
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 41
.....think about his case. As he is a man who needs a lot of family, what if he goes to his work, if she doesn't stop him and the wife misses him, he doesn't want to do that. And even if he comes, if she doesn't bring herself to him, he won't ask for it. She thought it was his pride that was part of doing that. It was only when her mother started to worry about her that he was looking for her and he started to think about her, but her heart didn't agree and she was whispering to him with a smile. But to this day her heart seems to have started to feel safe with this conversation, especially when she remembers the words of some of her friends and she stood up against her husband who is a member of the army. These thoughts that Nabeeha continued to have that night are more and more inciting and confusing her. But she called her mother again and told her what happened with her husband and she once again confirmed to her that their prediction was true, Zak-Shadow does not know how to give birth in reality. And of course she has to stand up and investigate him to make sure that he is not looking for her. Anyway, she climbed more and more.....
_____________________
.........Zaram tasha gabansa, sai dai ta gagara kallonsa kamar yanda shi yake kallonta. Zuciyarta na mata ƙuna da raɗaɗi, shawarwarin mahaifiyarta na bata ƙwarin gwiwa ta ce, “Haysam kana saka min shakku a zuciyata da jin yarda akan maganganun mutane. Kodai baka son haihuwa ne kamar yanda kowa ke faɗa?”. Ya daɗe bai ji abinda ya sokar masa zuciya kamar kalamanta ba. Cikin wani irin yanayi mai girman gaske ya zuba mata idanu yana mata wani irin kallo mai zafin gaske. Zuciyarsa kuwa tuni ta yinƙuro ta tokare maƙoshinsa. Ya tabbata in dai ya buɗe baki akan bata amsar kalamanta zai iya gaya mata mai zafin gaske da zata ninka wadda ta gaya masa sau dubu. Dan haka sai kawai ya zagayeta ya fice a ɗakin gaba ɗaya. Fashewa tai da wani irin kuka tana kaiwa ƙasa ta zube. Jifa ta fara yi da duk abinda ya tare mata gaba. Babu abinda ke ƙara ingiza fushinta sai kalaman mahaifiyarta. Tabbas ta yarda gaskiya Momy ke faɗa akan mijinta. Dan ita kanta a wasu lokutan takan zauna taita tunani game da al'amarinsa. Yanda yake mutum mai yawan buƙatar iyali miyasa idan ya tafi wajen aikinsa in ba ita ta takura masa da magiyar yazo tana missing ɗinsa ba dan kansa baya shiryowa yazo dan yin hakan. Sannan ko zuwan yayi idan ba ita da kanta ta kawo masa kanta ba bazai nema ba. Da tana ɗauka tsabar girman kansa ne ke sashi yin hakan. Sai da mahaifiyarta ta fara fargar da ita ne akan kodai yana neman mata ne sannan ya ɗan fara taba tunaninta, sai dai zuciyarta bata amince ba tana wasi-wasi dan tasan sa da ƙyanƙyami. Amma zuwa yau zuciyarta kamar ta fara jin aminci da wannan zance, musamman idan ta tuna maganar wasu ƙawayenta da kance ta tashi tsaye akan mijinta dan wasu sojojin akwai son matan tsiya, shiyasa ma basu cika son haihuwa ba dan kar aima ƴaƴansu abinda sukema wasu. Waɗan nan tunane-tunane Nabeeha ta cigaba da tasirantarwa a wannan dare suna ƙara tunzurata da rikita mata sissafi. Koda ta sake kiran mahaifiyarta ta gaya mata yanda sukayi da mijin nata sai ita kuma ta sake tabbatar mata hasashensu ya zama gaskiya dai, Zak-Shadow baya san haihuwa a gaske. Kuma tabbas dole ta miƙe tsaye da bincikensa dan ta tabbatar shin baya neman mata. Ai ko haka ta ƙara hawa ta zauna. Da safe har ya shirya ya fito bata leƙashi ba. Sai shine ya shigo ɗakin nata. Yanda ta faffasa abubuwa kawai ya tsaya yana kallo, kafin ya maida idanun kanta. Tana kwance a kan gado da waya a hannunta. Sarai kuma ta ji shigowar tasa amma tai biris. Uffan baice mata ba ya juya ya fice a ɗakin. Sai ta raka bayansa da harara tare da jan tsakin daya shiga kunnensa a bazata, dan ya juyone da nufin dawowa ɗakin ya mata magana. Cak ya tsaya tamkar wanda akai ma tsawa, sosai fuskarsa tayi masifar sake haɗewa fiye da yanda take, idanunsa sun wani juye alamar zuciyar ƴan maza ta motsa, dan ni kaina na tsorata addu'a kawai nake kar yace zai koma ɗakin. Ganin ya bar wajen ya sani sauke ajiyar zuciya. Sashen Mammah ya nufa, a kallo ɗaya kuma ta fahimci ransa a ɓace yake. Sai dai batayi magana ba saboda ƙannensa. Shima cikin dannewa da haƙuri da ALLAH ya bashi ya fuskanci ƴan uwansa ya ajiye batun Nabeeha gefe.....
>>>>>★<<<<<
Gaba ɗaya wannan yinin su Major Imran sun yishi ne akan ƙafafunsu wajen binciken son sanin su wanene suka kawo musu wannan harin, ta wani ɓangare kuma hankalinsa a tashe yake matuƙa akan son samun Zak-Shadow kafin zancen harin da aka kai musu ya kai Headquarter asan baya jejin tunda yayi fita ne irin ta sirri. Amma har wani daren bai samu mafita ba. Sai dai sun sake shiri na musamman akan kowane sansani dama jejin gaba ɗaya. Dama haka wannan munafukai ke buƙata, wato karkatar da hankalin su Imran ɗin, sun ko samu nasara zamuce, dan ana cikin sallar isha'i suka sami nasarar kai hari a ƙauyuka uku. Bankaura dake babban ƙauye na wannan yankin, sai wani ƙauye da ake kira Gangare, sai kauyen Marke. Wannan sabon tashin hankali ne da waɗan nan ƙauyuka basu taɓa fuskanta ba a baya, dan rikicin shekarun baya daya faru a sauran ƙauyukan ne banda nasu. Ruwan fitar harsasai da ƙarar tashin nakiya ce ta fara jan hankalin wasu a yaran su Imran. Cikin gaggawa wani haziƙin matashin soja ya silalo yabaro inda suke da bayi da nisa da ƙauyukan ya sanar da Imran. Ai babu ɓata lokaci ya zabura da wasu tawaga suka nufi wannan waje. Ƙauyen Gangare suka fara shiga kasancewar shine farko. Tun a farkon shiga suka fara cin karo da gawarwakin mutane. Hankalinsu ya tashi dan sun fahimci al'amarin da lallai babba ne. Ai babu wani maganar ɗaga ƙafa suka buɗe ma yaran su Dagger wuta, nan fa sabon wasa ya koma tsakaninsu, mutanen gari kuwa tashin hankali yasa sun watse cikin jejin, wasu kuma a cikin gidajensu suka samu wajen ɓuya. Matuƙar bata kashi akasha a wannan dare, kowane ɓangare sun gama jigata musamman mutanen gari da sukafi fuskantar ƙalubale, an kashe mutane da yawa, a wannan ƙauye. Ba'a samu lafawar wannan hargitsi ba sai zuwa ƙarfe shida da rabi na asuba gari ya fara haske, daga ƙarshe dai su Dagger suka gudu, an kashe wasu a cikinsu suma, an kama mutane biyu kuma, kamar yadda wasu a cikin yaran su Imran suma aka ji musu ciwo, sai dai soja ko ɗaya bai mutu ba. Sojoji na tattara mutanen da suka jikkata Imran ya samu waya ta wani da aka kashe, gefe ya koma ya shiga neman layin Zak-Shadow, a lokacin kusan ƙarfe tara na safiya. A kuma dai-dai wannan time ɗin ne Zak-Shadow yake a sashen Mammah tare da ƴan uwansa bayan ya baro nashi sashen da ɓacin ran matarsa.
★ Bilal ne yaga wayarsa na haske, dan shi hankalinsa ya tafi kan magana da Mammah. “Dada kamar ana kiran wayarka”. Bilal ɗin ya kalla, sai kuma ya juya yana kallon wayar dake a gefensa. Baƙuwar number ce, shi kuma baya ɗaga baƙuwar number. Dai-dai nan kiran ya katse, har zai ɗauke kansa sai kuma wani kiran ya sake shigowa a karo na biyu, cikin takaici ya ɗauki wayar zai kashe gaba ɗaya dan zuciyarsa sam babu daɗi... “Ya kamata dai ka ɗauka kasan waye”. Maganar Mammah ta dakatar da shi daga kashe wayar, cikin bin umarni ya ɗaga tare da sakawa a hansfree. Jigatacciyar muryar Imran ta daki kunnensa, “Imran ne Sir!.........” Wayar ya ɗauka yana miƙewa tare da cireta daga hansfree ɗin gaba ɗaya. Cikin wata irin razananniyar murya ya ce, “What! Shine sai yanzu kuke sanar dani. Imrannn!!!”. Yanda ɗakin ke amsawa da amon muryarsa yay matuƙar tada hankalin ƴan uwansa, a zafafe ya yanke kiran yana mai isowa gaban Mammah. Kai tsaye ya ce, “Mammah zan wuce akwai matsala”. “Ya rabbi, miyake faruwa?”. “Ba lafiya Mammah, hari aka kai mana. Kiyi haƙuri zamuyi waya”. Daga haka ya fice daga falon kamar wani yunwataccen zaki. Hankalinsu a tashe duk suka miƙe suna kallon juna, sai kuma duk sukayo waje suma. Dai-dai nan yake fitowa daga sashensa da jaka a hannu, sai hular mashin ɗinsa. Gaban Mammah yazo ya ɗan rungumeta, ta shafa kansa tana mai masa addu'a, dan yanayinsa kawai ya tabbatar mata al'amarin babba ne sosai. Hakama ƙannensa a tare suka zo suka rungumesa tare da masa addu'a. Da sauri yabar wajen ganin su dukansu suna faman sharar hawaye, har Mammah duk jarumtarta sai da ta kauda kai gefe, yana hawa ƙaton mashin ɗinsa da in yana tafiya baka jin ƙara Bilal ya zabura ya nufi gate da gudu ya buɗe masa. Ai ko a guje ya fice daga gidan shima, dan ji yake kamar ya rufe ido ya gansa a jejin...
Ganin kowa ya fito babu Nabeeha ƙanwarta ta tafi da gudu tana buga mata ɗaki da kiranta. “Aunty!. Aunty! Ki buɗe dan ALLAH Dada fa zai tafi”. Wani irin dukan zuciyar Nabeeha kalmar zai tafin tai a karo na farko. Cikin sauri ta diro a gadon da take kwance. Yanzu fa taji yana buga mata ƙofa da kiran sunanta tai banza da shi, a zatonta kan maganar jiya ne yazo ko fitinarsa ce ta motsa, duk da tasan kome yake ji idan yana fushi zai iya danne abinsa ya haƙura, shiyasa taƙi buɗewa. Tana buɗe ƙofar ƙanwarta taja hannunta kawai suka fito, sai dai rashin sa'a suna fitowa tsakar gidan ana rufe gate alamar harya wuce. Sharrr hawayen da suka cika mata ido suka shiga rige-rigen zubowa, sai kawai jikinta ya kama rawa har tana neman faɗi sai da ƙanwarta ta riƙeta. Ciki suka koma, dan su ma su Mammah sun shige nasu sashen. Bedroom Nabeeha ta shige tana mai fashewa da kuka, dan ita duk tunaninta abinda tayi jiya ne da ƙin buɗe masa ƙofa a yanzu ya fusata shi. “Aunty dan ALLAH ki daina kukan nan, kimasa addu'a kamar yanda sauran ƴan uwansa ke masa. Dan ita yafi buƙata a garemu baki ɗaya”. “Ismat bazaki gane ba, laifina ne, nasan nina fusatashi ya tafi. Miyasa daya buga ban buɗe masa ƙofar ba....” “Anya haka ne kuwa Aunty. Kamar fa kiransa akai daga wajen aiki inaga wani abu ne ya faru”. “Wajen aiki?”. “Tabbas haka ne Aunty, amma ki bincika wajen su Mammah”. Hawayenta ta shiga sharewa da sauri. Sai kuma ta jawo wayarta ta shiga kiran number ɗinsa. Amma harta katse bai ɗaga ba. Ta jera masa fin kira goma no answer, sai ta sake fashewa da kuka tana yin jifa da wayar, ALLAH ma ya sota bata faɗi ƙasa ba Ismat ta cafe..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 42_
__________________
https://wa.me/+23408067422528 Kina son rage kiba ba tare da kin daina cin abunda kike so sannan ba tare da kinyi gudawa ba? To kimin magana domin samun hanyoyi da zaki rage kiba ba tare da kinsa wahala ba. Ko kuma matsalar gashi ce ke damunki, ko rashin tsahon gashi ne, shima muna da solution dinsa. Ko kuma fatar ki tana lalacewa ne a sanyin? Muna da ingantaccen man da zai gyara miki kafafunki ko kuma kamar ta jarirai. Ko kuma kafarki ce take kaushi a sanyin nan muna da ingantaccen mayuka Ko kuma man gyaran fata kike so da zai gyara miki jikinki a sanyin Nan ?duk muna dasu ba tare da kinsa wahala ba sannan 100% natural ne. Yar uwa idan ma bangaren samun kudi shima kike nema shima duk zamu koya miki. Kedai kawai ki mana magana domin karin bayani.
https://wa.me/+23408067422528 “Shin Ke uwa ce, kina son samun kuɗi ba tare da kin fita kin bar ’ya’yanki a gida ba?” ko kuwa ke student ce kina son samun karin kudin shiga ko kuma ma dai kawai kison karin side hustle ne Tare da Oriflame, za ki iya yin kasuwanci daga wayarki a gida. Ba tare da kin fita ba. Mata da yawa sun riga sun farga da wannan Kasuwanci kuma suna moriya dashi sosai, suna making kudi daga gida, kuma ke ma za ki iya sannan bayan ribar ki zaa biyaki salary a karshen wata. ko kuma kina son yin siyayya for personal use ne ba tare da anci riba dake ba ga link nan a kasa zaki iya register da kanki it's free👇
https://shop.oriflame.com/NG-salmaibrahimismail/3M3HmQWe
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________