Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 29

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 29

.....he is completing his push-ups and standing straight on his feet, as if he is only breathing, it is not difficult. Surprised, one senior cadet came with a scared face, trying to scare him, "You think you're tough, new boy?!!". Haysam didn't say anything. He was standing and on his feet looking at him straight in the eyes with no sign of doubt. Just then the Senior stopped and looked him in the eye, seeing that Haysam would not withdraw from him, he withdrew knowing that he smiled full of meaning, shaking his head and saying, "Hmm... we'll see how long you last". Haysam didn't do that either. Imran was beside him and was trembling, in his mind he was surprised by Haysam's stubbornness. He didn't cry but he could feel his stomach move. But look at him who is wearing slippers. Not only Imran, his other mates and the Seniors also focused on Haysam, but no one said anything and continued to train them. After the first training, we entered the weapon drill. They are taught to hold a gun and stand like real soldiers. Some of them were talking and couldn't balance their hands, but Haysam was on the side holding his gun as if he...

Standalone post1,875 words

........WASHE GARI su Haysam suna tsaye a layi, jiki a sharɓe da zufa, wasu har suna rawar tsoro saboda an ce yau ce the real beginning. Major Adetunji, babban jami’in horo, ya tsaya a gaban su da ƙarfi, yana ta kallonsu ɗaya bayan ɗaya kamar mai tantance fuskokinsu. Kafin cikin buɗaɗɗiyar muryarsa mai kaɗa hanjin marasa ji ya shiga faɗin, “Welcome to the Nigerian Defence Academy. From today, you are no longer civilians! You are cadets, and you will either become men here or quit!”. Sai kuma ya ƙara ƙarfin muryarsa cikin sabon ihu ya sake faɗin, “Drop down! Ten push-ups… No, make it twenty!!”. Cike da zafin kai irin na farkon balaga da jin kansu su maza ne wasu a cikinsu suka fara gunaguni ƙasa-ƙasa. Sai dai babu damar cewa baza'ayi ba. Dan haka suka fara kamar yanda aka umarcesu a tare kuma. Ai ba'a wuce 7-8 ba wasu suka fara zubewa ƙasa saboda gajiya. Sai ƙalilan a cikinsu irin su Haysam masu taurin zuciya da sabon wahala ne suka cigaba da yi har ƙarshe. Haysam da idanunsa ke a rufe yana kammala nashi push-ups ya miƙe tsaye a kan ƙafafunsa daram, kamar wanda yake numfashi ne kawai, ba wahala yayi ba. Cike da mamaki Senior cadet ɗaya ya zo da fuskar tsoro, yana ƙoƙarin tsoratar da shi, “You think you’re tough, new boy?!!”. Haysam dai bai ce komai ba. Yana tsaye kuma akan ƙafafunsa yana kallon sa kai tsaye idanu ƙyam babu alamar jin shakka. Kawai sai Senior ɗin ya ɗan tsaya yana kallonsa shima cikin ido, ganin fa Haysam bazai janye nashi ba sai shi ya janye nasan yayi murmushi mai cike da ma'anoni yana girgiza kai da faɗin, “Hmm… we’ll see how long you last”. Nan ɗin ma ko gezau Haysam baiyi ba. Imran kuwa yana gefensa yana rawar jiki, a ransa yana mamaki taurin kan Haysam. Bashi akema tsawar ba amma ji yake ƴan cikinsa na motsi wlhy. Amma kalla shi wanda akemawa ɗin ko a slippers ɗinsa ma. Ba Imran kawai ba, sauran mate ɗin nasa ma da Seniors ɗin hankalinsu ya koma kan Haysam ɗin, sai dai babu wanda ya sake cewa komai aka cigaba da basu horo. Bayan horo na farko, aka shiga weapon drill. Ana koya musu riƙe bindiga da tsaye kamar sojoji na gaske. Wasu sai mutsu-mutsu suke sun kasa daidaita hannayensu, amma Haysam yana gefe yana riƙe da bindigarsa tamkar wanda ya shekara yana yi. Tsayawa Captain Adetunji wanda yake lura da su yay a kusa da shi. “You! what’s your name, cadet?”. “Cadet Haysam Abdul-rasheed Shehu, sir!” “Good stance. Good grip. You’ve done this before?” “No, sir. But I learn fast.” Captain ya ɗanyi shiru yana masa kallon mamaki, sai kuma ya ɗan murmusa da ba kasafai yake yin haka ba dan irin mutanen nan ne da sam basa fara'a basa wasa. “Keep that spirit. Nigeria needs men like you”. Ya sake faɗa yana ɗan bubbuga kafaɗar Haysam ɗin. Kai Haysam ya jinjina masa cike da girmamawa.

Bayan an kammala an sallamesu suna shiga hostel, Imran ya jingina da gado yana magana cike da raɗa idonsa akan Haysam. “Kai Haysam kana bani tsoro wlhy, ni kam ban taɓa ganin wanda yake da karfin zuciya da rashin tsoro irin naka ba.” Ɗan harararsa Haysam ya yi da murmushi mai sanyi kawai yana girgiza kai. Sai da ya kai zaune a bakin gadon su yana cire takalmin ƙafarsa sannan ya bashi amsa da, “Ba ƙarfin zuciya bane ko rashin tsoro Imran. Imani ne da abin da nake so in zama, tare da son cika burin Abiy na”. Zama shima Imran yayi yana sauke ajiyar zuciya. Ya ce, “Gaskiyar ka kuma Zaki na. Nima in sha ALLAHU zan dinga jin ƙarfi da ƙarfin son cikar burina kamar kai. Da yardar ALLAH wataran sai mun tuna hakan munyi dariya tare munyi kuka tare”. “ALLAH ya tabbatar”. Cewar Haysam yana kaiwa kwance a gadon.

__________★

Da daddare gari ya yi sanyi sosai a NDA. Ko ina ya cika da shiru sai ƙarar iska dake kaɗawa da motsin fallen langa-langar rufin ɗakunansu. An kashe fitilun waje, sai hasken ƙaramin bulb da yake haskaka ɗaki na 17 Alpha room da sautin minsharin room mate ɗinsu biyu masu saurin barci. Haysam yana kwance kan gadonsa, jikinsa har yanzu na ciwo amma zuciyarsa cike da natsuwa. Imran kuwa yana daga sama shima ya kasa barci sai faman juyi yake a gadon, yana gumi alamar wanda ke mafarki mai nauyi. Can kuwa sai ga muryarsa na fita kamar cikin kakari irin na wanda yasha shaƙa a hannun wani. “Ka barni… don ALLAH kar ka sake min haka… Mama… Mamaaa!”. Da sauri Haysam ya tashi, ya sauka daga gadonsa cikin sassarfa. Tsaye ya miƙe tare da kai hannu kan Imran ya shiga jijjiga kafaɗarsa, “Imran… hey, wake up. Lafiya kuwa? Kaga tashi…” A firgice Imran ya buɗe ido da sauri, sai kuma ya zabura zaune jikinsa na rawa. Idonsa cike da hawaye, numfashinsa na fita da sauri kamar wanda aka fito da shi daga ruwa. Hannun Haysam ya damƙe tare da matsowa sosai kusa da shi cikin muryar kuka ya ce, “Na… na sake ganin su.. sun sake kamani Haysam”. Kallonsa Haysam yake cikin tausayi, sai kuma ya ɗan dafa kansa kamar mai dafa kan Bilal. “Shhhh… ka yi shiru. Mafarki ne. Ba kowa a nan. kai da ni ne kawai da su Peke. Kayi addu'a ka canja kwanciyarka ta wannan ɓarin”. Sai kuma ya juya ya ɗakko ruwa ya miƙa masa. “Ka sha ruwa, ka huta. Kada ka bari mafarki ya firgita ka. Ka dinga ƙarfafa kanka Imran, kaifa soja ne da wasu ke jira ka basu garkuwa anan gaba”. Imran ya kalle shi da hawaye, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin cikin rawar murya, “Haysam mutanen nan bazasu barni ba, duk da iyayena sunyi nasarar fiddani a ƙungiyarsu tare da baro yankinsu gaba ɗaya lokaci-lokaci suna cigaba da bibiyata a mafarki. Wlhy gaba ɗaya a tsirace nake. Kai dai kamar komai ba ya tsoratar da kai.” Shiru Haysam ya yi na ɗan lokaci, yana kallon tagar da iska ke busowa, sai kuma ya dawo da dubansa kan Imran ɗin, “Kowa yana da tsoro Imran. Amma na koyi ɓoye nawa, dan idan na bari duniya ta gan shi, zata yi amfani da shi wajen zubar da ni, lalatattun mutane masu ƙazamar zuciya subi takai na su taka tamkar yanda suke taka ƙasa. Ni mutum ne kamar kowa. Amma Abiy ya sanar min sai na zama jarumi a zuciya sannan jarumtar jiki ke tabbata har wasu su kalleni wataran suce wannan shine wane. Kasa a ranka babu abinda mutanen nan suka isa suyi maka kamar yanda basuyi maka a baya ba. Idan suna taƙama da tsafi kai ka tuna ALLAH kake da shi”. A hankali ya saki murmushi mai ciwo yana ƙoƙarin danne damuwarsa, “Imran! Idan har Mammah dake mace mai amsa sunan UWA zata ɓoye dan mu rayu cikin salama da nagarta bayan ta rasa daga kowane garkuwarta ni data haifa na zame mata farkon nauyi kuma ƙalubale a yau mizai hana bazan jure ba kodan na maida murtani daga ahalin da suka nuna mata amfaninta ya ƙare garesu saboda mai musu amfani ya gusa daga jikinta a yanzu. Zan cigaba da ɓoyewa domin na zama abinda nake fata iyayena ma suke fata. Amma kai kada ka koyi ɓoyewa. Tsoron ka… shi ne dalilin da yasa kake da rai da jinƙai Imran.” Lumshe idanu Imran yayi yana jin kalman Haysam masu fita da harshen damo da saƙo na musamman suna ratsa shi kamar magani. Koda ya motsa lips dan yin magana sai Haysam ya girgiza masa kai, tare da masa nunin ya kwanta kawai. Bai musa ba a hankali ya kwanta, shiko kuma ya cigaba da tsaiwa a jikin gadon yana tofa masa addu'ai har sai barci ya kwashe shi.

Kwanaki sun cigaba da shurawa, sannu-sannu su Haysam sun zama ƴan gida a NDA. Dan kuwa zuwa yanzu watanni na biyar suke ƙoƙarin cikawa. Jiki da zuciya sun saba da sabon waje sun kuma karɓi sauyin horo da suke fuskanta. Hakama ƙwaƙwalwa tana ɗauka daga koyarwa da dabarun rayuwa irin ta mazan fama. Ranar yau asabar ta zo da rana mai tsananin zafi. An fito dasu Haysam duka don wani obstacle training na tsalle, gudu, juyawa cikin laka, da rarrafe ƙarƙashin waya. Duk wanda ya yi wasa ko nauyin jiki kuwa yaji a jikinsa ne a hannun Seniors. Kamar ko yaushe Haysam yana cikin ƴan gaba-gaba yana yin komai da cikakken natsuwa kamar wanda ba ya jin ciwon gaɓɓansa. Yayin da wasu ke gunaguni, shi kuwa ko numfashi bai tsananta ba. Wannan yasa wasu senior cadets da suka fara saka masa tsama suka fara saka masa ido sosai. Bayan horon rana, lokacin da su Haysam suka koma sashen su, Senior Cadet Garba ya kalli abokansa yana murmushi mai ɓoye makirci, “Na fahimci fa yaron nan mai kama da haihuwar sahara ya fara kama da jarumi yana son fara yima mutane ɗagawa da girman kai, ya kamata mu gwada wane irin ƙarfe ne da shi.” Dariya John ya sanya da faɗin, “Wato Garba kaifa mugun icce ne. Na kula ka saka idonka akan yaron nan kamar yana barci a kanka cikin NDA ɗin nan”. Hararsa Garba yayi, cikin ƙyaɓe baki ya ce, “Shi ɗin banza da zai yi barci a kaina. Kawai na tsane shi ne, wlhy tun randa yay mana rashin kunyar nan nake ji kamar na kashe banza dan na tsane shi har cikin raina”. “Ba kai kaɗai ba fa, ALLAH nima bana son shi sam a raina. Gashi naga ya fara kama zuciyar basawan gidan nan”. “Mtsowww! Zai ci uwarsa ne. Mune maganinsa ai”. Dariya suka sanya suna tafawa su da sauran abokansu da basuce komai ba.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 30_

__________________

https://chat.whatsapp.com/L3BXH7JYlBRHIkFRiOjeW3?mode=ems_copy_t

UMMU KHALIFA COLLECTION

Ina Mata Yan kwalisa ina mata masu san kayan ado kamar Egyptian abaya sleeping drees kids were shos bags musk dahara original.

To kukanku yazo karshe domin ummu khalifa sun zo muku da duk wadannnan kayan dierct suke order dinsu daga Egypt zuwa gida Nigeria kaidai kawai kashiga link dinsu domin gani ya kori jiii..

Ba nan ummuh khalifa suka tsaya ba suna nemawq mutane visa masu shaawar shugowa kasar ta Egypt karatu ko yawon bude ido ko kasuwanci ku tuntubeta a number dinta +201017018846/07048811474/

KO kuma shafinta na tiktok https://vt.tiktok.com/ZSU1FEkjc/ __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________