Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 33

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 33

.....ah. Especially the Jaafar secondary students. He was also pleased to see how Mammah's market had an impact at home. He visited Malam Zayyanu and his friend Malam Datti. They prayed for him a lot and expressed happiness for his success in NDA. Although he was on vacation, he did not stop exercising in the morning and evening, as they do in NDA. Sometimes when he is struggling Mammah even tells him to rest. He would just say, "Mamma, if I don't give it to you, my body will hurt." She had to let him go until their holiday was over, as he promised to go to Bauchi with Ma'aruff during the weekend. They visited the grave of their father and Umma and even their grandfather, Malam. No one knows that they went to their father's relatives except their uncle Jamilu, they did not spend the night that day when they returned to Kano. In August, he returned to Jaji, to do the Young Officers Course, where he was reunited with Imran, this time they stayed in the same room. Alhamdulillah they completed their course at the beginning of 1999, from then everyone was pushed where to start working. but there was a problem when we posted them in different places, he and Imran, but since they have exp

Standalone post1,935 words

......Zak-Shadow da su Mammah sun wuce Kano, zasuyi hutu na makwanni har shida. Ashe walima Mammah ta shirya masa. Dan haka suka iske gida cike da danginta anata girki. Ƴan Bauchi dai iya kawunsa ne kawai sai Khadijah da Alawiyya suka zo. Bai damu ba, wanda ya gani ɗin ma sun wadatar. Anci ansha an masa addu'oi kala-kala harda mutanen anguwa. Bayan kwanaki biyu gida ya koma sai su kaɗai, Zak-Shadow ya sake fahimtar rayuwa ta canja ga mahaifiyarsa, ta tabbata dai bata tare da sabon mijinta. Sai dai yanzun ma bai tambaya ba saboda girmamawa har sai da Mammah ta sanar masa komai a wannan karon da bakinta. Tabbas zuciyarsa ta hasala matuƙa, amma bai ce komai ba dai a zahiri. Itama Mammah data fahimci yanayin nasa sai tai masa nasiha da gargaɗinsa akan kar taji wani abu daga garesa. An riga anyi ya wuce sai a tari gaba. Badan yaso ba yay shiru kamar yanda ta gargaɗe san. A cikin wannan hutu ya samu damar bibiyar karatun ƙanensa, har zuciyarsa kuwa ya gamsu da yanda komai ke tafiya Alhamdullah. Musamman ma su Ja'afar ƴan Secondary. Ya ji daɗin kuma ganin yanda kasuwar Mammah tai tasiri a gida. Ya ziyarci Malam Zayyanu da abokinsa Malam Datti. Sun masa addu'a sosai da nuna jin daɗin nasarar da ya samu a NDA. Duk da yana cikin hutu bai daina yin motsa jiki da safe da yamma ba, kamar yadda suke yi a NDA. Wani lokacin idan yana fama Mammah har faɗa take masa ya huta. Yakan yi murmurshi ne kawai ya ce, “Mammah idan banyi ba jikina zai yi ciwo ne”. Haka dole ta ƙyaleshi har hutunsu ya ƙare, kamar kuma yanda yay alƙawari yaje Bauchi tare da su Ma'aruff cikin weekend. Sun ziyarci kabarin mahaifinsu da Umma har ma da kakaninsu su Malam. Babu wanda yasan yaje a ƴan uwan mahaifinsu sai kawunsu Jamilu kawai, dan basu kwana ba a ranar suka juyo Kano. A watan Agusta ya koma Jaji, domin yin Young Officers Course, inda ya sake haɗewa da Imran, a wannan karon ma a ɗaki ɗaya suka zauna, dan sai da sukai duk yanda zasuyi aka haɗasu cikin amincewar UBANGIJI. Alhamdullahi sun kamalla course ɗin su a farkon shekarar 1999, daga nan kowa aka turashi inda zai fara aiki. sai dai an samu matsala dan anyi posting ɗinsu waje daban-daban shi da Imran, amma da yake suna da oganni tuni suka nema oga Adetunji suka sanar masa damuwarsu. Shine yay ta kai kawo har aka haɗasu waje ɗaya yanda suke fata, antura su aiki zuwa 82 Division Enugu, inda suka fara rayuwar soja ta zahiri. A can suka gane cewa aikin soja ba na jarumtaka kaɗai ba ne, aikin zuciya da sadaukarwa ne.

★Su Zak-Shadow na Enugu cikin sabuwar rayuwar aikin soja, anan rayuwar Mammah da marayun ƴaƴanta na neman canja salo da fuskantar sabuwar jarabawar rayuwa. Domin kuwa Zak-Shadow bai wuce watanni uku a Enugu ba Tasi'u ƙanin Mammah ya zo kwatsam. Zuwan daya saka Mammah a farin ciki dan tayi tsammanin har abada ta rasa dukkan ƴan uwa a duniya. Da farko dai kamar abin arziƙi tsakaninta da Tasi'u, dan harda zama ya bata labarin rayuwar da yake ciki ta tashin hankali. Yarinyar daya aura basu ko ƙulla shekara ɗaya ba a rayuwar aure suka rabu, ya shiga halin rayuwa mai tsanani a sabuwar ƙasar da bai san kowa ba, haka ya jure saboda karatun da yake yi. To zuwa yanzu ya kammala, acewarsa har ya samu aiki, yanzu ma yazo gida ne domin wani aiki da zai yi na wata uku ya koma. Mammah ta jajanta masa ta kuma tayashi farin ciki. Sunyi sati kamar uku a wannan farin cikin kwatsam rana tsaka sai ga Tasi'u da lauyoyi har biyu da wasu mutane, wai yana son a raba gida a bashi nashi kaso. Mamaki ya kama Mammah, ta kalla gida ta sake kallo, tabbas gidansu babba ne, gashi a bakin titi, kusan a yanzu ma gidan yafi duk wani gida na layin ƙyau saboda gyaran da Alhaji Nura yay masa lokacin daya aureta. Da farko ta ɗan so tirzawa tai masa faɗa, ya nuna mata shifa ba yaro bane, sannan gidan nan dai yana da hakki ai kuma dolene a bashi nashi hakki. Ganin yana son su zubar da mutunci a anguwa tace ba damuwa yayi duk yanda yaso, ko ɗaki ɗaya ta samu ALLAH ya amfana zata zauna da yaranta. Haka kuwa akai yayta shiga da fita batare daya bari tasan yaya komai yake tafiya ba. Kwatsam a cikin wata na biyu da zuwansa ta nemeshi ta rasa. Duk inda ya kamata ta bincika kuma tayi amma babu shi. Hankalinta yaso tashi kawunsu yace karta damu kanta, ta barshi duk ma inda yaje zai dawo tunda ba yaro bane. Haka dole ta haƙura ta share. Abin mamaki cikar wata ɗaya saiga wasu mutane wai sunzo gidan nan da take ciki nasu ne an sayar musu, suka nuna mata takardu harma da shaidun gani da ido da akai ciniki da su. Hankalin Mammah ya tashi kwarai da gaske, sai ta rasa inama zata saka kanta dan tashin hankali, kawai ta yanke jiki ta faɗi sai da aka kaita asibiti. Kwananta biyu aka sallamota, abu dai kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba Tasi'u ya saida gida ya gudu. Masu gida kuwa sun bata wata ɗaya kacal suna buƙatar gidan akwai abinda zasuyi da shi. Wannan tashin hankali ya saka Ma'aruff da Ja'afar sulalewa suka tafi Enugu suka sanar ma Zak-Shadow. Kwatsam babu zato ya gansu, mamaki ya kama shi ya balbalesu da faɗa domin a ganinsa ai kasada ce zasu kamo hanya batare da sanin gari ba su taho. Su dai haƙuri suke ta bashi, Imran dai ya kwacesu da ƙar, shine ya basu abinci sukaci ya basu wajen kwanciya. Zak-Shadow bai saurarensu ba sai dare, anan ne suka sanar masa abinda ke faruwa da halin da Mammah ke ciki, suka tabbatar masa a yanzu ma sunzo ne bada saninta ba, dan sun tabbatar tana can tana nemansu ƙilama hankali a tashe.. Jin wannan zance ya sake ɗaga hankalin Zak-Shadow, haka ya samu da ƙyar da kamun ƙafa aka bashi damar zuwa gida kwana uku kawai. Ya taso ƙanensa gaba suka nufi Kano. Aiko hasashen su ya tabbata, dan sun sami Mammah cikin tashin hankalin rashin sanin ina su Ja'afar ɗin suke, sai kuma gashi ta gansu harda uban gayya Haysam. Kukan dake danƙare da ƙirjinta sai a lokacin ne ta samu ta yi shi. Wannan al'amari ya sosa zuciyar Zak-Shadow matuƙa. Wanda ma bai san fushinsa ba a wannan karon ya gani kwarai da gaske. Ɗan kuɗin albashinsa da yake faman ajiyar taro da kwabo a account ya kwashe domin sayen fili, sai dai a karo na farko Kano ta fita masa a rai gaba ɗaya, yana son yin nesa da ita nisa mai yawa ko mahaifiyarsa zata samu salama tamkar yanda ta baro Bauchi, amma kuma bai san ina zai maidasu ba, dan haka ya nema shawarar Imran ta hanyar kiranshi a wayar landline. Babu wani ja'in-ja Imran ya bashi shawarar zuwa Abuja kawai, ya kuma haɗashi da yayansa. A ranar Haysam ya bar Kano zuwa Abuja. Inda da taimakon yayan Imran suka samu fili suka saya. Sauran kuɗin daya rage ya sayi siminti da bulo aka fara ginin ɗakuna ƙwara biyu kacal. Kwana uku aka bashi kawai a wajen aiki, dan haka dole ya koma Kano yabar sauran aikin wajen yayan Imran. Yana zuwa Kano ya sanar ma Mammah komai, mamaki ya kamata sai kuma ta shiga yi masa faɗa akan dammi zai yi hakan. Shi dai kansa a ƙasa kawai yana bata haƙuri ne. Sai da ta kammala yace su fara shiri kawai, nan da kwanaki kamar goma zasu koma can shi kuma ya shirya ya koma Enugu. Haka kuwa akayi, kwanaki goma bayan komawar Zak-Shadow yayan Imran yazo har Kano da mota ya kwashi su Mammah da yaranta. Tafiyar data sakata kuka sosai, jikin ƴan uwanta yay sanyi da rashin taimakonta da basuyi yunƙurin yi ba har Haysam ɗin ya yanke hukunci. Dan sun so hanata da nuna mata zasu ɗauki mataki tace ba komai zata koma Abujan kawai dan itama bata son zaman Kanon a yanzu. Wannan shine sanadi kuma mafarin barin Kano dasu Mammah sukai suka dawo Abuja. Ɗaki ne guda biyu kawai, sai aka zagaye gidan da kwanon langa-langa. Dan Zak-Shadow ya nuna baya son taimakon komai daga wani saboda Yayan Imran yaso yin hakan. Shima kuma Imran ɗin yaso yin hakan amma ya haƙura dan yasan wanene Zak-Shadow, idan yace baya son abu to kawai baya so ɗin da gaske. Yana sake ɗaukar albashin watan ya nufo Abuja, kuɗin yay amfani da su wajen maida ƙannensa duk makaranta, su Ammar ma da ba'a saka ba ya sanya su. Dama Mammah tunda suka dawo bata zauna ba, haka ta dinga shiga tana fita wajen nunama mutane kayan sana'arta ta koli. Sannu a hankali aka fara ganewa, kasancewar sabuwar anguwa ce kafin mutum yaje kasuwa sai yafi ganewa zuwa wajenta sayen abu a sauƙaƙe. Ganin haka ta fara haɗawa da kayan miya, da wannan sana'ar da albashin Zak-Shadow suka cigaba da rike rayuwarsu, idan an samu ɗan rarar kuɗi a sai siminti a ɗan ɗora gini. Kwatsam sai kuma ga wata ƙaddarar ta sake afkawa Zak-Shadow lokacin da yake shekara biyu da fara aikinsu, wai ya buɗe wata gaskiya wani ogansu yayi kutun-kutun an saka shi a prison. ALLAH sarki rayuwa, a wannan gaɓar ALLAH dai ya ƙaddara Mammah kam bazata rasa ranta ba. Dan bama ita kawai ba hatta su Ma'aruff sun shiga wata irin gigitar rayuwa. Haka Mammah ta dinga bin duk wanda ta sani cikin roƙo da magiya don ganin Haysam ya kuɓuta. Amma ina, Imran ma iya bakin ƙoƙarinsa yake amma al'amarin kamar da wani babban shiri a cikinsa. Hatta su Adetunji sunyi iya yinsu Zak-Shadow bai fito ba. Ga baƙar wahala suna bashi ta tashin hankali kamar sun sami criminal, duk mai hankali yaga wannan al'amari yasan akwai lauje cikin naɗi a ciki, sai dai kai tsaye basu san wa zasu fuskanta suce yayi ɗin ba..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 34_

__________________

https://chat.whatsapp.com/L3BXH7JYlBRHIkFRiOjeW3?mode=ems_copy_t

UMMU KHALIFA COLLECTION

Ina Mata Yan kwalisa ina mata masu san kayan ado kamar Egyptian abaya sleeping drees kids were shos bags musk dahara original.

To kukanku yazo karshe domin ummu khalifa sun zo muku da duk wadannnan kayan dierct suke order dinsu daga Egypt zuwa gida Nigeria kaidai kawai kashiga link dinsu domin gani ya kori jiii..

Ba nan ummuh khalifa suka tsaya ba suna nemawq mutane visa masu shaawar shugowa kasar ta Egypt karatu ko yawon bude ido ko kasuwanci ku tuntubeta a number dinta +201017018846/07048811474/

KO kuma shafinta na tiktok https://vt.tiktok.com/ZSU1FEkjc/ __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________