Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 37

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 37

..... Nimrah's trial, if I say that everyone knows her in this village, I am not lying. Full of controversy, she started to sneak in among the children to see what was happening, or to fear that the peanut butter in her hand would be spilled. Bako did not stand anywhere but the middle of the battlefield. As she entered, she put down the gallon of oil and the leather, took off her hijab, tied it, and went back to the middle of the fighters and stopped. She scolded and shook her head and said, "Abubu, push me to buy this fight, I can feel the anger of this Daharen sheriff. There is no need for Abubu to push Nimrah out, it is not strong for her since Dahare is throwing her, and she is older than Nimrah. Dahare will be nine years old. Dahare was looking at Nimrah while she was resting and pointed at me with her finger saying, "You Nimrah, why do you leave this fight? My son, I will join you with your mother's possessions in this field". so.....

Standalone post2,512 words

.......Taron yara ne a filin da ake kira dandali a ƙauyen. A wannan dandali duk wani abun kwalam da maƙulashe ana saidawa, da daddare kuma nan ƴammata ke taruwa yin gaɗa da hira da samari. Yanda ƙura ke tashi da ihun yaran da suka taru zai baka tabbacin faɗa akeyi. Gashi hantsi ne maza duk suna gona, kusan duk ta inda ka zagaya yaran ne sai mata masu satar fita anguwa ganin mazan basa nan. Tafe take tana ƴan waƙe-waƙenta da ƙaramar galon fara mai cin kwalba uku ta mai an zuba man gyaɗa da zai iya kai kwalba ɗaya da rabi a ciki, sai leda baƙa a ƙulle. Yanda aka ɗaure bakin galon ɗin harda leda zaka gane anyi haka ne dan karta zubar. Harta kama hanyar da zata sadata da gidansu ta canja saboda hango ƙurar dake tashi a dandali da ihun yara irinta. Sauri-sauri gudu-gudu kuwa ta nufi can, dan a duniya babu abinda ke burge Nimrah irin damben tsiya, iyayen sunyi faɗa har sun gaji, ga kawunta Tanimu na ɗaure mata ƙugu, da anyi magana yace a barta dan ita *_Zakanya_* ce soja ma zata zama. Tsabar fitinar Nimrah idan nace kowa ya santa a ƙauyen nan banyi ƙarya ba. Cike da rigima ta fara kutsawa ta cikin yaran dan son ganin abinda ke faruwa, ko tsoron a zumar da man gyaɗan dake hannunta batayi. Bako ta tsaya ko'ina ba sai tsakkiyar filin faɗan. Tana shiga kuwa ta ajiye galon ɗin man da ledar ta cire ɗan hijjabinta taci ɗammara ta koma tsakkiyar masu faɗan ta tsaya. Cikin tsiwa da rawar kai ta ce, “Ke Abubu matsa na sayi faɗan nan, dama haushin wannan shegiyar Ɗaharen nake ji. Babu musu Abubu ta matsa ta bama Nimrah waje, dama ba ƙarfi gareta ba tun ɗazun Ɗahare ke jibgarta, dan kuwa ta girmeta har ita Nimrah ɗin ma. Ɗahare zata kai shekara tara ma. Ɗahare dake kallon Nimrah tana huttai ta nunata da yatsa tana faɗin, “Ke Nimrah wlhy ki fita a wannan faɗan ba ruwanki, dan sai na haɗa ke da Abubun naci uwarku a filin nan”. “Sai dai kici uwarki”. Cewar Nimrah cike da tsiwa tana girgije-girgijen jiki ita a dole mai ƙarfi, sai kuma ta duƙawa ta dimtsi ƙasa a hannu biyu, ta sake matsawa gaban Ɗahare sosai ta nuna mata. “Gata tsiya gata arziƙi ki zaɓa”. Cikin takaici Ɗahare ta kaɓe ta tsiyar, ai ko sai kokawa ta kacame tsakaninta da Nimrah. Nan fa ihun yara ya ƙaru dan kamar wasa sai ga mutuniyar taku takai Ɗahare ƙasa ta dimbiji ƙasa ta cika mata baki da ita. Dambe yay dambe aka tambaɗar da man gyaɗar Nimrah, ledar ma dake ɗauke da ƙuli-ƙuli ciki tuni yara sun saka mata wawa. ALLAH ne ya kawo wata mata ta raba wannan tsiya da ƙyar bayan ta kori yaran wajen da bulala. Nimrah na huci tayi buɗu-buɗu da ƙasa har cikin gashin kanta ta fara neman galon ɗin mai da ledar ƙuli, yayinda Ɗahare ke kuka da zaginta da cewa sai ta rama. Da ƙyar matar nan ta janyeta ita kuma Nimrah ta ɗauki galon ɗin manta data kimbiɗe matar ta sakata a gaba suka wuce. Sai lokacin kuma kuka da tsoro sukazo mata. Amma taƙi bari kukan ya fito har matar ta rakata ƙofar gida tace ta shiga ita kuma ta wuce... Hassatu da a yanzu Nimrah ke kira Umma nata aiki da kallon yanda rana ke ƙarayi zuciyarta cike da tunanin ina Nimrah ta tsaya, ta ajiye iccen data ɗebo zata ƙarama wutar dambu da take yi. Gidansu gidan yawa ne mai sassa daban-daban dan haka ta shiga ƙwala kiran sunan ɗan facalarta da take jiyo suritunsa a sashensu. Daga can ya amsa yana fitowa, yazo gabanta yana faɗin, “Umman Nimrah gani”. “Lawwali taimakeni dan ALLAH ka bimin sawun Ninrah gidan Inna Yalwa na aiketa sayen mai da ƙulli tun gama karin kummalo ga shi har sha biyu ta wuce bata ba labarinta, maza ka duba min ita kaji”. “To”. Ya faɗa yana nufar hanyar babbar ƙofarsu, sai ga Nimrah dake jin duk abinda ma ke faruwa rakuɓe a bango da galon a hannu. “Ke Nimrah kizo Ummanki na kira”. Harararsa tayi, cikin son huce haushin faɗan da tayi a kansa ta ce, “Baza'azo ba ɗin, munafuki”. “Kece munafuka dai, minai miki zaki ce min munafiki?”. Duka takai masa da galon ɗin man, ya koma cikin gidan da gudu. “Lawwali ina aikar da nai maka kake shigowa da gudu?”. Nimrah ce zata dakeni, tana zaure”. Umma najin hakan tasan tayi tsiyar ne, in dai har ba'a zubar mata da mai ba to an zubar da kuɗin ne. Batace komai ba ta cigaba da aikinta. Sai da ta kammala ta shiga wanka ganin azhar ta gabato sannan Nimrah ta lallaɓo ta shigo cikin sanɗa ta ajiye galon ɗin. Ta juya zata koma da gudu Umma data fito a bayin ta manta sabulu ta kamata caraf. Wani ihu ta fasa mata kuwa. “Wayyo ALLAH na shiga uku Umma dan ALLAH kada ki dakeni, Inna ku kawo ɗauki Umma zata tumurmusa ni, wlhy kunkuru na da kafaɗata ciwo suke, na mutu na lalace a taimakeni.” Tsayawa kawai Umma tai tana kallon yanda take ihun da dire-diren iskancin. Sai ko ga kakarta da wasu a matan gidan sun shigo. Dai-dai Umman ta kai hannu zata mangareta surukar tata ta dakatar da ita. “Karki sake ki taɓata Hassatu, ke wai baƙya tausayin yarinyar nan ne kullum duka dai duka dai, gata abu ba abuba ko jikin kirki ta gagara yi saboda masifarki”. Ran Umma a ɓace ta ce, “Inna nagaji da al'amarin Nimrah a gidan nan, tun gama karin kummalonta fa na aiketa sayen mai gidan Inna Yalwa sai yanzu take dawo min da galon ɗin babu man babu kuɗin, dan iskanci kuma ta shigo ta faɗa min yanda akayi shine ta laɓe a zaure har tana shirin dukan Lawwali dana aika ya nemo min ita. Wannan wace irin rayuwa ce, jiba jikinta daga gani dambe taje tayi yarinya kamar wata namiji”. “Koma dai miye dukan ai ba shine magani ba addu'a ce, sannan kowane yaro da irin ƙuruciyarsa”. Inna tai maganar tana ƙwace Nimrah a hannun Umma. Dole ta sakar mata ita, tanaji tana gani ta wuce da ita sashensu aka barta da takaici, sai sake bada wasu kuɗin tayi aka sayo mata wani man. Ba kuma ta sake saka Nimrah a idonta ba sai dare da babanta ya dawo gidan....

>>>>>>★<<<<<<

Sai da suka je sallar azhar massalaci suka dawo sannan ya koma sashensu. Ƴammatan ɗazun kawai ne a falon, suna ma jin motsinsa suka shiga rige-rigen faɗawa bedroom ɗin kwanansu. Sai dai hakan bai hanashi fahimtar suna a gidan ba har yanzu. Sai da ya shige ɗakinsa ɗaya daga cikinsu ta fito cikin sanɗa ta shiga bedroom ɗin matar gidan. Tana zaune a bakin katafaren gadonta da yaji shinfiɗa ta alfarma kamar yanda jikinta ke cikin kwalliya. Ɗakin ya haɗu matuƙa, komai tsaf babu wani tarkace. Waya ce a kunnenta alamar magana take da wani, sai dai ganin yanda ƙanwar tata ke tsaye a bakin ƙofa fuska a marairaice ya sata ɗan kauda wayar a kunnenta ta rufe speaker ɗin da hannu. “Miya faru?”. “Aunty ya dawo fa, dan ALLAH kije ki bashi haƙurin”. Hararta ta ɗanyi da faɗin, “Naji. Fita ki bani waje.” Sai da ta tura baki gaba sannan ta juya fuuu ta fita. Ita kuma tai ƙaramin tsaki tana janye hannunta. “Mommy Please ina zuwa, wai ya dawo sashen. Bari naje kin san shi da baƙar zuciyar tsiya, duk yanda mukai zan kiraki. Amma dan ALLAH ki kwantar da hankalinki babu inda zasuje”. Banji mi akace mata daga can ba, ta dai yi ɗan shiru alamar saurare kafin ta yanke kiran ta ajiye wayar. Gaban ƙaton mirror ɗin ɗakin taje, ta ɗauka wasu turare ta ƙarama jikinta tare da mouch freshener sannan ta fito. Dining ta nufa ta ɗauki wani ƙyaƙyƙyawan basket ƙarami da aka shirya abinci a ciki ta nufi ɗakinsa. Shigowarta dai-dai da fitowarsa a bayi jikinsa na raɓar ruwa farar fatarsa tayi wani fayau sai towel ɗaure a ƙugunsa. Tabbas Zak-Shadow murɗaɗɗen mutum ne bana wasa ba, dan ko wasu ƴan wrestling ɗin albarka. Sarai yaji sallamarta da motsinta, amma yay biris ko kallon ƙofar baiyi ba yama wuce bakin gado abinsa yana ɗaukar wayarsa dake a bed side drawer tana vibration. Kiran ya ɗaga tare da kai wayar kunnensa. Dai-dai lokacin ta ƙaraso wajen itama bayan ta ajiye basket din acan saman table dake a tsakiyar kujerun ɗakin. A hankali ta manna jikinta da bayansa, ta zagayo da duka hannyenta biyu, ɗaya a ƙirjinsa ɗaya a saman shafaffen cikinsa mai manyan layukan six-pack. Sai ko daya ɗan lumshe ido saboda yanda ta fara zagaya hannun a jikin nasa, sai dai ya dake abinsa, yana cigaba da wayarsa hankali kwance. Bai kuma ajiye ba sai da ya kammala. Yana cireta a kunnensa yay ƙoƙarin janye jikin nasa daga riƙon datai masa, sake ƙanƙameshi tai cike da shagwaɓa ta furta, “Please my Cool one, I really miss you wlhy. I'm so sorry, dan ALLAH kada kaimin hukunci da laifin daba nawa ba. Bance kazo dan na ɓata maka rai ba”. A hankali ya ɗan saki huci, batare da yayi maganar da take son yayin ba yasa hannu ya cire hannayenta dake a jikinsa. Da sauri ta dawo ta gabanshi ta rungume shi tsam-tsam, tare da sakar masa kuka. Karo na farko ya ɗan ciji gefen lips ɗinsa, shiru kamar bazai kulata ba sai kuma a hankali ya ɗaura duka hannayensa biyu akan bayanta shima ya zagayeta yana sake matseta. Cike da farin ciki ta sake ƙanƙameshi da bashi kissis masu zafi a saman ƙirji, kafin ta ɗago tai ɗiɗɗishe da ƙafafunta dan ya fita tsawo kawai ta haɗe lips ɗinsu waje guda. (Ehem-ehem nai gyaran murya dan ganin al'amarin babbane), dan kuwa tuni ya ɗagata cak ya ɗora a gadon ta yanda tsahonsu yay dai-dai, tun abun nasu na iya tsayen ana sumbatar juna har takai suka zube a gadon gaba ɗaya...........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 38_

__________________

🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

https://chat.whatsapp.com/DMCa4TXOqV712jNc1UBBRH?mode=ems_copy_t

*_GYARA SHINE MACE_*

*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF 'YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_* 🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327

*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,

Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,😍

Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji😍

Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki💃

Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai , Mmn Yusuf likitar Mata💃😍

Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin sauki💃💃💃

Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babuku💃💃💃💃💃

Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima

KADAN DAGA CIKI WASU KALOLIN👇🏻👇🏻

Kalolin gumba Kalolin matsi Kalolin gari Kalolin tsumi

Zumar dabino Zuma Mai rubutu Zumar goron Tula Zumar ridi

Dahuwar kaza Dahuwar zabo Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar tsoka Tara Dahuwar Yan shila Dahuwar kwai Mai rubutu

Turaren mallaka Turaren Mara Turaren tsugunno Turaren k'irji Shuumar humra HATSABIBI turare Hatsabibiyar humra

Matan gaske Maltinat Mata Shayin Mata Tsumin kankana Sirrin tafin k'afa

Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a Akwai hadin farinjini na matar aure Akwai kwallin mallaka Zoben mallaka Set na Jigidar mallaka

*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbers👇🏻👇🏻👇🏻

07069711327 call or Whatsapp ,Ina maraba daku customers😍😍😍😍😍

Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327 sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata😊😊😊😊😊😊😊😊😊

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________