Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 46

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 46

..... she went to his stomach and he was smoking his big cigarette and he was looking at Dagger with a look that looks like contempt and humiliation. But because Dagger has glasses on his eyes, he can't see. He said in the language they were talking to, "You mean to come and tell us that you can't do it because the bastard took your children?". "Either way, sir! It's like the dust has weakened the strength of the wild beasts. Who is Zak-Shadow, let alone his children. I want to know if there is a way to get them out of his hands? Or should we just kill them before he takes them to the city as he is planning, but you should know that all of them who have been captured are very useful in our journey, especially this man from Bankaura, the son of this man has our biggest secrets that I am not sure if it is difficult, he will not reveal it like how he neglected his wife's daughter open work for us. His wife didn't hurt me either, this girl who looks like a little demon, since he met them, Ganuwa is his daughter and he hid from them..." "Do you think that means that he came to..." Black Spider said in anger and sadness. "I don't think so, Oga, because Ganuwa made sure that the girl came

Standalone post2,028 words

.........*_01:am_*

Zama a duhu tamkar ɗabi'a ce ta wannan ƙungiya, musamman a lokacin yin meeting. A yau ɗin ma da zaman nasu ya kasance na gaggawa ba kowa da kowa bane a falon. Ogansu ne kawai sai Black Spider da yaronsu Dagger. Dagger bawani muhimmanci ne da shi a wajensu ba face KAREN FARAUTA. Dan kuwa suna kwance ne yana musu yaƙi da horar da yaran mutane a tafarkin hatsabibanci. Shike da yaran dake musu haƙar ma'adanan yankin Bankaura da sauran ƙauyukan wajen da adalinsu suka samar da ƙungiyar ga'addaci da zata janye hankalin mutane daga ma'adanan saboda kafawa da tsarewar jaruman jami'an ƙasar sukayi irin Zak-Shadow. Kuɗi kam suna sakarma Dagger ta yanda yake sake ruɗuwa da zama a rufewar idon sai da ƙasarsa da yankinsa hankali kwance batare da jin yana aikata kuskure ba ma. Shima kuma yana amfani da kuɗin wajen ɗibar ƴaƴa a cikin tafiyar cikin sauƙi saboda ƙarancin tallafi daga matasan ta hanyar ayyukan yi akoda yaushe. Ogan nasu daya kasance bamai yawan magana ba sai baƙar mugunta taf cikinsa ya wani zuƙi ƙaton sigarinsa yana ma Dagger wani kallo mai kama da raini ƙo ƙasƙanci ne ma oho masa. Amma kasancewar eyeglass ne a idonsa shi Dagger ba gani yake ba. Cikin harshen da suke magana da shi cike da isa da ƙasaita ya ce, “Kana nufin kazo gaya mana bazaka iya ba saboda banzan can ya kama maka yara?”. “Ko ɗaya sir! Ai ko kura ta rame tafi ƙarfin wawason namun jeji. Waye wani Zak-Shadow ballantana yaransa. Ina son naji ne ko akwai hanyar fitar da su a hannunsa? Ko kuma mu kashe su kawai kafin ya kaisu cikin birni kamar yanda yake shiri, amma ku sani dukansu da aka kama sunada matuƙar amfani a tafiyar mu, musamman ma mutumin nan na Bankaura, dan mutumin nan yanada manyan sirrikanmu da bani da tabbacin idan yaji wuya bazai tona ba kamar yanda yay sakacin da ƴar iskar matarsa ta buɗe mana aiki. Na matar tasa ma bai ɓata min rai ba, wannan shegiyar yarinyar mai kama da ƴar aljanu, tun randa ya haɗu da su Ganuwa ashe ƴarsa ce ya ɓoye musu......” “Kaga hakan na nufin da saninsa tazo wajen....” Black Spider ya faɗa cikin fushi da ɓacin rai. “Bana jin haka oga, domin kuwa Ganuwa ya tabbatar a bazata yarinyar tazo musu. Kuma yana ganinta ya rufe fuska. Sai dai ina yin zargi ɗaya, uwarta ce ta turota danta tabbatar mata shine, dan bana raba ɗayan biyu tare yarinyar take da uwarta ita ta laɓe.” “Idan ko haka ne baka buƙatar wani umarni anan. A kashe matar tasa da ƴar gaba ɗaya. Shima bama buƙatarsa ya gama aikinsa”. “An gama Sir! Dama wannan umarnin kawai nake jira. Sai dai a majiya mai ƙarfi na samu labarin ɗazun iyayenta sunzo sun ɗauketa a gidan. Tana gidansu. Babanta kuma shine hatsabibin malamin nan daya hana mu rawar gaban hantsi a farko.” “Duka ahalin nata a kashe su. Dan bamu zo ƙasarku dan wasa ba, buƙatarmu ta lokaci ce muna kammala ɗiba zamuyi gaba. Duk wanda yace kuma zai tari gabanmu koda uban waye sai mun kawar da shi ya koma ƙasar takawarmu a hanyar samun cikar wannan burin. Kar su wuce gobe...” Yay maganar ƙarshe da umarni yana barin falon gaba ɗaya, ba kowa bane face oga kwata-kwata. Shima miƙewa Black Spider yayi yabi bayan oga, hakan ya tabbatar ma da Dagger sun gama da shi. Ji yay kamar ya harari bayansu, amma ya kanne. Sai dai ƙasan zuciyarsa yana jin wani nauyi da shi kansa yakan kasa tantancewa. Shin ɗan sauran ɓurɓushin kishin ƙasar ne a wajen kokuwa takaicin dukiyar da mutanen ke samu ne su ana ɗan tsakura musu ke son saka masa jin hassadarsu...

<<•>>•<<>>•<<•>>

Asubar fari wani irin hayaƙine ya turniƙe illahirin garin Bankaura da in kai wasa ganin gabanka ma zai iya maka wahala. Ga wani irin rigugi da ke tashi mai matuƙar saka razani a zukata duk wani mai rai. Kai da kaji amon kasan sautine dake fita daga bindigogi ko wasu nau'in makamai masu fashewa. Kasancewar asubahi ce barcin da mafi yawan mutane basa samu saboda tsoro a farkon dare yanzu gabanin asuba duk ya kadasu sun ɓingire. Hakan yasa shiru yayi yawa tako ina gaba ɗaya jejin ya ɗauki sautin da har saƙon ya isa cikin kunnuwan su Zak-Shadow. Ai ko shine ya fara fitowa a tantin da ake tsare da su Baban Nimrah sakamakon tuhumar da ya saka ake musu tun daren jiya, dan yafi son samun dukkan bayanan da yake buƙata kafin ya miƙasu hannun hukumar bincike gudun samun matsala. Jin fa al'amarin na gasken-gaske ne dan har wani jijjiga jejin keyi saboda azabar fashewar gurneti ya zabura cikin wani irin rawar jikin jarumta. Kafin cikin gigitacciyar muryarsa ya furta, “Are you soldiers or a bunch of jokers?!!?”. Gaba ɗaya sansanin ya amsa da faɗin, “No, Sir! We are Soldiers, Sir!!”. Cikin ƙanƙanin lokaci wajen ya rikice da ƙarar gudunsu ta yanda suke rige-rigen shigewa motocin yaƙi, wasu dokuna, wasu mashina. Wasu kuma suka ƙara zagaye tantin da su Baban Nimrah suke dan kar ya zaman irin takun ranar ake son maimaita musu. A janye hankalinsu can gaba ɗaya nan kuma aka musu kwaf ɗaya. Saboda sun kula koma wace ƙungiyace wannan da ƙarfinta take. Sojojin na isa garin ya ƙara hargitsewa da musayar wuta, tsawon awa ɗaya a wannan yanayin kafin sautin ya fara lafawa sai kukan yara da mata ya fara fitowa.. A dai-dai lokacin jirage masu saukar angulu na soji suka fara isowa suma. Cikin ƙanƙanin lokaci suka zagaye ƙauyen musamman ta yankin da abin yafi ƙarfi. Sosai tsakkiyar gidan Malam Hamisu mahaifin Umman Nimrah yayi kaca-kaca da jini, yayinda gawarwaki kusan biyar na maza ke kwance. Ta gefe kaɗan ƙyaƙyƙyawan dattijo ne mai cikar kamala ma'abocin furfura da dogon gemu durƙushe a ƙasa da Handcuffs a hannunsa da aka maida ta baya wani soja na ƙoƙarin kunce masa amma da alama al'amarin yaci tura dan kamar an kulle handcuffs ɗin da wani kwaɗon sirri. Idanu kawai kyakkyawan tsohon ya zubama gawarwakin ƴaƴansa da su Dagger suka kashe yana kallo hawaye na bin kamilalliyar fuskarsa ta girma da kwarjini. Ta gefe kaɗan matane da yara da zasu iya kaiwa adadin talatin da ɗoriya. Suma dai kukan suke sosai wasu har sunayi tamkar zasu shiɗe. Fitowar Zak-Shadow daga cikin ƙaton gidan na ƙasa mai sassan da yawan gaske da zai tabbatar maka family house ne na waɗan nan mutane ya saka sojin dake zagaye da mutanen shiga sara masa cikin nuna girmamawa a garesa. Kansa kawai ya jinjina musu yana yamutse fuskarsa da tai kaca-kaca da jini ta yanda ko iya gane ainahinsa ba'ayi sosai. Hakama farar rigarsa da wandonsa na sojoji duk sun ɓaci. Cikin bada umarni yay nuni da gawarwakin dake a yashe a ƙasa tare da tsohon nan. Da sauri ɗaya daga cikin yaran nasa ya furta, “Sir za'a fara gaba da su ne?”. Maimakon yin magana yanzun ma kansa kawai ya jinjina. Basu damu ba, domin sun san shi mutum ne mara son yawan magana. Sai da suka gama kwashe gawarwakin da aka saka a cikin wasu ledoji sannan aka samu nasarar kunce handcuffs ɗin hannun dattijon nan. An kama shi da nufin miƙarwa dan jikinsa rawa yake a bazata kawai ruwan harsasai suka fara sauka a jikinsa. Gaba ɗaya wajen ya rikice, Zak-Shadow da yaransa suka fara dube-duben ta ina harsasan ke fitowa, yayinda wasu sukai kansa akai ƙoƙarin riƙoshi da hanashi kaiwa ƙasa daya tafi zai zube. Kukan yaran nan da mata ne ya ƙara ƙarfi. Yayinda wasu a cikinsu suka miƙe da gudu zasu nufesa, amma sai sojojin suka hana hakan ta hanyar shan gabansu. Dai-dai nan wani taƙadari cikin yaran Dagger ya buɗe ƙaton dirom ɗin dake tsakar gidan ya fito yana dariya. A take sojoji suka ɗana bindugu, masu tunanin yin fata-fata da namasa har sun ɗana kunamin bindugun nasu ya turo Umman Nimrah gabansa bindiga a kanta daya ɗora mata. Sai lokacin su Zak-Shadow suka fahimci shine yayi harbin ta cikin drom ɗin kenan. Cikin bada umarni da kaushin harshe Major Imran ya furta, “Idan kana son tsira da sauran abinda ya rage maka na numfashi ka ajiye bindigarka”. Dariyar shaƙiyanci yayi, ga fuska ya shafe da baƙin abu ko gane kalar fatarsa balle kamaninsa ba'a iya yi. Da yanayin shaƙiyanci ya amsa ma Imran da, “An gaya maka goro na kasa a duniyar da har nake son ya ƙare na ƙirga riba da jari balle na damu da rayuwata. Kama bar wahalar da kanka, jinin wannan matar halattacene a wajena dan koba komai zanyi jihadi kashe mata mai tona asirin mijinta.” Ya faɗa yana ƙara danna kan bindigar a kan Umma dake hawaye tana kallon Zak-Shadow da zuciya ta kume ƙirjinsa, yanda kawai zai fasa kan tsinanne yake yi. Aiko tamkar wani abin siddabaru babu ma wanda ya kula da sanda ya ja kumar bindigar hannunsa ƴar mitsitsiya balle ɗagawar hannunsa sai saukar Bullet akan shegen, dan shi ɗin ƙwarraren maharbi ne kowa ya sani kuma. Kasancewar shi kuma ɗan iskan ya riga ya ɗana kunamar bindigar hannunsa a wuyan Umman Nimrah tun ɗazun harbin da akai masa ya tafi baya sai kawai yatsarsa ya motsa harsashin ya fita ya shige jikinta. Kusan tare Zak-Shadow da Imran suka zabura kanta. Sai dai kafin su dire ma ita ta dire a ƙasa rikica. Cikin matsanancin gigita Imran ya riƙota yana jijjigata da gwala kiran sunan Captain Musa. Murmurshi tayi mai ɗaci da ciwo hawaye na zubowa ta gefen idanunta dai-dai da malalowar jini a hannun Zak-Shadow da ya kai hannu shima zai riƙota Imran ya rigashi, sai ya kasa ƙarasawa da hannun kuma ya kasa janyewa. Da ƙyar ta iya sake yin wani murmushin tana juya idannunta da ƙyar akan Zak-Shadow... A dai-dai nan shima munafukin nan mafi kusanci da Zak-Shadow ya katse videon daya ɗauka a wayarsa yana ɗan sakin munafukin murmurshi nasara guda biyu..........✍🏼

_Wato a duniyar nan ALLAH ka rabamu da maƙiyi mai fuska biyu. Kunga wanda zai nuna maka soyayya a gaban idonka a bayan idonka yafi kowa ɓataka da aibantaka ba ƙaramin azzaluminka bane. Wannan shegen na tsaneshi tun kan aje ko ina. Duk wanda yake tare damu a zahirin rayuwa da baɗini da wata manufa ya rabbi ka rusashi kafin shi ya ruguza mu😭😭🙏._

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 47_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________