
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 39
.....of ghosts. They have left the big bags, they told me they will go to Garjalle village..." Umma looked at her for the first time, then she took her head not taking the conversation seriously and said, "So, mother of soki burutsu, will you start complaining about your noises? In the mother's house, a ghost is seen during the day. Get out of here, I don't want to talk." Baki pushed her mouth hard, as if she was going to cry, and said, "I swear I'm Umma. And I even went to their place, and I saw someone with the same clothes..." "GOD, if you don't shut up, I will break your mouth, please get up and go to Inna's place, if I bother you, you will do it." "And she said that her mouth will be broken? After a while, you finished beating her." Baba, who was coming in, said. Hello, Umma greeted him and said, "She told me that she was making noise. It is said that there is a ghost in the window, even in the house of the mother, a ghost can be seen." He laughed, he just shook his head and laughed and said, "Mother king of speech, Zakanyar Kawu Tanimu, as long as it is a conversation, you should be left with what you have." he is recovering.. even Nimrah window, Umma and Baba refused to list
........Hajiya Nimrah kam dai koda ta bar wajen gidan sayen awara ta nufa, koda ta sayo yaran gidansu data samu acan gidan awarar sunzo saye suka janye ra'ayinta suka tafi tare ta cikin gari bata dawo ta bayan gidan ba. Ta samu Umma na murza taliya, dan wannan itace sana'arta. Tuni Bana ya sayo mata wata fulawar ta murza a maimakon wadda Nimrah ta zubar, wannan ma ta wasu ce take murzawa a yanzu. Nimrah ta zauna kusa da ita tana shan majina da buɗe kwanon awararta. “Umma kalla, Baba Zinai ta zubo min da yawa”. Batare da Umma ta kalleta ba ta ce, “Kin gode. Sai ki tashi ki cire wannan majinar da kike faman sha ki wanke hannu sannan kizo kici dan nasan a fitarki kaf tarkacen garin nan sai da kika taɓa”. “To”. Ta faɗa cike da abin arziƙi ta tashi tayi duk yanda Umma tace. Harda ɗebo ruwa a moɗa cikin randarsu. Tazo ta ajiye ta kaiwa zaune. Kamar wadda aka tsikara ta ce, “Umma kinga ko, da zanje ta bayan gida nabi, a gonar Baban Zakiru naga wasu mutane da yawa zaune, idanunsu jajaye kamar na fatalwa. Hadda jakunkuna manya sun ajiye, wai sukace min ƙauyen Garjalle zasu je......” Kallonta Umma tai a karo na farko, sai kuma ta ɗauke kai cikin rashin ɗaukar zancen da muhimmanci ta ce, “To uwar soki burutsu zaki fara baƙin surutun naki ba. A gidan uwarwa ake ganin wata fatalwa da rana. Ɗauki awararki kici bana son magana”. Baki ta tura sosai, kamar zatayi kuka ta ce, “Na rantse da gaske nake Umma. Kuma har wajensu naje ma, har naga wani mai irin kayan......” “ALLAH idan baki min shiru ba sai na fasa maki baki, koki tashi ki wace wajen Inna in damuna zakiyi.” “Mi kuma tayi za'a fasa mata baki? Bayan ɗazu kika gama dukanta”. Baba dake shigowa ya faɗa. Sannu Umma tai masa sannan ta ce, “Ta isheni da surutu ne. Wai taga fatalwa ko a gidan uwarwa ake ganin wata fatalwa”. Shi abin ma dariya ya bashi, ya kaɗa kai kawai yana ƴar dariyar da faɗin, “Uwa sarkin magana, Zakanyar Kawu Tanimu, in dai zance ne a bar miki abinki”. “Baba banyi ƙarya ba fa, kuma harda mai irin kayan......” Murfin kwano da Umma ta jawo ya sakata saurin dafe bakinta dan tasan kaɗan daga aikinta ta kwafɗeta da shi. Shima Baba sai ya shige kawai yana murmurshi.. koda Nimrah taga Umma da Baba sun ƙi sauraren labarinta na fatalwoyi sai ta surare ta koma sashen kakarta Inna. Acan ta fara bata labari, sai dai anyi rashin sa'a itama Inna ta kwaɓeta batare data maida hankali a zancen ba ta ɗauka soki burutsinta ne kawai data saba. Daga ƙarshe ma korota tayi daga sashen akan ta tafi ta bata waje barcin zatayi. Daga haka Nimrah ta fice cikin yara suka kama wasa. Can kamar an tsikareta taba yaran labari suma, abinka da ƙuruciya sukace ƙarya ne, sai ta dage akan suje ta nuna musu. Aiko haka suka haɗa gayya suka fita bada sanin iyayen ba bayan gidan. Tafiya takanas babu ko gargada ta kaisu har wajen mangwaron nan dake cikin gonar Baban Zakiru kamar yanda ta faɗs, sai dai a yanzu babu kowa wajen mutanen sun tashi sai robobin ruwa da suka sha da takardun nama, wata ledar ma ba'a cinye naman ba. Haka sukaita tsincewa suna ci, suka tattaro robobin ruwan dana lemo suka dawo gida. Yawancin iyayen sun gansu da waɗan nan robobin ruwa dana lemo, amma sai basu tambayesu daga ina ba saboda a wasu lokutan kawunsu Tanimu kan raba musu dan su dinga zuba ruwan zuwa makaranta, shima kuma yana zuwa dasu ne daga birni. Da yamma gab da magriba Umma ta gama aikin tuwon dare. Ruwan data ɗumama ta ɗiba taima Nimrah dake ta damunta da surutu tana cin gyaɗa wanka. Ta shafa mata mai ta saka mata kaya. Tuwon Inna data zuba a langa ta saka a botiki ta tura gaban Nimrah ɗin. “Ki ɗauki tuwon Inna kikai mata, sai ki dawo ga miyar nan itama zan saka miki a wannan botikin ki ɗauka ni zan shiga wanka bana son a kira magriba, saura kuma dan ALLAH kiyi abinda ban saki ba, ALLAH bazaki bini gidan Malam ba in har kikai min wata ɓar nan”. “To Umma, ALLAH ba abinda zanyi, dan ALLAH kada kice bazaki je dani ba, ina son na gaida Malam da Iya”. Nimrah ta faɗa cikin tsalle-tsalle tana daukar botiki. Ita kuma Umma ta ɗauki ruwan wankanta ta shige bayi tana faɗin, “In da kinso ganinsu ai ƙafarki tasan inda suke”. Nimrah da bataji mi Umman ta faɗa ba ta ɗauki tuwon Inna ta fita cike da murna zasu gidan Malam, (Malam dai shine mahaifin Umma, babban malami ne a yankin kuma dattijon arziƙi da kowa ke girmamawa) koda Nimrah ta shiga sashen Inna babu kowa, dan dama ita kaɗaice a sashenta tunda kishiyarta ta rasu sai dabbobinta. Ɗaki ta shiga ta ajiye mata kwanon tuwon ta fito, ta sake komawa sashensu ta ɗakko miyar ma ta kawo. Harta juya zata tafi ta hango ƙwayayen kazar Inna dake akurkin jikin katanga gab da fita a sashen. Kwana tayi ta koma wajen akurkin ta duƙunna ta ɗauki ƙwai ɗaya ta saka a botikin hannunta, sai kuma tayi ɗan tsai kamar mai lissafin sauran ƙwayayen, hannu tasa ta ƙara ɗaukar ɗaya, ta ce, “Ni ɗaya Umma ɗaya. To Baba fa, shima bari na ɗaukar masa, idan Inna taji harda shi akaci ai bazata dake shi ba tunda yayi babba sosai.” tana maganar tana leƙa cikin akurkin duba wasu ƙwan. Sai dai maimakon ganin ƙwari taci karo da wata jaka. Hannu tasa ta jawo jakar. Tare da faɗin, “Lah Inna har cikin jaka take ɓoye ƙwai, aiko saina ɗibawa Babana da Kawu”. Tana maganar tana kici-kicin buɗe jakar, sai dai ta kasa. Abinka da yaro tana jiyo maganar Inna ta yayimi jakar ta jefa a botikin ta ɗauka da gudu ta shige bayi, sai da Inna ta shigo ta shiga ɗakinta Nimrah ta fito da gudu nan ma ta fice zuwa sashensu da wannan ƴar jaka da zato ta ke ita ƙwai ne Inna ta ɓoye a ciki. Lokacin da take shigowa sashensu Umma ta shige ɗaki dan anata kiran sallar magriba. Anan tsakar gida ta ajiye botikin da jakar duka ta nufi ɗakin gayama Umma takai wa Innar tuwon. Koda ta faɗa mata sai tace taje tayo alwala suyi salla su tafi. Cikin farin ciki ta fito, dan tasan koba komai zatayi wasa da ruwa ai. Sai da ta gama facaccalinta kuwa sannan ta tafi ɗakin tayi sallar. Ta mance da batun ƙwai taci tuwo suka tafi gidan Malam. Kafin su dawo ta ɓingire barci, sai goyota Umma tayi ma. Sanda Baba ke shigowa gidan ta jima da yin barci. Misalin sha ɗaya na dare Umma da Baba sun gama cin abinci da hira Umma ta fito kaye-kaye tsakar gida sai ga Tanimu ya shigo sashen da sallama. Amsa masa tayi, tana murmurshi da faɗin, “A'a kawun Nimrah baka kwanta ba?”. “Wlhy kuwa ban kwanta ba Yaya, nace bari nazo nai muku sallama dan in sha ALLAHU gobe zan koma birni. Amma sai yamma zan wuce da safe dai zanje hayi wani ɗaurin aure, daga can nake son nabi wasu abokanmu da zasu zo ɗaurin auren suma daga birni.” “Kai kawun Nimrah da wuri haka, wannan karon ai baka daɗe mana ba, kwata-kwata bakafi sati biyu ba”. “Wlhy naso yin sati uku ne fa, to ganin mota a sauƙaƙe yasa zan wuce kawai. Amma bazan jima ba nanda ƙarshen wata zan dawo yin dashen albasar nan.” “Ato da gaskiyarka, ALLAH to ya kaimu. Ka shiga Yayan naka na ciki ai, bari nima na ƙarasa kaye-kaye dan karnuka na shigo mana da dare”. Amsawa yay da to yana shigewa, ita kuma ta cigaba da tattare kayan tsakar gidan. Ciki harda botikin nan da Nimrah ta sakawa jaka a ciki. Batare da Umma ta damu da miye cikinsa ba ta rufe shi da murfinsa dan dama tana kwaɓin fulawar taliya ne a ciki idan zata murza. Ɗaki ta shiga da su ta ajiye, daga haka ta zauna suka cigaba da hira da Baba da Tanimu....
★>>>>>★<<<<<★
Tunda ragamar jejin ta koma hannunsa a daren jiya duk ya kasance a tsarguwa. Ko barcin kirki baiyi ba, dan haka kawai yake jin wani abu mai nauyin gaske a zuciyarsa. Ga yawan faɗuwar gaba dake samunsa. Bafa yau ne karo na farko da Zak-Shadow ke barin jejin shugabanci ya koma hannunsa ba, amma sai yake jin na wannan karon da girma sosai. Wajen misalin ƙarfe uku na dare barci ya gagaresa gaba ɗaya, sai kawai ya tashi. Wayar sadarwa ya ɗauka, yay kira kai tsaye ga dukan Captains dake cikin rundunar, cikin bada umarni ya buƙaci ganinsu. Basu ko ɓata lokaci ba, dan kafin ƙarfe huɗu na asuba sun tattaru a sansanin nasu. Meeting Major Imran yay da su na minti talatin kawai, kafin biyar na asuba ya sallamesu kowa ya nufi komawa sansaninsa....
★A lokacin da Major Imran Abbas ke zaman wannan meeting da Captains ne yaran ƙungiyar duhu suka samu damar kutsa kai cikin wasu sansani kamar yanda suke iso tun farkon dare. Mataki na farko da suka fara amfani da shi shine datse na'urorin sadarwa dake cikin sansani uku. Cikin bazata ƙarfe biyar dai-dai na asuba matasan jaruman sojojin na ƙoƙarin gabatar da al'awalar shiga sallar asubahi, wanda basa sallar na ƙoƙarin amsar duty kawai sukaji saukar harbin kan mai uwa da wabi. Tabbas duk wanda bai zama jami'in tsaro ba bai san minene tashin hankali da ainahin jarumtar mazan ƙwarai ba. Cikin abinda baifi minti biyu ba sojojin nan sun rikiɗe maida raddi, hatta waɗanda suka sami harbi bata ciwon suke ba sam balle zubar jinin da suke yi. Lokacin da Captains ɗinsu suke dawowa wajen ƙarfe biyar da wasu mintina wasa yayi wasa, domin kuwa waje ya hargitse hargitsewa irin ta MAZAJEN FAMA. Cikin tashin hankali Captains ɗin sukai ƙoƙarin kai rahoto ga sauran sansani ta hanyar wayoyin sadarwa, amma abin mamaki duk basa aiki. Makircin masu makirci yayi tasiri kenan bisa ƙaddarar UBANGIJI. Ba wannan bane hari na farko da suka taɓa fuskanta, amma wannan kam ya girgiza hazo sakamakon tsahon shekaru uku kenan babu wani damuwa har suna jin sun gama nasara akan azzalumai, domin kuwa shiri suke na barin jejin a cikin wannan shekarar ganin zaman lafiya ya samu a yankin fiye ma da yanda ake fata..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*