
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 42
.....re where are Imran. With the collection of dead bodies of the people of the town, more than forty people started to encounter them and Imran stopped them in one place. Then the wounded soldiers are examined by others in the town who are also wounded. In a quiet town, people are all hiding, except for the soldiers, just one look will tell you that they are all wet, some are fixing their guns, and some are checking their small wounds. The car stopped and they all stood up. With restraint they cut him. As his Captains arrived in front of him quickly, their faces also showed tiredness and worry. Zak-Shadow and his eyes reddened, his voice full of strength and pain, his eyes on Major Imran Abbas said, "I left the camp for two days only, but you are so careless that everything collapsed like this? What the hell is this?! Are you ladies or soldiers?!". When he spoke, his eyes were once again like coals of fire, and he was extremely agitated. Everyone couldn't speak, not even the one who was so shocked, like Major Imran, so even now he is the one who speaks. With great respect, Major Imran, who was standing next to him with his body covered in dust, said, "I'm sorry sir. We tried our
........Mahaukacin gudun da yay a hanya, wanda UBANGIJI ne kawai ya tsaresa kusan ƙarfe biyu na rana ya iso cikin jejin. Tun daga sansanin farko da aka kaima hari a daren shekaran jiya ya fara cin karo da tashin hankali, dan gaba ɗaya sansanin a hargitse yake, an fasa tantunan da harsasai tako ina huji ne, ga karnuka nan kusan huɗu kwance a mace an harbesu. Shiru babu kowa alamar mazaje nakan aiki. Sansaninsu ya ƙarasa da sauri, tuni ƴan tsirarun sojojin da ke a sansanin suka tareshi tare da miƙa gaisuwa. Ajiye mashin ɗinsa yay a wajen da yake ɓoyewa, tare da canja kayansa zuwa uniform ya zubama bindugu biyu bullets sannan ya fice. Kai tsaye inda baradan karnukansa suke yaje ya buɗesu. Ai ko suna ganinsa suka fara wani mahaukacin haushi. Bayan mota dake fake irin ta sojoji dake shiga kowane kwazazzabo saboda ƙarfin tayoyi ya buɗe musu duk suka shiga, shima ya zagaya gaba inda aka buɗe masa kusa da mazaunin driver, cikin sauri wanda zai tuƙa shin ya fice a wajen a guje zuwa ƙauyen Gangare inda su Imran suke. Da tarin gawarwakin mutanen garin fin arba'in ya fara cin karo su Imran sun taresu a waje guda. Sai sojojin da suka samu raunuka ana duba su da wasu a jama'ar gari da suma suka sami raunukan. Garin tsit mutane duk sun ɓuya, sai su sojojin kawai da kallo guda zai tabbatar maka duk a jikace suke, wasu suna gyara bindiga, wasu kuma suna ta duba ƙananun raunikan jikinsu. Motar na tsayawa duk suka miƙe. Tare da ƙamewa suka sara masa. Yayinda Captains ɗinsa suka iso gabansa da sauri, ilahirin fuskokinsu suma na nuna gajiyawa da damuwa. Zak-Shadow da idanunsa sukayi ja, muryarsa cike da ƙarfi da zafi idonsa akan Major Imran Abbas ya furta, “Na bar sansani na kwanaki biyu kawai, amma ku kai sakacin da komai ya rushe haka? What the hell is this?! Are you ladies or soldiers?!”. Yanda yay maganar idanunsa na sake rikiɗewa kamar garwashin wuta yay matuƙar hargitsasu. Kowa ya kasa magana, dan babu ma mai wannan zarran bare gigin, garama Major Imran, dan haka a yanzu ma shine yay magana. Cikin matuƙar girmamawa Major Imran dake tsaye a kusa da shi jikinsa da kura, ya ce, “I'm sorry sir. Mun yi iya ƙoƙarinmu. Amma mun ji kamar makiyan suna sanin duk motsinmu ne kafin mu yi. Kamar ana gaya musu abin da muke shiryawa ne kai tsaye. Sannan hari ne na bazata. Mun rasa haɗin sadarwa tun daren shekaran jiya. An kai hari biyu lokaci guda a Arewa da Yamma. Sojojinmu sun watse, mun rasa mutane da yawa. Wannan dalilin ne ya janye hankalinmu da sansanin mu, ashe shiri ne na musamman, hari ne na kauda hankali aka kaima sansanin nan shine ainahin target ɗinsu”. Sosai zuciyar Zak-Shadow ke hanƙoro a cikin ƙirjinsa, wani irin raɗaɗi da zafi mai ƙuna yake ji a ransa. Dan ya fahimci bayanin Imran fiye da yanda yayi masa shi, tabbas yaji a ransa dole ne harin ya kasance shiryayye, sannan an tsarasa ne ta hanyar amfani da fitarsa a jejin. Sanin fitarsa kuwa dole tana da nasaba da munafiki a cikinsu. Dan Imran bazai taɓa aikata wannan kuskuren a gareshi ba. Da rinannun idanunsa masu saka tsinkewar zuciya ya juya yana ƙarema sojojin da duk suka nutsu kallo. Nazarinsu yake ɗaya bayan ɗaya. Ya daka tsawa yana zagaya tsakaninsu, yana kallonsu kamar zai cinye su da idanun. Wasu daga cikin sojojin suka sunkuyar da kai, wasu suka tsaya cak saboda tsoro. “Wanda ya ɗauki nauyin ƙasarmu ba zai yi wasa da jinin mutanenmu ba!, dan kuwa duk soja na gaskiya ɗan ƙwarai ne kuma ɗan jalak ne. Yanda ya shiga da ƙarfin zuciya, haka yake karɓa da ƙarfin imani, sannan ya sadaukar da dukkan gaskiya. Ku sani duk wanda na gano yana fitar da wani sirri namu komai ƙanƙantarsa wlhy sai ya ɗanɗana kuɗarsa da mafi girman hukunci. Zan gano shi, ko da kuwa yana tsakanin ku kuma mafi kusa da ni. Dan haka tun kafin guri ya ƙure masa stand up! Fix this mess now!”. Shiru kake jin wajen ya ɗauka kowanne yana kallon kasa. Har kana iya jin bugun zuciyoyinsu dake kai kawo a ƙirazansu. Ya ɗan ja numfashi mai zafi shima, yana kallon garin da ya rikice. Sai ya sake daka musu tsawa cikin murya mai zurfi, wacce ke cike da takaici da iko, “You call this a village? Pathetic!” Janye idanunsa yay daga kansu ya fara taku a hankali yana kallon gawarwakin bayin ALLAH da basu taka ma kowa ba balle zubarwa amma aka musu irin wannan kisan zalunci. A wannan lokaci Zak-Shadow ya fahimci cewa ba kawai yaƙi da makiya yake yi ba, akwai wani babban yaƙin da munafukan cikin gida da haɗarinsu yafi na waje. Cike da zafin zuciya ya juyar da kallonsa zuwa sama, inda hayaƙi ke hargitsewa cikin iska. Ya rufe idonsa na ɗan lokaci, a saman lips ya furta, (Wannan ba yaƙi da bindiga bane kaɗai. Babban yaƙi ne duhu). Idanun ya sake buɗewa a kansu ya sake binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, yanzu kam cikin ɗan sauƙaƙa zafinsa amma da ɗaga murya da ƙarfin soja ya cigaba da faɗin, “Kun bar harin bazata guda ɗaya ya rikita ku haka? Kuna nunama shashashu masu dattin kai su masu ƙarfi ne akan karfinku why?! Why? My Soldiers! Why?”. Suma ji sukai gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi, kalamansa na ratsasu da sake ƙarfafasu da zaburar dasu. A tare suka sara masa tare da faɗin, “I'm sorry Sir!”. Iska ya ɗan furzar, cikin tsawa da sake zaburarwa ya ce, “Ku tattara mutane a bama ƴan uwansu su musu wanka ayi jana'iza, zamu mayar da martani kafin gari ya waye!” A tare suka amsa cikin murya mai rawar tsoro da ƙwarin gwiwa: “Yes, sir!” Shima cikin ƙara ƙarfafawar ya ce, “Move! Let’s show them what real soldiers look like!” Nan masa suka sake faɗin “Yes sir!” a tare.
★ Zak-Shadow baifi mintuna goma sha biyar ba jiragen sama na soji masu saukar angulu suka fara sauka a kauyen, yayinda sojoji ke shiga gida-gida suna fito da mutane kamar yanda ya bada umarni, a wannan fitowar kuwa sai gashi an zaƙulo yaran Dagger har uku da suka ji rauni suka ɓuya cikin wasu gidaje. “You see! Kuna nan zagaye da gawarwaki maƙiyanku na fake a cikin al'ummar da kuke bawa garkuwa. Abin takaici abin a kamaku da duka. Ƙasa duk sukai da kawunansu musamman Captains da Major Imran. Yayinda shi kuma ke ƙara hasala, ji yake kamar ya dawo da hannun agogo baya ya goge wannan zuwa gida nashi. Duk da ya san zamansa a jejin bazai hana komai ba matsayinsa na mutum kamarsu, amma yana jin kamar shine sanadin komai, kamar anyi amfani da tafiyar tasa ne aka tsara komai. An kwashe sojojin da suka raunata da wasu a mutanen gari da suma suka ji raunuka. Gawarwakin kuwa aka shiga gidaje da su akai musu wanka aka shiryasu cikin likafanin da su Zak-Shadow suka bayar. Haka aka jera su reras abin tashin hankali akai musu salla su arba'in da uku. Harda su Zak-Shadow akai sallar, sannan aka haɗasu a babban rami guda ɗaya da aka haƙa. Tuni rahotanni sun fara fita ga jama'ar gari, dan har sallar da sojojin sukama gawarwakin sai da aka nuna. Hankali ya matuƙar tashi, zantuka suka fara kai-kawo barkatai, dana gaskiya dana ƙirƙira. Yayinda anan cikin jeji su Zak-Shadow suke sabon shiri. Dan sun bar ƙauyen Gangare bayan an zuba sojoji tako ina suka shiga ƙauyen marke da shi ma aka kaima harin duk a daren jiya. Anan ɗin ma akwai sojojin, sannan harin baiyi tsamari kamar na Gangare ba, dan ba'a rasa rai ko ɗaya ba. Wanda suka jikata kuwa an kwashe su zuwa asibiti cikin birni kamar na Gangare. Suna cikin ƙauyen Marke suka sami rahoton gaggawa daga sojojinsu cewar a ƙauyen Bankaura an rasa yara matasa har guda hamsin da wani abu maza da mata. Cikin tashin hankali Major Imran da Zak-Shadow suka ɗauki hanyar ƙauyen Bankaura tare da wasu sojoji. Suna shigowa ana kiran sallar magriba. Sun sami garin a hargitse, iyayen ƴaƴa nata koke-koke cikin matsanancin tashin hankali. Tun ba'aje da nisa ba Zak-Shadow ya fahimci koma yaya ne ba'akai ga fita da yaran a garin ba sai dai wasu a ciki. Sannan dole-dole akwai bakin wasu a garin, dan wannan tarko ne na da ɗan gari akanci gari. Tuni yasa sojoji suka zagaye duka ƙofofin shiga da fita na garin. Tun a daren suka fara bincika wasu gidaje daki-daki. Binciken daya sa aka fara zaƙulo wasu makamai a wani gida an ajiye ƙarƙashin gadon matar gidan. Ta kuma rantse akan bata san wanda ya ajiyesu ba, kuma ko miji bata da shi ALLAH yay masa rasuwa sai yaranta huɗu duk bama masu wani girma ba. Amma babban an haɗa da shi a yaran da aka sace dudu kuma bai wuce shekara sha biyar ba. Kasancewar an sake haɗa musu na'urar sadarwa a yammacin yau cike da bada umarni Zak-Shadow yasa a kawo musu wasu na'urorin, dan tabbas akwai magana a cikin wannan ƙauyen na Bankaura ƙwarai da gaske. Sojoji sun cigaba da shiga gidaje, inda bincike ya ƙara tsauri matuƙa hatta inda bakai zato ba a gidan ka sai an bincika kuwa. Wannan kuma umarni ne daga oga kwata-kwata, wato Lt. Col Haysam Abdul-rasheed Shehu (Zak-Shadow), ba kuma sojojin ne kaɗai keyi ba harda baradan karnukansa da suka samu training mai wahalar gaske dako su sojojin bazasu nuna musu komai ba....
<<<<★><★>>>>
Duk wanda ya kwana ya tashi a garin bankaura in dai ya kai shekarun banbance rayuwa da mutuwa barci sai dai ɓarawo ya ɗaukesa amma bana zahiri ba. Waɗanda ma aka ɗaukewa yara sun kwana ne suna kukan tashin hankali. Da asubahi sai sojoji ne sukai kiran salla, dan babu wani mai kiran salla daya fita balle liman ko mamu. Kai sallar ma a cikin gidaje wasu basuyita ba sai da rana ta haska. Anan kuwa mituniyarku Nimrah sarkin rikici da ire-irenta dama barcinsu suka sha hankali kwance. Tana farkawa ma ta fito tsakar gida abinta wai zata wanke ido, sai da Umma ta kamata da ƙyar ta maida ɗaki. Kuka ta fara da tirje-tirjen ita yunwa take ji, “Umma ki barni naje gidan Iya mai koko na sayo”. Baba ne ya kamata ya zaunar kusa da shi, cikin lallashi ya ce, “Uwa kiyi haƙiri, idan yunwa kike ji a saka miki fura kisha da ƙuli, yau iya mai koko bata koko dan garin namu ba lafiya”. Cikin rashin fahimta Nimrah tace, “Baba zazzaɓi akeyi?”. Kafin ya bata amsa sojoji suka shigo gidan. Dan sai yanzu ne aka iso ta bangaren gidajen su. Gida ne gidan yawa, dole sojojin suka kasu kowane ɓangare.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 43_
__________________
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JuUwr2QU7XMEYXZ7L7 Mmn surayya me kayan kamshi Ina amaran da uwayan gidan tou kumatso kusa Mmn surayya ta gwangwaje ku da kayan kamshi munada Turaran wuta na danal banat Kajiji Turaran kaya watau abbasiyya Kabbasa spray Humra Kwallacca Uwa uba Ina kuyarda yadda xaki hadasu Zaku iya samuna ta wannan number wayar kamar haka👇 08103143517 Ina katsina Ina aika kaya ko ina. __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________