
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 28
..... it was spoken. He has nothing to do with anyone but Imran, everything he does is quiet, he is always on the sidelines away from the noise and fun of others. However, wherever Imran is, a new friend and a new family member are attached to him. Since Imran is also not making a lot of noise, their friendship is perfect. But he made a lot of noise, and in the days before he finished telling Bama Haysam about their family members A to Z. While he, Haysam could not tell him anything after his name and their hometown Bauchi and Kano where they are now. It seems like now they are there from the back of the hall and they are chatting or I say Imran is making noise for him when the call of the new students reached them. Together, they stood up and went around the front, without looking for anything, they followed the rest of the caravan that was going to answer the call in the main meeting ground. After they finished gathering, when everyone was standing up, the chief officer stood in front of them with a paper containing a list of names and started speaking like this.. "Today, you will be assigned to your permanent companies. Once your name is called, move to your company's block. Tha
.......Rana ta biyu ta kasance da sabon sauyi ga su Haysam duk da dai zamu kira sauyin bamai yawa da tsanani ba ne. Domin kuwa daga gudu, sai tsalle-tsalle, da kiran Yes, Sir! da karfin murya, kowanne cadet ya fara jin cewa jikinsa na canzawa, kamar yanda rayuwa take canjawa daga barin ƙuruciya zuwa sabon ƙalubale mai banbanta kai da sauran jama'ar gari. Ba su da lokacin tunani na zahiri, amma kowannensu ya fara fahimtar cewa a cikin NDA duk suna amsa sunan masu daraja ɗaya ne da fuskantar ƙalulabe ɗaya a ƙarƙashin ɗoki, zumuɗi da burin zama soja...
>>>>>>>>•<<<<<<<<
Yau kwanakin mako cif da shigowar su Haysam NDA, a satin gaba ɗaya rayuwa mai sauƙi ce da cigaba da morar ƙuruciya da ƙarasa zazzage sauran wautar data rage a gaɓɓan jiki irin ta masu shekarunsu. Domin kuwa satin gaba ɗaya babu wani abin kuzo mu gani dake nuna musu ma an fara wasan, shiyasa wasu a cikinsu suka fara shagala da maida hankali a nishaɗi da ƙulla abota kawai a tsakani. Saɓanin Haysam yaro mara kwaramniya da yawan magana. Ba ruwansa da kowa sai Imran, komai nasa a nutse, akoda yaushe yana gefe nesa da hayaniya da nishaɗin sauran. Sai dai a duk inda yake Imran sabon aboki sabon ɗan uwa na manne da shi. Da yake shima Imran ɗin baida hayaniya sosai sai abotar tasu tai dai-dai. Sai dai shi yanada surutu, dan a kwanakin kaf har ya kammala bama Haysam labarin ƴan gidansu A to Z. Yayin da shi kuma Haysam bai iya gaya masa komai ba bayan sunansa da garinsu Bauchi da Kano da suke a yanzun. Kamar yanzu ma suna can daga bayan hall ɗin kwanan nasu ne suna hira ko nace Imran na zuba masa surutu kiran da akema su sabbin ɗalibai ya riskesu. A tare suka miƙe suka zagayo ta gaba, batare da neman ba'asi ba suka bi ayarin saura dake tafiya amsa kiran suma a babban filin taro. Bayan sun gama hallara kaf kowa yana daga tsaye a nutse babban Officer ya tsaya a gaban su da takarda mai ɗauke da jerin sunaye ya fara jawabi kamar haka.. “Today, you will be assigned to your permanent Companies. Once your name is called, move to your Company’s block. That will be your new home.” A tare suka amsa da kalmar, “Yes Sir!”. An fara kiran sunaye ɗakunan da sunayen wanda zasu kasance a cikinsu ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda aka kira zai amsa ya nufi inda aka nuna masa. Kowane ɗaki da iya adadin mutanen da ake buƙata. Kasancewar ana binsu a jere ne a kiran sunayen har aka zo kan H, Haysam na cikin H ɗin ƙarshe, cikin sa'a kuma Imran na cikin I ɗin farko. Kamar yanda ake kiran kowa aka kira sunan, Haysam Abdul-rasheed Shehu.” Cike da nutsuwarsa ya amsa yana mai miƙewa tsaye, “Yes, Sir!”, ya faɗa yana nufar inda aka nuna masa an rubuta Alpha room. Kamar abin almara sai ya sake jin an furta, “Imran Abbas.” Haysam ya juyo cikin mamaki, Imran ma yana kallonsa cike da farin ciki har murmushi na ƙoƙarin bayyana kansa akan fuskarsa. Shi kansa Haysam sai da ƙaramin murmushi ya bayyana kaɗan a saman tashi fuskar. Dan bayan ƙanensa Imran shine na biyu daya ji yana so tamkar jininsa. Gashi dai suna matsayin sa'anni ne a shekaru, amma raunin Imran dake a bayyane yasa yana jinsa kamar ƙaninsa daya kamata ya bama garkuwa. Badan Imran ya bashi labarin shine yake son aikin soja da kansa ba da ya ce an tilasta masa ne da tsiya saboda yanda yake a raunane. An ƙaro mutum biyu cikinsu, dan kowanne ɗaki na ɗaukar mutane huɗu ne. Gado biyu ne sama da ƙasa. Biyu a sama biyu a ƙasa. Sai lockers da sauran abin amfani kowa da nashi da ma sunansa a jiki. Kowane group an haɗa su da Officer ɗin da zai kula da su. Bayan sun shigo nasu ɗakin wanda ya jagorancesu ya nuna musu ɗakin da faɗin, “Each room, four cadets! You are brothers now. You eat together, you fight together, you win together.” “Yes Sir”. Sunan Haysam ya fara kira yana nuna masa nashi gadon. “Haysam Abdul-rasheed Shehu bunk na ƙasa, Imran Abbas kuma gadon saman Haysam. Da wani irin farin ciki Haysam da Imran suka kalli juna suna murmushi kamar ɗazun, wannan lokacin ya tabbatar musu cewa rayuwarsu zata ci gaba da tafiya a tare kenan, abotar da aka ƙulla batare da tabbacin rayuwar waje ɗaya ba bisa rahamar UBANGIJI da dubin zuciya ta tabbata.. Suma sauran kowa an bashi nashi. Basu zauna ba suka fara shirya abubuwansu a inda ya dace da yanda suke buƙata. Musamman ma abokai biyu da farin cikinsu ya kasa ɓoyuwa.
★Da daddare bayan kowa ya kwanta, sai Imran ya ɗan leƙo daga sama, yana magana a hankali da kallon fuskar Haysam da yay kwanciyar rigingine a gadonsa yay filo da hannayensa duk biyu. “Zak... kana jin kamar rayuwa ta canza ko?” Buɗe idanun Haysam yayi a hankali ya sauke su kan fuskar Imran daya leƙo ta sama. Wani ɗan guntun murmushi yay masa. Kamar bazai ce komai ba sai kuma a ciki ya furta, “Imran!. Tabbas rayuwa ta canza, canjawar data nisanta mu da ahalinmu da su kaɗai muka sani a rayuwar jiyanmu. Amma da kai tare a nan sai ta zama mai ɗebe kewa da koyar da sabon darasi” Ƴar dariya Imran ya yi cike da jin daɗin kalaman sabon abokinsa Haysam. Hankali kwance kuma kai tsaye cikin son fidda abinda ke zuciya ya ce, “Ni ma haka nake ji My Zak-Shadow, kamar kai ne garkuwata, ɗan uwana jinin jikina da ya ɓuya sai yanzu ne ya bayyana min kansa”. Hannu Haysam ya miƙa masa, shima Imran ya miƙo nashi suka riƙe juna. Cike da tabbatarwa ya ce, “Ni kuma ba zan bar ka ka faɗi ba in sha ALLAHU Imran. Ba'a nan kawai ba, a ko inama. Ka sani kana cikin lagona da in har aka hareni ta hanyarka tabbas zan faɗi, faɗuwa irin ta kwanciyar da babu juyi a ciki. Ka riƙe alƙawari, ka riƙe amana, ka tuna wannan koda anan gaba”. A hankali hawayen da suka cika idon Imran suka gangaro suna ɗiga a fuskar Haysam. Bai share ba, bai sakar masa hannu ba kuma har wani lokaci. A wannan daren kafin su rufe idonsu, sautin bugun tambarin alƙawarin riƙe amanar juna ya gama zagaye zuciyoyinsu. Rayuwar soja ta gaske ta fara a cikin ƙwaƙwalensu, sun yarda su biyu sun riga sun zama abokai, aminai, kuma ƴan uwan juna a cikin ɗakin Alpha dake wannan makaranta ta NDA.
Ƙarfe 4:30 na asuba aka busa ƙararrawa mai ƙarfi. Duk da har yanzu duhu ne muryar ɗaya daga cikin senior cadets ta farkar da su Haysam kamar sauran ƴan uwansu sabbin ɗalibai. “Wake up, gentlemen! You’ve got 5 minutes!” Imran sarkin tsoro kuwa ya zabura yana neman faɗowa a gadon, jikinsa sai rawa yake saboda tsoro. Haysam kuwa ya tashi da natsuwa kamar yanda ya saba a gida idan Mammah ta tashe sa. Gadon ya dafa cikin sanyi da muryar wanda ya tashi a barci ya furta, “Ka nutsu Imran, ka sauka a hankali. Ka tsaya a gefe na, ka koyi komai a hankali da nutsuwa, gaggawa taɗiye mutum take daga cimma burin nasara, haka Abiy na ke gaya min sanda ina yaro”. Ya ƙare maganar yana kama hannun Imran ya taimaka masa ya sauko a hankali. Suna fita daga ɗakin iska mai sanyi ta bugi fuskokinsu, sai ƙarar ƙafafun ɗalibai kake ji a kan ƙasa. Wani senior mai ƙarfin jiki ya tsaya a gaban su da fitilar hannu yana ta faman haskesu cikin ido da faɗin, “Down for push-ups! Let me see soldiers, not boys!” Gudu suka fara iya ƙarfi kamar yanda aka basu umarni. Tun ba'ai rabin filin ba wasu suka fara kukan gajiya. Imran kam da ba ƙarfin zuciya yana neman kaiwa ƙasa ne ma, amma Haysam ya matsa kusa da shi, yana faɗin, “Ka cigaba, kada ka tsaya Imran. Ka kalle ni kaji. Idan ka faɗi ka sani nima zan faɗi”. Wannan magana ta ƙarfafa shi sosai har ya yi mamakin kansa, ɗan daga nan yaji kawai ya ƙara ƙaimi har suna tafiya a jere da Haysam, Alhamdullah cikin nasara suka kammala round ɗin farko. Koda aka ɗan huta aka koma kuma nan ma bai sare ba sam. Dama shi oga kwata-kwata ko'a jikinsa. Komai Haysam na yinsa ne da ƙarfin jiki da zafin nama kasancewar zuwa yanzu ya saba da wahalar rayuwa, to tallar da yake yi ɗin nan zagaye kasuwa ai ba wasa ba. Wankau ɗin Mammah, ɗibar ruwa. Hatta daka idan ta amsa tare sukeyi in dai yana gida. Wannan wahalhalu sun taka rawar gani a rayuwarsa ƙwarai da gaske har yake jin wannan ƙwarin gwiwar a yanzu da son ƙarfafa irin su Imran masu rauni da gata yasa basu saba da wahala ba. Bayan an gama sunyi sallar asuba, suka dawo wajen rarraba breakfast packs. Imran yana jin kamar ƙafarsa bata motsi da ƙyau, sai Haysam ya karɓi nasa kwanon ya riƙe masa zuwa wajen zama. Sannan ya taimaka masa ya zauna yana jera masa sannu. A gefe ɗaya, wasu senior cadets suna kallon Haysam cikin mamaki, sauran ƴan uwansa duk a galabaice, amma shi a tsayensa yake kamar ma baiyi komai ba yana a nutsuwarsa da karfin hali, ga kuma yana da tausayi fiye da kowane sabo a cikin su. Wani daga cikinsu ya ce, “Wato wannan yaron akwai wani abu daban a idanunsa, ku kula sam bashi da tsoro ko fargaba balle jin karaya kamar yanda sauran suka nuna”. Wanda ke kusa da shi ya ce, “Ƙaryar banza, yo mi aka fara da mazan. Yau kawai kake masa wannan yabon. Ka bari suci watan farko dan Babansa wlhy sai ya rusuna wannan zafin kan nasa yabi iska”. Dariya suka sanya suna mai tafawa cike da shaƙiyanci. Duk abinda suke faɗa kuwa a kunnen Haysam, amma ya basar kamar ba jinsu yake ba yana maida hankalinsa ga Imran dake shan ruwan zafi a wahale. Koda Imran ya kallesa sai ya sakar masa murmurshi, baki Imran ya ɗan tura tare da faɗin, “Ka bar yi min wannan murmushin naka mai kama dana ƙeta. Wlhy da kai ne kawai nake jin karfin hali a nan, amma ji nake kamar na fasa na gudu gida”. Haysam ya sake murmusawa yana daidaita beret ɗinsa a saman kai. “ Haba mazan fama wane gudu kuma ana zaune ƙalau, ai in ka ganka a waje hutu zamu, in sha ALLAHU kuma mu dawo da ƙafafunmu a ɗora daga inda aka tsaya. Daga yau ka ɗauka mu biyu ne a tare, wani bazai bar wani a baya in sha ALLAHU. Ba zan a taɓa barin wani ya cutar da kai ba. Kaima bazaka taɓa barin wani ya cuta min ba”. “Yes Sir! Ina sha ALLAHU”. Imran ya faɗa yana salute ɗinsa. Dariya Haysam yayi yana kai masa naushi. Da sauri ya kauce shima yana dariya. Idan ka gansu dole su birgeka, dan a kallo ɗaya zaka tabbatar da aminci mai tsafta ya shiga zukatan waɗan nan matasan zakunan guda biyu. Kuma ina sha ALLAHU zasu kafa tarihi mai ban mamaki da taɓa zuciyar duk wanda zai bibiyi labarinsu.........✍🏼
__________
TALLAH
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JuUwr2QU7XMEYXZ7L7 Mmn surayya me kayan kamshi Ina amaran da uwayan gidan tou kumatso kusa Mmn surayya ta gwangwaje ku da kayan kamshi munada Turaran wuta na danal banat Kajiji Turaran kaya watau abbasiyya Kabbasa spray Humra Kwallacca Uwa uba Ina kuyarda yadda xaki hadasu Zaku iya samuna ta wannan number wayar kamar haka👇 08103143517 Ina katsina Ina aika kaya ko ina
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 29_
__________________
https://wa.me/+23408067422528 Kina son rage kiba ba tare da kin daina cin abunda kike so sannan ba tare da kinyi gudawa ba? To kimin magana domin samun hanyoyi da zaki rage kiba ba tare da kinsa wahala ba. Ko kuma matsalar gashi ce ke damunki, ko rashin tsahon gashi ne, shima muna da solution dinsa. Ko kuma fatar ki tana lalacewa ne a sanyin? Muna da ingantaccen man da zai gyara miki kafafunki ko kuma kamar ta jarirai. Ko kuma kafarki ce take kaushi a sanyin nan muna da ingantaccen mayuka Ko kuma man gyaran fata kike so da zai gyara miki jikinki a sanyin Nan ?duk muna dasu ba tare da kinsa wahala ba sannan 100% natural ne. Yar uwa idan ma bangaren samun kudi shima kike nema shima duk zamu koya miki. Kedai kawai ki mana magana domin karin bayani.
https://wa.me/+23408067422528 “Shin Ke uwa ce, kina son samun kuɗi ba tare da kin fita kin bar ’ya’yanki a gida ba?” ko kuwa ke student ce kina son samun karin kudin shiga ko kuma ma dai kawai kison karin side hustle ne Tare da Oriflame, za ki iya yin kasuwanci daga wayarki a gida. Ba tare da kin fita ba. Mata da yawa sun riga sun farga da wannan Kasuwanci kuma suna moriya dashi sosai, suna making kudi daga gida, kuma ke ma za ki iya sannan bayan ribar ki zaa biyaki salary a karshen wata. ko kuma kina son yin siyayya for personal use ne ba tare da anci riba dake ba ga link nan a kasa zaki iya register da kanki it's free👇
https://shop.oriflame.com/NG-salmaibrahimismail/3M3HmQWe
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________