
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 31
... Haysam let go with a loud sigh, even though he wanted to laugh, but she was silent. From that day she refused to let him talk about this marriage until his vacation was over and he was ready to go back and leave them again soon. Two weeks passed and she was married to Alhaji Nura. Harga ALLAH does not want to marry A'isha, but she is determined to see that Alhaji Nura is a good man, there is no need to worry and there is no noise. As he promised and he kept the orphan women as his children. He didn't get involved with her business and he started fixing her house. There is no food problem, so he arranged for Malam Sulaiman to accompany him to Kaduna to check on Haysam. Haysam didn't understand anything, he thought he was just a friend of Malam Sulaiman. So he greeted him with respect and calmly answered his questions. Life went on and Mammah found peace with her husband again. She loves her children and they love her studies. Even though Ja'afar did not let go of Alhaji Nura at first, Mammah kept telling them and advising them. So Haysam went to rest again and found what he didn't give him. But since he was so satisfied with his education, he kept it in his heart and did not eve
.......Kwanansa biyu ya huta Mammah ta zaunar da shi tai masa bayani akan matsin lambar kawunanta game da aure. Abin mamaki sai taga Haysam yay kicin-kicin da fuska har idanunsa sun kaɗe. Cikin son kwantar masa da hankali dan ta fahimci kishin mahaifinsu yake ta ce, “Nima ba auren nan nake so ba, dan da ina da damar dazan bijire musu tabbas da nayi hakan. Bani da wani buri sai na ganin na tsaya a kan tarbiyyar ku, rayuwarku ta inganta kuma. Amma na rasa ta inda zan zamewa al'amarin su. Yanzu haka jiya-jiya Kawu Rayyanu ya kawo min wani mutumi wai makwafcinsu ne, yanata damunsu a kaina, shi da gaske yake ba wasa yazo da shi ba. Ban ɓoye masa akan ku ba yace yaji ya gani ya kuma yarda nai zamana anan shi zai dinga zuwa.” Karo na farko Haysam ya ɗago yana kallonta, idanun nan sun kaɗe jazur. Cikin ɗacin murya ya ce, “Kuma kin yarda Mammah?”. Rasama mi zatace masa tayi, dan gaba ɗaya ya juye mata tamkar Abdul-rasheed a gabanta. Sai kawai ta girgiza masa kai. “A'a ban amince ba”. Ajiyar zuciya Haysam ya saki tare da furzar da huci, harma abin yaso mata dariya amma ta gimtse. Daga ranar bata yarda ta sake masa batun auren nan ba, har hutunsa ya ƙare ya shirya ya koma ya sake barinsu da kewa. Ya wuce da sati biyu aka ɗaura mata aure da Alhaji Nura. Harga ALLAH ba son auren nan A'isha take ba, amma haka ta daure ganin Alhaji Nura mutumin kirki ne, baida damuwa bai da hayaniya kuma. Kamar yanda yay alƙawari kuma ya riƙe mata marayu kamar ƴaƴansa. Bai rabata da sana'arta ba ya kuma shiga gyara mata gida. Matsalar abinci babu ita, haka ma ya shirya Malam Sulaiman ya rakashi har Kaduna ya duba Haysam. Shi Haysam bai fahimci komai ba, a tunaninsa abokin Malam Sulaiman ne kawai. Dan haka ya gaishesa da girmamawa tare da sakin jiki yana amsa masa tambayoyin daya dinga masa. Rayuwa ta cigaba da shuɗawa Mammah ta sake samun kwanciyar hankali da mijinta. Tayi ƙyau yaranta sunyi ƙyau suma sunata karatunsu. Duk da dai su Ja'afar da farko basu saki jiki da Alhaji Nura ba suma sai da Mammah ta dinga musu faɗa da nasiha. A haka Haysam ya sake zuwa hutu ya tarar da abinda bai masa ba. Amma da yake ya kwankwaɗi tarbiyya ya ƙoshi haka ya danne a ransa bai ko nunama Mammah ba har hutunsa ya ƙare ya koma. Tafiyarsa babu jimawa ciki ya bayyana a jikinta. Sosai Alhaji Nura ya nuna farin ciki mai tsanani da wannan ciki, dan matansa biyu babu wadda ta taɓa ko ɓatan wata shekaru fin goma-goma yana tare da su kuma sai Mammah a yanzu. Aifa kafin kace mi zance ya zagaye ko'ina, Mammah na samun gata iya gata a wajen mijinta kamar zai lasheta da wannan ciki, in dai kaga bata samu abu ba sai dai in batace tana so ba. Haka aka cigaba da rainon wannan ciki. Cikin Mammah nada wata bakwai abubuwa suka fara canjawa a yanda suke. Hidimar Alhaji Nura ta fara raguwa, hakama ɗokin wannan ciki, kai takai yanzu sai yay sati bai leƙo gidanta ba. Tun mutane basa fahimta har aka fara fahimta, wasu suka fara faɗin bai san haihuwa ne ai dama, wasu suce matansa ne sukai masa asiri, dan yaje ya tare a gidansu sai hidima yake musu. Al'amarin kamar wasa ƙaramar magana ta fara zama babba, takai Mammah tayi wata guda bata saka Alhaji Nura a idonta ba. Su Ammar da suka buɗi ido da shi suna kallonsa matsayin mahaifi sunci kukan har sun gaji sun haƙura. Inda ta godema ALLAH yanzu sana'arta ta zauna da ƙafafunta, dan tunda ta samu ya ƙara mata jari ta sake miƙewa da ƙafafunta. Ganin haihuwa ta kusa zuwa mata ta samu kawunta da batun abinda ke faruwa duk da tasan ya sani. Haƙuri ya bata da mata nasiha, ya tabbatar mata subi komai a hankali Alhaji Nura baya cikin hayyacinsa ne, dan al'amarin nasa akwai ƙamshin gaskiya game da asirin da ake faɗa matansa sun masa. Amma dai zai sameshi yaji mike faruwa. Jiki a sanyaye tace to ta koma gida.
________★
Kamar yanda Kawu ya faɗa zai samu Alhaji Nura ya same shin, amma mi abin mamaki sai Alhaji Nura ya murje ido ya fara tujara ma Kawu, daga ƙarshe ma yace shi ba cikin shi bane ba, A'isha taje ta nema wanda yay mata ciki. Idan kuma aka matsa zai kai kotu. Kai shi yama saki Mammah taje can ta nema uban cikinta. Wannan magana ta girgiza kawu matuƙa. Ya ce, “Haka kace?”. “Eh haka nace, ku kaini duk inda zaku kaini, ina kan gaskiya ta ciki ba nawa bane ba. Kuma na saketa saki uku”. “Babu inda zamu kaika, amma zamu zauna tare da waliyanka ka maimaita dukkan abinda ka faɗa kodan watarana kar kace sharri akai maka”. Daga haka Kawu ya miƙe yayi gaba abinsa. Kamar yanda ya faɗa haka yaje ya samu waliyyin Alhaji Nura daya kasance mahaifinsa ya sanar masa. Shima kansa ya girgiza da wannan magana, babu ɓata lokaci ya nemo ɗan nashi akan batun, abinda kuma ya gayama Kawu shi ya maimaita ma mahaifinsa da waliyyan Mammah babu tsoro babu shakka. Sai kuma zancen yaso zama hayaniya a tsakani, dan kuwa ya sheganta cikin da cewar ba nashi ba, kamar wasa sai da aka dangana da mai-anguwa akai zama tsakanin Mammah da Alhaji Nura, anan ɗin ma bai canja ba daga batunsa na ciki ba nashi bane. Mammah taci kuka matuƙa da yin nadamar aurensa, daga ƙarshe akace sai a bari saita haihu aga mi zata haifa, idan gwaji ya kama sai aje ayi. Da wannan batu aka kashe magana, Mammah taje ta cigaba da rainon wannan ciki cikin matsanancin yanayi da ƙuncin zuciya da kewar Abdul-rasheed, har ALLAH ya kaita ga haihuwa aka samu mace. Abin mamaki yarinya kamar Alhaji Nura yayi kaki ya ajiye saboda kamanni, dan tun tana jinjirarta kamanin a bayyane suke. Mammah ta gode ma ALLAH mutane kuma sun tayata murna. Ita kuma daga nan ta hau kan nata dokin zuciyar, ta tabbatar ma Alhaji Nura bata buƙatar komai daga gareshi game da rainon ƴarta, kuma ko anan gaba kada yace yana da wata alaƙa da yarinyar. Babu ko musu yace ya amince tabbacin yana cikin mayen asiri har lokacin. ALLAH sarki sai mahaifinsa ne yay komai na sunan yarinya aka saka mata suna Habibah. Suna kiranta Biebah. Haysam yazo hutu lokacin yana shekara ta biyu a NDA ya tadda Biebah, yanda yake son sauran ƴan uwansa haka yake jin ƙaunar ta. Mammah bata gaya masa komai daya faru ba shi ma kuma bai tambaya ba duk da yaga Alhaji Nura baya zuwa gidan, a haka ya kammala hutunsa ya koma....
>>>>>>•<<<<<<<
Shekaru Sun shuɗa, Sabbin Jarumai Sun girma. Lokaci ya tafi kamar iska mai kaɗawa a zamanin rani da damuna. Shekaru uku sun shuɗe cikin gumi, jini, da hawaye ga matasan soji. A yau Haysam Abdul-rasheed Shehu, wanda aka fi sani da Zak-Shadow ya zama ɗaya daga cikin fitattun senior cadets na NDA. Yanzu idan ya wuce, sabbin cadets suna tashi tsaye domin girmamawa a garesa. A gefe kuwa Imran Abbas wanda a da yaro ne mai rauni ya zama ɗaya daga cikin masu kwarewa a sashen signals and intelligence unit. Ba wanda ya taɓa zato cewa shi ne sarkin kukan nan da ya shiga makaranta a shekarun uku da suka shuɗe. Duk inda suka shiga ana kiran jaruman biyu da suna (The two Shadows). Domin kuwa suna aiki tare tamkar gangar jiki ɗaya da zuciya biyu. Sunan Zak-Shadow da Imran ya sanya ma Haysam ya bishi, har takai Zak-Shadow ɗin yayi gaba fiye da sunansa na yanka. A yau suna aji ɗaukar darasi da Major Adetunji ke ɗaukarsu, wanda ya horar da su tun farkon shigowarsu NDA. Bayan ya kammala ya sallamesu su Zak-Shadow suka iso gaban allo ɗaukar masa kayansa domin yi masa rakkiya kamar yanda suka saba. Kallonsu ya tsaya yanayi cikin murmushi, “Haysam Abdul-rasheed Shehu, Imran Abbas the two Shadows”. Murmushi sukayi a tare, duk da kuwa idan yana jin nishaɗi yakan kirasu da sunan ne daman. Batare daya jira amsawar su ba ya cigaba da faɗin, “Kuna cikin waɗanda suka fi nuna mana menene juriyar soja a wannan mate ɗin naku. Shiyasa kuke na daban a zuciyata yaran albarka, ina son a shekarar ƙarshen nan ku ƙara ƙwazo da jarumta fiye da shekaru uku da suka shuɗe, dan ina son ku zama misali ga duniya idan kuka fita ba cikin makarantar NDA kawai ba”. Ƙaramin murmushi Haysam ya yi tare da salute ɗinsa, hakama Imran, a tare suka amsa da murya mai zurfi, “Yes, sir.” Major Adetunji yay murmushi shima, dan har cikin zuciyarsa yake jin ƙaunar Haysam da Imran. Yaran akwai tarbiyya da nutsuwa. Babu wanda zai ce yau ga wani laifinsu ko wani ya kawo ƙararsu ana faɗa dasu a cikin ɗalibai. Gasu da maida hankali akan komai. Duk wahalar da Haysam yaci a hannun Seniors bai taɓa kai ƙarar kowa ba, sai idan su sun gani su hukunta Seniors ɗin musamman idan muguntar tayi yawa. Sai gashi a yanzu komai yana neman zama tarihi, dan watanni kaɗan ta rage su shiga shekarar ƙarshe a NDA ɗin........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 32_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp
07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________