
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 44
....mci the truth of her words. There are still signs that people have stayed. The other pieces of meat that the children didn't take because they were eaten there, even though the wind took them away, they moved, except for the bone on the side that shows the signs of mosquitoes and urine, eggshells and other cigarettes and akasha. Nimrah was eating her date and pointed somewhere else, looking at Zak-Shadow. "Dad is a policeman, and here I see someone with the same clothes as my dad sitting and covering his face because he is afraid of ghosts". "Your father?". "Yes for us". she fell into her bed while eating her palm. Looking at each other between Zak-Shadow and Imran. Imran focused his attention on Nimrah, and cleverly said, "And you didn't talk to him?". "I was afraid of the ghosts, and he covered his face. Do you think he is afraid of them, or is he a policeman?" "Why didn't you tell your mother?". "I told her and she and Inna said I was full of noise. I told them Fatsima and they said I was lying. I followed them and the ghosts ran away." Zak-Shadow bit his lip, his heart was guessing that there must be a hidden issue about this girl's father. They left there and went back to
.....Hannu ya miƙa mata shima yana cigaba da murmushin nasa dai, babu musu ta tafi wajensa. Cikin wayo da dabara ya tambayeta miye fatalwa? Yaushe ta ganta kuma?. Yo har a gayama Nimrah zance, ba'a tambayeta ba ma faɗa take balle wannan harda cin hanci aka bata. Ai tsaf ta shiga bama Zak-Shadow labarin fatalwoyin bayan gida. Koda yace zata kaishi ya gani? Sai ta bashi amsa da, “Ai sun gudu tun ranar, koda na raka su Fatsima ma da sukace zasu gani babu kowa sai dai mun samo jarkoki harda nama”. (Anzo wajen) Cewar Zak-Shadow a zuciya. Dabino ya sake cirowa a aljihu ya bama Nimrah, sannan ya fita da ita su Imran biye da shi ransu fal mamakin al'amarin wannan yarinya. Ranar fa da taimakon ALLAH da wayon nan nata suka gano makamai na ban mamaki a gidan, yau kuma ga wata sabuwar magana da tabbas tunda sukaga oga ya maida hankali akai tana da muhimmanci. Tsaf Nimrah ta dinga nuna musu hanya har cikin gonar nan da taga mutanen ranar da take kira fatalwoyi. A kallon farko kuwa sojojin suka fahimci gaskiyar zancenta. Dan har yanzu akwai alamar mutane sun zauna. Sauran takardun nama da yaran basu ɗauka ba saboda an cinye suna wajen duk da iska ta ɗan ɗaukesu sun matsa, sai kashi a gefe dake nuna alamar na gardawane da kufan fitsari da akayi, ɓawon ƙwai da akaci da sauran sigari da akasha. Nimrah na cin dabinonta ta nuna wani waje tana kallon Zak-Shadow. “Baba ɗan sanda, kuma anan naga wani mai irin kayan Babana zaune shima ya rufe fuskarsa saboda tsoron fatalwoyin”. “Babanki?”. “Eh mana”. ta faɗa cikin shiririta tana cin dabinonta. Kallon kallo akai tsakanin Zak-Shadow da Imran. Imran ya maida hankalinsa kan Nimrah, cike da wayo ya ce, “Shine kuma baki masa magana ba?”. “Ai tsoro naji na fatalwoyin, kuma ya rufe fuska fa, shima kaga ai tsoron su yake ji ko baba ɗan sanda?”. “Miyasa baki faɗama mamanki ba?”. “Na faɗa mata ita da Inna sukace na cika surutu, shine na gayawa su Fatsima sukace ƙarya nake, niko na rakosu harnan fatalwoyin kuma har sun gudu”. Wani irin cije baki Zak-Shadow yayi, zuciyarsa na hasaso masa tabbas akwai ɓoyayyen al'amari akan mahaifin yarinyar nan. Barin wajen sukai suka koma can gidan su Nimrah. A karo na farko Zak-Shadow ya buƙaci zama da Umma dake cikin tashin hankali tunda suka fita da Nimrah, sai dai ganin sun dawo ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere. Dan haka ma koda Zak-Shadow ɗin ya nema suyi magana bata musa ba. Tabarma ta ɗakko ta kawo ƙarƙashin inuwar ceɗiya dake a sashen nata. Dan haka kawai take jin girman mutumin nan a ranta tun randa suka fara haɗuwa shekarun baya. Bai musa ba ya zauna shi da Imran. Ita kuma zata zauna ƙasa yace ta ɗakko wata tabarmar. Ɗaki ta koma ta ɗakko tabarma ta shinfiɗa itama ta zauna. Shiru wajen ya ɗauka kafin ta motsa baki cike da ƙarfin hali ta ce, “Kayi haƙuri da abinda nayi ranar, ban san kuskure bane ba. Wlhy farin ciki ne kawai ya kamani na ganinka saboda tun wancan shekarun da muka haɗu nai maka alƙawarin baka abinda na haifa sai nake yawaita mafarkinku a barci na. Kullum kuma cikin addu'ar ganin ba haifi namijin da zan baka ba nake, amma har yanzu ALLAH bai cika min burina na ba”. Karo na farko Zak-Shadow ya kalleta, kai tsaye ya furta, “Ina abinda kika haifa wancan karon?”. Cikin sauke ajiyar zuciya ta kalla Nimrah dake wasa da ƙasa gefensu kaɗan, “Itace waccan da kuka fita da ita ɗazun”. Daga shi har Imran kallon Nimrah sukai suma. Imran dake murmushi ya ce, “Masha ALLAH, ALLAH ya albarkaci rayuwarta. Minene sunanta?”. “Naja'atu, amma muna kiranta Nimrah saboda sunan mahaifiyar maigidana ce.” Ɗan huci Zak-Shadow yayi kaɗan, ƙasa-ƙasa ya ce, “ALLAH ya rayata”. Sai kuma ya cigaba da faɗin, “Ranar tace miki taga fatalwa a bayan gida, miyasa baki saurareta ba?”. “Nimrah nada surutu sosai, shiyasa nakan ƙwaɓeta da irin waɗan nan abubuwan saboda tarbiyyarta matsayinta na mace”. “Hakan ba laifi bane, amma yana da ƙyau idan yaranmu sukazo mana da maganar abinda ba kasafai ake zancen sa a cikin al'umma ba mu basu lokacinmu, idan na gyara ne mu gyara musu, ko muyi musu ƙarin bayani ta yanda zasu fahimci abin a yanda yake. Idan ba haka ba zasuje su faɗa a inda bai dace su faɗa ɗin ba, maybe ya cutar da su, ko kuma ya zama na cutarwa ga kowa. Yanzu kamar ita zancen fatalwa data kawo miki mutanen da sukai muku ɓarna da ɗibar yaranku ta gani a wannan ranar, da kin saurareta da kin fahimci abinda take magana akai, koda bazaki iya ɗaukar mataki ba zaki iya faɗawa maigari, kinga kin taimaki garinki da al'ummar garin. Saɓanin haka kuma kinga sakamakon daya kawo.” Ba ƙaramin tashi hankalin Umma yay da bayanin Imran ba. Ta zubama Nimrah ido da har yanzu ke wasa hawaye na silalo mata. Imran ya sake katseta da faɗin, “Minene sana'ar mahaifinta?”. “Manomi ne kamar sauran mazan garin, sai sana'ar kifi da yake yi kuma”. “Ɗanye?”. “Eh, harda soyayye, a can yara yake zama, duk zagayen ƙauyukan nan shi kaɗai ne ke wannan sana'ar shiyasa yake samun kuɗi sosai dan wajensa ake zuwa a saya ƙauye-ƙauye dake kusa damu”. “Ƙarfe nawa yake fita da kayan sana'ar tasa?”. “Sai da yamma bayan la'asar. Dan haka yake jimawa bai shigo gida ba sai irin sha biyu haka, wani lokacin kuma baya kaiwa musamman idan Tanimu ƙaninsa na gari, dan yakan amsheshi shi kuma ya dawo gida”. “Shi Tanimun miye sana'arsa?”. “Shima yana noman ne, amma yana fita balaguro cikin birni. Yaro ne mai ƙoƙari sosai, dan kusan cigaban dake yankin ƙauyukan nan namu duk da taimakonsa da tsayawarsa aka samesu.” “Kamar mi da mi?”. “Kamar makarantu, asibiti, wutar lantarki. Shi ne yayta wayar da kammu har muka saka yara a makaranta musamman mata da mukaƙi da farko.” “Idan yaje birni yakan daɗe ne?”. “Baya wuce wata uku yake zuwa gida yay kamar sati biyu ko uku sai ya koma”. “Shida mijinki waye yafi wani kuɗi?”. “To bana ce ba, dan shi samun namiji ba kai tsaye mu muke iya ganewa ba anan. Amma su duka kowa na samu gwargwadon iko, sai dai shi Tanimu mutum ne mai hidima ga ƴan uwansa gaskiya. Shi ko mai gidana in banda mu da Innarsa babu nauyin kowa a kansa”. “A wannan zuwan da Tanimu yayi gida kwanansa nawa a garin?”. “Bai wuce sati ɗaya ba”. “Yana taya maigidanki zama wajen kifinsa kamar yanda ya saba?”. “Eh yana taya shi”. “Kwana huɗu da suka wuce ina maigidanki ya je?”. “Yaje Gangare ɗaurin auren ƴar wani abokinsa”. “Ƙarfe nawa ya dawo?”. “Da daddare ne sosai gaskiya dan har munyi barci ma?”. “Tunda kika aureshi, kin taɓa kama shi da wani laifi?”. “A'a gaskiya, shi mutum ne mai haƙuri da rashin son magana. Tun a rayuwar samartaka ma ban taɓa jin ance ga abokin faɗansa ba. Koni aka ɓatawa rai na tashi da nufin yin faɗa ko ramawa yakan zauna yayta bani haƙuri da hanani.” “Kasancewar sana'ar dare yake yi yana zama a gida tare da ku ya yini?”. “A'a gaskiya, yin haka zai iya zama abin magana mu anan balle gidan yawa, yakan fita kamar kowa amma yana shigowa gida musamman lokacin cin ɗumame da kuma in an gama abincin rana”. “Zamu iya ganin kayan sakawarsa?”. Ɗan shiru tayi a karo na farko ta kasa amsa Imran a wannan karon, sai da Zak-Shadow ya ce, “Karki damu ba wani abu bane”. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke. Kafin ya miƙe ta shiga ɗaki, babu jimawa ta fito da akwatin ƙarfe babba. A gabansu ta ajiye sa, Imran ya ce ta buɗe da kanta. Buɗewar tayi tana fiddo kayan ɗaya bayan ɗaya, gaba ɗayansu basufi kala bakwai ba, duk yadi ne irin na mai ƙaramin ƙarfi. Bayan ta gama gaba ɗaya yace ta maida, ta kawo masu datti suma. Haka ta miƙe ta ɗebo su, suna ɗaure a cikin zaninta, harda nata dana Nimrah. Nashi suka saka ta ware, nata ma haka, sai na Nimrah da sukafi duk nasun yawa. “Zaki iya lissafa min ranakun da duk kuka saka waɗan nan kayan?”. Da yake basu da yawa sai tace zata iya. Da nata ta fara, sai nashi. Ta ɗakko kala na huɗu tai ɗan shiru tana kallon kayan, a karo na farko ta kallesu, sai kuma tai ƙoƙarin ajiye kayan batare da tayi magana ba”. “Miyasa zaki ajiye?”. “Na manta ranar daya saka waɗan nan gaskiya, shiyyasa zan ajiye gefe kozan tuna kafin na gama”. “Ya yi cigaba”. Cigaba da lissafa sauran kala ukun da suka rage tayi. Imran zai yi magana Zak-Shadow ya katsesa ta hanyar yi mata nunin ta ɗauki kayan ta koma da su. Ƙoƙarin kwasa tai harda wanda ya ware ɗin nan yace ta barsu. Haka ta barsu ya kwashe sauran. Tana barin wajen Zak-Shadow yay kiran Nimrah. Da gudu kuwa tazo, ya kama hannunta ya zaunar a kusa da shi, sai kuma ya jawo kayan baban nata gabansu ya ajiye. “Kalla wannan kayan na waye?”. Cikin wasa tace, “Babana”. “Yaushe ya saka su a jikinsa?”. “Na manta”. “Tuna dai, kamar na ranar da kikaga fatalwoyi ne a bayan gida fa”. Kayan ta zubama ido kamar mai son tuno haka. Sai kuma ta kalli Zak-Shadow. “Eh-eh irinsu ne wanda ya rufe fuska ya saka”. “Dami ya rufe fuskar?”. “Bansan sunan abin ba, amma Babana na saka irin shi shima”. “Jeki ɗakko min na gani”. Da gudu ta tashi zuwa ɗakinsu. Umma dake tsaye tana kallon su hankalinta ya fara tashi, zata bi bayan Nimrah Imran ya hanata. Kusan mintuna uku kuwa sai ga Nimrah da hiramin Babanta ta dawo. Karɓa Imran yayi, ya ce, “Kin tabbatar shine wannan?”. Kai ta jinjina musu kawai. Imran ya kalla Zak-Shadow, kai ya jinjina masa. Shima sai ya jinjina nashi yana ɗaukar kayan ya fara bincikar aljihunnan jikin wando da rigar. Ana farko ya ciro kuɗi ƴan ɗari biyar bandir biyu sabbi, ɗayan ya ciro wata takarda ƙarama a nannaɗe. Gaban Zak-Shadow ya ajiye kuɗin, sannan ya warware takardar.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 45_
__________________
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp
07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok
IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________