
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 32
....itow now. The way he kept calling him was part of him coming back from the world of his thoughts on Imran, he turned around and saw the Senior Garba, as if he was going to clear him and pass him, he thought it was a prankster so he broke off and went to where he was. Wanting to destroy Haysam's honor in front of the children, Senior Garba said, "Cadet Haysam! You think being praised makes you a soldier? We made you, remember that." Zak-Shadow's eyes were just staring at him as if he wouldn't touch him, his hands were in his pants pockets, and he wanted to compliment him. Garba smiled with sadness and hate that hides his anger, he looked at the boy and saw that the boy felt as if he had suffocated him and died, may God rest in peace. Looking into the eyes of Haysam, who was also looking at him with awe, he said, "Hmm.. perfect cadet. We will see how you face the Special Night Drill". Only Zak-Shadow shook and left the place, for several times he took the matter of Garba as a criticism of the movement.....
.......Komai ya cigaba da canzawa a kowane sakan zuwa minti da awoyi tamkar yanda kwanaki suka shuɗa zuwa watannin suka bada shekara uku data shuɗe. Su Senior Garba dake shekarar ƙarshe suna nan akan bigiren iska mai wahalar da kayan kara, domin kuwa har zuwa yanzu suna jin haushin yadda Haysam ya zama abin koyi, har officers ke yaba masa a bainar jama’a da yi musu misali da shi matsayin abin koyi. Sai dai kasancewar Haysam da kowa ke kira Zak-Shadow a yanzu ya zama jan wuya yasa su kansu shakkarsa suke basa iya yimasa abu kai tsaye kamar yanda sukeyi a shekarun baya na farkon shigowa. A yau ma ya fito massalaci da yay zaman yin azkar ɗin yamma bayan sallar la'asar Senior Garba ya kira shi gaban sabbin cadets da yake jagoranta. Harga ALLAH shi Zak-Shadow baiga ma Senior Garba ba, saboda hankalinsa yayi kan tunanin ina Imran ya shiga ne dan batare sukai sallar la'asar ba. Bayan an idar shi kuma ya zauna ɗaukar karatu kamar yanda ya saba a wajen malaminsu, daga nan yay azkar shine yake fitowa a yanzu. Yanayin yanda akai kiran nashi ya sashi dawowa daga duniyar tunaninsa akan Imran, cike da nutsuwarsa ya juyo sai sukai ido huɗu da Senior Garba ɗin, kamar zai shareshi ya wuce dan yasan shashasha ne sai ya fasa ya nufi inda yaken. Cike da son zubarma da Haysam ɗin mutunci a gaban yara Senior Garba ya furta, “Cadet Haysam! You think being praised makes you a soldier? We made you, remember that.” Idanu Zak-Shadow kawai ya ɗan zuba masa kamar bazai tanka shi ba, hannuwansa a cikin aljihun wandonsa, har yay niyyar yaɓa masa baƙar magana dan ya iyata kwali-kwali, bashi da yawan magana, amma idan ya yaɓa maka baƙa ɗaya sai ka kwana ka yini tana cizon zuciyarka, amma miya tuna sai ya fasa, a taƙaice ya ce, “With all due respect, senior, the Academy made us all.” Garba ya yi murmushi mai cike da baƙin ciki da tsana wanda ke ɓoye fushi, shifa duk sanda yaga yaron nan ji yake kamar ya shaƙeshi ya mutu ya huta ALLAH. Cikin kallon idon Haysam ɗin da shima ke kallonsa ƙyam ya ce, “Hmm.. perfect cadet. Zamu ga yadda zaka fuskanci Special Night Drill”. Kai kawai Zak-Shadow ya girgiza yana barin wajen, dan lokuta da dama ɗaukar al'amarin Garba yake matsayin soki burutsu da motsuwar kai. Yasan night drill ba abune mai sauƙi garesu ba cadets, ana amfani da shi ne wajen gajiyar da mutum ta jiki da ta zuciya matuƙa, gudu cikin duhu, rarrafe cikin laka, da ɗaukar kaya masu nauyi har zuwa safe. Wasu ma daga cikin cadets suna jin tsoro idan aka ce “special night drill”, amma shi bai taɓa ɗaukar hakan matsayin wani abun tsoro ko tashin hankali ba balle ya nuna damuwa. Ɗaki ya koma abinsa inda ya samu Imran ya dawo yana jiransa.
★ Da daddare kamar yanda Senior Garba ya faɗa ɗazun da yamma su Zak-Shadow suka fita Special night drill. Kasancewar akwai abinda Garban da abokansa suka shiryama Zak-Shadow yana gefe yana kallonsa cikin murmushin mugunta. John da shima ke kallon Zak-Shadow cikin taɓe baki da ƙwafa ya ce, “Wai shi yana jin kansa wani shege ko, zamu bashi banbancin kare da uban gida a yau, wannan karon sai mun karya shi”. Ƙwafa kawai sauran sukai batare da sun tanka ba. Shima Zak-Shadow da bai san sunayi ba ma ya cigaba da motsawa cike da karsashi da ƙarfin jiki mai tafiya dana zuciya. Sam babu gajiyawa a tare da shi, sai ma taimakawa waɗanda suka faɗi a hanya yake yi. Sun dawo a zagaye na biyu wasu sun fadi ƙasa, wasu suna shashshekar wahala harda masu share hawaye, amma shi yana tsaye, yana kallon Garba kai tsaye cikin shirun daya saba kowa kuma ya sanshi da shi. Shiru ne mai zurfi dake ƙona zuciyar maƙiyansa. A zuciyarsa kuwa ayyanawa yake. (Yau zan nuna maka Ba ruwan jarumta da wanda ya fara zuwa duniya ko ajin karatun duniya Garba. Ba zan rushe ba, in sha ALLAHU har abada bazan faɗi a ƙasanka ba sai dai kabar NDA da takaici na a zuciyarka kuwa. In yaso ka ajiye aikin soja ka koma rawar ƙoroso). Yanda Zak-Shadow ke kallon Garba sai ya ɗan ji tsarguwa a zuciyarsa ga shakka da kwarjininsa na cizonsa a rai, amma sai ya dake saboda izza, shawarar da zuciyarsa dake gargaɗinsa yabi cike da gadara ya ce, “Dismissed!”. Ba abinda Zak-Shadow da abokan Garba sukai tunanin ji zai fito a bakin Garba ɗin ba kenan. Dan haka ya bama abokansa haushi. Zak-Shadow kam ya wani bisu da kallo cikin ƙyaɓe baki ya bar wajen. Yana fara tafiya Imran ya ƙaraso suka jera yana goge laka daga fuskarsa. “Wallahi ba soja bane kai Zak… kai dutse ne. ALLAH tsoro ka bama Garba fa amma wata maganar banza yaso gaya maka da farko kamar yanda ya saba”. Zak-Shadow ya murmusa cikin nutsuwa da kallon Imran ya ce, “Kaji tsoron rabbi Imran. Ai dama dutse baya jin zafi, ni kuwa mutum ne ina ji, kawai ban bari su gane ne dan har abada bazasu ga Haysam Abdul-rasheed a ƙasan takalmansu ba in sha ALLAHU”. “In sha ALLAHU kuwa ƴan wahala.”
__________★
KOMAI NISAN JIFA....
Alƙawarin ALLAH ya cika. Shekaru sun wuce cikin wahala da zafi, ƙura da ruwan sama harma da sanyi. Haysam Abdul-rasheed Shehu da abokinsa Imran Abbas sun girma a cikin NDA kamar ƙasar da take haifar da ƙarfin hali da gwagwarmayar neman ƴanci.. Tabbas zuwa yau an manta da lokacin da ake kiransu “new boys.” Yanzu sune manya Seniors dake faɗa aji da shugabantar masu shigowa har ma da masu bi musu. Tabbas shekarar ƙarshe shekarar ƴanci amma shekara mafi tsaurin gwagwarmaya da karatu mai tabbatar da yaro soja. Haka su Zak-Shadow sukai juriya ƙwarai da gaske wajen tsallaketa tamkar yanda suka shallake na baya da suka shuɗe. Alhamdullah ga burin ƴan maza ya cika, NDA ta zama tarihi tamkar yanda primary da Secondary suka zama tarihi suma. A daren da suka karɓi takardar kammalawa, Zak-Shadow ya tsaya yana kallon harabar NDA, zuciyarsa cike da tunani. Wajen da ya sha ruwan sama, gudu a cikin laka, da azabar push-ups har yatsunsa suka kumbura, yau shi ne wurin da zai barwa tarihin da sai dai a tuna a bama ƙanne da ƴaƴa labari watarana. Imran ya matso kusa da shi murmushi na bayyana cikin fuskarsa mai tarin nutsuwa, “Zak-Shadow” ya kira sunansa da murya mai sanyi, bai jira amsawarsa ba ya cigaba da faɗin, “ka tuna ranar farko da muka shigo nan?”. Juyowa yay yana kallonsa fuskarsa da murmushi mai nauyi, cikin buɗaɗɗoyar muryarsa mai fita da amon mazaje ya amsa masa da, “Idan zan mance da wannan ranar tabbas zan mance da kai My Imran. Yanzu kamar jiya ne... kai da kukan nan naka da yasa na tsaya ina kallonka tamkar Ma'aruff ko Ja'afar a gabana”. A tare sukayi dariya, abinda Zak-Shadow bai cika son yi ba. To dama mai ganin suruntun nashi kamar hakan sai dai Imran ɗin ai.
★Alƙawarin ALLAH ya cika, Haysam ya samu cikar burinsa daya ginu bisa burin mahaifinsa. Ya kammala NDA bayan shekaru huɗu na wahala, gwagwarmaya, juriya da jarumta. A yau suke bikin Passing Out Parade ɗin su, musalta irin farin cikin da yake aciki abu ne mai wahala. Ba shi kaɗai ba, hatta Mammah da ƴan uwansa da malam Sulaiman da kawunsa da yazo daga Bauchi, da Innarsa Khadijah da Alawiyya suna cikin farin ciki. Domin kuwa sun halarci bikin passing out ɗin nasu su duka. Yanzu Haysam ba ɗan takara ba ne, soja ne cikakke, Second Lieutenant Haysam Abdul-rasheed Shehu (Zak-Shadow). Sun yi parade a gaban manyan jami’an soja da iyaye da ƴan uwa da abokan arziƙi. Ɗalibai da yawa da suka nuna ƙwazo a fannoni daban-daban sun samu ƙyautittuka na girmamawa, ciki kuwa harda Haysam. Lokacin da aka kira sunan Cadet Haysam Abdul-rasheed Shehu, sai dukan ɗakin ya amsa da ihun kiran sunansa daga mate ɗin nasa. “Sarki! Sarki! Zak-Shadow! Zak-Shadow!”. Kai kace zasu fasa hall ɗin ne har iyaye da suka halarci taron najin ƙagara da mamakin wane yarone wannan mai farin jini ga yaransu haka?, sai da aka tsawatar musu saboda ihun kiran Haysam da ya kasa miƙewa sai da Imran ya kama shi ya miƙar tsaye. Cike da nutsuwarsa ya tako ya fito inda ake buƙatar ganinsa. Ba ƙaramin ƙyau kayan sukai masa ba, sun zauna a ginannen jikinsa na asalin zakin ga ƙƴawu ga nutsuwa ga addini, dan goshinsa kawai ya isa baka shaidar shi mai ibada ne kodan damɓareren tabon sallar da yake da shi. Ba tabon salla kawai ba a yanayin nutsuwar Haysam kawai zaka tabbatar da akwai ilimin addini sosai a tare da shi.. Zak-Shadow ya amshi lambar yabo ta Discipline and Endurance. Ya kuma samu ƙyautar girmamawa ta Best in Field Tactics & Discipline, abin da ya sa Mammah da ƙannensa suka yi kukan farin ciki a wajen kallon taron da suka halarta. A tare ƙannensa suka tashi mazansu da matansu sukaje suka rungumeshi. A karo na farko idonsa ya cika da ƙyallin hawaye, wannan ba kawai nasara bace, ƙarshen tafiyar jarumta ce da cika burin Abiy da samar da farin ciki a zukatan ƴan uwansa da Mammah, inama Abiy na raye ya cimma wannan rana.. isowar Imran daya ɗan buga kafaɗarsa da dariya ya sashi haɗiye hawayen nasa. Sai kuma ya juya yana kallonsa, suma ƙanensa sakinsa sukai suka koma wajen zamansu. Kashe masa ido ɗaya Imran yay da faɗin, “My Zak-Shadow yanzu zai koma gida a matsayin soja na gaskiya. kaga yanda Mammah take kukan murna ita da su Ma'aruff.” Haysam ya murmusa, yana mai lumshe idanunsa ya sake buɗewa akan su Mammah sannan ya dawo da su kan Imran. “Tabbas Mammah tana kuka ne irin na farin ciki da cikar burin mijinta Imran, ba kukanta ita kaɗai take ba harda kukan Abiy da Umma duk a tare. Amma nima ba zan taɓa manta nan ba Imran. Wannan wuri ya juya ni daga maraya marar gata, zuwa mutum mai ƙarfi da damammaki da samun cikar burin mahaifi. Imran in sha ALLAHU sai na kaima Abiy wannan albishir har Bauchi a gobe-goben nan in dai ina da rayuwa”. “ALLAH ya cika maka burinka, kuma ba kai kaɗai zaka Bauchi ba harda Imran Abbas ɗan Abiy da bai sani ba”. Wani ɗan dukan basawa Zak-Shadow ya bama Imran a kafaɗa, sai kuma ya rungume shi hawayen da yake ta shanyewa suka samu damar ɗigowa. Shima Imran hawayen ne ke zubo masa. Yana ƙaunar Haysam, yana tausayinsa ƙwarai da gaske. Dan shi har yanzu bai san maraici ba, uwa da uba duk suna raye, kai shi tunda yasan kansa ba'a taɓa mutuwa a gidansu ba ma gaskiya. Sai dai a dangi haka sai kakarsu da ta rasu yana yaro sosai. Sannan gidansu su suna da kuɗi.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 33_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp
07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________