
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 15
..... he smiled at her, then he beat the girl who didn't answer and grabbed her shoulders with both hands and handed her over. He hugged her again and greeted her. Before he closed by saying, "The people of Kano all greet you, including houses and cars. The greetings of Inna and theirs, Tasi'u, are half a bag." She happily said, "Thank you! But why didn't Mom follow you and give them Tasiu. GOD, I always cry when I remember them." "If I drink ALLAH, from today I won't let the tears of missing Mom fall again, I will wipe them away with a smile and happiness. As for Tasi'u, don't worry, they will come, Nasiru said he will bring them to you. Mom is not really around here, maybe you have to give birth." It is not a small shame that the word was born. After that her mouth fell dead and she didn't speak again and then she slipped her body from his that was resting her head on the floor. One of the mats grabbed her, she answered and spread it to him, he was struggling with her and his recovery, seeing how she was struggling with his face, he said she was going to give birth. Tsaff prepared the food for him on the mat, he also sat down and ate, he was very hungry. He said he was satisfied
....Zata fara mutsu-mutsu ya ce, “No Matar Abdul-rasheed relax mana, haka matan ƙwarai suke tarbar miji idan ya dawo daga tafiya. Shin bakiyi kewata bane? Wata shida ba kwana shida ba A'ishatul-humairah. I miss you fiye da yanda kike zato”. “Shi miye A mis ɗin?”. Ta faɗa cike da jin kunyar yanda ya dabaibaiyeta, gashi yaƙi bata damar fita a jikin nasa yanda take fata. Siririyar dariya yayi yana ɗago fuskarta ya lakace mata hanci. Sai kuma cikin raɗa ya furta, “Nayi kewarki buhu-buhu”. Itama murmushin tayi kanta a ƙasa. Sai kuma tace, “To wane yare ne kayi?”. “Turanci”. Ya bata amsa muryarsa na ƙara shigewa cikin maƙoshi, dan zuwa yanzu ta nutsu ta daina masa mutsu-mutsun son ƙwacewar. Zata ƙara magana ya ce, “Adana tambayoyi nan duk zan amsa ma Matar Abdul-rasheed anjima. Yanzu dai banu ruwa da abinci yunwa nake ji”. Zabura ta ɗanyi alamar tunawa, sai kuma ta janye jikinta a nashi ta durƙusa har ƙasa ta ce, “Kayi haƙuri ina yini, ka dawo lafiya ya hanya? Ya ka baro mutanen Kano?”. Idanunsa a kanta yay murmushi, sai kuma ya duƙa batare da ya amsa ba ya kamo kafaɗunta duka da hannu biyu ya miƙar da ita. Sake rungumeta yayi sannan ya amsa mata gaisuwa. Kafin ya rufe da faɗin, “Mutanen Kano duk na gaisheki harda gidaje da motoci. Gaisuwar Inna da tasu Tasi'u kuwa tafi rabin buhu”. Cike da farin ciki ta ce, “Na gode! Amma miyasa Inna bata biyoka ba dasu Tasi'u. ALLAH kullum sai nayi kuka idan na tuna su”. “In sha ALLAHU daga yau bazan sake bari hawayen kewar su Inna su zuba ba, zan dinga share su da murmurshi da farin ciki. Su Tasi'u kuwa karki damu zasu zo, Nasiru yace zai kawo miki su. Inna ce dai ba lallai anan kusa ba, ƙila sai kin haihu”. Ba ƙaramin kunya kalmar sai ta haihun nan ta sakata ba. Dan haka bakinta ya mutu bata sake magana ba daga nan tama zame jikinta daga nashi dake mata daɗi kanta a ƙasa. Tabarmar daya ɗakko mata ta amsa ta shimfiɗa masa, shiko yana faman binta da murmurshi ganin yanda take ta faman sinne fuska dan yace zata haihu. Tsaff ta shirya masa abincin a tabarmar, shima sai ya zauna yaci dan yunwa yake ji sosai. Yaci ya ƙoshi yasha fura. Itako daya mata tayi tace ta ƙoshi bai takurata ba. Yana kammalawa ta kauda kwanikan, shi kuma ya hau zame kaya yana faɗin, “Saura wanka. Bari nai amfani da ruwan drum ɗin can ƙila yafi ɗumi, tunda naga da alama amarya bata fara girki ba a gidan nan har yanzu”. “Inna tace ba yanzu ba”. Ta bashi amsa kanta tsaye. Ƴar dariya yayi da faɗin, “Ƴar gatan Inna kenan, wato ba yanzu ba”. “Eh mana, sai na ƙara girma tace”. “To Inna ta shirya kayan girki kam dan yau zaki girma”. Sam A'isha bata wani gane mi yake nufi ba. Shima kuma bai ƙara cewa komai ba ya fita. Koda tace bari tazo ta kai ruwan sai yace ya hutar da ita ta zauna ta jira shi...
Koda Abdul-rasheed ya fito wanka samun A'isha yayi ta ɓingire barci, bai tadata ba ya saka babbar riga a jikinsa ya fita a gidan, bai wani jima ba ya dawo da ledar nama tsire sai ƙamshi yake. Tadata yayi cike da lallaɓawa, zata fara masa shagwaɓar ya barta ita barci take ji ya dai lallasheta taje ta wanko fuska. Naman ya bata yace taci. Da farko kunya ta hanata ci saboda shi. Ganin haka yasa shi fita ya bar mata ɗakin, sai ta samu taci kuwa sosai, ta ɗauki sauran ta ajiye gefe. Ta fito danta kuskure baki ta ganshi zaune a waje, miƙewa yay yana tambayarta mi take so? Tace zata wanke baki ne. Bakinta ta wanke da gawayi da gishiri kamar yanda Inna ta koya mata tun a gida safe da dare idan za'a kwanta. Shima sai ya amsa yayi duk da yana da brush shi kam, itama kuma ya sayo mata. Suna komawa ɗaki A'isha ta kama gadonta zata haye. Riƙo hannunta yayi, dan haka ta juyo, suna haɗa ido tai maza ta duƙar da kanta ƙasa. “Barci kike ji?”. Ya tambaya cike da kulawa. Kanta a ƙasa ta jinjina masa. Ya ce, “Na baki gado na ki ɗana yau?”. “A'a ga nawa nima zan kwanta anan, kaima sai ka kwanta a naka”. “Miyasa baƙya so?”. “Saboda kowa yana da nashi”. “Toni nazo na ɗana naki?”. “Ai bazai ishemu ba”. “To shike nan ki hau nawa sai ki bani naki”. Bai jira tayi magana ba ya ɗauketa camak ya dire a saman gadonsa bayan ya ɗago labulen. Wani daɗi ya ratsa A'isha, a ranta tace (Ashe gadon daɗi ne da shi haka, kai miyasa ban taɓa ɗanawa da baya nan ba) shi dai dake kallonta bai san abinda take ayyanawa ba ya ce, “To kwanta sai da safe”. Ya zuge mata labulen mai suna zuge shige. Aiko tana ganin ya rufeta ruf ta wani baje a gadon tana murmushi, ALLAH a kwai daɗi, ga taushin katifa gana zanin gado. Ga filo sun zagaye gadon reras har sha biyu gwannin sha'awa, ai saiga hajjaju matar Abdul-rasheed cikin ƴan mintina barci yayi awon gaba da ita. Duk abinda take Abdul-rasheed na kallonta ta tsakanin labulen yana danne dariya. Sai da ya bari barcin ya mata ƙarfi yaje ya rufe gida ya dawo. Duk abinda ya dace tayi matsayin matar gida sai shine yayi. Ya kashe fitilar ƙwan su gaba ɗaya dan baya son kwanciya da haske shi kam sam, sai dai akwai Torchlight a kusa da shi koda yaushe. Labulen ya ɗaga kaɗan ya leƙasata, ganin yanda ta ɓararraje dole ya dara kaɗan yanzun kam. Dan da alama dai gadon nan ya lula da matar Abdul-rasheed ba ƙarya. A haka ya samu ya hau shima ya gyara mata kwanciya, sannan ya zuge labulen suka koma ruff. Haskata ya ɗanyi da fitila, da gaske barcinta take hankali kwance alamar bata da wata matsala, wato babu abinda yakai ƙuruciya daɗi, ita yanzu bata san mi yake ji ba, shiko tsahon watanni yana azabtuwa a kanta. Hora kan nasa kuwa ya zame masa alkairi, dan tabbas da ya taɓata kafin tafiyarsa da bazai iya sati biyu a Kano baizo Bauchi ba. Amma gashi Alhamdullah har ya cika watanni shida ciff ya dawo garinsa na haihuwa dawowa ta har abada, inma da abinda zai sake biyo baya da zai sa ya fita bazai kai kamar wanda yayi a baya ba, duk da yana da burin sake zurfafa iliminsa again. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, tare da kashe fitilar ya ajiyeta gefe ya gyara filo da ƙyau shima ya kai kwance.. Cikin barci A'isha ta fara jin saɓanin abinda bata taɓa ji ba tsayin rayuwarta. Wato hannun mutum a jikinta a firgice ta farka tare da zabura ta ƙwalla masa ƙara. Ƙarar data sashi saurin ɗora hannunsa a saman bakinta ya rufe shi ruff, tare da kamota ya riƙeta a jikinsa da ƙyar tana fisgewa. Babu shakka da ace akwai wani a gidan sai ya jita, ALLAH ya soshi su biyu ne. Da ƙyar ya tausata ta nutsu, bayan ya maimaita mata kalmar shine da Abdul-rasheed yafi sau goma kafin ta fahimta. A hakan ma bata nutsu ba ta saka masa kukan ita ta haƙura zata koma gadonta ta kwanta. Lallashinta yake da iya iyawa da kwantar da kai amma taƙi fahimta. Shi ko yana cikin wani hali, dan haka ya fara mata nasiha da son fahimtar da ita da yaren da zata gane. Ina hajjaju bata gane ɗin ba, daga ƙarshe dai dole ya barta ta sakko a wannan gado kuwa, dan neman shiɗe masa take alamar dai ta riga ta tsorata da shi.
A gurguje Please 🏃🏼♀️
>>>>>•<<<<<
Wasa fa farin girki tsakanin Abdul-rasheed da A'isha, dan tun yana ɗaukar al'amarin mai sauƙi harya fahimci baya samuwa cikin sauƙi. A washe gari wasan ɓuya ta sanya da shi. Zuwa wani daren yana fita sallar magriba ta sulale itama tabar masa gidan. Koda aka idar da salla bai dawo ba sai da akai isha'i. Nan ɗin ma Baba yabi gida duk dan ya bata dama ta yi barci cikin salama, dan ya fahimci yinin yau gaba ɗaya a ɗarare take da shi ko fara'a batayi ma har yara dake shigowa. Wajen ƙarfe tara baba yace ya tashi yaje gida dare nayi. Haka yay musu sallama shi da Inna ya taho, koda yazo gida ya shiga ɗaki wayam babu A'isha, sai yay tunanin taje bayi ne. Zaman jiranta yayi, duk da yayi mamakin ganin tiren abinci da aka aiko daga gidansu a ƙofar ɗaki, sai shine ma ya shigo da shi ciki. Shiru-shiru babu motsin Indo, dole fa ya miƙe ya fito tsakar gidan da Torchlight a hannu, ya gama haske-haskensa babu alamarta, ƙarshe dai har bayin ma ya leƙa nan ma babu ita. Hankalinsa ne ya tashi, babu shiri ya fito ya nufi gidansu, abinka da ba wani nisa ba, dan can hankalinsa kawai ya bashi zata iya zuwa. Inna da Baba na haramar shigewa suma su kwanta ya shigo, da mamaki suke tambayarsa lafiya?. A ruɗe yace, “A'isha. Naje gida ban sameta ba, na zata tana bayi ne sai dana ga daɗewan yayi yawa na leƙa babu alamarta, ashe ma ban lura bane buta na nan a ɗaki. Sosai hankalin Baba ya tashi shima, sai dai ita Inna abinka da mace sai ta tafi tunani. Ganin suna sallallami tace, “Ku dakata, nasan babu inda zataje tunda ba wani waje ta sani ba daga nan dai sai gidajen ƴan uwanka, kuma dai duk gamu a kusa. Bari mu fara duba nan gidan kota shigo”. Inna ta amshi Torchlight ɗin baba ta fara leƙa ɗakuna tana haskawa. Ilai kuwa sai ga A'isha a cikin yara su Alawiyya ƙannensa da yaran maƙotansu da suke zuwa kwana gidan tana shaƙar barcinta hankalinta kwance. Inna ta ce, “Yau ga ja'ira, ai gata nan tsakkiyar su Nana kuwa tana barci. Bara na tasota”. Lokaci ɗaya shima Baba tunaninsa ya harba, dan haka yace, “Kinga barta kada ki tasheta Karimatu.” “A'a ya zakace kada a tasheta Malam. Miye amfanin kwanciyar anan?”. “Barta ke dai, kai jeka sai da safe”. Duk da ba haka Abdul-rasheed yaso ba bazai iya musawa ba, cike da ladabi yay godiya ya tafi ransa fal mamakin A'isha. Ya fahimci yarinyar nan so take ta ƙwaɓa masa aiki dai kawai. Ashe labarin da abokinsu ya basu akan tashi matar data dinga komawa gida ma ita ana maidota kasancewar garinsu ɗaya suna masa dariya ashe shima tashi Shatun jiransa take. Tirƙashi akwai aiki kenan dai...........✍🏼
🤣🤣🤣Babban yaƙi kam😂.
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 16_
__________________
https://chat.whatsapp.com/Kf6jd57OsXHCG7cODNAje6
*_Kowace mace na matuƙar son taga ta gyara kitchen ɗinta kodan ta kalla itama taji daɗi 💃_*
*_Dunƙule kuɗin ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_*
*_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_*
*_To kwantar min da hankalinka ƙawata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sauƙi da rahusa._*
_Ta buɗe adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da daɗi, akan farashi mai sauƙi, kaya ƴan zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._💃💃
*_Za'a fara zubi 25th October in sha ALLAH 💃_*
20k monthly kayan 100k 10k monthly kayan 50k
*_Arha tafi bashi, hakama adashe yafi bashi. 💃 Ga sauƙi abaka tamkar ƙyauta 💃💃😀_*
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________