
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 35
.....take them to the big villages near Bankaura for sale. When the rains are not left behind, those who are diligent tend to cultivate their own crops or work in other people's farms. Around the village of Bankura there are other villages that can reach seven. And it seems that they do not have any improvement in life that the world is looking at. They have been living like this for years, but in 2002 a young man named Tanimu brought wealth to the villages of the area and not only Bankaura, even though he was born in Bankaura. Tanimu is the kind of people who are enlightened like in the blood of their bodies, and my son did not have any formal education except for the board in his town. At the age of eighteen, he joined the ranks of youths who went to Lagos to seek money. From the first time Tanimu realized that the world is far away from them, he kept feeling in his heart that they are not welcome to the animals that live in the desert, they just lie down and sleep. At that moment, his heart began to warm and feel the pride of his region and his community. So he went into research with his imagination and his vision, and he understood that if they want the kind of development tha
BANKAURA dai wani ƙauye ne da mutanen cikinsa bazasu wuce adadin dubu uku da ɗari biyar ba. Ƙauye ne sosai domin kuwa akaf gidajen dake cikinsa babu wani gida ginin siminti duk gidajen laka ne. Mutanen wannan ƙauye duk manoma ne. Idan ka cire harkar noman nasu babu wani cigaba da suke da shi na sabuwar rayuwar wannan ƙarnin. Kai idan mutanen wannan ƙauye sukace maka basu san ma akwai gwamnati ba karka zagesu. Dan kuwa babu wani abu da gwamnati ta taɓa musu na cigaban rayuwa. Basu da makaranta koda primary ce balle ai maganar wutar lantarki ko ruwan fanfo, Kai hatta asibiti basu da shi. Amma abinda zai baka mamaki idan zaɓe yazo sai kaga an shiga har ƙauyen ana son su kaɗa ƙuri'arsu. Wannan rashin cigaba da koma bayan cigaba da suke da shi yasa mafi yawan yaran garin kan fita neman kuɗi wasu jihohi bayan an kwashe amfanin gona, amma fa da ance ruwa ya zuba zaka gansu sunata dawowa gida. Maza na fita neman kuɗi a lokacin rani, da damina suyi noma. Mata kuwa kanyi ƙuli-ƙuli da mai da man-kaɗe da sabulun salo su kaishi manyan ƙauyukan dake kusa da bankaura domin siyarwa. Da damunar ma dai ba'a barsu a baya ba, masu himma kan yi noma suma nasu na kansu ko suyi ƙwadago a gonakin wasu. Zagaye da ƙauyen bankaura akwai wasu ƙauyukan da zasu iya kaiwa bakwai ma. Suma kuma kamar hakan ne basu da wani cigaban rayuwa da duniya ke kallo. Haka suke rayuwa tsawon shekaru, sai a shekarar 2002 wani matashi mai suna Tanimu yay sanadin wani tagomashin arziƙi ma ƙauyukan yankin ba Bankaura kawai ba, duk da kuwa shi ɗin haifaffen ɗan bankaura ɗin ne. Tanimu irin mutanen nan ne masu wayewar kai tamkar a jinin jikinsu, dan kuwa baiyi karatun boko ba sai na allo kawai a cikin garinsu. Yana da shekara sha takwas ya shiga cikin matasa masu tafiya neman kuɗi zuwa Lagos. Tun fa a fitar farko Tanimu ya fahimci duniya tayi nisa mai yawa ta barsu, ya dinga ji a ransa basu da maraba da dabbobin dake rayuwa a jeji sai dai suci su kwanta suyi barci. A take zuciyarsa ta fara sosuwa da jin kishin yankinsa da al'ummarsa. Dan haka ya shiga bincike a iya ɗan tunaninsa da hangen nesan sa, sai ya fahimci idan fa har suna son irin cigaban da al'ummar birni ke ciki dole-dole sai sun tashi daga barci da suka jima sunayi, su cire tsoro, su cire gidadanci. Yaransu su shiga makarantar addini data boko ba noma kawai da fita neman kuɗi cikin birane ana musu kallon ƙasƙantattu ba. Tun a Lagos ya fara latsa tunanin ƴan uwansa, ƴan garinsu dama ƴan wajen garinsu akan al'amarin. Kai tsaye wasu ke bashi goyon baya, yayinda wasu ke ɗaukarshi mahaukaci. Bai damu ba ya cigaba da son fahimtar da su har lokacin da ruwan damina ya fara sauka suka koma gida. Kowa ya duƙufa noma, shi ko ya duƙufa nazari da tuntuɓar manyan ƙauyukan musamman masu gari. Kai tsaye ba kowa ke fahimtar Tanimu ba, dan wasu ma kance yana son zuwa musu da kafirci ne kawai da lalata tarbiyyar yaransu da al'adarsu. Sai dai baya nuna jin haushi ko ƙosawa, sai ya zauna yay musu bayani na gamsuwa da nuna musu ai a yanda ɗin suke bai hana yaran nasu su lalace ba, dan akwai da yawan matasan da tunda suka fita neman kuɗi birni a ƙauyukan sunƙi su dawo gida, wasu ma sun faɗa mummunar hanya acan birnin. Kamar wasa sai al'amarin ya fara tasiri, a shekarar 2007 da akazo zaɓe sai suka haɗe kai suka nuna bazasu kaɗa ƙuri'arsu ba suma. Sai ƴan takarar dake ƙasa-ƙasa sun musu alƙawrika sannan. Shi ɗan siyasa babu abinda yafi ƙauna musamman a lokacin zaɓe sai kuri'a, idan kuma za'a haɗa ƙauyen bankaura da sauran ƙauyukan dake makwabtaka da shi dole za'a samu ƙuri'a mai yawa. Aiko sai ga ƴan takara kowanne na nashi alƙawarin musamman ƴan takarar chairman da kansiloli. Sunko cika alƙawari, dan cikin dabarun Tanimu aka samu tsara yanda za'a kaɗama kowanne ƙuri'ar, kunga duk wanda ya dace yaci bashi da bakin cewa basu zaɓesan ba. Bayan gama zaɓe da samun sakamako chairman ɗin da yaci da kansiloli suka nema saɓa alƙawari, Tanimu bai gajiya ba ya cigaba da zungurar masu gari shima yana haɗa gangamin matasa zuwa garin da chairman ɗin yake suna masa tini. Da suka ga anƙi ɗaukar abin da muhimmanci sai suka nuna ai zaɓe zai sake zagayowa. Daga haka suka watsar da batun su suka koma kan harkokinsu. Wannan abu da sukai ta farkar da masu wayon cikin ƴan siyasar, musamman ma kansiloli sai suka fara ƙoƙarin yin fanfon tuƙa-tuƙa a kowane ƙauye. Fara kuma wannan fanfuna ya saka ƙauyukan a farin ciki sosai, sai dai kuma masu aikin fanfuna suna fahimci kauyen bankaura da ƙauyikan gefensa akwai wasu ma'adanai dake rayuwa a wajen. Ma'adanai ne kuma masu ɗunbin daraja da zasu zama dukiya. Waɗan nan ma'aikata sune suka tsogunta batun ga wanda suka sakasu aikin fanfunan nan, suka nuna idan aka basu dama zasu dinga tonowa da wayo ana kashe muraba. Kuɗi ƙunbar susa, dan danan kuwa suka amince musu. Aka sake zuba ayyukan fanfuna tuƙa-tuƙa tako ina. Su ƴan gari na farin cikin ana masu aiki masu aiki na farin ciki da ɗibar ganimar dukiya. A hankali-ahankali zance ya kai ga kunnen manya irinsu chairman da ɗan majalisar yankin, ai babu ɓata lokaci hankalinsu ya fara dawowa ƙauyukan. Amma sai basu nuna a fili ba aka cigaba da yaudarar su da ayyuka. Dan kuwa babu wani jimawa akai musu makarantun primary, aka kuma musu asibiti ƙarami, hanyar ma an gyara amma ba kwalta aka zuba ba. Ba'anan aikin ya tsaya ba sai ga wutar nefa an jawo musu. Bayan yin waɗan nan ayyuka ne wasu a manyan garin suka fara farga, nan fa ƙaramar rigima ta tashi har abu dai ya kai ga manya, sai ga baƙin fuska sun fara shigowa ƙauyukan harda ƴan ƙasar waje. Wannan al'amari ya fara tada hankalin mutanen wannan yanki, sai kawai suka miƙe da addu'a tamkar anyi ruwa an ɗauke masu haƙar ma'adanai dama shugabannin yankin dai suka ja baya. A shekarar 2008 kwatsam wasu mutane daban suka shigo yankin suka cigaba da aikin haƙa, sai dai suna a ƙauye guda ne ba duka ƙauyukan ba. A ƴan ƙananun magana suka fahimci akwai bakin wasu a manyan garin, sannan masu wannan haƙa sun sha banban da na baya. Akwai kuma kasuwa babba a yankin da ake cinikin amfanin gona da dabbobi tamkar ba'a so itama al'amarinta ya fara canja salo. Wannan kasuwa dai itace taƙamar wannan yanki gaba ɗaya bama ƙauyikan ba, kai arewa ma kasuwa ce ta alfahari ga kowa. Dan haka suka shirya ɗaukar mataki dan basa son rasa kasuwarsu, batun ma'adanai ma bai canja ba, dan yaransu sun dawo sune masu haƙa ana biyansu maƙudan kuɗi, ta wani fannin kuma basu san darajar ma'adanan ba sam. Ƙoƙarin hana taɓarɓarewar kasuwar nan da daina fitar yara neman kuɗi ne ya fara jawo rikici, rikici babba da ya kai har gwamnatin jiha ta shiga, daga ƙarshe ma aka turo sojoji domin kwantar da tarzomar su kuma tarwatsa ƴan ta'addar. Haka kuwa akayi dan wannan shine sanadin zuwan su Zak-Shadow cikin dajin yankin a karo na biyu. A lokacin yana matsayin Major Haysam Abdul-rasheed Shehu. Akwai runduna a ƙarƙashinsa, rundunar tasa kuma itace ta kawo dai-daiton cigaban kasuwar da har ya zamto an ƙaramasa muƙami na bayan abubuwa sun lafa gaba ɗaya. Sun bar jejin har na tsawon shekara ɗaya da wasu watanni da tunanin komai ya dai-daita, sai dai a shekarar 2010 wasa na biyu ya nema fin na farko, dan kuwa horarrun ƴan ta'adda da ba'asan daga ina suke ba sunzo sun ragargaza jama'ar wani ƙauye da ake kira Gunda gaba ɗaya, an kashe wasu an jikkata wasu. Wannan rikici shine yay sanadin sake dawowar sojoji a yankin, ba kowa kuma aka maido ba sai Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu Zak-Shadow ganin shine ya dai-daita rikicin farko. Zak-Shadow ya kafa ya tsare a wannan yanki matuƙa, ta yanda ƴan ta'addan nan sun kasa ko numfashi mai ƙarfi, dan tarwatsawar da yay musu ta ƙarshe sai da ya samu nasarar kashe shaƙiƙin ƙanin shugaban ƴan ta'addar. Maganar tonon ma'adainai kuwa tuni ya dakatar da shi sai a ɓoye, a ɓoyen ma yana musu wuya sosai.
Wannan ƙauye na Bankaura shine ƙauyen su matar nan mai ciki da su Zak-Shadow suka haɗu dasu a shekarar 2006 da suke shigowa jejin. Ita da mijinta duk asalin ƴan ƙauyen ne. Mijinta Maude, shine yaya ga Tanimu da yayta gwagwarmayar jawo cigaba a wannan ƙauye. Ita ko sunanta Hafsatu, amma ana kiranta da Hassatu a gaba ɗaya ƙauyen. Shekararsu tara da aure ALLAH bai basu haihuwa ba, sai daga baya kwatsam ta samu ciki, cikin daya saka duk wani masoyansu a farin ciki da su kansu. Kamar yanda Hassatu ta faɗa tana jin labarin aikin sojoji ne a rediyon ƙanin mijinta Tanimu idan ya kunna musu, yakan kuma bata labarai irin na birni da abubuwan cigaba da ƙoƙarin da jami'an tsaro musamman sojoji keyi a yankin nasu kan ta'addacin dake faruwa dan su ƙauyensu lafiya lau yake zaune har lokacin. A hankali zuciyarta ta dinga kwaɗaituwa da son abinda zata haifa ya zama soja, kullum wannan shine fatanta, har mutane kan mata dariya a kan hakan da ɗaukarta shashasha, burinta ya sake girma da faɗi a lokacin data haɗu da su Zak-Shadow, haka ta dawo gida cike da farin ciki a wannan ranar, ta bama mijinta Maude labarin komai daya faru. Shi mutum ne mai sanyin hali da rashin yawan magana, sai kawai yay dariya dan ya ɗauki zancen nata kawai shiririta irin ta mata ne. Ita kuwa tun daga ranar ta addabeshi da labarin sojoji da fatan haihuwar namiji ɗanta ya zama soja. Tun yana mata dariya har ya fara jin haushin hakan yana mata faɗa, da taga haka sai ta daina masa maganar kawai. Cikin aminci UBANGIJI kwanaki goma sha shida da haɗuwarsu da su Zak-Shadow a daren juma'a ta haihu, sai dai kash maimakon ɗa namiji da take fatan haihuwa dan kawai ya zama soja sai aka samu mace........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 36_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp
07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________