Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 16

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 16

...even when the evening prayer is being performed, he came in and said he would take a bath at that time, but he did not have time to do it during the day, and he knew that he would not be able to sleep if he did not do it. At night, she was going to run away, but she found the door of the house closed. As if she was going to cry, she turned around and came back. But then the trick of getting under the bed came to her. So she quickly laid out a mat and brought some empty clothes in front of her as you can't bring a person under the bed. She went to bed without fear. GOD, the king, the servant of GOD, Abdul-rasheed, his mind was lying down and he thought that she would not be able to open the house, even when he entered the room, he did not see her, and he thought that she was where she had locked herself in the morning. Then he put down the bathroom clothes and went to persuade her to come back, but there was no sign of her. He quickly went to the attic and closed the door the way he had left it. He came back inside to look for Aisha. He was surprised and afraid, so where did she go? (Katanga), his heart declared for him. Zama yay is just scratching his head, he is ashamed that he

Standalone post2,110 words

...Aiko dai akwai aikin babba ma kuwa. Dan kuwa da asuba dai koda Inna tasa su Alawiyya su rakota gida suna juyawa suka fita tai alwala sai ta shige ɗakin girkinsu dake a tsakar gidan, da yake ba girkin ta taɓa yi ba babu komai a ciki sai icce da aka tara da kayan ruwa da abubuwa da take kaiwa ciki ta aje, anan tayi sallar sai da gari ya waye sannan yaji motsinta zata fara shara. Fitowa yay daga ɗakinsu yana kallonta. Dan massalaci ma kasa zuwa yayi saboda ciwon daya kwana da shi na ciki. Tana ganinsa ta ajiye tsintsiyar zata gudu ya ce, “Kinga yi haƙiri tsaya. Cigaba da shararki in dai nine ma na koma”. Ya koma cikin ɗakin ya ƙyaleta. Baki ta tura itama, ta ɗauki tsintsiyar ta cigaba da sharar. Haka yau ma sukai wannan yini tana masa wasan ɓuya. Da yaga ta takura a gidan sai ya lallaɓa ya fita ya koma tsohon ɗakinsu dake soron gidansu ya kwanta a can. Abinci ma aikowa yayi aka amsa aka kai masa can duk da kuwa daga gidansu aka aiko. Hajjaju amarya Indo ba jiya taji daɗin gudu ba, yau ma ana yin sallar magriba ganin ya shigo yace zaiyi wanka a lokacin dan bai samu yayi da rana ba, yasan kuma bazai iya barci ba in baiyi ba. A ɗarare takai masa ruwan bayi, yana shiga ta sulale zata gudu, sai dai ta samu ƙofa a rufe ta gidan. Kamar zatai kuka ta juyo ta dawo. Amma mi sai dabarar shigewa ƙasan gado tazo mata. Dan haka sauri-sauri ta shimfiɗa tabarma ta kawo wasu ƙorai da babu komai tasa a gaba-gaba ta yanda bazaka kawo da mutum a ƙarƙashin gadon ba ta shige abinta ta kwanta ko tsoro ma bata ji. ALLAH sarki bawan ALLAH Abdul-rasheed, hankalinsa kwance ya fito yasan dai bazata iya buɗe gidan ba, koda ya shigo ɗakin bai ganta ba yayi tunanin tana inda ta maƙale ɗazun da asuba. Sai ya ajiye kayan wankan yaje ya lallasota ta dawo, amma mi babu ko alamarta, da sauri ya nufi soro kofa a rufe yanda ya bari, ya sake dawowa ciki neman duniya ba A'isha. Mamaki da tsoro suka kama shi, to ta ina tabi ta fita? (Katanga), zuciyarsa ta ayyana masa. Zama yay yana dafe kansa kawai, dan wlhy kunya yake ji bazai iya zuwa gidansu ba yau kuma. Idan jiya basu gano shi ba ai yau sai su gane. Haka ya haƙura ya miƙe ya tafi massalaci sallar isha'i. Duk abinda yake tana jinsa, daya fita kuma bata kawo a ranta ya fito ba ta fice gidan ta cigaba da kwanciya a ƙarƙashin gadon har barci yay awon gaba da ita anan. Bayan sallar Isha'i Abdul-rasheed ya dawo, haka ya zauna shiru zuciyarsa na masa saƙe-saƙe, gefe yana ƙalubalantar kansa da rashin haƙurinsa, dan ƙila da bai mata abinda yay matan ba da hakan bata faru ba. Ga tsaraba ma ta kasa zama ta duba sam. In sha ALLAHU zai daure ya riƙe kansa ya bita a hankali. Da wannan tunanin ya ɓingire. Da asuba fitsari ya kama A'isha har yana neman zubowa, dan haka ta fito cike da sukur-sukur ɗin daya tada Abdul-rasheed, dan haka ya haska fitila da tunanin ko ɓera ne ya shigo musu. Amma yana kunnawa ya haske A'isha na fitowa a ƙasan gado. Mamakin duniya ya ishe sa, ya zuba mata ido kawai. Itako tayi tsuru-tsuru kanta a ƙasa tana matse ƙafafu dan fitsarin neman kufce mata yake. Fahimtar hakan da yayi ya saka shi sakin murmurshi, muryarsa a sauƙaƙe yace, “Amshi fitila kije kiyi”. Da sauri ta amsa kuwa ta fice. Shima ya miƙe ya sauka a gadon yana sauke ajiyar zuciya. Amma lallai yarinyar nan ta cishi wasa jiya. Yanzu nan tana ƙasan gado dama duk bulayin daya dinga yi. Wato ita dai mace duk ƙanƙantarta akwai wayo da dabara. Da wannan tunanin ya fito da buta a hannu, baice mata komai ba ya ɗauki fitila data ajiye zata fara alwala ya wuce bayi, sanda ya fito ta gama zata wuce. Dan haka cike da lallashi ya ce, “Dan ALLAH ki zauna a gida to kada kije ko ina na dawo na baki tsarabarki da saƙon Inna, kada yazam akwai abin lalacewa a ciki kinga zai lalace”. Kanta dake ƙasa ta jinjina masa. Sannan sum-sum ta shige ciki. Shima yay alwala ya fita. Koda ya dawo da wannan buɗe tsaraba yaja ra'ayinta, har hantsi ya fito ya fita ya sayo mata shayi, sai kuma ga kayan kari Inna ta aiko. Da lallaɓa, da lallashi da kwantar da kai ya samu wannan yini dai aka yi shi lafiya. Da dare kuma ya kafa ya tsare ya nuna mata shi tayi duk yanda take so. Ganin yaƙi kulata da abinda take gudun a yinin ma ko kusa da ita bai zauna ba balle ya taɓa mata hannu sai ta haƙura ta kwanta a gadonta, amma acewarta da ido ɗaya zatai wannan barci. Da yake shi barcin ya fita wayon bata ma san ya kwasheta ba har wanda take tsoron ya zauna a bakin gadon kusa da ita yay mata addu'ar barci sannan ya koma nashi gadon. Wannan sabon yin biris daya ɗauka ya kawo masalaha a tsakaninsu, itama ta sake jiki suka koma kamar da. Sai dai kwana kusan shida kuma yaji fa yana neman halaka, a daren ya kasa haƙuri ya sake maimaita na wancan daren, koma muce abinda yafi na wancan daren dan ya sameta fiye da waccan ranar, sai dai kuma ta fitgice masa dole ya barta batare da cimma buri ba. Daga nan ne fa ta sake birkice masa. A daren washe gari kuwa bata kwana a gidan ba, ta sake gudawa gidansu cikin su Nana ta kwana. Ita kanta Innar da su Nanar basu farga da ita ba sai da asuba da Inna ta tashesu suyi salla. Rasama abin faɗa tayi, yau ma sai tace su Alawiyya su rakata gida kawai. Kwanakin da suka biyo baya har huɗu A'isha bata daina yo tsere ba. Abdul-rasheed kuma ya zuba mata ido, hasalima ya koma maida hankalinsa batun buɗe wajen ɗinkinsa ya ƙyaleta. Hakama Baba yana sane A'isha a gidan take kwana, amma bai ce komai ba sai dai yayi murmushi kawai. Koda Inna tai masa magana a cikon kwana na huɗun sai cewa yay, “To mizance, tunda shi bashi da haƙuri da kawaicin barin yarinya ta sarara kaɗan ma kenan. Ke kuwa naga kema haka kika dinga yi min Karima, ƙarshe sai da Baba ya rakoki da tsumagiya gidan nan saboda can kike zuwa.” “Ai kai ka jika Malam, ana maganar arziƙi saika dinga sakko wadda ba'a tambayeka ba. Amma ka bani dabara nima da tsumagiyar zan korata yau. Ina laifin yaron nan ai yayi kawaici ma. Aure wata shida haba ai a yaba masa. Abdul-rasheed da haƙuri da zurfin ciki. Su sauran ƴan uwansa wa yayi wannan haƙurin. Tijjani ma da yafi kowa rashin ta idonsa ko tsallake rana yayi”. Haka ta fita tana sababi. Baba kuwa sai murmushi yake abinsa kawai...

Washe gari kuwa Inna ta shiryama A'isha tsaff, dan yanzu dai sune iyayen tunda babu wani nata a kusa. Kuma a wannan zamanin nasu na adalci ɗa na kowa ne. Babu wani surukutar mugunta ga matar ɗa da uwar miji, yanda suke ma ƴaƴansu haka suke ma matan ƴaƴansu saboda adalci da ƙyaƙyƙyawar zuciya, haka suma surukan suna ɗaukar iyayen miji iyayensu ba irin na yanzu ba da suke ganinsu kamar koshiyoyi. Kamar ko yanda ta saba ana cikin sallar isha'i sai gata ta shigo soron gidan da sanɗarta. Caraf Inna dake a soron ta dalleta da Torchlight, A'isha tai tsaye cak tsuru-tsuru da idanu, sai kuma ta duƙa tana gaida Inna dake tsaye kawai tana kallonta. Batare da Inna ta amsa mata ba ta ce, “Juya muje”. Kallonta A'isha tayi kamar zata fasa kuka, Inna ta haɗe fuska kuwa ciɗin-ciɗin. Sum-sum ta nufi ƙofa dan tasan dai yau ruwa ya ƙarema ɗan kada kam. Haka Inna ta sata a gaba har gida da ƴar tsumagiyarta a hannu, badan ta daketa ba sai dan ta tsoratata. Karo na farko da Inna tazo gidan kenan, suna isa ƙofar ɗaki taci karo da buta, ɗauketa tai ta maida gefe suka shiga ɗakin. A mamakinta sai suka samu Abdul-rasheed a ciki kwance a tsakar ɗaki kan tabarma. Ashe ma yana gidan ta fita, baida lafiya, amma saboda wauta saita wayance da ɗaukar buta kamar zata fitsari daga nan ne ta sulale, butar ce Inna taci karo da ita yanzu da suna shigowa. Ganin Abdul-rasheed ɗin a ɗakin kuma yasata fahimtar ma'anar zaman butar a waje. Tashi yay da ƙyar cikin dauriya yana ma Inna sannu da zuwa. Inna dake binsa da kallo ta ce, “Lafiya kuwa ana salla kana gida Abdul-rasheed?”. “Ba komai Inna kawai banjin daɗi ne, shiyyasa ma ban shigo gidan ba ɗazun da yamma”. “Subahanallahi, amma shine ja'irar nan ta sulalo ta taho can. Nikam ya zanyi da A'isha jama'a. Mijinki na kwance a gida babu lafiya amma kina guduwa wani waje. A'isha wane haline wannan? Idan baki taimaki mijinki ba wa zaki taimaka. Kina son ki mutu a saki wuta ne? Ko kuwa na shirya naje Kano na gayawa Innarki halin nan da kike yi?”. Cikin sauri A'isha dake kuka ta shiga girgiza kai. “Dan ALLAH Inna kiyi haƙuri bazan ƙara ba wlhy na tuba”. “A'a nasan zaki ƙara A'isha. Wata nawa ana abu guda. Ai gara dai na tafi Kanon nan tunda mu baki ɗaukemu iyaye ba. Shima Abdul-rasheed ɗin ne ya ƙyaleki, sai kace wadda tafi ƙarfinka. Kafi son kaita fama da ciwo sai ka halaka kanka ne......” Inna dai nata sababi ta inda take shiga bata nan take fita ba. Taima A'isha dake durƙushe tana kuka, taima Abdul-rasheed dake zaune kansa a ƙasa kunya da ciwo duk sun dabaibayesa. Sai da tai musu tas sannan ta wuce tana sake jaddama Ai'sha idan ta sake ganin ƙafarta a waje koda da rana ne ma zuwa can gidan saita zane ta, kuma sai ta tafi Kano ta sanarma Innarta. A'isha tasan aka sanarma Inna ai taga boni, dan haka ta sake rikicewa, dan Innarsu akwai zafi sosai tana da faɗa, duk da tana jansu a jikinta idan sukai ba daidaiba bata raga musu, balle ma ita ɗin nan da take kamar ƴar fari. Dan kafin ita Inna ta haifi yara kusan biyar suna rasuwa ne itace ta fara zama, a tsakanin ta da Bashir ma wani ya rasu shiyyasa ta bashi kusan shekara biyar........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 17_

__________________

_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM 👇🏻👇🏻👇🏻 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr CALL/WHATSAPP 👇🏻👇🏻 wa.me/2349030398006

TIKTOK 👇🏻 https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________