Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 18

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 18

..... sweet and cheerful that makes people happy. In Mom's room, the cry of a strange baby reached the ears of everyone in Dad's house at that time. At that moment, everyone's faces were filled with joy, and as soon as Aisha went down, the Lord brought the limit. "Thank God!" said old woman Inna Salame, who was taking delivery, wiping her sweat and smiling after completing the umbilical cord cutting. In the bright light of one day, Mom looked at the window of her room and said, "Hello, welcome to this little girl, it's a boy, and he's very healthy, thank God." A'isha, a new mother, shed tears of joy as she looked at the child from the corner of her eye and moved in Inna Salame's arms, wiping him and wrapping him in a white cotton cloth to carry the baby that Inna brought. She began to pray for him in her heart, like the way she used to pray for him when she was on the verge of experiencing the pain of labor, that for her was Abdul-rasheed's teachings, since she got pregnant, he has increased his efforts in teaching her to raise her in the womb and start him with a Muslim education from the inside, she also prays. It was Inna Salame who came to her rescue after calling Inna a strang

Standalone post1,856 words

........Ranar 10 ga Oktoba, shekara ta 1972, garin Kobi na cikin Bauchi ya tashi da sanyi mai ɗauke da ƙamshin ƙasa na ruwan da aka sha da asubahi. Saukar ruwan data kasance kusan dai-dai da farkawar A'isha dake gidan su Abdul-rasheed ɗakin Inna tashi a gigice da ciwon mara. Inna ma dai dama ta farka, dan haka tai kanta tana salati, tunfa lokacin aka fara gumirzun naƙuda, makwafciyarsu Inna Salame dake unguwar zoma tuni ta shigo suna kanta ita da Innar, baba nata addu'a a cikin ruwa Inna na amsowa ana bata da sauran saƙe-saƙin ruwan magani da Inna Salame tazo da su. Dama kuma tunda cikin ya shiga watanni bakwai take shansu kala-kala, duk da Abdul-rasheed baya so dole ya haƙura, amma yana ɗaukarta a ɓoye ya kaita asibiti gudun kar su Inna suyi faɗa dan basa so. Shi kuma yana son lafiyar matarsa da kulawa mai tsafta. Har gari ya waye tangaran, matan yayun Abdul-rasheed ma da maƙwafta suka shigo A'isha bata haihu ba, sai zuwa can hanci ya ɗaga kaɗan, rana ta leƙo kaɗan da yanayin ɗuminta mai daɗi da armashi dake ma mutane daɗi. A cikin ɗakin Inna kukan jariri baƙon duniya ya ratsa kunnen duk wanda ke cikin gidan Baba a wannan hantsi. A take farin ciki ya mamaye fuskokin kowa, dan kuwa dai A'isha ta sauka kenan, UBANGIJI ya kawo iyaka. “Alhamdulillah!” in ji tsohuwa Inna Salame mai karɓar haihuwa, ta share gumi tana murmushi bayan kammala yanke cibiya. Cikin ɗan hasken ranar daya hudo tagar ɗakin ta Inna ta ɗagashi da ƙyau tana faɗin, “Barka-Barka yar nan kinji, yaro ne, kuma lafiyyayen gaske masha ALLAHU.” A'isha, sabuwar uwa, ta saki hawayen farin ciki tana kallon yaron ta gefen ido daketa motsi a cikin hannun Inna Salame tana gogeshi zata naɗeshi a farin mayafi na auduga na ɗaukar jariri da Inna ta kawo. Addu'a ta shiga jera masa a zuciyarta, kamar yanda take yi masa tun tana a gaɓar ɗanɗana zafin naƙuda, hakan a gareta koyarwar Abdul-rasheed ce, dan tunda ta samu cikin nan ya ƙara ƙaimi wajen koya mata rainon ciki da fara masa tarbiyya irin ta musulinci tun a ciki, addu'oi yanayi itama tanayi. Inna Salame ce ta shiga gyarata bayan ta mikama Inna baƙon duniya daketa callara kukansa tamkar yana shelantawa ƴan Kobi da garin Bauchi baki ɗaya zuwansa duniya. Sosai wannan haihuwa ta saka mutane da yawa a farin ciki, yaro yasha addu'a kala-kala ga iyaye da kakanni. Yayinda bakin Abdul-rasheed ya kasa rufuwa dan ana haihuwa yara suka je suka sanar masa a ƙofar gida shi da su baba. Dan bayan idar da sallar asuba ya rako Baba gida kamar yanda ya saba, ga ɗan yaf-yaf na ruwa da ake yi har lokacin, shine sukaci karo da Inna a ruɗe zata fita kiran Inna Salame take sanar musu A'isha ce ke naƙuda, tun daga lokacin bai iya barin gidan ba yana nan tare da Baba yana mata addu'a a zuciya. Bayan ɗan lafawar hayaniyar gidan da saukar garwar ruwan wankan maijego aka kwashe mata zuwa bayi, aka ɗiba na jariri shi kuma zuwa ɗakin Inna. Saura kuma nata ƙoƙarin ɗaura kunu da za'a dama na jego a wuta. Gefe ga kawunan akuyoyi masu ƙyau da Abdul-rasheed ya shigo da su yanzun nan babu jimawa. Ransa fal yake da son ganin A'isha, amma ya daure bai takura ba kada ace ya cika rashin ta ido. Sai ma wajen Baba dake ɗaki daya shiga kamar yanda Inna ta bashi umarni dan a kawo masa abinci ya karya. A lokacin ne aka kawo baƙon duniya daya sha wankan ruwan zafi yay luff a cikin showal yana barcin huce gajiya. Baba ya amsheshi fuska da murmurshi yana faɗin, “Baƙon hantsi ne zance kona asubahi”. Cikin dariya Inna tace, “Mai tada mutane da asuba dai baƙon hantsi”. Dariya Baba yayi kaɗan da faɗin, Kinga yaci suna biyu kenan, KIƊA A RUWA MAI TADA HANKALIN DODO”. Abdul-rasheed dake saurarensu ma na ɗan murmushi da cin abincinsa sai dai yana satar kallon ƙyautar da ALLAH ya bashi ta gefen ido. Baba ya furta, “Masha ALLAH, wannan dai gida ka ɗakko abinka baka tafi kalar dangi Kano ba. Gashi nan kamar ranar aka haifi ubansa kwabo-da-kwabo sai hasken fata na ɗaukar magana na kanawa”. Inna ta ce, “A gida kam ya ɗakko, ni kaina tun kan ma a gogeshi nace wannan Abdul-rasheed sak. ALLAH yasa yayo halinsa shima ɗan albarka”. “Amin ya rabbi”. Baba ya amsa mata yana masa addu'a. Sai da ya kammala ya miƙama Abdul-rasheed shi. Kasa amsarshi yayi saboda kunya. Sai da Baba ya ce, “Ka jimin ja'irin kaya, amsheshi mana ka masa addu'a ka sanya masa albarka. Ga dabino ka tauna ka bashi”. Hannu biyu Abdul-rasheed ya saka ya amshi gudan jinin nashi, kuma tsokar jikinsa daya fito daga masoyiyarsa A'ishatul-humairah. Ƙasa-ƙasa ya saki ajiyar zuciya yana kallonsa. Lallai kamaninsa da yaron a bayyane take, Banbanci kawai shi jinkiri ne ɗan a wanni a duniya kuma mai hasken fata irin ta A'isha, shi kuma uba daya fara nisa a gwagwarmayar rayuwa zuwa yanzun. A cikin zuciyarsa yake faɗin (Zakina kazo duniya a ranar da ƙasarsa ke murnar cika shekaru goma da kwana goma da samun ƴanci, jarumin da aka haifa cikin sabuwar ƙasa mai sabuwar fata. A zahiri ƙasa bata san tana buƙatarka ba, amma ina sha ALLAHU sai ka zama wani ginshiƙin riƙeta a yayin girma da ƙarfin ikon ALLAH. ALLAH yay maka albarka, yasa ka zama mahaddacin Alkur'ani da sauran ilimomin littatafan addini, ka zama mai aiki da su bamai karatu kawai da shagala ba. UBANGIJI ya wadata zuciyarka da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W) UBANGIJI ya soka damu gaba ɗaya ya yarda da mu. ALLAH yasa ka zama mai jin ƙan iyaye da al'umma, ALLAH ya ɗora nasarar ka akan ta maƙiyanka, ALLAH ya rayaka rayuwa mai tsaho da nagarta, ya shimfiɗa tausayin al'umma a zuciyarka, ya baka zuciyar nema daga halak ya saka maka ƙyamar haramun). Yana kammala wannan addu'a a zuciyarsa ya tauna dabino kamar yanda Baba ya bashi umarni ya sakamasa a baki. Da farko fuska ya yamutse, sai kuma ya fara motsa ɗan bakin nashi a hankali. Inna dake kallonsu cike da tsokana tace, “Anya wannan mai gidan bazai fini kwaɗayi ba”. Dariya Baba da Abdul-rasheed suka sanya suma. Inna ta sake faɗin, “To jifa yanda ya lamushe abinsa tsaf.” Nan ma dariyar dai sukayi, kafin baba ya saka Abdul-rasheed yayma yaron huɗuba da sunan da yake da ra'ayin saka masa. Nan ma yayi sannan Inna ta amsheshi ta koma da shi. Abdul-rasheed ya sanarma Baba sunan da yay masa huɗubar da shi, Baba ya sanya albarka tare da tambayar ma'anar sunan. Daganan suka cigaba da hirarsu. Duk yanda Abdul-rasheed yaso ganin maijego a yinin ranar bai yiwu masa ba, sai dare bayan sallar isha'i Inna tana ɗakin Baba kai masa abinci ya samu wuff ya shige, dan kuwa zuwa yanzu babu kowa duk matan yayunsa sun koma gidanjesu da maƙwafta sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai ƙannensa biyu ƴammata Nana da Alawiyya. Yana shiga ɗakin ya aike su dan kawai ya musu wayo, a bazata A'isha taji ya rungumeta. Kunya ya sakata fara mutsu-mutsun janyewa. Cikin raɗa ya ce, “Haba Shatuna matar Abdul-rasheed ki barni naji ɗuminki, na samu tubarrakin jego mana. Na rage kewarki ta kwana da kwanaki. Sannu-sannu kinji baiwar ALLAH, ALLAH yay miki albarka, lallai yau UBANGIJI ya azurtani da babbar ƙyauta ta hanyarki, ke mace ce mai daraja da kimar da bata da misali a wajena. Ina fatan kina lafiya babu inda ke miki ciwo ko?”. Kanta ta jinjina masa alamar eh. Ya ce, “Alhamdullahi, zuwa safe zan roƙi baba ya bari na kaiku asibiti a ƙara dubaku kinji. Goben kuma in sha ALLAHU saƙo zai isa gasu Inna suma na samun jika mai kama da Babansa, yanzu kin yarda na fiki ƙarfin jini ba”. “Ni ban yarda ba, kawai dan ya ɗanyi kama da kai kaɗan kake cika baki”. Abdul-rasheed ya yi dariya, yana kallon jaririn da idonsa cike da jin daɗi. “Indo kiji tsoron ALLAH, wato kamar ma kaɗan yayi dani ashe, wannan dai kishi ne kawai kike dani. Amma kowa yaga Zakina yasan photo copy ɗinane ai. Za mu sa masa suna *Haysam*.” Karon farko ta ɗan kallesa, “Wannan wane irin suna ne? Karfa ace ka sama ɗanka sunan aljanu”. Murmushi yayi da ja mata hanci kaɗan, “Sunane kamar kowane suna, kuma yana da nashi tarihi shima. Fassararsa na nufin (Zaki). Ina fatan nawa Zakin ya tashi da ƙarfin zuciya da jarumta irin ta baradan Zakuna. Yayi nagarta irin ta mutane masu dattako da tsaftataciyar zuciya, mai jinƙai gana ƙasa da shi, mai ƙyautatawa da girmamawa gana sama da shi. Mai kishin ƙasa da son cigabanta, da haka ina fatan ki bani gudunmawa wajen gina tarbiyyarsa da waɗan nan jimlolin, amma ginshiƙinsu ya zama ilimin addini dana zamani ne”. Cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, “In sha ALLAHU zaka sameni mai biyayya a gareka. ALLAH ya bamu tsahon rayuwa mu da shi mai albarka”. “Amin ya rabbi Matar Abdul-rasheed, sannan Maman *_Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi_*”. “Niba mamarsa bace, ga iyayensa nan cike da gida”. Ta faɗa tana kauda kai irin na kunya. Dariya yayi shima da sake rungumeta, kafin sallamar su Nana ta sakashi mata sallama ya fito kamar ba shi ba..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 19_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________