Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 45

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 45

.....and he only knew him since he was a young man". "Where is Abashen's house?". "This is our neighbor, but they moved to a new house three years ago?". Imran just greeted her, then he turned and looked at Zak-Shadow who was studying the questions that Imran asked Umman Nimrah and her answer. Zak-Shadow changed his language and said in English, "There must be a new investigation in this house. Call Captain Musa right now". Then he stood up and went out pressing his phone as if he was going to talk to the other day... Tanimu's wife, who had been hiding since their entry, Zak-Shadow, behind her wall and separated their son Umman Nimrah, saw them go out and Imran also went out to chat. Then she was clapping her hands and holding her mouth as if she was gossiping. It was a word that was bothering her mother, there was no way to go out and gossip nearby, she was unable to. When she got there, a girl took a nap on her animal stall and went to the same place as her husband.

Standalone post2,014 words

.....Layukan waya ne a ciki har huɗu. Suma ajiyesu Imran yayi, sai kuma ya juya yana kallon Umman Nimrah dake kallon kuɗin da mamaki, dan ita kam bata san da su ba sam, kai kayan ma ta kasa tuna randa mijin nata ya sakasu a jikinsa.... “Ko zamu iya ganin wayarki?”. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke na katsewar tunaninta, ta girgiza masa kanta. “Banda waya”. “Mijinki fa?”. “Shima baida ita, sai dai ranar yake cemin yana son ya saya mana ni da shi, zai ba Tanimu ƙaninsa idan zai dawo sai yazo mana da ita. To ban sani ba ko ya ba Tanimu sautin a randa zai tafi”. “Kota wani baki taɓa gani a hannunsa ba?”. “Eh to sai ta matar Tanimu, itama kuma sai in Tanimun ya kira dan suyi magana take kawo mana, ta kuma kaima Inna. Daga ba wannan ba ban taɓa ganinsa data kowa ba, kai gidan nan ma duka daga Tanimu sai matarsa keda salula”. Zaki iya faɗa mana abokan mijinki da kike yawan ganinsu tare, har suke zuwa gidan nan”. “Abashe ne kawai abokinsa. Kuma ALLAH yay masa rasuwa watanni goma sha ɗaya kenan. Kowa da shi kawai ya sanshi tun yana saurayi”. “Ina ne gidan Abashen?”. “Da nan makwaftanmu ne, amma yayi sabon gida sun koma can farkon gari shekara uku kenan?”. Kai kawai Imran ya jinjina mata, sai kuma ya juya yana kallon Zak-Shadow da duk ke nazartar tambayoyin da Imran kema Umman Nimrah da amsar da take bashi. Canja harshe Zak-Shadow yayi, cikin harshen turanci yace, “Dole a sake sabon bincike a gidan nan. Kayi kiran Captain Musa yanzun nan”. Daga haka ya miƙe ya fita yana latsa wayar hannunsa alamar zai yi magana da wuni...

Kandala matar Tanimu dake laɓe tun shigowar su Zak-Shadow a bayan katangarta data raba sashensu dana su Umman Nimrah na ganin su Imran sun fita itama tabar wajen saɗaf-saɗaf. Sai faman tafa hannaye take da riƙe haɓa irin na gulma. Magana ce ke tsikarar mata uwawu gashi babu damar fita kai gulma maƙwafta, ta gagara zaune ta gagara tsaiwa. Zuwa can dabara ta faɗo mata, wata ƴar dusa data shanya akan rumfar dabbobinta ta ɗauka ta juye a roba. Sashen ɗayar facalarsu da mijinta da su Tanimu ke uba ɗaya ta nufa. Tun daga farkon shiga ta ce, “Ramma ga dusa, naji kina jaje ɗazun na gagara tashi ne na miƙo muki ita tun ɗazun ina fama da ciwon kai”. Ramma da tasan batai jajen dusa ba ita dai ta buɗe baki zatai magana. Da sauri Kande ta ƙyafta mata ido alamar tai shiru. Sai ko ta wayance itama ta ce, “Kai aiko na gode. Tun ɗazun dabbobina ke kuka na rasa tudun dafawa”. Ƙasa-ƙasa Kande tace, “Ramma akwai matsalafa a gidan nan”. “Matsala ai dama cikinta muke Kande. Yau kwana biyu mazanmu na can a hannun sojoji”. “Ai inaga gaskiya ta kusa bayyana, ALLAH ya kusa ƙwato mana su. Tun ɗazun wannan bahagon sojan da kallon fuskarsa kawai tashin hankali ce yazo gidan nan. Naga ya ɗauki waccan yarinyar ƴar gori ya fita da ita, tunda kuma suka dawo suka tsare uwarta da tambayoyi tana basu amsa, har kayan sakawar Yaya mai kifin aka sakata ta ɗakko suka zazzage, naga sun fiddo kuɗi sabbi fil ƴan ɗari biyar, da layin waya. Kin kuma san bashi da waya ai. Gashi can sun sake fita dai....” Ramma dake zazzare ido ta ce, “Mun shiga uku Kande, kar dai ana zaton wuta a maƙera a ganta a masaƙa”. “To aiko da alama can ɗin take. Yo ai biri yayi kama da mutum, ki kula a kwanakin nan basa shan koko kullum sai shayi da burodi, ranar ƴar naba su Laminu labari wai sunci tsire da daddare babanta ya sayo. Ke dama ki kiyayi mutum sumu-sumu wlhy abin tsoro ne. Randa Tanimu zaiyi tafiyar nan da daddare yake gaya min ya ranci kuɗi a wajensa har dubu arba'in, naita mamaki har ina jin haushi, ashe-ashe kuɗin bana ALLAH bane”. “Kande ni abinda ban gane ba anan. Kenan dai shine ya kawo mana wannan masifar da aka samu shekaran jiya cikin gidan nan?”. “A to ke da mi kike tunani, shine mana. Dan bala'i ya rasa inda zaije ya ajiye sai ɗakin tsohuwarsa, yanzu da wannan abun daya kashe mutane a Gangare ne a ciki tunda ance fashewa yake shi ai kinga shike nan ya kasheta ko yama ɗiyanta asara. Maganinta itama, badai tafi sonshi da ƴarsa ba kamar shi kaɗai ta haifa, mai mata wahala daban wanda take riritawa daban”. Salati kawai Ramma take tana ƙarawa, dan maganar ta girgizata matuƙa. Kasancewar ita babu wani jin haushin su Umman Nimrah a ranta ita tausayinta ne ma ya kamata wlhy. Ka daɗe baka haihu da mutum ba sanda kuma ALLAH ya fara baku ace ga wannan masifa mutum nayi, ga yarinya mace, idan wannan magana ta fita wazai aureta a wannan garin basu da ba'a manta abin gori....

<<<<<•>>>>>

A ɓangaren su Imran mintuna talatin ba'ai ba Captain Musa ya iso da wata tawagar soji, da karnuka. Sai da suka miƙa gaisuwa ga Zak-Shadow dake a ƙofar gida har yanzu yana waya sannan suka shiga cikin gidan. Kamar yanda ya bada umarni haka sojojin nan keyi, bincike ake mai zafi da yafi na farko har a jikin bango da ramin ɓeraye ba'a bari ba. Kai saida takai hatta ledar ƙasan ɗakin Umman Nimrah sai da aka kwaye gaba ɗaya, da ledar sama da akai kamar silin. Cikin filos ba'a bari ba. A ɗayan ɗakinsu da take ajiye-ajiyen kayan aiki da icce sai randunan ruwa sai da aka fidda komai. Wani guri ne ya nuna kamar an tona aka maida ƙasa aka rufe Zak-Shadow yace a tone shi shima. Haka suka shiga tonawa kuwa, abin mamaki sai ga tunkunyar ƙasa, ana buɗe murfinta sai ga kuɗi masu yawa a ciki kusan cike. Nan fa aka shiga fiddosu bandir-bandir sabbi ƙal. Hakama a cikin ɗakin Umma an ƙara samo kuɗi cikin katifar rimi ta gadon da yake kwana, harda wayoyi har biyu. ALLAH sarki Umma zuwa yanzu kuka take sosai, hakama Inna sai surutai take kamar wadda ta zautu. Tana son baban Nimrah sosai fiye da sauran yaranta musamman yanda bashi da yara sosai ɗin nan. Duk da kuwa Tanimu yafi ƙyautata mata da yi mata hidima a rayuwa, shi baƙin halin matarsa ne yasa bata sakewa da shi, itako Umman Nimrah tana mata abu kamar ƴarta. Idan ma ta nema abu Baban Nimrah ɗin bai mata ba ita takanyi a madadinsa batare da Innar tasan ba shine yayi ɗin ba. Bincike na biyu shine gidan abokinsa mai rasuwa Abashe, inda su Zak-Shadow suka gane shine gidan matar nan mai yara marayu da suka fara samun abubuwa tace ita kuma bata san da su ba. Ashe kuwa da gaske bata sani ɗin ba. Dan sai yanzu ne da zance ya kai ya kawo akan lamarin Baban Nimrah ɗin ta tuna ya kawo musu hatsi kusan sati ɗaya kenan, da yake tunda mijinta ya rasu haka yaketa ɗawainiya da ita da yaran babu gajiyawa, randa ya kawo hatsin yace babban yaronta da yaci sunansa suke kira da Aboki yaje ya amso musu kifi. Tabbas taga yaron nata da bako bayan ledar kifi, koda ta tambayesa sai yace mata Baba ne ya bashi ajiya yace zai amsa ranar kasuwar Gamau. Itako bata maida hankalin sanin minene a ciki ba yaron ya shiga da bakko ɗin ɗakinta ya ajiye. Bako ta sake tunawa ba sai yanzu ma. Gari fa ya ɗauki sabon tashin hankali. Dan duk wanda keda alaƙa da Baban Nimrah sai da aka kamashi a wannan yinin, hatta wajen kifinsa da inda yake zuwa sari a can cikin local government ɗinsu sai da aka bibiya. Zuwa dare sai ga ƴan uwansa na nan gidansu duk an sakko, sai dai banda Tanimu dan basu gama bincike a kansa ba. ALLAH sarki Umman Nimrah idan ka ganta abin tausayi, wuni ɗaya duk ta susuce ta fita a hayyacinta. Dan zuwa dare ma zance ya gama baje gari dan ma akwai sojoji da sukai musu takunkumin hana yawo barkatai ƴan uwanta sukazo suka tafi da ita harda Nimrah bisa umarnin mahaifinta dattijon arziƙi, babban malami ne a yankin ma ba garin kawai ba, dan bazasu so abin kunyar da mijinta ya aikata ya shafeta ba, musamman da matan gidan suka fara mata habaice-habaice da yada magana a kai-kai ce bisa jagorancin Kande matar Tanimu data fara yaɗa maganar, dan ma dawowar mazan gidan ya sata komawa tai laƙwas ganin babu nata mijin itama....

>>>>>><<<<<<<

A sansanin su Zak-Shadow cikin tantin Imran da bai cika zama ba ake tsare da su Baban Nimrah, zuwa safiya ake son fita da su daga jejin zuwa birni, ana ƙara tantance wanda basu da alaƙa da al'amarin ne musamman waɗanda aka tattaro yau da rana. Kwanaki na uku kenan bayin ALLAHn nan su Zak-Shadow basuyi barcin rabin awa ba. Yaransu da manyansu tsaye suke akan ƙafafunsu. Kai ko abincin kirki basa ci sai ƴaƴan itatuwa. Duk mai imani ya gansu sai ya tausaya musu. Amma a haka muda muke kwance a gidajenmu muci mu ƙoshi mu kunna tv muyi kallo, mu hau gado muyi barci har muke iya zagin jami'anmu da kallonsu muce basa aiki. Musani ganin jami'an dake ofisoshi zaune, da wanda ke yawo akan hanya suna nuna wasu halayya mara ƙyau bashike nufin mun rasa zakaƙuran jarumanmu dake cijin jeji daban-daban suna gumiruzu akanmu ba. Akwai irinsu Zak-Shadow da su Imran da yawa da bamu san da su ba, sai dai ALLAH ya saka musu da alkairi kawai zamuce.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 46_

__________________

https://wa.me/+23408067422528 Kina son rage kiba ba tare da kin daina cin abunda kike so sannan ba tare da kinyi gudawa ba? To kimin magana domin samun hanyoyi da zaki rage kiba ba tare da kinsa wahala ba. Ko kuma matsalar gashi ce ke damunki, ko rashin tsahon gashi ne, shima muna da solution dinsa. Ko kuma fatar ki tana lalacewa ne a sanyin? Muna da ingantaccen man da zai gyara miki kafafunki ko kuma kamar ta jarirai. Ko kuma kafarki ce take kaushi a sanyin nan muna da ingantaccen mayuka Ko kuma man gyaran fata kike so da zai gyara miki jikinki a sanyin Nan ?duk muna dasu ba tare da kinsa wahala ba sannan 100% natural ne. Yar uwa idan ma bangaren samun kudi shima kike nema shima duk zamu koya miki. Kedai kawai ki mana magana domin karin bayani.

https://wa.me/+23408067422528 “Shin Ke uwa ce, kina son samun kuɗi ba tare da kin fita kin bar ’ya’yanki a gida ba?” ko kuwa ke student ce kina son samun karin kudin shiga ko kuma ma dai kawai kison karin side hustle ne Tare da Oriflame, za ki iya yin kasuwanci daga wayarki a gida. Ba tare da kin fita ba. Mata da yawa sun riga sun farga da wannan Kasuwanci kuma suna moriya dashi sosai, suna making kudi daga gida, kuma ke ma za ki iya sannan bayan ribar ki zaa biyaki salary a karshen wata. ko kuma kina son yin siyayya for personal use ne ba tare da anci riba dake ba ga link nan a kasa zaki iya register da kanki it's free👇

https://shop.oriflame.com/NG-salmaibrahimismail/3M3HmQWe __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________