
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 36
..... her mouth is full of noise and slurs. Son, if you are called the leader of insensitivity and conflict, then Nimrah is in the first line. Her maternal uncle Tanimu is privileged, as well as her parents have been childless for a while and she is the only one. You will always find her in fashionable clothes, Tanimu's son never gets tired of buying clothes for her even though he also has children but they are both men. But the way he claims Nimrah's privilege, you think he is the one who gave birth to her, the thing that bothers his wife is why she hates Nimrah and her parents, she always wants to separate her husband from them, but he stands firm that she is not enough. Today is Nimrah's seventh year and a few months in the world. It is very big, the son is twice the size of his wife's room. But even so, it is fixed to a scent that puts the heart and calmness of waking up with the cold air. There was no noise except for the sound of the AC and the TV that was on mbc channel 3. Even though there was no one, he had to say goodbye and go in, then his eyes landed on the boy who was completely focused on the TV. The boy may not be more than 9 years old, he has fat hair and a long hai
......Duk da namiji Hassatu taso batai baƙin cikin samun macen ba, sai ma farin ciki mara misali ta shiga, tare da addu'ar ALLAH ya bata namijin a can gaba. Ranar suna shagali akayi sosai saboda wannan haihuwa ta farin ciki ce a garesu, hidimar da Maude yayi da danginsu har ba'a magana. Yarinya taci suna *_NAJA'ATU_* sunan mahaifiyar su Maude, dan haka sukai mata alkunya da Ummi, sai Tanimu yace tsohon yayi ne a dinga kiranta *_Nimrah_*. Tun mutane na kananun magana akan sunan aljanu Tanimu ya sakama Naja'atu ƴar Hassatu har suka haƙura, dan kuwa itama uwar ƴar Hassatu sunan ya mata daɗi. Bayan haihuwar Nimrah burin haihuwar ɗa namiji da zai zama soja bai bar zuciyar Hassatu ba, sai dai wani ikon ALLAH har Nimrah takai shekara biyar ko ɓatan wata Hassatu bata sake yi ba. Sai dai bata fidda rai daga rahamar UBANGIJI ba ta cigaba da addu'a da fatan samu. Nimrah yarinya ce ƙyaƙyawa. Irin black beauty ɗin nan da baka gajiya da kallo, akwai dogon hanci da manyan idanu masha ALLAH. Sai ƙaramin bakinta na surutu da tsiwa. Dan kuwa idan kaji ance shugaban rashin ji da rikici to Nimrah na layin farko ne. Ga gata kawunta na mata Tanimu, hakama iyayenta kasancewar sun jima basu haihu ba kuma ita kaɗai ce. Koda yaushe zaka sameta tsaf cikin kayan kwalliya irin na zamani, dan Tanimu baya gajiya da saya mata kaya duk da shima yana da yaran amma duk maza ne su biyu. Amma yanda yakema Nimrah gata sai ka ɗauka shine ya haifeta, dan har abun na damun matarsa shiyasa ta tsani Nimrah da iyayenta, kullum cikin son raba mijinta take da su amma shi ya tsaya tsayin daka akan bata isa ba. A kwana a tashi yau ga Nimrah na shekara ta bakwai da wasu watanni a duniya....
>>>>>>•<<<<<<
Cikin takunsa na nutsuwa da ƙarfin jiki ya shigo falon. Babba ne sosai, dan ya ninka falon sashen matarsa sau biyu girma. Amma duk da haka a gyare yake ƙal ga wani ƙamshi mai saka zuciya nutsuwa na tashi da sanyin ac. Shiru babu hayaniyar komai sai ta ƙarar ac da tv dake kunne tashar mbc 3. Duk da babu kowa sai da yay sallama sannan ya shiga, sai lokacin idanunsa suka sauka akan yaron dake zaune hankalinsa gaba ɗaya a kan tv. Yaron bazai wuce 9years ba, yana da ƙiba gashi ƙyaƙyƙyawa masha ALLAH. Tvn ya ɗan zubama ido shima, kafin ya maido su kan yaron yay ƙaramar gyaran murya. Da sauri kuwa yaron ya juyo inda yake, suna haɗa ido ya zabura tare da dirgowa a saman kujerar yayo kanshi da gudu cike da farin ciki. A karo na farko ya saki wani ɗan murmushin gefen baki, sai kuma ya ɗan kai dirƙushe gwiwar sa ɗaya a ƙasa ɗaya a zaune ya tokare ya warema yaron hannayensa ya shige. Gaba ɗayansa ya rungumeshi, hakama yaron yay masifar ƙanƙamesa cikin matsanancin farin ciki yana faɗin, “Oyoyo Dada na”. Murmushi ya sake yi yana rungume da shi, dai-dai ya ɗagoshi daga jikin nashi wata ƴar budurwa da bazata wuce 17years ba ta fito daga wata ƙofa hannunta ɗauke da ƙaramin bowl dake tururi alamar abinci ne a ciki. Sosai itama farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta ƙaraso wajen da sassarfa tana faɗin, “Dada sannu da zuwa”. Kansa kawai ya jinjina mata, sai itama tai saurin sake risinawa tana gaishe shi. Bai amsa ba sai da ya miƙe tsaye hannunsa riƙe dana yaron, sai dai idanunsa a kanta shiyasa ta sake nutsuwa sosai amma har lokacin fuskarta da murmushin farin cikin ganinsa. “Miya hanaku zuwa makaranta?”. Ya faɗa cikin buɗaɗɗiyar muryarsa. Da sauri ta ce, “Anyi hutu ne jiya Dada”. Nan ma kansa ya jinjina da maida kallona kan yaron daya amshe zancen yana bashi labarin yazo na biyu a ajinsu. Hannunsa yaja suka ƙarasa cikin falon sosai, zama yay a kujera ya zaunar da yaron a kusa da shi. Itama budurwar da yaron ya kira Aunty Biebah bowl ɗin hannun nata mai ɗauke da dafaffiyar indomie ta ajiye a gaban yaron. Ta miƙe zata bar wajen ya ce, “Ina Mammah?”. “Tana ciki Dada, tayi sallar walha ne dama zan gaya mata kazo ne”. “Barta, haɗa min breakfast, bana son jagwalgwalo kuma”. “Yes Dada, yanzu fa na iya duk irin abincin da kake ci, tunda ka tafi na dage inata koya. Da Yaya Ma'aruff yaga na dage shine ya sani makarantar koyon girki ma”. Shi dai idanu kawai ya zuba mata tana zuba surutu. Dukan ƴan uwansa yana son su ƙwarai da gaske. Amma tausayin autar tasu Biebah mai girma ne a zuciyarsa saboda ita kaɗai ce ba mahaifinsu ɗaya ba, sannan kamaninta daban da su. Mahaifinta na raye, amma bata da maraba da su da suka rasa nasu, dan har yanzu Alhaji Nura yaƙi karɓarta a matsayin ƴarsa, duk da kuwa har yanzu ba'a sake masa haihuwa ba bayan ita. Tunanin nasa ya ture gefe, sai kuma ya miƙe yana faɗin, “To akku sarkin magana jeki min abinda na saki”. Daga haka ya nufi wata hanya, itama dake tura bakin shagwaɓa sai ta juya hanyar kitchen cike da farin cikin yau zatama Dada abinci mai daɗi. Dan a wani zuwa da yay ya taɓa sakata ta haɗa masa salad kawai tai masa shirme, tako sha faɗa, shiyasa ta dage da burin duk randa ya dawo zata faranta masa rai da abinci.
Dai-dai ƙofar farko ya tsaya, a buɗe take sai labule dake a sake, cike da nutsuwa yay sallama. Daga ciki wata dattijuwar murya ta amsa masa a tausashe. Labulen ya ɗaga ya shiga cikin ɗakin, mamallakiyar muryar na zaune akan sallaya alamar salla ta idar take addu'a ta ɗago tana kallonsa. Tabbas shekaru sunja, fata ya canja daga mai laushi da santsi zuwa mai ɗan tattarewa da hasken kwarjinin ibada, bazamuce da ita tsohuwa ba, amma zamu kirata dattijuwa dan kuwa a sittin kaɗan ne babu. Tana nan da hasken fatarta da annurin fuska. Tunda tai masa kallo ɗaya ta ɗan kauda kanta tana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. A duk sanda yay nesa da su kewarta gareshi mai girma ce, idan ya ziyarcesu tana jin nutsuwa amma takan danne da yanayi irin na masu dattako. Gaba ɗayansa a halittar jiki Abdul-rasheed take gani, duk da kuwa ya fishi buɗewa da ginannen jiki, dan Zak-Shadow irin mutanen nan ne masu ƙirji gashi a murɗe sosai musamman daga sama, cikin nan a lafe tamkar ba'a zuba masa abinci. Sai hasken fatar ta daya ɗauka kawai, da halin rashin yawan magana irin tata data kakarsa mahaifiyar Abdul-rasheed. Dan tun yana ƙarami Baba yasha faɗin halayyar Haysam ta rashin yawan magana da murɗin hali irin na Inna ne, kawai shi dan ya haɗa biyu ne dana mahaifiyarsa shiyyasa abin yay masa yawa..... “Barka da hantsi Mammah”. Ya faɗa cikin tausasawar data katse mata tunaninta. Wata ajiyar zuciyar ta sake saukewa ta shafa addu'ar data kammala sannan ta fuskanceshi tana gyara zama da faɗin, “Wannan tafiyar daren dai bazaka dainata ba, ko tsoro baka ji Muhammad”. Murmushi yayi mai ƙayatarwa yana ɗan sunkiyar da kansa. “Kiyi haƙuri Mammah, tafiyar daren ce tafi sauƙi a garemu kodan yanayin rayuwar”. “To ALLAH ya rufa mana asiri, ya baku kariya ya tsare mana ku da tsarewarsa”. “Amin ya rabbi Mammah ina kwana. Na sameku lafiya?”. “Komai lafiya lau Alhamdullah. Fatan kuma kuna cikin ƙoshin lafiya?”. “Alhamdulillahi, sai kewarku”. “Kewa kam muma a cikin taku muke akoda yaushe. Amma ya za'ayi tunda haka UBANGIJI ya tsara”. Murmushi yayi nan ma kawai, ita kuma ta jawo ƙaramin flaks dake gefenta da wani kyakkyawan mug, shayin dake ciki ta zuba ta miƙa masa. “Mammah kamar kin san nayi kewar shayin nan naki kuwa”. “Ai gashi sai kaita sha har ka koma. Jiya muke zancenka da Momy ashe kana tafe?”. “Tafiyar tazo ne kawai nima. Bata daina yawon nata ba kenan dai”. “A'a yanzu kam ta rage ai, tanata fama ma da laulayin ai yawo dole a barshi”. “Mammah baki son laifinta dai kawai”. Karo na farko Mammah tai dariya, dan kusan su duka haka suke gaya mata akan Momy idan suna faɗan yawonta tana kareta. Sun cigaba da hirarsu cikin nutsuwa, anan ma yake jin Ma'aruff da Ja'afar sun wuce Chaina. Dan su harkar kasuwanci suke yi. Tun dai kasuwar daya zama sanadin kafawa itace ALLAH ya sanya ma albarka zuwa yanzu har suna da manyan shaguna kusa shida da zamu iya cewa ma sune sanadin arziƙin da suke ciki a yanzun haka. Dan haka Ja'afar da Ma'aruff tagwayen Mammah ke kula da su, sune suke zuwa ƙasashe kawo kaya kuma da kansu. Sunyi nisa da hira akan dai lamarin sauran ƴan uwan nasa da bikin su Ja'afar dake tunkarowa Biebah tai sallama. Amsa mata sukai da bada izin shigowa. Ta shigo ɗauke da tire yaron nan na ɗazun biye da ita. Sai da ta durƙusa a gabansa sannan ta ajiye tiren, yaron kuwa yaje kusa da shi ya zauna. Dukan abinda Zak-Shadow zai ci yanada ƙa'ida da tsarinsa, baya cin abinci sai mai amfani da gina jiki, shiyasa kayan ganye, nama, ƙwai, kifi, vegetables, fruits sunfi yawa a abincinsa. Sauran kuwa yana cin komai dai-dai misali da kuma tsari. Kwata-kwata baya shan suger, baya cin magi da yawa da gishiri. Baya cin mai da yawa koda nama mai kitse ne, hakama duk wani drinks. Yanzun ma ƙwai ne guda huɗu da nama sai vegetables wadatacce a ciki da agada ta kawo masa. Sai fruits salad data haɗa masa kaɗan. Fuskarta washe da murmushi ta ce, “Dada idan kaci abincin nan yau nasan har ƙyauta sai kayi mini”. “Ko kuma kisha zana ba idan babu daɗi”. “ALLAH Dada akwai daɗi, ai Mammah ma ni nake mata girki yanzu ko?”. Tai maganar tana juyawa ta kalla Mammah ɗin cike da shagwaɓa. Dariya Yaron nan ya sanya, dan haka ta maida dubanta kanshi tana harararsa. Dai-dai Zak-Shadow na kai naman bakinsa. Kusa da shi ta koma cike da ƙosawa tana jiran ya yaba mata, harda yin tagumi fuska a shagwaɓe. Sai da yay lauma ta biyu sannan ya ɗago kyawawan idanunsa yana kallonta, sai ta waro masa idannunta. Harararta ya ɗanyi, tai saurin risinar da su. Ya ɗan girgiza kansa da faɗin, “Irin wannan sakani a gaba Auta, shike nan yayi daɗi, tashi ki bani waje karna ƙware”. Ai da wani irin murna ta miƙe ta fita, yaron nan da Mammah ta kira Mu'azz ya bita yana tayata. Kansa kawai ya girgiza nan ma, Mammah kuwa tai murmushi. “Ai daga nan kuma munga boni a gidan nan wajenta, yanzu zata fara bazama sauran ƴan uwan a waya duk da nasan tunda ta ganka ma ta kira kowansu. Amma kai miyasa ba zaka saka matarka tai maka girkin ba, nifa bana son ana tauye mutum ka sani”. “Kiyi haƙuri Mammah nima bana tauyeta bane, idan tayi na rana ba sai naci ba, itama Autan ina son ganin farin cikinta, tana son tayi bai kamata na sare mata gwiwa ba”. “Shike nan, a dai dinga kula”. “In sha ALLAHU”.
Kamar yanda Mammah ta faɗa kuwa tuni Biebah ta bazama sauran ƴan uwan batun zuwan Dadan, kafin 12 har sun cika gidan. Idan ka cire Ma'aruff da Ja'afar da basa nan. Hatta Ammar dake Zaria yana makaranta yace sai yazo gida komai dare.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 37_
__________________
https://chat.whatsapp.com/L3BXH7JYlBRHIkFRiOjeW3?mode=ems_copy_t
UMMU KHALIFA COLLECTION
Ina Mata Yan kwalisa ina mata masu san kayan ado kamar Egyptian abaya sleeping drees kids were shos bags musk dahara original.
To kukanku yazo karshe domin ummu khalifa sun zo muku da duk wadannnan kayan dierct suke order dinsu daga Egypt zuwa gida Nigeria kaidai kawai kashiga link dinsu domin gani ya kori jiii..
Ba nan ummuh khalifa suka tsaya ba suna nemawq mutane visa masu shaawar shugowa kasar ta Egypt karatu ko yawon bude ido ko kasuwanci ku tuntubeta a number dinta +201017018846/07048811474/
KO kuma shafinta na tiktok https://vt.tiktok.com/ZSU1FEkjc/ __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________