
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 17
...and then we will know who we are and what we should do. I pray to GOD, that will make you understand what marriage is for himself." She bowed to him, and in a trembling voice she said, "Be patient, I won't do it again. And son of GOD, don't be patient with Inna, and tell the great son of GOD not to go to Kano and tell Inata, GOD if she tells her, she can draw me, and she will be angry with me." The little boy smiled, in his heart he was expressing his fear of not listening. Clearly, he said, "That's it, I'm going to lose patience. I hope you don't blame me for anything. Get up and wash your eyes. Have you performed the Isha prayer?". "No". Then squeeze some lemon juice for me in hot water and the rest in the flax, right?". "Yes, since the one who drank the tea, there is no more tea left". She bowed to him and said, "I don't climb the walls of GOD. I always go out through the door." He laughed now. He said, "Oh, Abdul-rasheed's wife, go to Abdul-rasheed. She laughed and covered her face with her palms. IN.....
...Bayan ficewar Inna ɗakin yay shiru, sai shashshekar kukan A'isha daya cikashi, shi dai Abdul-rasheed yana zaune har yanzu kansa a ƙasa yana saurarenta. Sai da yaga ba dainawa zatai ba sannan ya ɗago cike da ƙarfin hali dan da gaske baida lafiya ya zuba mata idanunsa dake jajur irin na mai ciwo. Muryarsa da sanyi sosai ya ce, “Kibar kukan nan ya isa haka, ko kina son kanki yay ciwo ne?”. Kanta ta girgiza masa alamar A'a. Ya ce, “To share hawayen ya isa. Kin daiji abinda Inna tace. Ke ko tsoro ma baƙyaji kiyita kai kawo a tsakanin dare. A'isha auren soyayya mukayi bana ƙiyayya ba. Mu da kanmu muka zaɓi juna muka kuma so mu zama ma'aurata ba haɗamu akai ba balle muce an mana auren dole ne. Kina da muhimmancin da bazan iya bari wani ya cutar dake ba balle ma ni kaina. Abinda kike gani yana faruwa tsakanina dake shi ne aure. Ina ga dole zamu fara karatu daga gobe, ba karatun Alkur'ani kawai kike buƙata ba a rayuwa da ibada, duk da Alkur'ani yazo mana da komai, amma dole sai mun haɗa da hadisi sannan zamu san su wanene mu da abinda ya kamata muyi. In sha ALLAHU hakan zai sa ki fahimci minene auren ma kansa”. Kanta ta jinjina masa, sai kuma cikin rawar murya ta ce, “Kayi haƙuri bazan sake ba. Kuma dan ALLAH ka bama Inna haƙuri, sannan kace dan girman ALLAH kada taje Kano ta faɗama Innata, ALLAH idan ta gaya mata zata iya zane ni, kuma tayi fushi da ni”. Ƙaramin murmushi yayi, a ransa yana ayyana ga tsoro ga rashin ji. A fili kam sai yace, “Shike nan zan bata haƙuri. Nikam baki min laifin komai ba. Tashi ma kije ki wanke idonki. Kinyi sallar isha'i kuwa?”. “A'a”. “To maza yo alwala kizo kiyi. Sai ki matsa min lemon tsamin can a ruwan zafi ai da saura a cikin flaks ɗin ko?”. “Eh, tun wanda kasha shayi ɗazun ba'a ƙara ɗiba ba ai”. Yauwa to yi sallar sai ki haɗa min wani shayin nasha kinji. ALLAH yay miki albarka ya shirya min ke ki daina haura katanga, dan nasan yanzu dai Shatuna ta girma, ta girmi haura katanga ta barma ƴan baya ko?”. Kanta ta jinjina masa, sai kuma ta ce, “Nifa bana haura katanga ALLAH. Kullum ta ƙofa nake fita”. Dariya yayi yanzu kam. Ya ce, “Oh oh matar Abdul-rasheed tafi Abdul-rasheed wayo”. Dariya tayi itama tana rufe fuska da tafukan hannunta. A haka ta fita a ɗakin, shiko yana binta da kallo da murmushi...
Bayan A'isha tayi salla ta haɗa masa shayin lemon tsami ya sha. Ita kuma ta haɗa mai madara dan tace bazataci tuwo ba. Shi kuma bazai iya fita sayo mata nama ko kifin daya saba kullum ba. Dan bayi ma da ƙyar ya iya fita yaje. Hira ya dinga janta da shi yanda suka saba. A hankali ta saki jiki tanata masa dariya, dan labarin ƙannenta su Bashir yake ta bata da yaran gidan su Nasiru. Sai da yaga ta fara hamma sannan yace taje ta kwanta. Maimakon ita shi zaman lalubo litattafan da zai fara mata amfani da su ya shiga yi. Dan dama yana da burin hakan a kanta tuni. Sai da ya ajiye komai sannan yay tashi kwanciyar a ƙasa ma yau, dan bai hau gadon ba. Washe gari kamar yanda yay alƙawari hakan akai. Da hantsi bayan ta kammala aikin gida ya fita ya dawo sukai zaman karatu. A ɓangaren Alkur'ani kam A'isha Alhamdullah, sai gyara na abinda baza'a rasa ba dai. Dan haka ya fara mata da sauran littatafai. Abin nasu kamar wasa sai ya fahimci tana ɗokin karatun, cikin kwanaki kaɗan kuma ta maida hankali. Har takai yanzu karatun ma yafi cinye lokacinta fiye da biyema yara masu shigo mata da rana. Sun ja kwanaki suna karatun yana buɗe mata komai yanda zata fahimta da ƙyau, abinda yake na kunya taita sinne kai sai yayi kamar bai ganta ba ma, a dalilin wannan karatun ya fahimci A'isha ko jini bata fara ba ashe. Eh lallai aiki babba a gabansa, dole kam ta dinga masa gudun fanfalaƙe ashe. Ganin tana fahimta ya haɗa mata da karatun boko, sosai al'amarin ya fara bashi mamaki, dan gaskiya Alhamdullah tana da brain na fahimtar abu da wuri, gata kuma da nacin son karatun. Satin su uku da fara wannan karatu al'amarin UBANGIJI A'isha ta samu baƙuncin prioud ɗinta a bazata, babu ciwon mara babu komai. Da yake ya karantar da ita hakan sai bata ruɗe ba, sai ma matsananciyar kunya data sata ɓoye masa, ta shiga kici-kicin gyara kanta ita kaɗai. Sai dai ba'ai nisa ba tun a yinin ya ganota. Haka ya zaunar da ita ya sake mata dalla-dalla akan abinda ya shafi jinin haila, ya kuma sake koya mata yanda zata dinga tsaftace kanta da ƙyau. Wato ilimin addini duniya ne, dan kuwa babu mace ƴar gata kuma sarauniya irin mai ilimin addini, mata mu farka dan ALLAH musan kammu, ba'ace karki boko ba, amma ki tuna shifa bokon nan amfaninsa nada iyaka, shiko wannan da muke ɗauka ƙauyanci da shine za'a mori rayuwa mafi tsada dake can gaba garemu. Ba zaki gane wannan zancen ba sai randa mala'ikan mutuwa ya ƙwanƙwasa miki ƙofar amsa kiran ALLAH wlhy😭. Kwanaki uku A'ishatul-humairah tayi, a kwana na huɗu tai wanka abinta ta koma salla, sai da ta koma sallar ne ma Abdul-rasheed ya fahimci baƙo dai ya tafi, ya zaunar da ita ya mata tambayoyi akan yanda ta tsaftace kanta. Tana ɓoye-ɓoyen fuska ta sanar masa da komai. Shi dai nashi dariya ne. Fara ɗinkinsa da samuwar aikin koyarwa ta rage masa zaman gida, sai dai kuma a ɗan tsakanin ya gama shiryama tsuntsuwarsa. Dan kuwa a wani dare na juma'a ya maida Shatunsa cikakkiyar mace. Ya dai sha rigima mai saka ciwon kai da rakinta. Haka yayta lallashi da riritawa, dan sai da ya koma komai shike mata a wannan yinin. Ya kuma sanarma Inna cewar A'isha ta kawo mutuncinta, bawai da baki ko gatsal ba, a'a ya sayi abubuwa ne ya kai ma Innar, kansa a ƙasa ya furta, “Saƙo ne da za'a kai can gidansu A'isha, ai musu godiya da karamci”. Wannan batu nashi kai tsaye ya fahimtar da Inna ina ya dosa, dan wannan al'adace mai girma da a wannan lokacin baka da dalilin ɓoyewa kodan mutunta matarka da kimanta iyayenta a idon naka iyayen. Sosai Inna ta nuna farin ciki tare da sanyawa A'isha albarka matuƙa itama. Shi dai Abdul-rasheed kansa a ƙasa yana amsawa a laɓɓa. Ƙanwar mahaifinsu da suke kira Gwaggo Gaji aka aika aka kira, itace taje can wajen A'isha domin bata kulawa. Anan kuma Inna ta shiga haɗa garar arziƙi itama bayan ta sanar da Baba wannan daddaɗan labari. Ba A'isha kawai aka shiryama garar arziƙi ba, harda mutanen Kanon dabo. Dan abubuwa sosai aka haɗa aka tada ɗan aike tun daga Bauchi har Kano gidansu A'isha shaidar ta kawo mutuncinta gidan aurenta, hakan kuma shine zai ƙarama iyayenta nutsuwa da farin ciki. Dan kuwa abin zai baka mamaki, sanda ɗan saƙo yaje da wannan albishir guɗe-guɗe aka dinga yi a gidan Inna. Daga ƙarshe aka raba kayan arziƙin da aka aiko aka dinga kaisu gidajen maƙwafta da abokan arziƙi. Suko sai gasu suna shigowa taya Inna murna da barka da arziƙi. Dan kuwa ashe anata ƴan ƙananun magana tun bayan auren A'isha cewar ba'aji komai daga dangin miji A'isha takai budurci ba, ashe-ashe angon mai kunya ne da kamun kai. Sai ko aka shiga yabonsa dan ya nuna dattako mai girma. Ita kanta Inna ranta fes, dan harda hawayenta tayi sosai a wannan gaɓar. A'isha ta gama biyanta, ita kaɗai ƙwalli ɗaya mace dama gareta.
________★
Anan Bauchi ma dai A'isha taga gata tako ina daga gidan su Abdul-rasheed dama dangin mahaifiyarsa. Dan labari har Maiduguri, haka suma kuwa suka haɗo garar arziƙi aka kawo mata har Bauchi. Bawai ana zancen bane haya-haya, a'a cikin hikima ne irin ta manya kawai. Kamar dai yanda Abdul-rasheed ya nuna alama ga Inna ta hanyar sayen abubuwa masu daraja yakai yace a aika su Kano gidan su Ai'sha ai musu godiya irin ta mutuntawa. Bayan ƴan kwanaki ta miƙe, sai dai ƴar kunya tsakaninta da Abdul-rasheed, shi dai nashi lallashi da lallaɓa. Gashi yanzu an bata girki, zata fara girki da kanta a gidanta an daina kawo mata daga gidan surukanta kuma. Wannan shine tushe kuma mafari, na fara gina sabuwar ƙyaƙyƙyawar rayuwa tsakanin A'isha da Abdul-rasheed data ninka ta farkon aure matuƙa. Kuɗi suka fara shigo masa ta ɓangaren albashinsa na aiki da harkar ɗinkinsa. Lokacin da suke cika shekara ɗaya da rabi da aure ya gyara gidan Baba sannan ya ƙara gyara nashi, ba wani gini ne sabo kona zamani ba, a'a buhunan siminti ya saya aka shafe ko'ina ginin laka ya ɓoye. Bai tsaya anan ba suma ƴan uwansa ya fara bin nasu gidajen yana gyarawa. Ya kuma dinga ƙara musu jari a harkar sana'o'in su. Bai tsaya anan ba ta kai har haihuwa idan anyi musu shine mai ɗawainiyar komai, yaransu kuwa ya ɗiba yakai makaranta. Baba kuwa ya hanashi yin komai hatta zuwa gidan Sarki yin hidima. A haka rayuwa ta shura suka cika shekara biyu cif da aure, sai kuma lokacin ne ALLAH ya bama A'isha ciki. Abdul-rasheed yayi farin ciki ƙwarai da gaske da wannan ciki, hakama A'isha da sauran dangi, sai dai kunya tanasa su ɓoye a gaban kowa sai sun keɓance. A shekarar 1972 data kasance shekarar cikar samun ƴancin ƙasa goma cif, auren A'isha da Abdul-rasheed cikin na uku cikin jikin A'isha ya fara haramar fitowa duniya, domin kuwa ya tsufa sosai, dan ma abinka da cikin fari ga ƙuruciya harkokinta take kai tsaye kamar bata jin nauyinsa, sai dai Abdul-rasheed shi yayta tausayinta da hanata wasu abubuwan musamman idan yana gidan, dan wani lokacin koya hana daya fita take tashi tayi, idan ya dawo yana faɗan ba yace ta bari ba, sai ta marairaice tace ba ita tayi ba su Alawiyya ne, dole zai haƙura yay shiru..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 18_
__________________
LADY'S BEAUTY PALACE
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE? KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU? KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI? KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA? Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa, Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba Zumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa Lace Hijabs Supplements Kayan yara Saloon Kunshi na salatap Dana zane Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko Sari
Zamuyi promo din kayan mu na hijabs da Kuma zuma
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯
Whatsapp or call 08169307477
Tiktok Hajara Rabiu (lady's beauty palace)
Instagram Hajara Rabiu
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________