
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 43
.....holding her hand, his crouching body leaning on her, his face with a smile said, "My daughter, what is your name?". She directly said, "Zakanyar Kawu Tanimu". He laughed a little bit, the way she said it, but then he said, "After Zakanyar Kawu Tanimu, what is their name?". She said, "Naja'atu. Nimrah. Mother. I have many names". Captain Musa smiled and patted his head. "The names are sweet, just like how beautiful you are. Do you think Inna's eggs are in this bag? What do you know about them?". When the people of their house were watching, she turned away and put her mouth to Captain Musa's ear and whispered, "Yesterday, Umma sent me to see her in the store, so I took his from the shop, so I didn't respect my father and my uncle when she came back. He rubbed his head more while he was recovering, and then he extended his hand to the soldier next to him. He quickly handed him the phone. He reached his ear tightly and stood up, one hand holding hers. It was as if he was in front of the officer he called and said, "Sir, we have found two thousand bullets again.....
......Kaf gidan sai da kowa ya fito tsakar gida suka fara bincike a kowane sashe. Nimrah uwar magana sai son sakin zance take yi Umma ta toshe mata baki da hannu. Sojan dake bincike a sashensu ne ya fara fitowa hannunsa ɗauke da botiki, gaban shugaban su ya ƙaraso dake tsaye inda kowa na gidan yake... “Mun samu bullets da yawa a nan ɓangaren”. Yay maganar dai-dai yana ajiye bitikin gaban ogan ya fiddo jakar dake ciki. Wani irin bugawar zukata Baba da Umma suka samu a tare. Musamman da Captain Musa ya buga tsawa da faɗin, “Suwaye masu wannan sashen?”. Rikicewa Umma da Baba suka sake yi, a take suka fara rantsuwar su basu san da jakar bama a sashen nasu. Zaram Nimrah dake kallon jakar ta ce, “Umma kwai ne a ciki fa”. Sai kuma ta zabura gaban sojan tana cigaba da faɗin, “Kai Baba ɗan sanda ƙwan Inna ne a ciki ka ɓoye kada ta gani ta dake ni”. Yanda tai maganar ƙasa-ƙasa cikin raɗa tana cacumar jakar ta maida a botikin yasa sojojin zuba mata ido, sai kuma Captain Musa ya kai duƙe gabanta ya riƙo hannunta, jikin ƙafarsa dake tsugunne ya jingina ta, fuskarsa da murmurshi ya ce, “Ƴata miye sunanki?”. Kai tsaye ta ce, “Zakanyar Kawu Tanimu”. Kaɗan ya rage yay dariya, dan yanda tai maganar, amma sai ya danne ya ce, “Bayan Zakanyar Kawu Tanimu sai wane suna kuma?”. Ta ce, “Naja'atu. Nimrah. Uwa. Sunana da yawa”. Murmushi Captain Musa yayi yana jinjina kansa da shafa kanta. “Sunayen kuwa masu daɗi, kamar yanda kike mai ƙyau kema. Kince ƙwayayen Inna ne a cikin wannan jakar? Ya akai ke kika sani?”. Inda mutanen gidansu suke ta kalla, ganin duk ita suke kallo ta kauda kanta da kai ɗan bakinta wajen kunnen Captain Musa cikin raɗa ta ce, “Jiya da Umma ta aikeni kai mata tuwo naga ƙwanta a akurkuki shine na ɗauka nasa a botikin, to sai ban ɗaukama Baba ba shima da Kawu ta dawo, shine na ɗakko duka jakar dan karta kamani, kaga ai zata iya zaneni ni kuma bana son duka”. Kanta ya ƙara shafawa yana murmurshi, sai kuma ya miƙama sojan dake kusa da shi hannu. Da sauri ya miƙa masa waya. Danne-danne yay ya kai kunnensa yana miƙewa tsaye, hannunsa ɗaya riƙe da nata. Sai da ya ƙame kamar yana a gaban ogan da ya kira sannan ya ce, “Sir mun sake samun harsasai da adadinsu zai kai dubu biyu a wani gida”. Banji mi akace masa daga can ba, yanda dai ya ɗan buga ƙafa da sake ƙamewa ya ce, “Yes Sir!”. Zai baka tabbacin umarni aka bashi. Daga haka ya sauke wayar ya miƙama yaran nasa. Idonsa ya maida ga mutanen gidan da sukai tsuru-tsuru cikin matsanancin tashin hankali. “Wacece Inna? Tare da iyayen yarinyar nan?”. ALLAH sarki su Umma duk sun ƙara gigicewa, musamman Inna da al'amarin ya haɗa da tsufa, tuni ta jiƙe jikinta da fitsari, jikin sai rawa yake yi sai da Umma ta kamata. Gefe aka maida su, babu jimawa Zak-Shadow ya shigo gidan baradan sojoji kusan huɗu biye da shi. Ƙamewa sojojin sukai a tare, suka sara masa. Hannunsa dake dunƙule kawai ya ɗan miƙar alamar amsa girmamawarsu. Fuskar nan kam ba sauƙi babu sassauci. Dan su kansu mutanen gidan su Nimrah shigowar tasa sake gogitasu tayi, kai da gani kasan BARADAN MAZA ne da kansu ba saƙo ba. Duk rashin tsoron Nimrah tana haɗa ido da shi da sauri ta koma bayan Captain Musa ta ɓuya tana ɗan leƙosa kaɗan da ido ɗaya. Zak-Shadow ya bi duk mutanen gidan da kallo irin na nazari, kafin ya ɗauke kansa ya maida ga sojojinsa, a nan ne ya hangi Nimrah dake ɓoye jikin ƙafafun Captain Musa. Da sauri Captain Musa ya shiga yima Zak-Shadow bayanin tattaunawar sa da Nimrah cikin harshen turanci. Sai da ya gama tsaf yana saurarensa sannan ya maida dubansa ga Nimrah. Abin mamaki a karo na farko yay mata wani ɗan murmushi, sai kuma ya muƙa mata hannu da muryar lallashi ya ce, “Zo Baby girl”. Kalmar Zo ɗin kawai ta fahimta, ta kuma san kiranta yake, dan haka ta maƙe kafaɗa alamar a'a, dan bata taɓa cin karo da mutumin daya bata tsoro da cika mata waje irinsa ba, ko babanta mutum ne mai sanyi hali da rashin hayaniya, bai taɓa dukanta ba, idan yaga Umma ma zata daketa shike cetonta. Haka ma Kawu Tanimu da kowa ke ɗaukarsa masifaffe a gidan, ita sangartata yake ko laifi tai baya dukanta. Risinawa Captain Musa yayi ya gwargwaɗa mata magana a kunne kamar yanda tai masa ɗazun. Karo na farko ta ɗago tana kallon Zak-Shadow. Sai kuma cike da ƙuruciya tace ma Captain Musa, “Da gaske baba ɗan sanda?”. Kai Captain Musa ya jinjina mata yana murmurshi. Kallon Zak-Shadow Nimrah ta sake yi, ganin har yanzu yana murmurshi sai ta nufesa da sauri. Hannu ya saka ya ɗauketa gaba ɗayanta, ɗaukar da ta saka Umma kallonsa hankali tashe. Wani mugun waro idanu tayi a kansa, jikinta da bakinta na ɗan rawa cikin suɓucewar harshe ta ce, “Bawan ALLAH kai ne?”. Ganin wanda take kallo take maganar yaran sojin suka daka mata tsawa, sai lokacin shi Zak-Shadow ma fahimci da shi take, karo na farko ya dubeta, kai tsaye kuwa ya gane ta, dan dama tunda ya kalla Nimrah zuciyarsa ke yi kamar yasan fuskarta, ashe kamanin mahaifiyarta ne. Hannu ya ɗagama sojan da ke mata tsawa, ita kuma duk ta firgice dan gani take harbeta sojan zaiyi. Zak-Shadow baiyi magana ba sai kallonsa daya maida kan Nimrah Ummanta kamar zatayi kuka. Cikin son kawar mata da hankali ƙasa-ƙasa ya ce, “Muje ki nuna min inda ƙwan Inna yake mu kwaso sauran ma, duka zan baku shi ke da mamanki”. Hawayen da take riƙewa na zubo mata ta ce, “To kace Kada Baba ɗan sandan can ya bugar min Umma na”. “Bazai bugeta ba ai”. Captain Musa ya faɗa cike da lallashinta shima. Sun motsa zasu tafi tace ita sai da Ummanta, babu yanda suka iya da wannan mulkin mallaka na Nimrah dole akabi yanda take so. Umma ce ta kaisu har sashen Inna, Zak-Shadow kam na ɗauke da Nimrah har yanzu. Sai da suka isa sashen ne ya sauketa ya riƙe hannunta, babu ko gargada ta kaisu inda akurkukin Inna suke jere da yawa dan tana kiwon kaji, zabbi sosai har ma da agwagi. Cikin bada umarni Captain Musa ya dubi yaransu uku dake biye da su, ai cikin sauri suka shiga bincike akurkayen ɗaya bayan ɗaya. Aiko abin mamaki daban tsoro sai ga abubuwa ana zaƙulowa. Ai tuni an shiga fancake komai dake sashen Inna, itama kuma an taso ƙeyarta. Baiwar ALLAH kuka take tana ƙari da rantsuwar bata san da wannan ajiya ba sam. Hasali ma bata san Nimrah ta ɗauki waccan jakar ba, ta dai ga an ɗiba mata ƙwai biyu, ta kuma san itace ke mata haka, wani lokacin ta kai cikin kajinsu wani lokacin tace zata soya taci. Ba ɓangaren Inna kawai ba gidan gaba ɗaya aka shiga masa filla-filla, yayinda aka tattare mazan kaf waje ɗaya, aiko mata da yara nata kuka. Bincike yay bincike har cikin rijiyar gidan da rumbuna ba'a bari ba, an ko samu abubuwa da yawa da sukafi na sauran gidaje da aka samu, kuma abin mamaki an rarrabasu a ɓangarori da dama ta yanda baka isa cewa tunda a sashen wane aka gani ba shine ya ajiyesu. Dole dai aka tattara su Baba da ƙanensa da yayunsa duka su kusan goma sha shida mazan gidan, idan ka cire Tanimu da yay tafiya a jiya da safe kowa yana nan. An bar wasu sojoji a gidan dan tabbas suna buƙatar tsaro, dan dole ne akwai mai alaƙa da su Dagger a gidan, idan kuma suka ji an samu kayan da ke gidan zasu biyo sahu na ganin sun ɓadda mai alaƙar da su ko ɗaukar wani mataki...
<<•>><<•>>•<<•>>
Kwanaki biyu kenan su Baban Nimrah na hannun su Zak-Shadow. Hatta Kawu Tanimu daya wuce birni anje an taho da shi. An kuma samu wasu tsirarun yara cikin waɗanda aka kwasa a garin a wani gida, sauran kuwa da alama an riga an fita da su. Har yanzu waɗan nan ƙauyukan suna zagaye ne da sojoji, musamman gidan su Nimrah dake cikin haɗari fiye da kowane gida a ƙauyen Bankaura, sai gidaje huɗu da suma aka samu makamai da yara tara cikin wanda aka sata. Tun waccan ranar Zak-Shadow bai sake shigowa ƙauyen ba dan yayi busy sosai, bincike suke babu wasa shi da su Imran da sabbin jami'ai da aka ƙaro musu. Yayinda su Captain Musa da sauran Captains ke aikinsu bisa jajircewarsu da yaran soji tako ina a cikin jejin. Yanzu ma sunzo yin wani sabon bincike ne a nan cikin gidan su Nimrah ɗin ta hanyar zanen hannun kowa, suma mazan gidan dake hannunsu duk an ɗauka acan sansani. Sun sami Nimrah na darzar kuka da birgima ita bazataci garin kwaki da Umma ta jiƙa ba shinkafa zataci. Umma kuwa ta zuba mata ido kawai tana kallo dan tashin hankalinta yafi ƙarfin rigimar Nimrah. Ba ita kawai ba duk macen dake gidan tana cikin tashin hankalin tafiya da mazansu da sojoji sukayi, ga yara babu su babu labarinsu dan har yanzu ba'a samo su ba. Imran sarkin son yara da tausayi ne ya zo har inda Nimrah take bori ya ɗagata cak batare daya damu da yanda tai buɗu-buɗu cikin ƙasa ba. Shi dai Zak-Shadow kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, sai da tai wani furuci ma Umma ya juyo a karo na biyu ya ɗan kalleta. Cikin kuka Nimrah ta sake maimaita, “Kuma sai naje na kira fatalwoyin bayan gida masu jan ido su saka ki a jakarsu su tafi dake tunda bazaki dafa shinkafa ba”. Mutane irin su Zak-Shadow nada wata baiwa ta tsarta da saurin tsarguwa. Sannan inda suna a gaɓar aiki basa raina abu komai ƙanƙantarsa koda ga waye yazo. Imran nama Nimrah murmushi da faɗin, “Yi haƙuri Baby kada ki kira ma Mama fatalwa in dai shinkafa ce ina da ita zan baki....” Zak-Shadow daya ƙaraso inda suke idonsa akan Nimrah da tunda ta hango yana tahowa ta ƙanƙame Imran da lafewa a jikinsa dan tsoronsa take ji. Yana isowa ta sake ɓoye fuskarta sosai a jikin Imran ɗin. Kai kawai Zak-Shadow ya ɗan girgiza, kafin ya saka hannu a aljihu ya ciro Dabino da yake yawan ci dan yana matuƙar son shi, zai iya ci miki dabino yasha ruwa matsayin abinci. Ɗan hannunta ya kamo ya saka mata, a karo na farko ta ɗan ɗago cike da shakka ta kallesa tare da hannun nata. Murmushi ya mata kamar ranar, sai ta tashi da ƙyau tana dariya cike da farin ciki.........✍🏼
Tunda aka ba Nimrah dabino aiko za'a sha labarin fatalwoyin bayan gida kenan, yau zamu san mai ɓoye fuska.🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️😂
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 44_
__________________
*🔥 RASH BEAUTY WORLD 🔥 duniyar kayan mata masu kyau da arha ,Ina masu son kaya na kyan gani, amma basu son tsada? To, *ki daina nema!* Rash Beauty World ta zo miki da komai:
*👗 Abaya masu kyau na zamani Egypt/dubai* 👜 *Bags masu kyau* *👠 Takalma masu ɗaukar ido* 💍 *Jewelry masu ƙyalli kamar na sarauta* 🍽️ *Kayan Kitchen masu amfani da kyau*
*Koma da Naira kaɗan za ki yi shopping kamar sarauniya!* 👑💃
✅ Farashi mai sauƙi ✅ Kayamasu quality ✅ Fast delivery
*Shiga group dinmu yanzu kiga sabbin kaya ,Kayanmu masu kyau ne kuma farashi mai sauƙi! Kar ki bari a baki labari don samun kayayyaki masu inganci* 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/GzcU1TcAem21oJedkisrhj?mode=wwt
*RASH BEAUTY WORLD – Inda kyawu da araha suka haɗu!* __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________