the naming ceremony continued. The meeting was pleasant, and it was as good as it should be. We ate breakfast with chicken and beef that was slaughtered after the lamb. A'isha is her eyes, and she is a little privileged girl, except for the window, if you remove the pain of missing her husband and seeing him now, there is nothing that bothers her. Let alone her family around her. The next day they were in the town as usual and Aisha's family took her to Kanon to get a bath, she was escorted by others from Abdul-Rasheed's family, while he would later go to see them in Kanon, who now had no chance to follow them. Even when Nasiru came, he was still here and after a week he will return to Kano. He is not married yet, but I have set the date of his marriage to a younger sister of their mother who lives in Kaduna. She is in school, that's why we are waiting for her to finish, and now she is just a few days away from finishing the holiday, I swear to GOD... <<<<<•>>>>> Today, Inna received the guests of her new grandson Haysam Abdul-rasheed Shehu and her daughter Aishatu. Ranta fez is happy, and Bashir wh

Standalone post2,057 words

.....Washe gari bisa roƙon da yay ma Baba ya amince ya kai A'isha asibiti, an dubata ita da jaririnta aka basu magunguna tare da rubuta masa takardar haihuwa kamar yanda Abdul-rasheed ya buƙata. Daga haka suka dawo gidan. Kwankin zaman bakwai sun cigaba da gudana cikin farin ciki da daɗin rai ga maijego. Tana shan ruwan zafi a hannun Inna Salame anguwar zoma. Sannan tana cin abinci mai inganci daga hatsi da kunu, ga mijinta ya tsaya mata da nama da abubuwa masu inganci da maijego take buƙata bayan namu na gida. Ƴan Maiduguri sun iso kwana biyu da haihuwa. Hakama ƴan Kano mutane uku sun iso saura sai ana gobe suna. Abubuwa fa nata ƙara armashi Alhamdullah, ana gobe suna gida ya gama cika taf da dangi tako ina, tako wane ɓangare kayan arziƙi ne ke shigowa daga ƴan uwa da abokan arziƙi, haihuwa tayi albarka kenan. An raɗama yaro suna da safe tare da yanka ƙatoton rago daga Baba. Sunan daya bama mutane mamaki da tunanin ina Abdul-rasheed ya samo wannan suna, dan kuwa suna ne da ba'a saba jiba a ƙasar hausa. Amma dai kowa yayi addu'a ga jinjiri Haysam, daga haka aka cigaba da shagalin suna. Taro yayi armashi, ya kumayi daɗi yanda ya kamata, anci ansha anyi asuwaki da naman kaji dana sa guda da aka yanka bayan ragon suna. Ita dai A'isha nata ido, dan kuwa ƴar gata take komai sai dai taga anayi, idan ka cire kewar mijinta da ganinsa ke mata wuya yanzu babu abinda ke damunta. Balle ga ƴan uwanta zagaye da ita. Washe garin suna bisa al'ada dangin A'isha suka wuce da ita Kanon dabo wankan jego, ta samu rakkiya daga wasu a dangin Abdul-rasheed, yayinda shi kuma sai daga baya zai je ganinsu Kanon, dan a yanzu baida damar binsu. Nasiru ma da yazo suna yana nan sai bayan sati zai koma Kano, baiyi aure ba har yanzu, amma na saka ranar auren nasa shida wata ƴar ƙanwar mahaifiyarsu da suke zaune a Kaduna. Tana makaranta ne shiyyasa ake jira ta ƙarasa, kuma yanzu saura kaɗan ɗin ta kammala asha biki in sha ALLAHU...

<<<<<•>>>>>

A yau Inna ta samu baƙuncin sabon jikanta Haysam Abdul-rasheed Shehu da ƴarta mai jego A'ishatu. Ranta fes da farin ciki, hakama su Bashir da suka ƙara girma suna cike da farin ciki. A'isha kam farin cikin ta baya misaltawa, tunda tai aure sai yau ne take zuwa Kano shekara uku ciff. Aiko dole tai kuka, tayi kewar Inna matuƙa mara misali, har tana jin kamar an rabata da itane gaba ɗaya. Dan tasha zama tayi kukan kewar Inna da su Tasi'u. Garama su sunje mata har sau kusan uku hutu. Amma Inna bata taɓa zuwa mata ba. Tun randa aka lulluɓa mata zanin aure sai yau ne suke ganin juna. Ƴan uwa da abokan arziƙi da maƙwafta da basu sami damar zuwa Bauchi suna ba sunata shigowa ganin jariri ɗan mutanen Bauchi. Yana shan addu'a kuwa daga bakuna masu albarka. Lallai dawowar A'isha Kano ta sake tabbatar da ita ƴar gata ce, dan kuwa jego take irin na ƴan gata masu capacity. Ba aikin fari babu na baƙi sai dai taci abinda take so ta ƙoshi tasha barcinta ta more. Idan kaga Haysam a hannunta abincinsa zata bashi. Amma koyaushe yana bayan Inna. A mata abinci mai rai da lafiya taci tayi nak abinta. Ai kafin kace mi ta ƙara wani uban ƙyau ta murje ta sake haske da cikar jiki. A kuma yanzu ne kayan arziƙi suka ƙara bayyana kansu. Maƙerin budurcin na gaskiya ya bayyana gareta, dan kuwa tana cika shekaru sha takwas ne a duniya. Satinsu uku Abdul-rasheed ya iso Kano da shatara ta arziƙi. Shi kansa yanda A'isha ta koma sai da ya ƙara bashi mamaki, kamar jira take tazo Kanon ta sake canjawa da buɗewa ne. Ga yaronsa Masha ALLAH, shima yayi ɓul-ɓul alamar yana samun kulawa mai daraja a wajen Inna kakar ƙwarai. Sai yaji ƙaunar tsohuwa Inna ta ƙara girma a zuciyarsa da daraja irin ta uwa mahaifiya bawai suruka uwar mata kawai ba. Satinsa ɗaya ya koma Bauchi. Daga nan sai yazamto duk bayan sati Uku yake zuwa ganinsu. A haka sukai arba'in uku ciff, arba'in uku kuwa kwana 120 kenan, watanni huɗu har Haysam ya fara ɗan wayo na jarirai. Daga nan aka fara shiryama A'isha komawa, bayan ta zagaya dangin uwa dana uba, sai dai ta jinkirta har akai bikin Nasiru da matarsa kuma ƴar uwarsa. Ƴan Bauchi sunyi kara sosai dan sunzo, a lokacin ne kuma yan Bauchin suka koma da ita, amma tare da rakkiyar danginta itama. Bayan A'isha ta dawo gidan aurenta sun sake gina sabuwar rayuwa da mijinta Abdul-rasheed da ɗansu. Ya ɗauketa zuwa Maiduguri dangin mahaifiyarsa a karo na farko, sun yo musu sati har biyu. A kuma wannan zuwa ne shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin A'isha da Yakura, idan bamu manta ba Yakura dai itace akama Abdul-rasheed tayin aurenta a lokacin bikin ƙanwarsa Khadijah. Yarinya ce mai natsuwa da hankali, ga haƙuri da ilimin addini, ga ƙalubalen rayuwa da take fuskanta hannun mijin mamanta saboda marainiya ce babanta ya rasu. A wannan zuwa ma su Baba Kalla sun sake kwaɗaitama Abdul-rasheed auren Yakura, halin daya sake ganinta a ciki kuma yasa ya amsa babu wani jayayya, koda ya tunkari A'isha da maganar tun a can sai yaga tanata farin ciki. Hakan ne ya saka masa nutsuwa yana dawowa ya sanar ma Baba. Baba yayi murna sosai kuwa shima, ya kuma saka masa albarka. Daga haka aka shiga kai-kawon maganar aure. Mata nada ba kishi ne basu da shi ba, zata iya yiwuwa ma sunfi matan yanzu kishi sosai. Sai dai akwai dattaku da kamun kai da sauƙaƙawa zuciya damuwa dama ɗaukar rayuwar aba komai ba. Dan haka A'isha koda ta nuna murnarta a fili a ɓoye tasha kuka, dan kuwa tana son mijinta sosai, amma son da take masa bazai saka ta tauyesa akan ƙarin aurensa ko bijire masa ba, ita dai aljannarta take nema da burin samu a wajen UBANGIJIN da yace ai aure kuma ayi biyayya ga maza, suma kuma su sauke haƙƙokinmu, wanda bai sauke ba kuma zaiga sakamakonsa. Iya ƙoƙari mijinta nayi akan ƙyautata mata da sauƙe hakkokinta dake kansa, ya ɗauki ɗawainiyar Innarta da karatun ƙannenta su Bashir, ga kulawar da Haysam ke samu ta musamman irin ta ɗan gatan ɗa, to mi zaisa kuma ta butulcema ALLAH. Yayta aurensa zata bishi da addu'a da kuma fatan zaman lafiya ita da amaryar. Dan a wajenta Yakura abar a tausayama ce ga duk mai imani. Gefe ɗaya kuma har cikin ranta son Yakura take ji, dan haka kawai ALLAH ya haɗa jininsu....

Haysam nada shekara ɗaya da wata ɗaya akasha bikin Abdul-rasheed da amarya Yakura, itama dai an kawota nan gidan kusa da A'isha, Alhmdllh kuma A'isha tasha yabo ga dangin mahaifin Abdul-rasheed dama na mahaifiyarsa saboda dattakon data nuna ƙwarai da gaske akan auren nan kamar ba ƙaramar yarinya ba. Babu wanda zai ce yaga fushinta ko ɓacin ranta koda a fuska ne, balle wata magana mara daɗi, hatta shi kansa ango Abdul-rasheed ma da take kwana take tashi da shi zakuma ayi kishin a kansa babu wani abun ALLAH wadai da zai ce ya gani daga A'isha, hasalima wani abun ita take dagewa akan ayi. Haka dai akai biki aka tashi lafiya kowa na san barka da sanya alkairi da addu'ar zaman lafiya na har abada. Tsabar kunyar A'isha da nauyinta da Abdul-rasheed keji bai bar aboki ko ɗaya ya masa rakkiya gidan da nufin sayen bakin amarya ba, hatta kuwa da Nasiru. Haka ya shigo shi kaɗai. Kai tsaye kuma ɗakin A'isha ya nufa, abin mamaki sai ya samu ita harma tayi barcinta, Haysam na jikinta shima yana nashi. Ya jima a kanta tsaye yana kallonta da mamaki, har zuciyarsa na masa tambayar wai kuwa anya A'isha na sonsa? To dole yace hakan, yasha jin tarihin matan abokansa idan zasu ƙara aure akan kishi, amma ita ko da wasa babu abinda ta nuna masa mara daɗi, kuma dai ance kishi nan na mata shike nuna tsantsar soyayyarsu gareka. Haka dai yayta saƙawa da kwancewarsa, daga ƙarshe yay musu addu'a ita da Haysam ɗin ya kashe mata fitila ya fito tare da karo ɗakin ya nufi ɗakin amarya. Washe gari ma Abdul-rasheed yata zuba ido yaga canji ga A'isha ko'a fuska amma shiru, sai ma wani annuri data tashi da shi da farin ciki. Wanda ya sashi kasa gane daga ina ta samosa. (Bai san daga sallar dare bane. Dan cikin dare ta farka tai alwalarta a cikin ɗaki a botiki, ta shiga kaima UBANGIJI buƙatunta da addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali ita da amarya da shi, Alhamdullahi kuma ta tashi ranta fes babu wani damuwa balle nauyin zuciya da take fama da shi a kwana biyun nan). Haka yay ta binta da kallo, musamman da zasuyi kari yaga ita da Yakura nata shan hirarsu hankali kwance kamar ma wasu ƙawaye. Kai daga ƙarshe ma sai bar musu gidan yayi, koda ya dawo samunsu yay suna aiki a tsakar gida suna hirarsu cike da nishaɗi da dariya. Ga Haysam a bayan Yakura a goye tana ƙulla aya da gyaɗar saidawa da A'isha keyi. Ita kuma tana girki. Harga ALLAH sai ya sake jin nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali, harma da son A'isha yana sake nunkuwa a ransa. Dan haka da daddare ya sake haɗasu yay musu nasiha da roƙon su ɗore a yanda suka fara, su toshe kunnensu daga munafukai, su kauda idonsu daga azzalumai masu haddasa fitina a bayan fage. Sun tabbatar masa zai samesu fiye da yanda yake fata, suma kuma sun roƙeshi ya kasance adali a tsakaninsu mai tsayar da gaskiya. Shima ya amsa da tabbatarwa... Tabbas Alhamdullah, babu abinda Abdul-rasheed da Ai'sha da Yakura zasu ce a wannan gaɓar sai tarin godiyar ALLAH. Dan kuwa gidan aurensu ya zama gidan farin ciki da ni'imarsu da kwanciyar hankali. Bawai basa kishin bane, sunayi, sai dai kowacce tana yin kishi mai amfani wajen ganin ta ƙyautata ma mijinta a ɓoye batare data sosa zuciyar ƴar uwarta ba. Haka shima mijin na ƙoƙarin yin adalci, wadda yafi so kuwa ya barma ransa ne.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 20_

__________________

_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM 👇🏻👇🏻👇🏻 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr CALL/WHATSAPP 👇🏻👇🏻 wa.me/2349030398006

TIKTOK 👇🏻 https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________