
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 21
.....squeeze them, half of his body outside his legs to the inner waist, the metal of the car separates them a little and lowers his waist and separates from the trunk. He is crying and calling the name of ALLAH and he is mentioning the name of Haysam and asking people to help him and look after his son who is dead. (GOD is the king, son and father😭, he is in torment but he is not himself. Oh GOD, forgive our parents 😭 🙏🏼, forgive them their sins O Rabbi😭😭). Abdul-Rasheed was barely able to get them in this car, and he went to the hospital with them. Before even reaching one of his friends, he was also full. It took almost an hour for her doctors to come to him before GOD accepted what he had done. This day must be a day of confusion and Abdul-Rasheed's family will never forget it in their lives. The day that separated them from Haysam and their father, came unexpectedly. (In other words, death! Death! Death creates tension, my brothers, death creates a great shock, wlhy we don't know what death is until the spirit comes to us. What plan do you have for her, what plan do you have for her? You finish, you don't finish or you haven't started, wlhy it comes, coming without lifting a f
......Tabbas an ɗauro auren Umaru lafiya a garin Barno, dan kuwa shi a can ya ɗakko tashi matar da suka haɗu a wajen karatu a Zaria. Su Abdul-rasheed sunyi gangami sun halarci wannan aure a sabbin motocin daya saya musu shi da yayunsa biyu, akan suma sauran zuwa ƙarshen shekara in sha ALLAHU zai saya musu nasu, sannan ya biya hajji zasuje shi da Babban yayansu. Amma rayuwa bata da tabbas, a yayin dawowarsu Bauchi motar Abdul-rasheed tayi haɗari, a ciki kuma shine da yayansa na uku a ciki, sai abokansa biyu da Haysam. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, haɗari ne mai gigitarwa da tada hankalin wanda ya gani, dan kuwa babbar mota ce ta hayesu tsaf. A take ɗaya a abokan Abdul-rasheed da Yayansa suka rasu, dan kuwa sune a gaban motar, abokinsa driver, yayansa a gefensa. Sai Abdul-rasheed da ɗayan abokin da Haysam dake tsakkiyarsu a baya. Wani hikima ta UBANGIJI sai akai kamar anyi wurgi da Haysam ta tagar motar, dan can waje gefe aka tsuntoshi babu rai, yayinda nan su Abdul-rasheed mota ya danne su, shi rabin jikinsa a waje ƙafafunsa zuwa ƙugu na ciki ƙarfen mota ya rabasu kaɗan ya rage ƙugunsa ya rabu da gangar jikin. Yana kuka da kiran sunan ALLAH yana kuma ambatar sunan Haysam da roƙon mutane su taimkesa su duba masa yaronsa karya mutu. (ALLAH sarki ɗa da mahaifi kenan😭, yana cikin azabtuwa amma bata kansa yake ba. Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭 🙏🏼, ka yafe musu laifukansu ya rabbi😭😭). Da ƙyar aka iya zaro su Abdul-rasheed a wannan mota, akai asibiti da su. Kafin ma a isa ɗayan abokinsa shima ya cika. Shi ko sai da yay kusan awa guda ma likitoci nata kai-kawo a kansa kafin ALLAH ya amshi abinsa. Wannan rana dole ya zama ranar ruɗani da ahalin Abdul-rasheed bazasu manta da ita ba a rayuwarsu. Ranar da ta raba su Haysam da mahaifinsu, ta zo cikin rashin shiri. (Wato mutuwa! Mutuwa! Mutuwa nada tashin hankali ƴan uwana, mutuwa nada gigita ƙwarai da gaske, wlhy bazamu gane wacece mutuwa ba sai randa tazo kammu. Wane shiri kai mata, wane shiri kake mata? Ka kammala baka kammala ba ko bakama fara ba wlhy sai tazo, zuwan da babu ɗaga ƙafa balle jiranka koda na sakan ɗaya danka kammala abinda ka fara😭😭).
Mata ƴan biki nata kai-kawo anan Bauchi, sai dai jikin A'isha dana Yakura duk a sanyaye kamar marasa lafiya. Ga yawan faɗuwar gaba da suke samu da nauyin zuciya. Ita Yakura sai kowa ke ɗauka ciki ne. Itako A'isha ganin tasha jiyya bata ko jima da miƙewa ba sai kowa ke mata uzirin da sauran nauyin jiki. Sai dai ba haka bane ba, mutane kuma basu gane ba haka bane sai lokacin da labari ya iso cikin Bauchi, tun anayi ƙasa-ƙasa kada su A'isha su fahimta lokacin ma da ran Abdul-rasheed har dai ta fasu bayan rasuwarsa. Dan dole aka kwaso gawarwakinsu huɗu reras idan ka cire Haysam ɗan shekara goma sha ɗaya dake gadon asibiti likitoci na ƙoƙarin ganin sun ceto tashi rayuwar. Hakama matar Ayuba Yayan Abdul-rasheed dake fama da tsohon ciki duk tayi sukuku. A lokacin da aka shigo da gawar Abdul-rasheed data Ayuba rawa jikin A'isha da ƙus-ƙus ɗin mutane ya fara shiga kunnenta ya fara. Cikin ɗimuwa ta fito daga ɗakinta batare data fahimci inama take ajiye ƙafa da ɗaukewa ba ta durƙushe a gaban gawar mijinta da aka shimfiɗar a ƙofar ɗakin nata, hawaye na zuba kamar ruwan sama da ba ya ƙarewa. Hannunta na karkarwa ta kaishi kan babbar rigarsa da aka rufa masa dake jiƙe da jini ta yaye a hankali, fuskarsa dake da ƴan ƙananun raunuka ce ta bayyana, sai kawai ta tafi luuuu ta kife akan fuskar tashi ta sume musu. Dai-dai faɗuwar Yakura itama data fito daga ɗakinta a guje, ita kam jini ne ya ɓalle mata abinka da mai ciki. Ga matar Ayuba can ma ƙudar dole ta sameta. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ya rabbi ya rabbi mun tuba, mun tuba ya ALLAH 😭😭. Gida ya ɗauki koke-koke da ƙyar ake tsawatama mutane. Yayinda aka zubama A'isha ruwa a jiki ta farfaɗo, Yakura kam dole Inna Salame ce a kanta ana ƙoƙarin tsaida jinin daya ɓalle mata. Haka aka shigar da Abdul-rasheed ɗakin A'isha da Ayuba cikin jini babban Yayansu da mai bi masa sukai musu wanka aka shiryasu a tufafinsu na gaskiya. Tufafin da kai da ni suke jiran mu ma. Duk yawan kaya masu tsadar man da kika tara bango guda na drawer da wanda ka tara duk nan za'a barsu dama anan muka samesu. A naɗemu a wannan yankin farin ƙyalle tal kamar yanda a yau akama Abdul-rasheed da Ayuba. Haka ma sauran abokansa biyu an kaisu nasu gidajen ana musu nasu shirin suma...
ALLAH sarki rayuwa kenan, taron biki ya koma taron makoki, da ƙyar aka samu A'isha ta iya sallama da gawar Abdul-rasheed. Yakura kam ma anata ƙoƙarin ceto rayuwar ta ne da abinda ke cikinta. Hakama matar Ayuba. Sauran ƴan uwansu makusanta sunyi sallama da gawar Ayuba da Abdul-rasheed kafin a fita da su ƙofar gida inda aka haɗe da sauran abokansa akai musu salla, sannan aka wuce da su makwancinsu na gaskiya. Makwancin da yake jiranmu ni dake, yanzu ko anjima ko gobe, koma yaushe ne dai sai tazo😭. Babu wanda hankalinsa ya koma kan batun Haysam sai washe gari. A'isha ta ɗan dawo hankalinta duk da a jiyan ma ba wani kukan shirme take ba. Yaran suna zagaye da su ita da Yakura da aka samu nasarar tsaida jinin daya ɓalle mata tun a jiya da dare. Sai Yakura ta ce, “Yaya ni naga kowa amma banga ɗan albarka na ba tunda gari ya waye”. A karo na farko A'isha tabi yaran da kallo itama. Su duka biyar suna nan, wanda take goye yana bayan Alawiyya. Cikin girgiza kai ta ce, Mama (dan haka take kiranta kamar yanda yaran ke faɗi) bana jin tun jiya ma ni naga ɗan nan naki ai”. A ɗan rikice Yakura ta tashi a zaune jikinta na rawa, idonta cike da hawaye ta ce, “Yaya tun jiya fa? Mun shiga uku ni Yakura, dan ALLAH ku nemo min cikin kawun nan ku, Haysam fa tare suke da Babansu Yaya. Kai Ma'aruff tashi maza kira min Kawu Nuhu”. Ba Yakura dake magana jikinta na rawa ba, itama A'isha rawar jikinta keyi, sai dai kamar wadda aka dokema ƙafafu ta gagara koda tashi balle cewa komai daga inda take. Har ita Yakuran ma tai ƙoƙarin daddafawa ta sauka a gadon tasa Ummi ta taimaka mata. Dai-dai nan Khadijah ta shigo, itama ido luhu-luhu alamar ansha kukan rasa ƴan uwa. Ganin halin da Yakura take ya sata saurin ajiye kwanon fura dake hannunta, dan ganin A'isha bataci komai ba tun jiya gashi yanzu har an kusa sallar azhar shine ta nema fura ta damo ta kawo mata nan ɗakin Yakura da taga ta shigo tare da yara duba ta. “Yi a hankali Maman Haysam (da yake haka suke ma Yakura alkunya, ita kuma A'isha suce Maman Ma'aruff) kin san da halin da kike ciki, inama zaki ke da akace ba'a son kina dogon motsi”. Muryar Fauziyya na rawa tace, “Yaya Khadijah Haysam, kin san fa tare suka tafi da Babansu, amma babu wanda yay batunsa tun jiya”. Sosai gaban Khadijah ya faɗi itama, dai-dai nan Ma'aruff ya shigo tare da kawunsu Nuhu, shima yana jin batun da suke tattaunawar hankalinsa ya tashi, sai lokacin ya tuna cewa lallai tare da Haysam aka wuce da Babansa asibiti, duk da shima babu wani alamu daya nuna yana a raye, amma yaji sanda ake sakashi a ambulance likitan na faɗin zuciyarsa na harbawa kaɗan-kaɗan, shiyasa ma ba'a sakashi cikin gawar su Ayuba ba. Ai babu zama ya fita da gaggawa, kai tsaye asibiti suka wuce shi da su Nasiru. Cikin amincin ALLAH suka samu Haysam ya farfaɗo tun da safe, likitoci nata cigiyar ƴan uwansa an duba kaf sun wuce tun juya kasancewar a rikice kowa yake. Tunda suka shiga ɗakin da Haysam yake kalma ta farko daya fara jeho musu shine “Kawu ina Babana?”. Babu wanda a cikinsu gabansa bai faɗi ba, amma suka dake cike da mazantaka suka zagaye shi suna lallashi da tambayar jikinsa. Shi ko yaro ne mai wayo, duk da shekarun nashi duka 11 ne a duniya ALLAH ya bashi basira sosai, sai ya ƙi amsa musu ya zuba musu ido kawai. Tausayinsa mai tsanani ya kama Nasiru, dama ga alhinin rasa aboki, kuma amini zagaye da ruhinsa. Sai hawaye sharr suka shiga rige-rigen zubo masa. Kafin ya kauda fuska Haysam ya ganshi. Kawai sai ji sukai ya ce, “Baban Kano kuka kake yi?”. Da sauri Nasiru ya shiga girgiza masa kai yana share hawaye. Amma sai Haysam ɗin ya ƙara faɗin, “Babanmu ya rasu ko? Irin rasuwar Baba da Inna da Gwaggon Maiduguri. Dama ranar nayi mafarki ai, dana gaya masa yace nai shiru kada na gayawa kowa mafarki ba gaskiya bane, gashi kuma ya zama gask....” Ya kasa ƙarasawa sai haɗiyar zuciya. Sai suka ga ya rufe idanunsa kawai. Gaba ɗayansu hawaye suke sosai, amma abin mamaki Haysam ko ɗigon hawaye babu a idanunsa, tunda ya rufe idanun nan shike nan, bai kuma sake magana ba har suka baro asibitin. Koda suka dawo gida mutane nata hamdala da ganin Haysam ɗin yana lafiya sai ƙananun raunuka. Kowa kuma na ƙara jinjina hukuncin UBANGIJI, dan duk wanda ya kalla motar su Abdul-rasheed da yanda su suka kasance, dan su dukansu likafaninsu sharkaf da jini aka bizne su a kabari amma ga Haysam ko babban ciwo babu a jikinsa. Babu wanda zai tunanin za'a samu wani mai sauran rai a motar nan. Rungume Haysam Yakura tayi tana kuka, amma A'isha ido kawai ta zuba musu. Koda Haysam ɗin yazo gabanta ya zauna bata iya ce masa komai ba, shima kuma bai iya yama kowa magana ba har lokacin. Duk wanda yace kuma yaga kukan Haysam a zahiri game da wannan rashi yayi ƙarya. Sai da dare A'isha ta kama shi a wani ɗan lungu cikin ɗakin Abdul-rasheed yana kuka shi kaɗai a cikin duhu. Hakan na nufin yazo ya ɓuya ne anan baya son kowa yaga yana kuka. A karo na farko taje kusa da shi ta zauna, tare da kamoshi jikinta ta kwantar da kansa a saman kafaɗarta, sai ya sake fashewa da kuka shima ya rungumeta. Itama kukan take yi sosai. Ranar a ɗakin nan suka kwana ita da shi, tana zaune dangan-gan, shi kuma tun yana a kafaɗarta har tai masa dabara ya zame ya kwanta kansa a cinyarta, a haka gabannin asuba barci ya sacesu su duka. Sai kiran salla ne ya farkar da su........✍🏼
Matan da suka rasa mazajensu ALLAH ya gafarta musu, ALLAH ya baku haƙuri bayin ALLAH, ALLAH ya raya muku zuri'arku ya albarkacesu, yasa su zama masu jinƙai a gareku😭😭🙏🏼.
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._